Monday, November 5, 2007

Tarihin Hausawa:

Addinin Gargajiya da Hanyoyin Yada Labarai da Kayan Sawa da Al’adu da Sana’o’i da Muhalli da kuma Tattalin Arzikinsu


Asalin Hausawa abu ne da aka sha kuma ake kan tambaya a kullum, sai dai abin takaici har yanzu ba a sami wata cikakkiyar amsa mai gamsarwa ba. Kafin mu yi nisa ya kamata mu san ko su wane ne Hausawa. Hausawa dai su ne mutane wadanda harshensu shi ne Hausa sannan dukkan al’adunsu na Hausa ne. Haka kuma addinin musulunci ya yi cikakken tasiri a kansu.

Mutane dabam-daban sun yi bincike sosai a kan ilmin harsuna da abubuwan da aka kattaba da kuma zantukan baka. Ta hanyar irin wannan bincike ne aka gane cewa wadansu harsuna suna da kama da juna ainun, wanda ya haifar da kara zurfafa nazarce-nazarce. Sakamakon haka ne kuwa aka karkasa harsunan Afrika ta yadda kowane kaso ya kunshi harsuna wadanda bisa dukan alamu tushensu guda. Ma’ana a asali su wadannan harsuna harshe ne guda daya wanda wasu dalilai irin su bambancin wurin zama, sanadin kaurace-kaurace da yake-yake da dai wadansu dalilai suka sanya ya karkasu ya kasance harsuna iri-iri a halin yanzu.

Akwai dangunan harsuna da dama a cikin Afrika. Misali akwai dangin Bantu a can wajen tsakiyar Afrika wadanda tushensu duka daga wani tsohon harshe ne wai shi Bantu; akwai kuma dangin Kwa wanda ya kunshi Yarabanci da Ibo da Nupanci da dai sauransu. Ita kuwa Hausa tana cikin harsunan iyalin Cadi. Ko da yake shi wannan harshe babu shi a yanzu, wannan suna na Cadi suna ne kawai da masana ilmin harsuna suka kirkiro. Dalili kuwa shi ne yawancin iyalin wannan harshe ana samunsu a farfajiyar tafkin Cadi. To saboda rashin sanin ainihin sunansa sai aka kira shi da sunan Cadi. Harsunan iyalan Cadi suna da yawa. Akwai Angas da Bacama da Bade da Bolanci da Bura da Hausa da Kanakuru da Karekare da Mandara da Margi da Miya da Ngizim da Tera da dai sauransu. A sakamakon kamanni da wadannan harsuna suke yi da juna ya sanya aka danganta su ga tushe guda.

A bisa wannan dan bayani muna iya cewa Hausawa da harshensu sun fito ne daga cibiya daya da sauran harsunan iyalin Cadi. Wannan kuwa zai ba mu damar cewa mutanen da suka zama Hausawa sun fito ne daga Gabas ko arewa maso gabas da wurin da suke a yanzu

Daga nan sai mu duba abubuwan da aka kattaba. A nan an samu mutane dabam-daban sun yi rubuce-rubuce a kan asalin Hausawa da harshensu. A wani littafi da ya wallafa a kan Daular Usmaniyya, Johnston ya bayyana cewa a tsakanin shekarar 1050 zuwa 1100 ta Miladiyya wadansu, Berbers, (Buzaye) sun ratso sahara suka zauna cikin Tukururu kuma suka yi auratayya da su. Wai a sanadin wannan cudanya ne aka sami Hausa da harshen Hausa.

Shi ma wani marubucin dangane da tarihin Hausawa da harshensu, M.G. Smith, yana da ra’ayi kusan iri daya da na Johnston. Wato ya amince da cewa akwai kaura da ta auku daga gabas zuwa kasar Tukururu, wanda ya yi sanadin samuwar Hausawa da harshensu. Ya kare da cewa wannan kaura ta auku ne wajajen shekarar 1350 ta Miladiyya.

Shi kuwa Abdullahi Smith nuna rashin amincewarsa ya yi da wannan bayani da aka yi dangane da asalin Hausawa da harshensu. Musamman ma cewa wai nan da shekara dubu da suka wuce babu Hausawa. Shi yana ganin cewa kasa rarrabewa tsakanin asalin Hausawa da harshensu da kuma asalin daular mulkin da suka kafa shi ne dalilin rashin fahimtar. Haka kuma bai amince ba da cewa Hausawa sun samu a sakamakon auratayya tsakanin Berbers (Buzaye?) da kuma Tukururu da suka taras a wurin. Hasali ma ra’ayinsa ya fi karkata ga cewa Hausa tana da alaka da harsunan iyalin Cadi, har hakan ma kuwa yana ganin cewa sun raba hanya shekaru dubbai da suka wuce.Ya kuma kara da cewa mai yiwuwa da can akwai dangantaka tsakanin harshen Berber da na Cadi, wato tun kafin Sahara ta zamo hamada.

Babu shakka ba abu ne mai karbuwa ba a ce nan da shekaru 950 da suka wuce babu Hausawa da harshensu, musamman idan aka dubi tarihin garuruwan Hausa da jerin sarakunan da suka mulke su. Misali an ce tun karshen karni na 9 na Miladiyya wadansu maharba suka zo suka zauna a duwatsun da ke kewaye da sararin da ake kira Kano yanzu. Idan haka ne wannan ya nuna cewa akwai Hausawa a wannan wuri fiye da shekaru 1,000 da suka wuce.

Addinin Gargajiya na Bahaushe

Adinin gargajiya wata hanya ce ta bautar da mutane dabam-daban kan sama wa kansu. Babu wata kabila da za ta bugi kirji cewa ita ta koya wa wata bauta wa (Ubangiji). Kusan kowace kabila nan take take ta kago hanyoyin bautarta. Wadannan hanyoyin bauta ana ganin sun samu tun farkon samuwar dan’adam. Masu binciken tarihi na ganin cewa makasudin bautar gumaka shi ne ganin cewa wasu abubuwa kamar rana da wata da kogi ko duwatsu suna yi dabi’a irin ta mutum wato in an faranta musu rai su ji dadi in kuma an bakanta musu su yi fushi. Masu bauta wa kogi ana ganin sun yi imani da shi ne saboda ganin cewa wani lokaci sai ya yi ambaliya su sami amfani mai yawa, wani lokaci kuma ya bushe. Daga ya bushe sai masu bautar su dauka cewa sun yi wani laifi ne, sai a sami wani babbansu ya kasance mai yin magana da gunkin, shi kuma zai rika gaya musu sakon gunki. Makasudi na biyu da ake zaton ya sa mutane yin bautar gunki shi ne ta wajen ciwo. Wani lokaci ciwo kan kama mutum a yi ta magani a rasa yadda za a yi ciwon ya warke. To, in aka yi katari wani ya zo ya ba da magani majinyacin ya warke, sai a dauka cewa wannan mutumin yana da wata daraja ta musamman. Saboda haka duk abin da ya faru, shi za a dosa, shi kuma ya rika dangana cuce-cucen da iskoki. Ta nan ne sai mutane su yi imani da iskoki.

Tun da yake za a yi magana ne a kan addinin gargajiya na Bahaushe, ya kamata a dan bayyana wasu misalai na tsafe-tsafen Hausawa a lokacin da suke yin Maguzanci da kuma barbashin tsafe-tsafen har zuwa yau. Amma tun da ba Bahaushe ne kadai yake yin irin wadannan tsafe-tsafe ba, za a bayar da takaitaccen misalin bautar gumaka a wasu kasashen. Misali a kasar Masar suna da nasu gumakan kafin zuwan musulinci, sanannu daga cikin gumakan su ne Ra da Osiris. Ra shi ne gunkin rana shi kuma Osiris shi ne mai kula da kogin Nil, kogin da shi ne kashin bayan rayuwar mutanen Masar. Idan muka matso wajen makwabtanmu za mu ga cewa Ashanti na kasar Ghana su ma suna da sanannen gunkin da suke kira Abosomi. Yarabawa kuma suna da Orisha. Orisha din nan shahararren gunki ne wanda Yarabawa ke wa bauta sosai. A duk lokacin da suka ga wani abu ba ya tafiya daidai, sai manyansu su kai kukansu ga wannan gunki. Daga nan sai a yi yanke-yanken dabbobi don Orisha ya sha jini. Da an ga wani canji sai a dauka cewa Orisha ya yarda. Mutanen Jukun ma suna da nasu gunkin da suke kira Jo. Barebari kuma na da nasu gunkin da suke kira Sanama. Kabilar Tangale da ke Bauchi ma ba a bar su a baya ba wajen bautar gumaka, suna da babban gunkinsu da suke kira Yeku. Ban da babban gunki Yeku akwai kuma kananan gumaka a kowane gida da ake bautawa, haka kuma a kowace unguwa.

Daga wadannan bayanai da aka yi za a fahimci cewa addnin gargajiya ya mamaye kasashe da yawa kafin zuwan addinin Almasihu da na musulunci. Kuma kusan kowane irin addinin gargajiya, sai an sami wani mutum wanda shi ne mai wucewa gaba don nemo bayani daga gunkin sa’annan ya sanar wa da mabiya.

Tun da yake an dan ji bayanan addinan gargaji na wasu mutane, sai kuma mu tsunduma ga na Hausawa. Hausawa ma kamar sauran mutane suna da addininsu na gargajiya tun kafin zuwan addinin musulunci. A gaskiya ba wanda zai ce ga lokacin da Hausawa suka fara bautar gumaka da tsafe-tsafe. Tarihi ya nuna cewa tun da aka halicci dan’adam, bautar iskoki ta cusu a zuciyarsa. Wannan shi ya sa yake da wuya a bayyana tun sa’ad da abin ya fara. Dalilai na biyu da ake jin su suka haifar da addinin gargajiya, ba kuma ga Hausawa kadai ba har ma da sauran jinsi iri-iri na duniya. Dalili na farko shi ne, shi dai dan’adam ya dauka cewa kowane abu a duniya yana dabi’a irin tasa, wato wani lokaci zai ji dadi musamman in an faranta masa rai, ya kuma ji zafi in an bakanta masa, har ya kai ga ramuwar gayya. Alal misali, lokacin da Kanawa ke bautar Tsumburbura a gindin Dala, zamanin Barbushe, duk shekarar da ta zo da wani bala’i sai mutane su dauka cewa lallai an saba wa Tsumburbura. Saboda haka sai a yi yanke-yanken awaki da karnuka don dodon ya sha jini wai ko ya huce. To wasu lokutan kuwa sai a yi sa’a abin ya yi sauki shi ke nan sai a dauka wannan sauki ya faru ne saboda yanke-yanken da aka yi wa gunkin ne.

Dalili na biyu da ake zaton shi ma ya taimaka wajen kago bautar gumaka shi ne ciwo. Sau da yawa akan sami ciwo ya ki ci ya ki cinyewa ga mutum, a yi ta neman magani, amma a banza, sai a dauka ba mai warkar da majinyacin sai dai mutumin da Allah ya yi wa wata daraja ta musamman. Ana nan har a sami wani boka ya nuna cewa iska kaza ce ta taba mutum amma shi zai warkar da shi. Idan aka yi katari sai kuwa mutumin ya warke. Da zarar haka ta faru fa sai mutane su yi imani da wannan iska da boka ya ambata, shi kuma boka kasuwa ta bude ke nan.

Ana yin bauta ta hanyoyi dabam-daban. Wasu sukan sassaka gunkinsu da kansu, su yi wani mutum-mutumi su rika bauta masa. Wasu kuma sukan bauta wa iskokai.

Dangane da bautar gumaka wajen Hausawa, su ba sa sassaka gunki don yi masa bauta, a’a, sai dai bautar iskokai ta hanyar bori. Kanawa suna bautar Tsumburbura a dutsen Dala.

Akwai wasu gumaka makamantan wadannan a wasu wurarae a kasar Hausa. A kasar Katsina, akwai mutanen Kainafara, arnan Birci a kasar Dutsin ma, masu bautar wani gunki mai suna Dan talle. Sunan mai kula da wannan gunki shi ne Sarkin Noma. Kamar Barbushe Sarkin Noma shi ne mai ba da labarin sakon da Dan talle ya yi ga mabiyansa. Su ma mabiyan Dan talle kabilar Kainafara na yin bikinsu ne shekara-shekara kuma suna yin yanke-yake kamar dai mutanen Barbushe.

Akwai kuma wasu maguzawa masu bautar wani gunki mai suna Magiro a dutsen Kwatarkwashi a cikin jihar Sakkwato. Mai kula da tsafin shi ne Magajin Ranau. Shi ma ana yi masa yanke-yanke kamar yadda ake yi wa Tsumburbura sai dai su bakin sa ake yanka masa ko bakar akuya.

Bayan wadannan gumaka kuma, Hausawa Maguzawa kan yi tsafe-tsafe na gida. Misali shi ne, kusan kowane Bamaguje ya ajiye wata halitta wadda ya dauka ita ce kan gidansa. Wasu sukan dauki dabbobi kamar damisa, kura ko zomo ya zama kan gidansu. Duk abin da aka dauka ya zama kan gida to ba hali wani dan gidan ya ci namansa, ko ya kashe shi ko kuma ya cuce shi ko ta wace hanya.

Tasirin Addinin Gargajiya

A halin da ake ciki yanzu, ko da yake mafi yawan Hausawa sun karbi addinin musulunci hannu bibiyu, har ma ta kai fagen da an ambaci sunan Bahaushe sai a kawo addinin musulunci ciki, don ganin cewa Hausa da musulunci sun kusa zama abu daya duk da haka akwai Hausawa wadanda har yanzu tasirin addinin gargajiya bai bar su ba. Sanin kowa ne cewa har yanzu akwai Maguzawa a kasashen Kano da Katsina wadanda ba su daina yin tsafi da bautar gumaka ba. Wadannan Maguzawa har yanzu sukan yi bukukuwa da tsafe-tsafe iri-iri. Ta hanyarsu ne wasu Hausawan musulmi kan nemi taimako wajen dodo don neman biyan bukata. Irin wannan da’awa ta sa na sami wani tsohon Bamaguje a Jammawa ta kasar Dawakin Tofa wanda ake kira Zuga don ya tabbatar min ko Hausawa musulmi sukan nemi taimako a wurinsu, Zuga ya bayya min cewa a matsayinsa na makeri, ya sha karbar ziyarar makera Hausawa kuma musulmi wadanda suke zuwa wajensa don neman taimako kan yadda za su sarrafa wuta. Ya ce yakan fayyace musu fa lallai sai an kauce kuma sun yarda suna kuma bin dukan abin da ya nuna musu na game da tsafi.

Haka kuma na sadu da wani dattijo a wani kauye mai suna Katsardawa ita ma a kasar Dawakin Tofa take. Shi wannan Bamaguje sunansa Girbau kuma gawurtaccen manomi ne, ya bayyana min cewa ya ba mutane da yawa Hausawa kuma musulmi asirin dodo don kawai su tara hatsi da yawa.

Idan muka juyo ta fannin bori (wanda al’ada ce ta Maguzawa masu bin addinin gargajiya), za mu ga cewa har kwanan gobe Hausawa musulmi suna yi kuma duk mai yi ya ba da gaskiya.

Hanyoyin Yada Labarai Na Hausawa

Hanyoyin yada labarai abubuwa ne da suke tattare da kowacce al’umma, kamar yadda Hausawa kan ce ‘tun ran gini tun ran zane’. Hanyar yada labarai hanya ce tsararriya da ake bi domin isar da sako ga daidaiku ko kuma jumlar mutane ba tare da wani tarnaki ba. Babu shakka hanyar yada labarai ta dade a cikin al’umma amma, tun tuni, mun dade a kasar Hausa muna da tsarin isar da sako ta hanyar yekuwa ko shela da sankira yake yi domin fadakarwa ko sanarwa ko kuma nusarwa ga mutane ko ilmantar da su dangane da wani muhimmin abu da ya shafi rayuwarsu. Irin wannan yekuwar (shela) tana daga cikin tushen kafafin yada labarai a kasashen Afrika, musamma ma kasar Hausa.

Kayan Sawar Hausawa
Hausawa a da can ba su da wata sutura da ta zarce warki sai kuma ganye, amma zuwan addinin musulunci kasar Hausa ya canza rayuwarsu ta hanyoyi da dama, misali, ko wajen sutura ma musulunci ya canza tsarin adon Hausawa, zuwan Larabawa da wasu kabilun Masar suka kawo wa Hausawa suturu masu rufe al’aura, kamar su riga ’yar Tambutu da jabba da Kaftani da Kubta da wanduna iri-iri da hular dara. Aka kuma tanadar wa mata zane (gyauto) da mayafi (gyale) da dankwali da riga. Saboda samun irin wadannan suturu su ma Hausawa suka kago irin nasu suturun don maza da mata kamar ’yar-shara da taguwa da aganiya da fatari da bante. Wasu sun ce bante Hausawa sun aro shi daga wajen Nufawa ne.

Ire-iren Suturun Da Hausawa Suke Amfani Da Su
Luru, Gwado-babbar kwarya da karamar kwarya
Babbar riga da ’yar ciki-gari
Shakwara da jamfa da wando
Doguwar riga

Launukan Babbar Riga
Gari da Sace da Shakwara da Aganiya- akwai wadanda ake yi musu ado a ba su wasu sunaye:
Kamar Aska tara mai cibiya da Aska takwas malummalun da Aska biyu mai wau da Girke da Girken Zazzau da Girken Nufe da Sace mai adda da Sace mai gafiya.
’Yar Tambutu da Doguwar riga da Fanjama da Hartin da Jallabiyya da Zuleka da Kaftani
’Yar ciki dahariya da ’Yar shara da Zuhuni da kuma Falmaran

Wanduna
Tsala da Fanyama da Bulus da Dan itori da Dantunis mai kamun kafa da kuma Kwarjalle.

Huluna
Dankwara da Bakwala da Damanga da Habar kada da Facima da Zanna da Kube da kuma Zita

Rawani
Harasa da Bakin fara da Dankura da kuma Mubarrashi

Takalma
Dangarafai da Sambatsai da Fade da Mai gashin jimina da Dan Maroko da kuma Huffi.

Zanin Mata
Saki da Bunu da Bakurde da Gam Sarki da Tsamiya da Dantofi da Fatari da Saro da kuma Mukuru

Sana’o’in Hausawa
Kasuwaci da Fatauci da Saka da Rini da Farauta da Jima da Noma da Kiwo da Kira da Sassaka da Dukanci da Gini da Fawa da kuma Wanzanci.

Muhalli
Bukka da Tsangaya da Dakin Hayi da Shigifa ko Soro da Kudandan ko Rudu da kuma Kago.

Al’adun Hausawa
Hausawa mutane ne musu tsananin rikon al’adunsu na gargajiya, musamman wajen tufafi da abinci da al’amuran da suka shafi aure ko haihuwa ko mutuwa da sha’aninmu’amala tsakanin dangi da abokai da shugabanni da sauransu, da kuma al’amuran sana’a ko kasuwanci ko neman ilmi.

Tun daga zuwan Turawa har yau, Hausawa suna cikin al’ummomin da ba su saki tufafinsu na gargajiya sun ari na baki ba. Galibin adon namiji a Hausa ba ya wuce riga gari da wando musamman tsala, da takalmi fade ko kafa-cik, da hula kube, ko dankwara, ko dara. In kuma saraki ne ko malami ko dattijo, yakan sa rawani. Adon mata kuwa, zane ne da gyauton yafawa, wato gyale da kallabi da taguwa da ’yan kunne da duwatsen wuya wato tsakiya.

Yawancin abincin Hausawa kuwa, ana yin sa da gero ko dawa ne. Sai kuma sauran abubuwan hadawa, da na marmari, kamar su wake da shinkafa da alkama da kayan rafi da sauransu.

Yawancin Hausawa Musulmi ne saboda haka yawancin al’adunsu da suka shafi aure da haihuwa da mutuwa duk sun ta’allaka ne da wannan addni, sai dan abin da ba a rasawa na daga al’adun gargajiya musamman a wajen Maguzawa.

Haka kuma wajen mu’amala da iyaye ko dangi ko abokai ko shugabanni ko makwabta ko wanin wadannan, yawanci na Musulunci ne. Haka nan sha’anin sana’a da kasuwanci da neman ilmi duk a jikin Musulunci suka rataya..

Da can, sana’a da kusuwanci da neman ilmi suna bin gado ne, wato kowa yana bin wadda ya gada kaka da kakanni. Kuma idan mai sana’a ya shiga bakon gari zai je ya sauka a gidan abokan sana’arsa ne. In ma koyo ya zo yi, zai je gidan masu sana’ar gidansu ne. Saboda haka kusan kowace sana’a akwai sarkinta da makadanta da mawakanta, kai har ma da wasu al’adu na musa yinta da suka sha bamban da na sauran jama’a.

Tattalin Arzikin Hausawa
Kalmar tattali tana nufin kula ko ririta ko tanadi da kula ko adana wani abu, wato tsiminsa. Ita kuwa kalmar arziki a nan tana nufin tajirci ko dukiya ko samu ko hali ko gafi ko kudi ko sukuni ko daula ko wadata ko abin hannu wato mllakar dukiya mai yawa fiye da sauran abubuwan bukata.

Daga wadannan bayanai za a ga, a ma’ana ta gama-gari, tattalin arziki yana nufin kula da dukiya. A fagen nazari kuwa, tsari ne na sarrafa al’barkatun kasa da sauran ni’imomin da Allah ya yi wa mutum, yadda za a samar da muhimman abubuwa da dan’adam yake bukata a kuma sarrafa su ga jama’a.

Dangane da haka, dan’adam tilas ne ya yi aiki ya sarrafa wasu abubuwa don ya kai ga biyan wadannan bukatu, amma kuma mutum bai iya wadatar da kansa da dukkan bukatunsa, don haka dole ya dogara da ’yan’uwansa wajen samun wadannan abubuwa, kamar yadda su ma suka dogara da shi.

Tattalin arzikin Hausawa na gargajiya abu ne kara zube inda ake barin abubuwa kara zube, ma’ana kowa yana ba da gudummawa gwargwadon karfinsa kuma yana samun abubuwa gwargwadon irin sana’arsa da kwazonsa da kuma sa’arsa. Ita kuma hukuma ta sa ido don tsaron mutunci da dukiyar al’aumma.

Sana’o’i su ne mafi girman tafarkin da Hausawa suke bi don samar da abubuwan bukata. Ta hanyar sana’o’i suke sarrafa albarkatun kasa da sauran ni’imomin kuma rarar da suka samu suke musanyawa su mallaki abubuwan da ba za su iya samar wa kansu ba. A takaice dai sana’o’i su ne kashin bayan tattalin arzikin Hausawa na gargajiya wadanda suka hada da noma da kira da wanzanci da fawa da saka da jima da dukanci da sassaka da rini da dillanci da bokanci da dibbu da dinki da magori da tuggu da kwarami da banbadanci da kuma koli da dai sauran su.

Daga cikin wadannan sana’o’i noma shi gidan kowa da shi, a gargajiyance duk Bahaushe manomi ne amma kuma yakan kara da wata sana’ar don tallafawa. Dangane da haka ne ake karkasa mazauna gari bisa tsarin sana’o’in kowane gida ko unguwa, don haka ne ma a Kano aka sami unguwannin Makera da Dukawa da Mahauta da unguwar gini da makamantansu.

Manazarta

Adamu, Muhammad Tahar; 1997: Asalin Hausawa Da Harshensu. Kano: Dan Sarkin
Kura Publishers Ltd.

Alhassan, Habibu da Musa, Usman Ibrahim da Zarruk, Rabi’u Mohammed; 1982. Zaman
Hausawa, Bugu na Biyu: Lagos:Islamic Publications Bureau.

Adamu, Muhammad Tahar; 1997: Asalin Magungunan Hausawa Da Ire-ire-iresu. Kano:
Dan Sarkin Kura Publishers Ltd.

Dawaki, Alahassan Muhammad; 1983. Tasirin Addinin Gargajiya Kan Hausawa:
Takardar da Aka Gabatar a Taron Malamai da Dalibai na Jami’ar Bayero, Kano,
Sashen Harsunan Nijeriya.

Gidan Dabino, A.A.; 2001. Gudummawar Finafinan Hausa Game da Addini da
Al’ada: An gabatar da Wannan takarda a Bikin Makon Hausa na 23 Wanda
Kungiyar Hausa ta Jami’ar Bayero ta shirya, a Tsakanin 5 zuwa 8/1/2001.

Gusau, Sa’idu Muhammad; 1982.Wasanni Don Yara. Kano:
Jola-Ade Printers.

Gidan Dabino, A.A.; 2003. Ta Leko ta Koma: Mujallun Hausa Ina Mafita: An gabatar da Wannan Takarda a Taron Shekara-shekara na Mujallar Ar-Risala, a Harabar Makarantar Farhan, Kabuga Jan Bulo, Kano.

Magaji, Ahamad; 1986. Gudummawa a Kan Kokarin da Ake yi na Samar da Cikakken
Tarihin Hausawa: Takardar da Aka Gabatar a Taron Malamai da Dalibai na
Jami’ar Bayero, Kano, Sashen Harsunan Nijeriya.

Nazari A Kan Harshe Da Adabi Da Al’adun Hausawa Na Farko.1978: Kano: Uniprinters
Ltd.

Nazari A Kan Harshe Da Adabi Da Al’adun Hausawa Na Uku.1993: Zariya: Gaskiya
Coporation Ltd.

Nazari A Kan Harshe Da Adabi Da Al’adun Hausawa Na Biyar. 2002: Kano: Benchmark
Publishers Ltd.

Yahaya, Ibrahim Yaro da Zariya, Mu’azu Sani da Gusau, Sa’idu .Muhammad;
1992. Darussan Hausa 1,2,3, Don Makarantun Sakandare. Ibadan: University Press,
PLC.

Tuesday, June 26, 2007

Nishadin Matan Kulle: Tsokaci a Kan Wasannin Cikin Gidan Sarkin Kano

Nasiru Wada Khalil da Sadiya Ado Bayero


An Gabatar Da Wannan Takarda a Babban Taron Kara wa Juna Ilmi Na Shida Kan Harshe Da Adabi Da Al’adun Hausa Wanda Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayero, Kano ta shirya a Ranakun 12 Zuwa 15 Ga Watan Disamba, 2004.


Gabatarwa:
Kowace Al'umma tana da tsarinta na zamantakewar rayuwa, wanda wannan tsari shi za a kira al'dar wannan al'umma. Misali al'adar Turawa, al'adar Fulani, al'adar Larabawa, ko Hausa Fulani a wannna zamani da muke ciki. Shima Bahaushe yana da al'adu da dama kamar na abinci da sutura da aure da farauta da nishadi da sauransu, yawancin wadanda suke aro su ya y daga al'adar makwafta da wadanda addinin musulunci ya kawo masa. Duk da haka al'adun sun dan banbanta a tsakanin Hausawa mazauna wurare daban daban, misali Bahaushen Sokoto al'adarsa ta bambanta da ta Bahaushen Katsina ko Daura, suma al'adun sun banbanta da al'adar Hadejawa ko Kanawa (mutanen Hadeja ko Kano).

A nan za mu dauki Bahaushen Kano a tsakanin sauran Hausawa sudanin Shehu Danfodiyo, za mu dauki nishadantarwa daga ciki sauran al'adunsa mu haska da madubi mu kalli yadda mata (daga ciki jinsin mutane) na kulle na gidan sarauta (daga cikin dangogin ayyuka) don yin tsokaci akan hikimomi da dabaru da Salo, da yanayin yadda harkar nishadantarwa take a wanna gida Zamanin da da na yanzu mu kuma yi nazari akan banbancin Nishadin da da na yanzu; ci gaba ko sauyi aka samu tsakanin nishadin da ake yi da a gidan Sarki da na yanzu?

Wannan mukala an yi ta ne domin a samu a mayar da wannan adabi na baka zuwa cikin rubutu, don amfanin 'yan baya da manazarta al'ada, musamman a wannan lokaci da tsohuwar al'adar Bahaushe take bata yau da gobe. Har ila yau an yi wanna mukala ne domin a bayyan hikimomi da fasaha da sigogin da matan kulle suke da su don jin dadin rayuwar su ta yau da kullum kamar sauran mata da suke a wajen kulle.

Ma'anar Muhimman Kalmomi
Nishadi: Yana nufin duk wani abu da aka yi don dadadawa rai.

Matan Kulle: A nan muna nufin bayi mata da musulunci ya yardarwa ubangijinsu ya take su, su haihu wadanda aka killacesu a gida basa fita ko'ina. A cewar Nast (2003) matan kulle "matan da ba auren mutum suke ba amma zai iya amfani da su don harkokin gida da samun haihuwa."

Gidan Sarautar Kano:
Gidan Sarautar Kano za a kira shi gda saboda akwai mai shi da iyalinsa zaune, kuma a iya kiran sa Unguwa, saboda yawan gidajen da suke ciki da jama'u sannan a iya kiran sa gari saboda ya tara abubuwan da gari yake tarawa kamar; unguwanni da Asibiti da Makaranta da Mahukunta da Doka, kai har ma da yare (salon magana) dalilin haka wasu ma sukan ce duniyar gidan sarki saboda kabilu na mutane daban-daban da suka hadu a ciki.

Nishadin Matan Bahaushe
Matan Bahaushe manyansu da yaransu masu aure ko 'yan mata suna da son nishadi kusan a komai na ayyukan rayuwarsu ko sana'a, domin su sami annashuwa a cikin wannan abin da suke yi, misali idan matar Bahaushe tana nika za ta rinka bin nikan nan da waka domin ta debewa kanta kewar wahalar wannan nikan, wakar nan za ta iya zama ta gargadi ko wa'azi ko kuma raha, kowacce dai ta yi za ta sami jin dadi da nishadi yadda saukin wannan nikan zai rayu a gare ta.

Haka nan a lokacin saka ta 'akwasa' nan na suna jefa akwasar suna waka, a haka sai su yi saka mai tarin yawa ba tare da sun ji wahalar komai ba.

Har ila yau, matan Hausawa suna kadi (mayar da auduga zuwa zaren saka ko dinki) a nan mata za ka ga suna kadin suna waka a gidajensu, haka zalika yaran mata "'yan mata" akan tara musu kada mai yawa su yi wada "didi".

Lokacin rarrashin yaro nan ma za ka ga mata na yi wa yaro rawa sun yin kida da hannunsu a bayansa, suna yi masa wasa suna rarrashin sa tare da nishadantar da shi, da su kansu, shi ne za ka ga yaro yana kuka ya dawo yana dariya bayan ya yi shiru daga barin kukan.

Gada, kamar yadda kowa ya sani; "rawa da waka ce da 'yan mata ke yi ta da yamma ko da daddare" ya danganta da gari-gari. Baya ga haka kawaye suna yin ta lokacin bikin "yan matancin Amarya", ma'ana idan ana auren kawarsu.

Ana daka ana waka ne dai ba a san Bahaushe da haka ba sai Fulani, su Hausawa Lugude aka sansu da shi, da sauran ire-iren ayyuka na Bahaushe babu inda ba ya nishadi sai a inda ya san idan yayi zai iya gamuwa da wahala ko laifi kamar tu}in tuwo ko sallah da sauransu.

Nishadin Matan Kulle Na Gidan Sarki
Baya ga wadannan nau'i na nishadi da ake samun su a ko'ina har a gidan sarauta, akwai kuma wadanda kwara-warai ne kawai suke yi a gidan sarki, wadannan sun hada da wasan gauta, kidan ruwa da warar guje, kidan sakaina da kuma tashe.

Wasan Gauta
Wannan wasa ne da sai kwara-warai ne kawai suke yin sa a gidan Sarki wanda aka fara shi tun kafin Musulunci ya kafu a kasar Hausa, kamar yadda Suwaid Muhammad ya fada ko da yake Alkali Usaini Sufi ya musanta hakan inda yake cewa "An ce an fara wannan wasa ne tun cikin yakin duniya na biyu, yakin da aka fi sani da yakin Hitila. Bayan an yi ne sau daya, sai aka dakata ba sake yi ba sai da aka gama yakin sannan aka ci gaba da shi......."

Shi dai wasan Gauta yadda ake yin sa shi ne kamar yadda Sufi (1993( ya kawo:

Shi wannan wasa ana yin sa ne a cikin wata Sallah Babba a lokacin kaka, lokacin da ake cin moriyar amfanin gona da aka samu a wannan shekarar, irin su gujjiya da gyada da rake da takanda da gauta ko data da yalo da dai sauransu. Wannnan wasa na kwaikwayo ne, wanda yake nuna yadda ake tafiyar da mulki irin na gargajiya da kuma yadda ake tafiyar da aikin hukuma na yau da kullum. Ta wani bangare kuma yana nuna cewa ata ma idan da za a ba su dama za su iya yin abubuwan da maza suke yi, domin a tsari nan na wasan Gauta akwai Sarakunan Yanka da Hakimai da Alkalai da "Yan doka da Wakilin doka, har ma da Yari mai kurkukunn tsarewa. Waje daya kuma ga asibiti har da Sitta mai bayar da magani tare da ma'aikatanta wadanda ake cewa da su 'yan diresin."

Daga wannan wasafcin na yadda ake wasan gauta da Alkali Usman Sufi ya yi, za mu ga cewar wasan ana yinsa ne lokacin Turawan mulkin mallaka, amma wasan Gauta ya sami canjin suna ya koma Wasan Gwamna. Saboda Turawan mulkin mallaka sun ga cewar wasan Gauta hanya ce ta fadakar da Jama'a.

Haka ya nuna cewar tun kafin zuwan Turawa aka fara wasan gauta. To amma kuma wane lokaci aka fara wannan wasa shi ne babu tabbas a kai, an daina shi ne a shekarar 1953 lokacin da Sarkin Kano Muhammadu Sunusi ya hau gadon karagar mulkin Kano, a cewar "Matar Daga."

An daina wannan wasa ne, saboda a wannan lokacin NEPU ta fara karfi, saboda haka akwai yiwuwar 'yan NEPU su yiwo shiga a matsayin matan maroka ko matan bayin sarki da suke waje su shigo gidan sarki. A wani bangaren kuma Matar Fada Fagi cewa tayi "An daina ne saboda kwarkwaran Sarki Sunusi ba su da yawa, ba za su isa yin wasan gauta ba kamar yadda aka saba.

Alkali Usaini Sufi (203-205) ya kawo sunayen wasu daga cikin masu wasan gauta da mukaminsu kamar haka:
SUNA LAKABI MUKAMI
Binta Yartsakuwa Sarkin Musulmi
Hasiya Asabe Sarkin Kano
Kayi Kayi Sarkin Katsina
Gaji Malama Sarkin Gobir
Dije Haji Galadiman Kano
Binta Rano Ciroman Kano
Hassana 'Yan Biyu Ciroman Kano
Gadan Gadan Makaman Kano
Jabu Jabu Wazirin Kano
Bilki Maigashi Dan Iyan Kano
Aishatu Iyantumi Tafidan Kano
Rabi Hajiya Ma'aji Walin Kano
Hamamatu Hauwa Magajin Malam/S/Shanu
Daso Tababa Makaman Kano
Rabi Jahun Sarkin Rano
Kubura Malama Alkalin Kano
Rabi 'Yarwawu Marusan Katsina
Aishatu Mai sunan Umma Wakilin Doka
Hauwa Dan Kulu Sitta
Kankani Kankani Yarin Kano
Fagi Yatafada Magajiyar Karuwai

Hikimar Yin Wasan Gauta
Babbar Hikimar yin wasan Gauta bayan nishadi shi ne, a janyo hankalin sarki a kan abubuwan kasarsa, halayya da dabi'un 'yan majalisarsa irin su Waziri da Madaki da Galadima da sai sauransu, wasu suna ganin gauta a matsayin wata dama da ake nusar da Sarki shi kansa irin matsalolinsa ko rauni don yi gyara.

Kidan Ruwa Da Rawar Guje
Shi kidan ruwa yadda ake yi kidan shi ne a sami masakai manya-manya a cika su da ruwa sai a kifa wata kwaryar a cikin ruwa, a sa abin kida ana kida, su kuma kwarakwarai kowace ta sha kitso Doka (za mu yi bayani sa a sakin layi na gaba) su yi da'ira suna rawa suna juyi, sai daya ta fito da sauri zuwa gaban makidiyar ta yi rawa, sai ta koma wata ta goya (ta shiga bayanta) daki-daki har sai an kewayo kan kowa. Shi wannan kidan ruwa da rawar guje ana yin su lokacin bikin sallah ko bikin 'ya'yan sarki.

Rawar Sakaina
Kowacce kwarkwara bayan an koya mata yadda ke rawar kidan ruwa sai ta taho wajen kidan sakaina ta ci gaba da koyo, sabanin kidan ruwa da 'yan soro rawa kawai za su yi, a kidan sakaina su za su yi kidan su, kuma su yi rawarsu.

Yadda ake yin rawar sakaina shi ne a samu sakaina ana kadada zabiya tana ba da waka ana amasawa ana rawa mutum daya-daya ko mutum biyu-biyu kamar rawar kureda ko rawa oba ko rawar a yi yamma, a wannan rawar mutum hudu ne suke yi ko shida a cikin fili suna maye juna wasu na shigowa wasu na ficewa.

A kidan sakaina ba wai kidan ko wakar ce mai ban sha'awa kamar rawar ba saboda irin hikima da kimiyyar da take cikin rawar, kuma ita ce ginshikin nishadin da ke ciki, shi yasa idan kwarkwara ba ta iya taka rawar ba, manyan kwara-kwaran in suna takawa sai su bude wacce bata iya ba da kasa komai fari ko tsadar zanin da ta daura.

I. Ayyaraye yurare

Ayaranye yuraye da wuya
‘Yan amshi: Ayaraye yuraye shawara da wuya
Ayyaraye iye shawara tsoro
‘Yan amshi: Ayaraye yuraye shawara da wuya
Ayyaraye duk mai shawara ba zai yaki ba
‘Yan amshi:Ayyaraye duk mai shawara ba zai yaki ba
Ba ya gudu ba ya ja da baya sai ya kama
‘Yan amshi: Baya gudu ba ya ja da baya sai ya kama
Ayyaraye mu sarkin mu Auwalin Allah ne
‘Yan amshi: Ayyaraye mu sarkin mu Auwalin Allah ne
Ayyaraye mu sarki mu Alhajin Allah ne
‘Yan amshi: Ayyaraye mu sarki mu Alhaji Allah ne
Ba ya gudu ba ya ja da baya sai ya kama
‘Yan amshi: Ba ya gudu ba ya ja da baya sai ya kama

II. Iya ranaye dede
Iya ranaye dede iyararaye
‘Yan amshi: Iya ranaye dede iyararaye
Ta ina ta haura
‘Yan amshi: ta shamakin dawakai
Ta sararin garke
‘Yan amshi: ta shamakin dawakai
Kaya kaya na keji a shamakin dawakai
‘Yan amshi: iyararaye dede iyaranaye
Ba ku amshi 'yan yara baku tafi
‘Yan amshi: Iya ranaye dede iya ranaye
Ba ku tafi 'yan yara ba ku amshi
‘Yan amshi: Iya ranaye dede iya ranaye

III. Ngalle Ngalle Ngalle
Ngalle Ngalle Ngalle
’Yan amshi: doki da rawa
Ku tafa
‘Yan amshi: doki da rawa
Ku juya
‘Yan amshi: doki da rawa
Ku amsa
‘Yan amshi: doki da rawa
Ba ga shi ba
‘Yan amshi: doki da rawa
Har na iya
‘Yan amshi: doki da rawa
'Yar mama
‘Yan amshi: doki da rawa
Ingalle le ingalle ingalle
‘Yan amshi: doki da rawa
Ku taka
‘Yan amshi: doki da rawa
Ku juya
‘Yan amshi: doki da rawa
Ba ga shi, ba
‘Yan amshi: doki da rawa
Har kun iya
‘Yan amshi: doki da rawa

IV. Ku Reda
Ayyaraye garin bara na yi dare
‘Yan amshi: ayyaraye garin bara na yi dare
Ayyaraye garin bara na yi tuwo
‘Yan amshi: ayyaraye garin bara na yi tuwo
Ayyaraye garin bara na yi fura
‘Yan amshi: ayyaraye garin bara na yi fura
Ku reda, kwarin duma ku rede mu reda
‘Yan amshi: Ku reda, Kwarin duma ku reda mu reda
kwarin duma mu reda, ku reda, mu reda.

V. Badagaraje
Badagaraje badagaraje
‘Yan amshi: Badagaraje badagaraje
Aye bada garaje yaro bada garaje kanyi raha ba.
‘Yan amshi: Badagaraje badagaraje
Da rarrashi da ban Magana
‘Yan amshi: Badagaraje badagaraje
Da kwaryar goro kanyi raha
‘Yan amshi: badagaraje badagaraje
badagaraje badagaraje
‘Yan amshi: badagaraje badagaraje
badagaraje yaro badagaraje
‘Yan amshi: badagaraje badagaraje
Kan yi raha ba.
‘Yan amshi: badagaraje badagaraje

VI. Alo lale lale
Ayyuriri a haiye alo manya
‘Yan amshi: alo lale lale
Mu sarkin mu ya tafi rangadi
‘Yan amshi: Alo lale lale
Allah kai shi Allah ya dawo shi
‘Yan amshi: alo lale lale
Ko da tuntube ko da sartse alo lale lale
‘Yan amshi: alo lale lale
Ko da 'yar kaya bai tako ba
‘Yan amshi: alo lale lale
Ayye iyara iye
‘Yan amshi: ayye iyara iye
Ayye indiro ba diro
‘Yan amshi: ayye indiro ba diro
Auririn ahaiye nanaye
‘Yan amshi: alo lale lale
Dan Allah ku sa mana 'yar guda
‘Yan amshi: alo lale lale

VII. Aya Aya Aya mai nono
Aya Aya Aya mai nono
‘Yan amshi: Haba ayalle
Aya biyar ta cika taiki
‘Yan amshi: Haba ayalle
ta goma rakumi ka dauka
‘Yan amshi: Haba ayalle
In kin ]iga ba kya tashi ba ne?
‘Yan amshi: Haba ayyalle
Ki hankali da baba a zaure
‘Yan amshi: Haba ayalle
Ki hankali da babbar tusa
‘Yan amshi: Haba ayalle
[ugus ta ]iga ta tashi
‘Yan amshi: Haba ayalle
Kanto mai dan boto
‘Yan amshi: Haba ayalle

VIII. Lallewa
Aye lalle waye, lallewa, aye lalle waye, lallewa
‘Yan amshi: Aye lalle waye, lallewa, aye lalle waya, lallewa
Kimba magani banga masoro ba
‘Yan amshi: shan yaji
na gano galadiman ki niba
‘Yan amshi: shan yaji
Ana daka ana zubga masoro
‘Yan amshi: shan yaji
Allah ya tsinewa buzu Albarka bani Kashi da bulala
‘Yan amshi: Aye lalle waye, lallewa, aye lalle waye, lallewa
Allah ya tsinewa buzu Albarka buzu mai taguwa mai mashi
‘Yan amshi: Aye lalle waye, lallewa, aye lalle waye, lallewa
Aye lalle waye, lallewa, aye lalle waye, lallewa
‘Yan amshi: Aye lalle waye, lallewa, aye lalle waye, lallewa

IX. Ga Danda
Aye ga danda ga danda
‘Yan amshi: Aye ga danda ga danda
Aye ga danda dokin kara
‘Yan amshi: Aye ga danda dokin kara
Doki na kora na zai gudu ba
‘Yan amshi: ga danda ga danda
Ko ya yi ma iska ya samu
‘Yan amshi: ga danda ga danda
Aye ga danda dokin kara
‘Yan amshi: Aye ga danda dokin
Ku bamu wuri mu sukwani danda
‘Yan amshi: Aye ga danda ga danda
Ga danda ga danda
‘Yan amshi: ga danda ga danda
Doki nakara ba zai gudu ba
‘Yan amshi: Aye ga danda a sukwane
Ga danga ga danda
‘Yan amshi: Aye ga danda dokin kara
Ga danda ga danada
‘Yan amshi: Aye ga danda dokin kara

X. Kigo mai yawan rabo
Amale amale kigo mai yawan rabo
‘Yan amshi: amale amale kigo mai yawan rabo
Kigo ka fi waiwaye amashi
‘Yan amshi: amale amale kigo mai yawan rabo
Kigo ka fi ma gamu
‘Yan amshi: amale amale kigo mai yawan rabo
Amale kafi mu gamu
‘Yan amshi: amale amale kigo mia yawan rabo
Tsara ta san tsara
‘Yan amshi: amale amale kigo mai yawan rabo
Kigo ka fi waiwaye
‘Yan amshi: Amale amale kigo mai yawan rabo
Mu sarkinmu ya ishe mu Ba za mu ko ina ba
‘Yan amshi: Amale amale kigo mai yawan rabo
Mu sarkin mu mai dubun doki mai amawali
‘Yan amshi: Amale amale kigo mai yawan rabo
Daga Daura nazo Kano lokacin ka na da dadi
‘Yan amshi: Amale amale kigo mai yawan rabo
Labarin ka na jiyo haka nan na tadda kai
‘Yan amshi: Amale amale kigo mai yawan rabo
Gara da nazo gara dana zo
‘Yan amshi: Gara da nazo gara da na zo
Gara da na zo na rarrabe
‘Yan amshi: Gara da na zo na rarrabe
dan duma duma da kabewa
‘Yan amshi: Haka na rarrabe
ga randa rana daka tulu ne ya kai ya kawo
‘Yan amshi: Amale amale kigo mai yawan rabo
Kigo mai yawan rabo
‘Yan amshi: Amale amale kigo mai yawan rabo
Amale kafi ma gamu
‘Yan amshi: Amale amale kigo mai yawan rabo
Baba Uban shamki, kowa sai ya durkusa
‘Yan amshi: Amale amale kigo mai yawan rabo
Baba uban maza da mata kowa sai ya durkusa
‘Yan amshi: Amale amale kigo mai yawan rabo
Amale Amale kigo mai yawan rabo
‘Yan amshi: Amale amale kigo mai yawan rabo
Masaki yafi ragaya, Goma ta wuce biyar
‘Yan amshi: Amale amale kigo mai yawan rabo
Idan riga ta wuya sai ba a zo wajenka ba
‘Yan amshi: Amale amale kigo mai yawan rabo
Idan wando yana wuya sai ba a zo wajenka ba
‘Yan amshi: Amale amale kigo mai yawan rabo
Idan hula tana wuya sai ba a zo wajenka ba
‘Yan amshi: Amale amale kigo mai yawan rabo
Mai Daura mai Kano, mai Jama'are mai Kazaure
‘Yan amshi: Amale amale kigo mai yawan rabo

Tashe
Tashe kamar yadda kowa ya sani al'adace da ake yin ta a lokacin watan azumin du gari, kuma kamar yadda aka sani a kasar Hausa cewa yara ne da maza manya suke yi, to amma a gidan Sarki mata ne manya suke haduwa su yi wa Sarki, kwara-warai da jadadu da sauransu.

Duk wadannan wasanni da kwarkwarai suke yi baya ga nishadantar da kansu da suke yi suna nishadantar da ubangijinsu, sannan kuma hanya ce ta samun ku]in shiga a wurinsu, don komai suka yi sai ubangijinsu ya biya su.

Nishadin Matan Kulle A Yau
Kamar yadda rayuwa da al'adar Bahaushe take samun canji haka zalika wadannan al'adu da matan kulle (Sadaku) suek canzewa, yanzu shekaru hamsin da daya (51) ke nan da daina wasan gauta kamar yadda muka fada a baya.

Samun hanyoyin nishadi na yau da kullum da ake yin su kamar su Gada duk sai bacewa suke yi, ana maye gurbinsu da abubuwan da zamani ya zo da su kamar su Ludo da "yar carafke da sauransu, bayan su talabijin ta fito, ita ma ta zama wata hanyar nishadantarwa, musamman zuwan satilayit, akwai tashoshin Indiya "Sony Channel" wasaninsu irin su: - Kusum da Kone Dilmile da Ayusha da Humbocane da Bedi da Jesi Jesi, da sauransu, sun zama hanyoyin nishadantar da 'yan soro ta yau da kullum haka zalika Kagaggun labarai na "adabin kasuwar Kano", finafinan Ibro da kuma wasannin Hausa na talabijin da na Bidiyo.

Bambancin Nishadin Da Da Na Yanzu

Da Yanzu
Ana nishadantar da kai a kuma Ya fi yawa ga nishadantar da kai
nishadantar da ubangiji

Akwai neman kudi Nishadin ne kawai ba wani neman kudi a ciki

Ana kulla alaka Babu kulla alaka da zumunci
Da al'adar Bahaushe zalla ake Har bakin al'adu na nishadantarwa
Nishadantuwa ana amfani da su kamar turanci da Indiya da sauransu.

Kammalawa
Kamar kowacce irin al'umma mutanen cikin gidan Sarki suma suna da al'ada tasu ta kansu wacce take karbar bakin abubuwa daga waje kuma take sauyawa yau da kullum, sannan tana tafiya da zamani, wannan shi ya nuna cewa cikakkiyar wayuwa ake yi kamar ta sauran jama'a ba zama ake yi kamar na gidan yari ba.

Manazarta
Littattafan da aka duba:
Sufi H. A. (1993) Mu san Kanmu, Kano Nigeria

Kofoworole, 2 da Lateef, Y. (1987) Hausa Performing Arts & Music nigeria Magazine, Lagos

Nast H.J. (1992) Space, History And Power: Stories Of Spatial And Social Change in The Place of Kano, Northern Nigeria, Circa 1500-1990 Ph.D. Thesis. Mcgrill Univesity, Montreal, Quebec.

Nast H.J. (2003) DISTRUPTING DECEPTIONS: A photographic, History of Kano Place, Nigeria Printed my Vic-O Graphic, Inc Willow Book, Illinois

Bayero, S.A (unpublish) Mata a Gidan Dabo

Hira da Mutane
Yaya Buruji ranar 13 ga watan Nuwamba, 2004 da 4:30 na yamma

Yakadiya Asabe Matar Daga, a soronta ranar 13 ga wanta Nuwanba, 2004 da karfe 3:00 na dare.

Yaya Tafada Figi, ranar 14 ga watan Nuwanba, 2004 da karfe 8:00 na dare a filin Sirada.

Yaya Maijidda ranar 15 ga watan Nuwamba, 2004 da karfe 6:00 na yamma a filin Sirada.

Yaya Rahmu ranar 17 ga watan Nuwanba, 2004 da karfe 5:00 na yamma a filin Sirada.

Yaya mai soron baki (Y aHajiya) ranar 17 ga Nuwanba, 2004 da karfe
3:00 na dare a filin Sirada

Jadadiya Uwani, ranar 18 ga watan Nuwanba, 2004 a soron Jakadiya Sabe Matar Daga

Ibrahim Mai Kano, (Galadiman Zagin Sarkin Kano), a soron gidan sa, ranar 21 Nuwamba, 2004.

Thursday, June 21, 2007

Hausar Gidan Sarauta: Sadarwa Cikin ‘Kiran Lafiya’ a Fadar Kano

Nasiru Wada Khalil
nasiruwada@yahoo.co.uk, nasiruwada@gmail.com
Sharia Court of Appeal, Kano.



Makala da aka gabatar a taron kara wa juna sani mai taken “Rayuwa da Ra’ayoyi da Gudunmowar Masu Bunkasa Hausa” a Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato. 6-8 ga watan Fabarairu, 2007.


Gabatarwa
Dan adam yana da hanyoyi da yawa da yake sadar da sakonsa, amma ya fi amfani da yare a kan sauran. Kowace al’umma da irin yaren da take amfani da shi wajen sadarwa. A daular Usmaniyya yawancin kasashen suna amfani ne da yaren Hausa, daga cikin wadannan kasashe masu amfani da Harshen Hausa akwai Kano wacce tana daya daga cikin tsofaffin cikinsu ta fuskar ciniki, da sana’a da kuma sarauta. Masarautar Kano ta samu ne tun hijira shekarar 389 (999AD) inda Bagauda ya zamanto Sarki na farko daga cikin habe, zuwa shekarar hijira 867 (1463AD). Daga nan sai gidan Rumfa suka karbi sarautar zuwa shekara 1538, Kutumbi suka karba a hannunsu wanda su ne Fulani suka karba a hannunsu daga karshe, cikin shekarar hijira 1235 (1819AD) (Dokaji,1978. East 1979. Smith, 1997. Fika, 1978. Palmer, 1928. Hogben da Kirk-Green, 1966). Kuma zuwa yanzu su suke yin mulki a Kano. Dukkanin wadannan kabilu da suka yi mulkin Kano sun yi amfani da harshen Hausa ne hatta kabilar Fulanin da suke ba Hausawa ba.

Haka zalika sadarwa a fadar Kano ana yin ta ne ta hanyoyi daban-daban wadanda suka kunshi ishara ta hanyar jinjina da karbar gaisuwa, sai kuma amfani da ala ta kida kamar Tambari da Kuge ko ala ta busa wacce ta kunshi Kaho da Algaita da Sarewa da Kakaki, hatta buga Bindiga da Guda da gyaran murya da yanayin shiga, duk hanya ce ta sadarwa a fadar Kano. Baya ga wadannan ana amfani da yare wanda shi ya fi komai yawa, yaren da ake amfani da shi shi ne Hausa.

Duk wadannan hanyoyi na sadarwa ana amfani da su ta bangaren isar wa da Sarki sako ko kuma Sarki ya isar wa da jama’a sako, misali idan Sarki ya yi hawa yana dunkule hannunsa na dama (Jinjina) wanda hakan wata tambaya ce yake yi wa jama’a cewar shikashikan Musulunci guda biyar kun rike? Su kuma jama’a in suka dunkule nasu hannun amsa ce suke ba shi da cewa; “Na’am mun rike” (Hira da Malam Yahya Salihi, 2006). A wani kaulin kuma cewar Wamban Kano Alhaji Abbas Sunusi (Hira a talabijin) ita jinjina jama’ar gari ne suke yi wa Sarki ita, abin da take cewa shi ne mun ba ka amanarmu, ka rike? Shi kuma Sarki in ya yi tasa jinjinar amsa ce yake ba wa mutanen garin cewar e na rike. A fadin Malam Nasiru Kabara a Tafsirin da yake yi da Azumi cewa ya yi Jinjina a wajen Shehu Usmanu tana nufin Yadin Wahidin Ala Man Siwahu Ma’ana Hannu daya a kan wanda ya wanicce shi (fassarar tawa ce).

A cikin wadannan hanyoyi na sadarwa da ake amfani da su a fadar Kano, babu abin da aka fi amfani da shi irin harshen Hausa, abin duk da sauran hanyoyi suke sadarwa yana da ma’ana cikin harshen Hausa, ma’ana za a iya fassara abin da kidan ko busar take cewa, ga misali Tambari in ana buga shi yana cewa “Sarki bakon dole.” Dama idan mutum ya ji tambari ya san Sarki ne ya iso domin ba a yi wa kowa tambari sai Sarki. Kakaki ma haka, in an busa shi yana sanar da mutane ne cewar ga Sarki ya zo, domin cewa yake, “Ga shi, Ga shi a fili, Ga bijimin Saraki, Ga Toya Matsafa, Babban Bajimi, Babban Bako, Ga Magajin Rumfa, Ga Magajin Dabo.” Algaita a halin tafiya tana cewa “Sukukun bakaka Jatau, mashin da wuta jatau, Idan mai sabo bai daina ba mai horon ma fa ba zai fasa ba.” Idan kuma mai algaita yana bin Tambura to za su rinka cewa, “Masu duniya kuna shagalinku, babban bajimi babban Bako” da sauransu. Baya ga wadannan abubuwa da za a iya fassarawa akwai kuma wadanda ba za a iya fassara su cikin Hausar ba sai dai a fuskanci ma’ana kamar buga bindiga da ake yi bayan an sauko daga sallar juma’a tana nufin an idar da sallar juma’a, saboda haka matan da suke gidajensu wadanda juma’a ba ta kama ba sai su yi sallah, in kuma daren kamawar watan azumi ne ko sauke shi, to wannan bindigar da aka buga sanarwa ce ga mutane cewar an ga watan Azumi ko na Sallah karama. Ko wadanda suke nesa da gari su ma su san sun makara an idar da sallah. Ko guda da ake yi a tsakar gidan Sarki ita ma tana sanar da cewar an yi haihuwa da sauransu.

Hausa a fadar Kano, Hausa ce tsantsa da ba ta da sirki da wani yare sai dan fulatanci kadan, kamar Lamido wacce take nufin babban dan Sarki, Yallabo yana amfani da ita wajen gaisuwa cikin girmamawa ga wanda yake ba dan sarki ba, Alasebbeni ita kuma ga dan Sarkin da ba shi da Sarauta, Ingwaiya kalma ce ta amsa gaisuwa (Sarkin Kano Abdullahi Bayero an ce shi ya fi amfani da ita in mata suna gaishe shi a gida), Modibbo kuwa kamar yadda kowa ya sani tana nufin Malami da sauransu, amma duk da haka Hausar gidan Sarki ta sha bamban da irin Hausar da ake yi a gari, domin ita an gina ta ne matuka a kan al’ada da dabi’a ta Hausawa da Fulani.

Bahaushe yana da wasu dabi’u da yake siffantuwa da su, wadannan dabi’u Kirk-Greene (1974) ya zayyana su wadanda suka kunshi Kunya da Gaskiya da Amana da Karamci da Hakuri da Hankali da Ladabi da Mutumci da Hikima da kuma Adalci. Haka zalika Alhassan da sauransu (1982) baya ga wadannan dabi’u da Kirk-Greene ya wassafa sun kara: Mu’amala da Zumunta da Rikon addini da Dattako da Kawaici da Rashin tsegumi da Kama sana’a da Juriya da Jarumta. Tattare wadannan dabi’u da Adamu (2001) ya yi ya saka musu “Mizanin Auna Tarbiyyar Bahaushe”, ya nuna yanayin yadda al’ada da zamantakewa ta Bahaushen kwarai ta ke, kuma wannan yana da tasiri ga yanayin maganar Bahaushe. Wadannan dabi’u Bahaushe ya yi tarayya da Fulani cikinsu, domin shi ma Bafulatani yana da su, wani sa’in nasa ma sun fi na Bahaushe wanda ake kira Pulaku. (Khalil da Bayero. 2006)

Pulaku dabi’a ce da take da matukar muhimmanci a wajen Fulani, ita take tafiyar da rayuwarsu da al’adunsu wadanda suka kunshi zamantakewa, yanayin sutura da gida da aiki da biki da yare da suke amfani da shi wajen mu’amalar yau da kullun. Abubuwan da Pulaku ya kunsa muhimmai guda uku ne, wato hakkilo da Hausa ‘hankali’, sai munyal, shi kuma ‘Hakuri da Juriya’, da seetu'dum ma’ana Kunya.

Wadannan dabi’u na Bahaushe da na Bafillatani (Pulaku) su ne suka haifar da yanayi da sigar yadda ake magana a fadar Kano, ma’ana su suka haifar da irin Hausar da ake yi a fadar Kano.

Fadar Kano ta kunshi: Sarakai da Malamai da Bayi da Barori da Masarta baya ga wadanda ake mulka kamar masu sana’a da sauran jama’ar gari (Talakawa) duk wata sadarwa a tsakaninsu take, amma ta fi yawa tsakanin Sarki da bayinsa, domin duk abin da zai isa wurin Sarki sai ya bi ta hanyar bayinsa ko da kuwa ba kai tsaye ba, misali idan hakimai ko malamai ko mutanen gari za su gaya wa Sarki magana kai tsaye sai bayin Sarkin sun yi musu iso (Dokaji, 1958: 42) ko da kuwa ba su ne suka fada wa Sarkin maganar ba.

Hausa a Fadar Kano
A fadar Kano akwai salo da yanayin yadda ake magana wacce ta saba da irin yadda ake yi a gari, ko da yake sun hada tushe guda wato musulunci da al’adar Fulani da ta Hausawa. A tsarin magana ta Bahaushe akwai girmamawa da alkunya saboda haka ne mata ba sa kiran mazajensu da sunansu na yanka sai dai su yi masu lakabi na girmamawa su kira su Alhaji ko Maigida ko Malam, baya ga haka duk sunan da ya zo daya da na mazansu ko iyayensu ba za su kira wannan sunan ba sai dai su kira sunan da mai sunan Baba, ga misali in sunan mahaifinsu ne ko ma dungurum su ce Baba (wannan al’adar ba wai ga mata kawai ta tsaya ba). Idan ma wani abu ne ko da ba mutum ba in yanayin sunansa ya yi kama da yanayin furucin sunan miji ko mahaifi da sauransu, mata ba za ka ji sun fadi wannan sunan ba sai sun canza shi yadda zai ba da ma’anar da za a gane abin, da haka za su kira shi. Ga misali a Kano an yi Limamin babban masallacin juma’a sunansa Mansur, saboda ganyen Lansur yana da yanayin furuci da Mansur, matansa ba sa cewa Lansur sai dai su ce koren ganye mai yaji.

Irin wannan yanayin magana yana da matukar muhimmanci a tsarin yadda ake magana a gidan Sarkin Kano, domin girmamawa, duk Sarkin da aka yi a Kano a zuriyar Fulani ba a fadar sunansa ko sunan abin da furucinsa yake kama da wannan sunan.

Jadawali na 1. Sunayen Sarakuna da Abin da Ake Fada a Makwafinsu
Sunan Sarakuna Suna Mai kamanceceniya
Makwafin sunan
Sulaimanu Sulai Karfe
Alu Allura Madinkiya
”Allo Dan Makaranta
”Alli Matabi
”Ludayi Mashayi
Abas Albasa ‘yar lambu
Abdullahi Aduwa Dabagira
”Auduga Kada
Inuwa Inuwa Mahuta
Ado Ado Kwalliya
Tushe: Lura da abin da ake cewa da kuma hirar baka 2005

Sarakuna da iyayen su mata ba kiransu ake yi da sunan su kai tsaye ba sai an saya, ga sunayen da ake kiran masu sunan sarakuna a jadawali na kasa:

Jadawali na 2 Sunayen Sarakuna da Ake Saya Sunayen
Sunayen Sarakuna
Sunayen da Ake Saya su da Su
Abbas
Maje Nasarawa
Abdullahi
Mai Kano / Alhaji
Ado
Sarki / Babban dodo / Amir
Aliyu
Sarki mai tafiya
Bello
Mai gari/Mai sadaka
Ibrahim Dabo
Cigari
Inuwa
Sarki mai sunan mahuta
Usman
Sarki dan tsoho / Maje Ringin
Tushe: Lura da abin da ake cewa da kuma hirar baka 2005

Baya ga wadannan sunaye, duk kalmomin da Bahaushe ba ya fadar su ko domin kunya ko kara da sauransu a gidan Sarkin Kano ma ba a fadar wadannan abubuwa, ga misali;

Jadawali na 3 Sunayen da ba a fada
Suna
Makwafin suna
Hikima ko Dalili
Dakuwa
‘Yar aya
Kama da zagi
Maroki
Masarci
Kama da cin mutunci
’Yan biyu
Daya da dan’uwa
Kunya
Haihuwa
kyankyasa
Kunya
Dan Sarki
Dan Fulani
Kara
Tsugunna
Durkusa
Ladabi
Shiru
Kawai
Ladabi
Zauna
Ladaf
Ladabi
Juyo
Ladaf
Ladabi
Tushe: Lura da abin da ake cewa da kuma hirar baka 2005

Yanayin magana a Fadar Kano ya ta’allaka ne da wurin da ake yin maganar da kuma halin da ake ciki, idan a cikin gida ne yanayin maganar daban, in a Fada ne ma daban, in a kan doki ake tafiya ma haka. Misali idan Sarki zai sauki bako a fada kamar a Soron Ingila Sarki zai yi wa bakon nan maraba kamar yadda aka saba, ma’ana ya yi masa maraba da kansa, kamar yadda in shugabanni ko baki sun zo yake yi. Amma in yana halin tafiya ne sai dai ya yi masa jinjina su kuma yaran Sarki su isar masa da wannan marabar cikin kiran lafiya, su ce gaishe ka wane.

Ma’anar Kiran Lafiya
Kiran lafiya wani abu ne da bayin Sarki suke yi wa Sarki wanda yake waka-waka ba waka ba, kirari-kirari ba kirari ba, mai dauke da fata da addu’a, wanda ake yi da Hausa ta hanyar nusarwa, ko umarni da kalmomin girmamawa da ake amfani da su a Hausar zamantakewa ta yau da kullum.

Shi kiran lafiya ana yin sa ne a halin tafiya a kan doki ko a mota ko a kasa in ba masallaci ko jana’iza za a ba. Amma kuma in a halin dawowa ne daga masallacin ko jana’izar za a yi kiran lafiya, sai kuma in ana zaman fadanci.

Kusan kowace fada a daular Usumaniya suna da irin kiran lafiyar da suke yi wa sarakunansu kamar Fadar Sakkwato sukan ce Alherin Allah ya isar ma uban musulmi ko Uban musulmi na gaishe ku a wajen amsa gaisuwa, ko hankali da kofa da ‘yan sauransu. Bidda kuma bagadogi, inah kana duwa, Wuri! Sarari! Alanguburo kuwa a fadar Maiduguri, ko Kabesi a Ile Ife, da sauransu. Amma duk wadannan fadoji babu wacce take da kiran lafiya mayalwaci kamar Fadar Kano, domin a Fadar Kano babu muhallin da ba shi da irin nasa kiran lafiyar.

Bambancin Kirari da Take da Kiran Lafiya
Shi kirari zuga ce da mutum yake yi wa kansa ko wani ya yi masa (Ames, Gregersen da Neugebauer, 1971 a cikin Furniss, 1996). Skinner (1980) ya wassafa sigar kirari a matsayin wake na yabo wanda yake ya kunshi kamanta mutum da jarumtar dabba, ko a alakanta mutum da kyakkyawan musulmi ko Balarabe. Skinner ya bayyana cewa kirari ana rera shi ne da karfi a wajen sarauta, biki da kwararrun masu sana’a. Kirari yana da tasiri wajen tayar da tsumi ko kiran aljan. Ana fara yin kururuwa kafin a fara kirarin kamar a wajen Dambe ko “Dambe karfe” ko wajen Kokawa (Lateef da Koforowola 1987:5). Take kuwa wani gajeren kirari ne da ake yi wa wani mutum a koda yaushe wanda da ka jiyo shi ka san na wannan mutumin ne (Furniss, 1996: 73-75). Dangambo (1984:42) ya bayyana bambancin take da kirari inda ya ce:

Take abu ne da ake danganta shi da bayyana wanda ake yabo, wato taken wani ya sha bamban da na wani. Misali, irin taken da ake yi wa samari da ‘yanmata wurin kidan kalangu da sauransu. Kirari kuwa, yana iya zama yabon kai, kamar yadda ‘yan tauri ko maroka ke yi; ko kuma yabon wani, kamar yadda maroka ke yi, da sauransu.

Kiran lafiya ya bambanta da kirari da kuma take, babban bambancinsu shi ne Take da Kirari yabo ne, shi kuwa kiran lafiya ba yabo ba ne, nusarwa ne da tunatarwa, a kiran lafiya akwai addu’a da kuma sako, sabanin kirari abin da mutum yake da shi ne na jarumta ake fada a kara masa gishiri. Shi kuwa take ba shi da tsawo, kuma ba ya wuce daya, amma shi kiran lafiya yana da yawa kuma ya danganta da inda ake. Inda kiran lafiya ya zama na yabo kamar yadda jama’ar gari suke yi wa S’arki, to, a nan ma akwai bambanci da kirari domin cikin fata da addu’a suke yi masa duk yabon da suke yi masa.

Jadawali na 4: Bambancin Kirari da Kiran lafiya
Kirari
Kiran lafiya
Zuga ce zalla
Bayan zuga akwai fata da addu’a
Akan fara shi da kururuwa
Ba a fara shi da kururuwa
Ana yi wa kowa da kowa
Sarakai kawai ake yi wa
Biki ko farauta ko bauta ta gargajiya
Ana fadanci ko a halin tafiya
Ana daga murya
Ba a daga murya sosai
Yankan yi alaka da tada iska ko tsimi (ga ’yan tauri)
Babu wata alaka ta komai sai ta nusarwa
Maroka ne suke yi
Fadawa ne suke yi

Nusarwa Cikin Kiran Lafiya
Akan nusar da Sarki halin da ake ciki ta hanyar kiran lafiya, kamar idan an yi ruwa Sarki yana tafiya a kan doki ko a kasa, ko a kan kwalta za a dinga nusar da shi cewa Rauni bisa rama mai nasara ba sake ba manko ga linzami ko ba bugu ba manko, ko amincinka ya fi ga linzami. A nan ana nusar da Sarki ne cewa kada ya sakankance ko kada ya bugi dokinsa yadda zai zaburar da shi, kada ya manta cewa akwai rauni a kasar da yake tafiya a kai zai iya zamewa ya fadi. Idan wani abu ya firgita dokin ko dokin yana dara (tsalle) ko nagarta (rawa) da Sarki, za a rinka fada wa Sarki abin da zai yi ana gaya masa cewa kiwo sannu alher, ba sake ba manko, kamazuru abokin dabara, amincinka ya fi ga linzaminka, ma’ana dokin ya koshi saboda haka kada a sakankance da shi. A nan za mu iya cewa ana fahimtar da Sarki ne cewa ya rabu da bayanin da ake yi masa, hankalinsa ya tafi kan linzamin dokin.

In kuma an ce Bilaka dama da hauni to akwai ruwa a gefe da gefe, kamar gada ko hanyar da ta ratsa ruwaye guda biyu shi ne ake fadar haka ko a ce jingine dama da hauni, ko kafin a hau gadar za a rinka ce masa hattara. Haka na idan kuwa abin da zai iya tuntube da shi ne ko wanda zai iya bata shi kamar danshi, ko gidan tururuwa, ko rami, ko marmara, ko tubali, ko tsittsige, shi ne ake cewa hattara salamun.

Idan kuma a saman Sarkin akwai wani abu wanda zai iya bugar sa ko wanda zai iya kama masa rawani, to za ka ji ana cewa shafi bisa alher, sunkuye salamun. Ma’ana akwai wani abu a samansa wanda zai iya shafar rawaninsa ko zai iya bugewa da shi, to shi ne ake nusar da shi halin da ake ciki da abin da ya kamata ya yi, wato ya sunkuya.

Idan an zo gangara kuma sai a ce Gangare Sabkawa, in kuma tudu ne sai su ce bisa Haikawa sannu, a kusurwa wacce take babba sai a ce mazgaye salamun a karamar kusurwa kuma kamar a cikin soro sai a ce Gicciye dama alher, ko Gicciye hauni alher, wato kenen ya karkata dama ko ya karkata hagu. Idan kuwa a abin da yake bukatar Sarki ya saurara ne ko ya rangwanta tafiya, kamar matsi ko cushewar hanya, ko akwai masu gaisuwa ko addu’a, to a nan sai ka ji ana cewa rangwame Tafsawa, ko a ce sannu rangwame alher, ka ga kenan ya san akwai wani abu da ake bukatar sa da ya dan tsahirta.

Lokacin da za a dauki Sarki a hoto ko wani bako zai shigo inda Sarki yake, to a nan akan jawo hankalinsa da cewa Gyara kimtsi ga kyau ko a ce Kimtsi gyara daidai alher, abin nufi a nan shi ne Sarki ya shirya, ko ya gyara ko ya kimtsa kamar yadda aka fada cikin kiran lafiya. A nan ko da wani ne yake gai da Sarki akan iya janyo hankalinsa zuwa inda mutumin yake kuma ana iya sanar da shi sunansa, misali idan Nasiru yana gefen dama yana gai da Sarki kuma hankalin Sarkin ba ya wurin, to za a iya jawo hankalinsa da cewa; Jinjina (ko jinjine) dama lafiya alher, gaishe ka Malam Nasiru, idan jama’a ne sai a ce gaishe ku Mauro, ko gaishe ku jama’ar gari.

Idan kuwa a mota ake tafiya idan akwai digar jirgi ta ratsa, ko rami, ko duwatsu, sai a ce kauwa sannu, ko kauwa daidai ko rangwame kauwa sannu. Zama a mota yayin sunkuyawa: lif bisa alher ko sunkuye salamun. Idan a jirgin sama ne kuwa yayin da Sarki zai hau matattakala za a shaida masa cewa Hattara salamun, lokacin da jirgin zai daga ya tashi sama sai a ce motsawa bisa alher ko a ce bisa ga kyau, wannan Kiran lafiyar shi dai ake fada lokacin da Sarki zai hau doki ko zai tashi daga kan karagarsa.

Yayin da Sarki yake zaman shari’a a fagaci, in an tsahirta kafin Sarki ya fadi hukunci Mutan Fada za su rika cewa da shi Lafiya Adali, Lafiya Mataimakin Musulunci da sauransu.

Umarni Cikin Kiran Lafiya
Akwai kuma kiran lafiyar da suke kamar umarni ne duk da cewa akwai nusarwa a ciki kamar; Takawa Sannu (in ana tafiya a kasa) da Daukawa sannu da Cirkawa sannu, sai kuma Caskawa sannu (a wurin tsakuwa), Turkawa sannu (a wajen Tirbaya) da sauran ire-iren su duk a wadannan kiran lafiyar umarni ne ake bai wa Sarki cewa ya tafi sannu a hankali, har ila yau ana nusar da shi ko tunatar da shi cewa ya tafi a sannu-sannu, domin ita ce tafiyar Sarki kada ya yi garaje. A wannan wurin kuma akan rika yi wa Sarki kiran lafiya da lafiya salamun alher, lafiyarka dama da hauni, dama da hauni lafiya, salamun salamun. Wani abu da kiran lafiya ya kebanta da shi, shi ne a kiran lafiya ne kadai ake kiran Sarki da wakilin suna na abokin magana.

Domin saukin fahimta da kiyayewa ga jerin kiran lafiyar nan da muhallin da ake yin su cikin jadawali na kasa.

Jadawali na 5: Kiran Lafiya da Muhallinsa
Kiran Lafiya
Muhallin Kiran Lafiya
Sabkawa sannu
Saukowa, ko Gangara
Haikawa
Hawa tudu
Gicciye Alher, ko Gicciye Salamun
Soro ko matsattsen wuri
Mazgaye Alher, ko Mazgaye Salamun
Kusurwar da take ba matsattsiya ba
Takawa, Cirkawa, Caskawa, Turkawa
Tafiya
Sunkuye
Sunkuyawa
Bisa ga kyau
Tashi ko hawa doki
Hattara
Wurin tuntube ko kurunkusai ko tsattsage
Bilaka ko Jingine
Kan gada
Rangwame Salamun
A saurara tafiya ko gurin tsaiwa
Kauwa sannu
Tafiya a mota in an zo gargada ko digar jirgi.
Kiwo sannu ko kamazuru abokin dabara
Idan doki yana fitina
Ranmi bisa rama, ba sake ba manko
Tafiya a doki kan jikakkiyar kasa
Gyara kimtsi ga kyau
Ana zaune ko a tsaye ko ana fadanci

Shi kiran lafiya bayin Sarki ne maza kadai suke yi, ko in ya shigo tsakar gida. Baya ga haka mutanen gari ma suna yi wa Sarki addu’a su ce Allah kara maka imani, wasu kuma kiran lafiya suke yi amma ba irin na yaran Sarki ba, domin su nasu kiran Lafiya ne na zuga da kambamawa, amma duk da haka ya saba da kirari saboda kalmar lafiya da ake fara fada kafin a ce komai. Ga irin abubuwan da suke fada:

Lafiya Sarkin yakin Sarkin musulmi
Lafiya maida garin wani kango
Lafiya Barden mahadi
Lafiya Sukukun bakaka
Lafiya Darzaza amalen sarakuna
Lafiya ba hau da wani ba sauke wani
Lafiya hana kangara
Lafiya Sakaka babban bako
Lafiya Bango madafar bayi
Lafiya hadarin kasa maganin mai kabido
Lafiya kwankwason jimina mai wuyar shafawa
Lafiya garkami wandon karfe
Lafiya jijjigen addini
Lafiya toya matsafa
Lafiya waliyin Allah
Lafiya baya goya marayu
Lafiya toron giwa
Lafiya tufaniyar gabas
Da sauransu


Amfanin Kiran Lafiya
Shi kiran lafiya yana matukar amfani ko kuma a ce duk amfanin da sadarwa take da shi akwai shi a kiran lafiya. A harkar mulki kiran lafiya ya taka muhimmiyar rawa wajen tafiyar da tsarin masarauta, yana kare darajar sarautar kamar wajen kare sarki daga yawan magana (wanda Hariri ya ce yana kawo tuntube), baya ga kasancewar sa gishirin harkar sarauta saboda a nishadance ake yin sa.

Kammalawa
Kiran lafiya wata hanyar sadarwa ce da ake yin ta da Hausa wacce tsawon zamani ko sauye-sauye da shigowar bakin abubuwa na kimiyya da fasaha kamar mota da jirgi da suka maye gurbin doki ba su sa yanayin wannan Hausar ya zanja ba. Wannan rashin canji da aka samu ba karamin nuna bajintar yaren ya yi ba, sannan kuma ya tabbatar da cewar Harshen Hausa arzurtacce ne da kalmomi masu game ma’ana mai yawa yadda za su iya karbar wasu bakin abubuwa ba tare da sun canja ba.

Bayin Sarkin Kano da suka fito da wannan tsari na sadarwa mai nishadantarwa sun taimaka sosai ko da ba wajen bunkasa Harshen Hausa ba har da wajen adana shi ga al’ummar Hausawan da suke yankinsu, tun da ba Hausa ce da ake yin ta a ko’ina ba a koyaushe.

Godiya
Ina mai mutukar godiya ga Danrimin Kano da Babban Zagi da Sarkin Malafa saboda tallafin da suka bayar a wannan Makala.

Manazarta
Adamu, A.U. (2001) Hausa Prose Fiction: Toward an Analytical Framework,

FAIS Journal of Humanities 1 (4) Alsharishi, A. A (2002), Sharh al Mukamatul Harir (Commentary) Dar il Fikr Beirut Lebanon.

Dokaji, Alhaji Abubakar (1958) Kano Ta Dabo Cigari, NNPC, Zaria.

Dangambo, Abdulkadir (1984) Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Triumph Publishing Company, Kano

East, R. M. 1971 (1930) Labarun Hausawa Da Makwabtansu: Littafi na biyu. Zaria, Nigeria: Northern Nigerian Publishing Company.

Fika, A.M.( 1978) The Kano Civil War and British over-rule 1882-1940, London:
Oxford.

Furniss Graham (1996) Poetry, prose and Popular Culture in Hausa, Edinburgh University Press, London.

Hogben.S. J. da Kirk-Green, A .H. M. (1966), The Emirates of Northern Nigeria: A Preliminary Survey of their Historical Traditions. London.

Khalil N. W. & Bayero S. A. (2005) Royal Communication in Traditional Setting: Language Patterns and Address Forms in Kano Emir’s Palace, Paper presented at Hausa week organized by Hausa students of Bayero University Kano on the 10th – 12th of June, 2005 at Bayero University Kano.

----------- (2004) Nishadin Matan Kulle: Tsokaci a Kan Gidan Sarautar Kano, a paper presented at international conference organized by Center for Nigerian Languages, Bayero University Kano.

Kirk-Greene, A.H.M. (1974) Mutumin Kirki: The Concept of the Good Man in Hausa.

The Third Annual Hans Wolff Memorial Lecture, Bloomington; African Studies Program, Indiana University.

Kofoworola Z. O. & Lateef Yusif (1987) Hausa Performing Arts and Music, Nigerian Magazine Publication.

Skinner, A. N. (1980) An Anthology of Hausa Literature in Translation, NNPC Zaria.
Smith, M.G. (1997) Government in Kano 1350- 1950 Westview press.


Rataye: 1

Wasu daga Sunayen Sarki:

Sakaka
Uban Gabasawa
Toron Giwa
Kigo
Jatau
Sukuku Bakaka
Bakon dole
Wandara
Takawa
Sabkawa
Haikawa
Daukawa
Cirkawa
Bajimin Duniya
Amale
Ginshiki
Ba takura
Saka takura
Kigama



Wednesday, June 20, 2007

MUHIMMANCIN MARUBUCI A CIKIN AL’UMMA

Na Gabatar da Wannan Jawabi a Wajen Taron Gangamin Marubuta, Wanda Kungiyar ‘Brigade Authors Forum’ Suka Shirya, Ranar Lahadi 21/05/2006, a ‘Government Girls Secondary School’ Gama Tudu, Kano.



Gabatarwa:
Rubutu rayayyen al'amari ne da kan wanzu matukar wanzuwar duniya, kuma tamkar shuka ce wace in har ka yi za ta girma ta ba ka inuwa ka kuma ci 'ya'yanta. Yana kuma iya zama tamkar dan kunama ko kuwa kaikayi wanda Hausawa ke cewa "koma kan mashekiya".

Manyan masana tuni sun bayyana abubuwa masu yawan gaske game da murubuci da kuma shi kansa rubutun, don haka duk abin da zan fada an riga ni fada sai dai na dan tsakuro abin da ya samu daga ire-iren abubuwan da suka ce.

An nemi in gabatar da takarda mai taken Muhimmancin Marubuci A Cikin Al’umma, ina godiya ga masu shirya wannan taro da suka ba ni wannan dama. Kuma ina yi musu fatan alheri da samun nasara a kan manufar wannan taro.

Wane Ne Marubuci?:
MARUBUCI Dan BAIWA NE, haihuwarsa ake yi ba yin sa ake ba. Marubuci shi ne wanda ta hanyar amfani da fasahar rubutu yakan kirkiri wani yanayi na gaske ko na almara ko tunani ya kuma yi amfani da shi don gina wasu mutane da abubuwa wadanda yake amfani da su don isar da sako ga al'ummar da ke karatun rubutunsa. Shi wannan sako ana tsara shi ne ta hanya ta musamman mai cike da hikima da hazaka don isarwa a saukake, kamar ta hanyar yin amfani da haruffa zuwa kalmomi zuwa jimloli zuwa si]arori da shafuka har zuwa cikakken littafi.

Wani ana haihuwarsa da rubutu wani kuma koyo yake yi, amma duk marubuta za mu kira su. Shi marubuci mutum ne na daban, ba wai ya fi sauran rukunonin bil'adama ba ne, a'a, shi dai daban yake da sauran mutane, wato dan baiwa ne. Marubuci na yin tunani ne iri na daban, yana kuma kallon rayuwa da al'amuran rayuwa da wata irin fahimta tasa ta daban, sannan ya bayyana ta a rubuce. Kamar yadda aka ambata a sama shi marubuci dan baiwa ne, sannan shi kansa rubutun baiwa ne.

Muhimmancin Marubuci A Cikin Al’umma:
Abu ne sananne ga al’umar da take da ilmi cewa marubuci yana da matukar muhimmanci da tasiri. Saboda haka ya wajaba a kan al'ummar da ta sami marubuci a cikinta ta yi kokaririn jawo ra'ayinsa ko yin tasiri a kan tunaninsa don ya yi rubutu na kwarai, in ba haka ba duk abin da ya rubuta zai yi tasiri a kan ita al'ummar.

Marubuci kan yi rubutu saboda dalilai da dama ko wani hali ko yanayi da ya sami kansa ko wani tarihi na kasa ko dadadde ko kuma wata manufa ko ra'ayi. Don haka marubuci na iya yin rubutu don ilmantarwa ko wayar da kai ko kyautatawa ko fadakarwa ko farfaganda ko ta da zaune tsaye ko cin zarafi ko kuwa tsokana. Yana iya yin rubutu don gina wata akida ko rusawa ko kuwa don ru]ar da jama'a ko kawo sauyi ko kuma don tabbatar da wani ra'ayi ko manufa. Saboda haka marubuci na iya zama dan kwarai ko kuma baragurbi, sai dai a koyaushe yana kokariri ne ya ga cewa ya shawo kan makaranta su amince da shi. Domin kuwa zai yi iya kokaririnsa ya nuna musu cewa sakon nan nasa gasgatacce ne, amintacce ne kuma dauwamamme ne mai farin jini.

Wani mawaki Sani Yusuf Ayagi, a cikin wakarsa ta Alkalami Ya Fi Takobi, ga abin da yake cewa:
Alkalami mai hagun da dama,
Mai haske ga duhu ku duba.

Mai zaki alkalam da daci,
Ko ba ku san me nake nufi ba.

Ai ma’ana gaskiya da karya,
Babu guda wadda bai iya ba.

In ya so yanzu ai zumunci,
Sai ya matsa can ya kulla gaba

In an so, sai a kulla yaki,
Ku hargitse ba da kun sani ba.

Da shi masoya ka daukaka,
Da sun rubuta ba a musa ba.

Da shi akan sa a kassara ka,
Da dai ba ka kara daukaka ba.

Da an rubuta ana yabonka
Ko kai sata ba a sani ba.

Da shi sukan bata dan adam kaf,
Akan abin shi dai sani ba.

Yana da kyau mu fahimci cewa marubuci na da matukar muhimmaci ga duk al'ummar da yake zaune a ciki domin kuwa kadara ne ga wannan al'umma kuma yana iya jawo wani ci gaba ko dakushewa da alkalaminsa. In har ba ka fahimci manufar marubuci a rubutunsa ba, to ka dauka cewa ka jahi1ci fahimtarsa. Don haka duk irin abin da marubuci ya rubuta akwai manufa a cikinsa sai dai ko ba a fahimta ba. Amma fa ba dole ne a ce koyaushe marubuci na yin rubutu mai ma'ana ba.

Wani abin lura shi ne, zama marubuci wani al'amari ne babba. Duk lokacin da mutum ya zamo marubuci ko yake son zama marubuci, to yana shiga wani hali ne mai wuyar gaske. Na farko marubuci a kullum cikin tunani da kokaririn fahimtar al'ummarsa yake. Na biyu duk lokacin da yake rubutu dole ne ya rinka sanya tunaninsa da kuma mutuntakarsa. Shi ne zai zama na kwarai yanzu, wani lokacin kuma ya zama mugu. Ya zama yaro ya zama babba ya zama namiji ya zama mace, kuma duk lokacin da yake rubutu yana tunani ne na irin mutumin ko halin da yake rubutu a kansa.

Wani lokaci kuma marubuci tamkar dan-leken asiri ne domin kuwa muddin zai yi rubutu in har marubucin kwararre ne sai ya yi bincike don gano wasu bayanai ko fahimtar su. In da za ku gamu da shi a irin wuraren da yake neman bayanansa sai ka rantse ba wani abu yake yi ba. Alal misali idan marubucin yana yin rubutun da a ciki sai an yi maganar karuwai ko mashaya, kada ka yi mamaki don ka gan shi a mashaya ko yana tattaunawa da karuwa neman bayani ne ya kai shi. Ta haka yakan bi sauran hanyoyi don gudanar da binciken sa.

Babban muhimmancin da marubuta ke da shi ga al'umma shi ne, na yin amfani da alkalaminsu wurin sauya al'umma. Ya zama lallai a fahimci cewa ayyukan marubuta kan yi tasiri ga al'umma kai tsaye ko kuma ta rashin sani.

Don haka ya zama wajibi ga al'umar da take da marubuta a cikinta ta ga ta taimaka musu ta kuma yi tasiri na kwarai ga tunaninsu don rubutunsu ya yi tasiri nagari ga al'uma.

Gwagwarmayar Da Ke Gaban Marubutanmu:
Babu shakka a 'yan shekarun nan mun sami wadatuwar marubuta littattafan Hausa daga kowane sashe a arewacin kasar nan, amma akwai kalubale mai yawan gaske a kan su marubutan, wato wajen rashin ingancin bugu da rabe-raben kalmomi da satar fasaha da maimata suna da kuma dagewa a kan jigo daya wanda a kansa ne yawa-yawan manazarta ake ta gwagwarmaya da su, wato jigon soyayya. Tun a shekarar 1992 aka fara wannan muhawara a cikin jaridu da mujallun Hausa kan dacewa ko rashin dacewar jigon da ake rubutu a kansa. Don haka wannan wata dama ce da su marubuta za su yi amfani da ita su gyara kurakuran da ake cewa suna yi, in sun san suna yi din. Domin idan mutum bai samu masu gane masa kuskure a aikinsa ba, to bai yi dace ba.


MANAZARTA:
Adamu, Yusuf M. (1994) Wane Ne Marubuci? Mujallar Zamani, Ta 1,
Fitowa Ta 1, Maris. Kano: Gidan Dabino Publishers.

Adamu, Yusuf. M. (2002) Print And Broadcast Media In Northern Nigeria.
www.kanoonline.com

Ayagi, Sani Yusuf, (2005) Wakar Shirin Alkalami Ya Fi Takobi, Freedom,
Rediyo

Gidan Dabino, A.A, (1995) Muhimmancin Marubuta a Cikin Al’umma,
Takardar da Aka Gabatar a Bikin Kaddamar da Littafin Karshen Mai Zalunci, Koko, Jihar Kebbi.

Gidan Dabino, A.A, (1993) Gudummawar Adabin Hausa Ga Addinin
Musulunci, Takardar Da Aka Gabatar a Taron Kara Wa Juna Sani Na Dalibai Musulmi Na Babbar Makarantar Sakandaren Dawakin Tofa.

Monday, June 18, 2007

Gwagwarmayar Da Take Gaban Hausa(Wa) A Karni Na 21

Hamisu Isa Sharifai

An Gabatar Da Wannan Takarda a Bikin Makon Hausa Na Kungiyar Habaka Hausa, Ta Daliban Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya Da Afrika, Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, a Dakin Taro Na Abdullahi Smith, Samaru – Zariya. Ranar 21 Ga Yuni, 1997



- Mai girma shugaban wannan zama, Shaihun Malami Dalhatu Muhammad
- Mai girma Uban Biki, Mallam Adamu Ibrahim Malumfashi
- Mai girma shugaban karamar hukumar Zariya, Alhaji Isma’ila Nabara
- Wakilin mukaddashin shugaban jami’a, Shaihun Malami Abdullahi Mahadi
- Shugaba da wakilan majilasar kungiyar habaka harshen Hausa
- Manyan baki maza da mata

Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Ta’ala wa Barakatuhu.

Ina mai matukar farin ciki da jin dadi saboda wannan girmamawa da aka yi mani, aka gayyato ni don yin jawabi a wannan wuri, indo Kungiyar Habaka Harshen Hausa ta ke bikin makon Hausa, na wannan shekara, a nan Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya. Wannan take da aka ba ni in yi magana a kansa babba ne. Sannan kuma wurin da zan yi maganar, a gaban shugabannin sashen harsunan Nijeriya na Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, shi ma hamshaki ne, saboda haka abin yana da ban tsoro. To, amma abin ya zo mani da sauki domin wannan sashe na harsunan Nijeriya gida ne a wuriña. A lokacin da nake Babban Editan Mujallar Rana wannan sashe ya taimaka kwarai da gaske. Lokacin da muka fara buga Mujallar Rana sai ya kasance ana samun matsaloli a kan adabi da nahawu. Da taimakon Malamai daga wannan sashe muka samu muka yi maganin wannan lalura.

Wadannan kuwa sun hada da su Mallam Bello Al-Hassan, (wanda a karshe shi ya karbe ni a zaman Babban Editan Mujallar Rana), Mallam Abubakar Kafin Hausa, da kuma shugaban sashen a lokacin, wato shugaban wannan zama, Shaihun Malami Dalhatu Muhammad. Saboda haka ba ni da fargaba; a gaban yayye da kanne nake, idon na yi kuskure to dama aikin naku ne, sai ku gyara.

Harshe: Gwagwarmayar da take gaban Hausa(wa) a karni na 21, magana ce ta harshe, kuma ta shafi sauran harsuna. Saboda hake dole mu fara ta kan nasabar da take tsakanin harsunan da kuma tushensu. Kamar yadda wani masanin harsuna, Shaihun Malami T. Hodge ya ce, a wajen taron kara wa juna ilimi kan harshe da adabin Hausa a Jami’ar Bayaro ta Kano, ranar 7-10 ga watan Yuli, 1978; dukkan harsuna sun tsiro daga tushe daya ne- Lislak. Daga wannan an sami manyan rassa guda biyu wato “Afroasiatic/Homito-sometic da Indo-European/lndo-Hitite”, su kuma suka haifar da wadansu rassan har zuwa harsunan da muke amfani da su a yau.

Misali; harshen Hausa ya tsiro ne daga reshen Afroasiatic wanda ya kunshi manyan rassa kamar haka: Afroasiatic/Hamawa da Samawa
Semitic – Larabawa da Yahudawa
Egyptian - Misirawa
Berber - Buzaya -
Cushitic - Samaliyawa da Galinyawa
Chadic - Hausawa

Wannan ya nuna mana a fili nasabar Hausa da harsunan gabas ta tsakiya da Arewacin Afrika. Haka kuma a nan kusa ma akwai harsuna da dama wadanda su kuma rassa ne da suka tsiro daga jikin Hausa, wato ke nan, shi harshe ba kirkirarsa ake yi ba. Canji ne yakan faru a harshen farko, wanda ake amfani da shi, kuma dalilai da dama na iya kawo wannan canji, ciki har da al’ada da addini da siyasa da tattalin arziki.

A yanzu haka akwai harsuna kusan dubu biyar (5000) (Shaihun Malami Joseph H. Greenberg) da ake amfani da su a duniya. Daga cikin wannan adadi; kadan ne za su kai karshen wannan karni - duk sauran za su mace - wato a daina amfani da su. Harsuna da yawa sun mutu a tarihi, yayin da wasu suka sami damar yin tashin gwauron zabo. Misali, masu amfani da harshen Turanci a farkon karni na goma sha tara 19 (kusan shekaru 200 da suka wuce) ba su fi mutun miliyan 15 (goma sha biyar) ba (Margaret M. Bryant) amma a yau, akwai sama da mutun miliyan 400’ (miliyan dari hudu), masu amfani da harshen Turanci. Game da harsunan da suka mace kuwa, sai dai mu ce Allah ya jikansu; amma yaya za mu yi mu raya namu? A nan sai mu fara duba ainihin harshen Hausa daga farkonsa zuwa yanzu.

Hausa: Harshen Hausa da al’adun Hausawa sun dade a wannan nahiya tamu. Amma harshen ya samu bunkasa ne a karni na goma (10) a lokacin da daulolin kasar Hausa suka kafu kuma suka samu ci gaba, Labarin wayawar kasar Hàusa ya yadu zuwa daulolin da ke kusa irin su Gana da Mali da Borno. Daga nan aki fara samun masu kasuwanci suna zuwa kasar Hausa. Da haka labarin kasar Hausa ya shahara har masu kasuwanci daga kasashen Larabawa da sauran kasashen gabas suka dimanci kasuwannin kasar Hausa. Tare da wannan kasuwanci Musulunci ya shigo kasar Hausa a karni nas 13-14 (kusan shekaru dari bakwai da suka wuce)

Zuwan Musulunci aka fare ilimin arabiyya wanda shi ya haifar da rubutun ajami. Kafin wannan lokaci ba wata shaida da ta nuna yin amfani da wani tsari na rubutu a al’ummar Hausawa. Shehu Usman Danfodiya da almajiransa sun yi amfani da shi sosai wajen jaddada ilimin addini. Rubutun ajami da shi aka yi ta amfani har lokacin da Turawa suka zo, a farkon karni na 20 (kusan shekaru 100 da suk wuce). Da Turawa suka zo, sai suka gina rubutun rumawa (boko) a kan na ajami. Haka aka ci gaba da koyar da karatu da rubutu a cikin Hausa. (Abubakar Imam).

A shekarar 1930, gwamnati ta fara buga jarida ta Hausa, Jaridar Nijeriya ta Arewa. Sannan kuma gwamnati ta kafa ofishin fassara a Zariya, a karkashin wani Bature, Mr. Tailor. Aikin wannan ofishi shi ne fassara da wallafa littattafai wadanda aká juya daga wadansu harsuna zuwa Hausa. Bayan Mr. Tailor, sai R. M. East ya zo ya ci gaba da aikin. A lokacin ne Mr. East da Abubakar Imam da abokan aikinsu, suka kafa harsashin rubutun Hausa sosai; suka kuma daidaita mata ka’idaji. (Abubakar Imam). Gasar talifi, wadda aka shirya a shekarar 1934 ta bunkasa boko sosai. A sakamakon gasar ne aka sami shahararrun littattafan Hausa irin su:
1. Shaihu Umar na Abubakar Tafawa Balewa
2. Ruwan Bagaja na Abubakar Imam
3. Jiki Magayi na Mr. East da M. Tafida
4. Idan Matambaya na Muhammadu Gwarzo
5. Gondaki na Mallam Bello Kagara

Bayan wannan gasa ce, Mallam Abubakar Imam ya kama aiki a ofishin fassara, inda ya rubuta littattafan Magana Jari Ce, juzu’i na 1-3 da Karamin Sani juzu’i biyu da kuma Ikon Allah wanda shi da abokin aikinsa, R. M. East suka wallafa.

A cikin watan Janairu a shekarar 1939, sai aka fara buga Gaskiya Ta Fi Kwabo, wadda ita ce jaridar farko da aka rubuta da Hausa zalla, (Jaridar Nijeriya Ta Arewa ana buga ta ne gefe guda da Hausa gefe guda kuma da Larobci). Haka dai aka yi ta tafiya, Hausa ta zama harshen karatu a makarantu a koina o arewo hor da kudqncin kasar nan. Sannan to ma shigo wadansu kasashe a nan yammacin Afrika (Imam). Wannan saurin yaduwa da bunkasa na harshen Hausa ya firgita Turawa, saboda haka aka shiga yi mata zagon kasa. Don a hana jihar arewa magana da murya daya, sai aka rika zuga kassashen Hausa da cewa Hausar da ake buga jaridar ‘Gaskiya Ta Fi Kwabo’ ba Hausa ba ce, sunanta ‘Istanci’ ko ‘Gaskiyanci’ Daga nan sai kowane lardi ya fara buga jaridarsa kamar haka:

1. Lardin Sakkwato - Zaruma
2. Lardin Bauchi - Zumunta
3. Lardin Zazzau - Bazazzaga
4. Lardin Kano - Sodangi
5. Lardin Borno - Albishir
6. Lardin Adamawa - Ardo (Fillanci)
7. Lardin Kasar Kuzo - Gamzaki
8. Lardin Binuwai - Nwanga (Tiv)
9. Lardin Katsina - Himma
10. Lardin Ilori - Durosi Otto (Yarbanci)
11. Lardin Neja - Nnanintsu (Nupe)

Daga nan sai aka kawo wani Bature ya bude ofishin koyar da harsuna, mai suna NORLA (Ofishin Adabi na Jihar Arewa). Aikin ofishin shi ne ya wallafa littattafai a cikin kowanne harshe na Arewa. Da yin haka, aiki sai ya tsaya cik, kamar yadda Abubakar Imam ya ce, “Shi ke nan babu sauran’ ken- ken- ken, mai kalangu ya fada rijiya”. Wannan shi ne dunkulallen tarihin harshen Hausa na wannan zamani namu.

Nasabar Harshe Da Ci Gaban Al’umma
Shaihun Malami Joseph Hell, wani Bajamushe masanin tarihi, ya ce “Daukacin tarihi na kowace al’umma labari ne na irin bukace-bukacen da suke da su, da kuma kokorin da suka yi wajen biyan wadannan bukatu.” Wato ke nan daga tarihin Hausa za mu gane irin ci gaban da Hausawa suka samu da kuma irin gwagwarmayar da take gabansu don karo ci gaba a karni mai zuwa - karni na 21 (ashirin da daya)

Tarihin Hausa da Hausawa daga karni na 10 (goma) yana da sauki gwargwado. Amma daga karni na goma zuwa baya yana da malsaloli iri-iri. Wadannan kuwa sun hada har da rashin hanyayin rubutu a lokacin, wanda ya sa ba a sami i sahihiyar hanyar ajiya tarihi ba. Kusan duk abin da aka samu daga lokacin ta hanyar tarihin boko aka same shi, wadda tattare take da gurbace-gurbace, na kara da ragi, daga karni zuwa karni. To amma duk da haka, irin wannan tarihin ya ba mu damar sanin wadansu dunkulallun bayanai na matakan ci gaba da aka samu al’ummar Hausawa na wannan lokaci. Misali, tarihin Daura da Sarauniya Daurama (kafuwar Hausa bakwai). Ko da yake wannan tarihi ya kawo tambayayi masu yawa, kusan fiya da amsoshin da ya zo da su, amma duk da haka ya nuna mana yadda al’ummar Hausa ta riga ta sami wayawar tsarin zaman jama’a da shahararriyar daula, wadda har Bayazid daga kasashen gabas ta tsakiya, ya ziyarta. Haka kuma a Kano, tarihin Barbushe da Tsimbirbira da su da jama’arsu da gina fadar farko a nan Madabo (A. Dakoji) da ginin Fadala ta farko da ta biyu da sauran kare-kare na daga baya da kafuwar sana’o’i kamar Noma da Kira da Rini da Gine-gine da kuma kasuwanci (Barkindo, Bawuro). Duk wadannan shaidu ne na ci gaba da Hausawa suka samarwa kansu a daukacin kasar Hausa, kamar yadda Girkawa da Rumawa da Larabawa, a nasu sassan su ma suka samu.

Zuwan Turawa Da Tauya Ci Gaban Harshe Da Al’adunmu
To amma kusan tun daga lokacin da Turawa suka zo irin ci goban da harshenmu da al’adunmu suke yi sun tsaya cak. Kusan duk wani abu na ilimi ko da koyar da Hausar ne, sai dai a yi da Turanci. Duk wata sabuwar hikima saa dai ka ji ta a harshen Turanci. Harshenmu an mai da shi na hira da wasan yara. Sababbin bincike-bincike na kimiyya da sana’a wadanda wannan zamani ya shahara a kansu, mu ba mu da su sai dai mu koya su a bakon harshe. Tun farkon zuwan Turawa, kokarin da aka yi ta yi shi ne, kafa Turanci cikin harkokinmu, yadda duk yadda muka yi, ba za mu yi tasiri ba, sai ta hanyar harshen Turanci da al’adun Turawa. Wannan kuwa an shirya ne don an san ba wata hanya da za’a ci gaba da bautar da mu sai ta hanyar sabauta harshe da al’adurmu.

Saboda hake sai aka shirya hanya mai sauki wajen samun wannan biyan bukata wato ta tsarin ilimi. Duk wani kokari na ci gaba ya dogara ne da samar da kwakkwara kuma sahihiyar hanyar bayar da ilimi. Wannan kuwa ya hada da tsarin manhaja da harshen koyarwa a makarantu. Lokacin da Turawa suka zo sun tarar da mu da tsarin karatu da rubutu wanda ya riga ya kafu a cikin al’ummarmu. Akwai makarantun alla a ko’ina a kasar Hausa da ake koyar da yara da samari, sannan kuma akwai manyan makarantu na littattafai don ilimi mai zurfi. Har ila yau akwai wurare da dama na koyan sana’o’i daban -daban. Sannan a duk makarantun ana koyan karatun ne da harshen Hausa. Kuma har zuwa yau za ka ga irin wadannan makaratun a ko’ina a kasar Hausa. Wadannan makarantu su suka haifar wa da Hausa hanyar rubutunta na farko wato ‘Ajami’. Sannan kuma ta hanyar wadannan makarantu ne aka sami shugabanni da manyan ma’aikatan hukuma da alkalai da shahararrun malamai wadanda suka samar wa harshen Hausa nahawu da sauran sharuddan karatu da rubutunsa. Wannan babban aiki ya sa harshen Hausa shi kadai yake da salon rubutu nasa na kansa a cikin jerin harsuna na iyalin chadi (cambridge encyclopedia of language).

Farkon zuwan Turawa, wanda duk zai zo sai ya koyi harshen Hausa kafin y iso mana nan. Haka kuma su ma Turawan mulkin mallaka, duk wanda za’a kawo shi aiki a arewacin kasar nan ma sai ya koyi harshen ta yadda jama’a za su iya hulda da shi. Saboda haka da farko ma duk wani aiki da kuma wasu takardu na gwamnati da Hausa ake rubuta su, kuma da Ajami. Don dama haka suka tarar ana yi. A hankali aka fara rubutawa a gwame (Ajemi da boko). Daga baya sai aka daina rubuta ajamin, da tafiya ta yi nisa sai aka daina Hausar ma dungurungun, mukk koma yin komai da Turanci. llar wannan kama karya da ak yi wa harshenmu da al’adunmu shi ne, mu mun zauna ke nan da kayan aro. Tun daga makaranta, yaro ya zo karatu an nuna masa cewa harshensa na iyaya da kakanni, harshen jahilai ne saboda haka ba shi da amfani a makaranta. Harshen Turanci shi ne kawai za’a ya amani da shi wajen ilimi da bincike-bincike da neman abinci da ci gaban al’umma.

To, tun da ba yadda zai yi, sai ya koyi wannan bakon harshe. Wajen koyar harshen kuma, dole a koyi al’adu da dabi’u. Wato ke nan, duk wani mai son ya yi nasarar samun ilimi a wadannan makarantu dole ya zage ya koyi harshen Turanci soai, wajen yin haka kuma dole ya dauki al’adunsu da dabi’unsu. Ka ga, ke nan, idan aka yi sa’a ya kammala karatunsa ya kware, to shi ke nan an samu bakin Bature, kamar yadda mutanenmu sukan kira fitaffun yan boko. Shi ke nan an rasa wannan mutum, damin an riga an jirkita hanyar tunaninsa ta yadda in ba tunanin da Bature ya tsara ba, ba ya ganin komai da daraja. Inda abin ya yi zurfi, za ka ga irin wadannan mutane sun zama ba sa ko iya zama cikin al’ummarsu, ballantana su iya taimaka mata. Sai dai su zama shugabanni ta yadda za su hau kan jama’a da sunan jagora, bayan su kansu ba sa san inda hanyar da suke kai za ta kai su ba. Haka kuma wannan ita ta haifar mana da shugabanni masu sha’awa da kwaikwayon Turawa, har ta sa suka sace kudin jama’a su boya a turai.

Da yawa ba a gane nasabar lalacewar shugabanci da jirkitaccen tsarin ilimi da koma bayan harshenmu da al’adurmu ba. Mutum yana yi maka shugabanci; amma ya dauko harshe da al’ada ta wadansu ya lakaba maka. Kuma yana amfani da su wajen yi maka kama-karya da danniya da yaudara da cim amana. Irin wannan ta’asa ba za ta yiwu ba, idan mutane sun san yadda ake gudanar da al’amurra; wato a cikin harshensu da kuma tsarin da suka sani. To, amma shi Bature dama haka ya tsara kusan duk inda suka yi mulkin mallaka a duniya, irin wannan shirin suke yi. Su kafa makaranta su kawo littattafai wadanda suka rubuta, su kawo malamai, su debi ‘yan kasa su mai da su Turawa. Shi ke nan ko da an ce an ba ku mulkin kai ya zama bonono ne, rufin kofa da barawo. Irin wannan ilimi shi ne ya zame mana sarka ya dabaibaya mu muka kasa ci gaba sai ma baya muke yi da mu da harshenmu da al’adunmu. Gwamnatoci daban-daban kowa ya zo da irin nasa kirarin, arnma har yanzu an kasa gane cutar ballantana a samu magani. Wannan irin irin halin da muke ciki ke nan a yau. Yaya za mu kwaci kanmu. Wannan ita ce tambayar da muke dubawa a wannan zama.

Tarihin Ci Gaban Daulolin Da Suka Shude
Yanzu duniya tana ta ci gaba, ga shi mun kawo karshen karni na 20 (ashirin). Mene ne Hausa za ta yi don kasancewa daya daga cikin Harsuna na ci gaba a karni na 21 (ashirin da daya). Kamar yadda Hausawa sukan ce matambayi ba ya bata, sai dai mu ce Allah ya ba mu sa’a amin. Za mu iya samun amsar wannan tambaya idan muka yi nazarin tarihin wayawar duniyarmu ta yau, da kuma tarihin daulolin da suka shude. Misali, wayawar kan wannan lokaci namu, tushensa yana cikin kokorin da Musulmi da Larabawa suka yi na daga bayyanar musulunci a karni na (7 bakwai) zuwa karni na 13 (goma sha uku).

Kamar yadda na rubuta a wata makala da aka buga a mujallar ‘Hotline’ (May 30, 1987), “Ba sai mun bar harshenmu da al’adunmu na gargajiya sannan za mu fara aikin ci gaba ba’. Kamar yadda wani masanin tarihin Larabawa ya rubuta “A sakamakon saduwa da tunanin Larabawa (musulunci), da karin kaimin sake samun tsofaffin hikimomin Girkawa, kwadayin Turawa ya karu game da karance-karance da falsafa, wanda ya kai su ga karuwar ilimi nasu na kashin kansu, mai yawan gaske, wanda make cin amfani a yau. (Hitti). Daga sanin irin wannan tarihi za’a gane cewa, duk wata al’umma da take kwadayin daukaka wayawar kan dan’adam to dole ta zama gulbin karbar ilimin kimiyya da sana’a ta kyautata su da kuma tanadar da su don amfanin jama’a ta gaba. Tsakanin karni na 7 (bakwai) zuwa karni na 13 (goma sha uku) Larabawa (musulmi) sun zama gulbin kimiyya da falsafar Girkawa. Sun fassara kusan dukkan manyan ayyukan Girkawa a kimiyya da falsafa zuwa Larabci, suka kyautafa su suka kuma gabatar da su ga Turawa da wasunsu, wanda shi ne ya haifar da ci gaban wannan zamani na Turawan yamma. A wajen yin wannan aikin Larabawa ba su zubar da harshe da al’adunsu ba. Sun rike su sosoi. Suka kuma yi amfani da su wajen yin wannan gagarumar gudummuwa ga ’Yan Adam.

Cikin fitattun musulmi wadanda suka yi wannan aiki na fassara akwai irin su, Muhammadu lbn Ibrahim Al-fazzri (ca-806) wanda shi ne ya fassara wani littafin ilimin taurari wanda aka samo daga kasar Hindu, kuma wannan mutum shi ya fara zama fitaccen masanin ilimin taurari na musulmi. Bayansa, saa shahararren masanin taurarin nan AI-khawarizimi (ca 850) wanda ya yi amfani da littattafan Al-fazari da na Girkawa wajen kyautata ilimin taurari. Hake kuma Al-fadi Ibn Nawbakht (ca 815) shi kuma ya fassara aikace-aikacen mutanen Pasha a kan taurari, Shaihun masu fassara kuwa, shi ne, Hunayn Ibn Ishaq (ca 873), wanda shi ne Khalifa Al-ma’amun ya nada shugaban makarantarsa ta fassara. Sau da dama masu fassara sukan kware har su ma ta kai su ga bayar da gudummawa wajen kyautata ilimi. Yahaya lbn Masawayh (ca 857) wanda shi ya fassara wa Al-Rashid wadansu aikace-aikace a kan aikin magani, yana daya daga cikin masu irin wannan basira. Ta fuskar hada magunguna uban tafiya shi ne Jabir lbn Hayyan (ca 776) wanda ya rubuta kundin hada magunguna na farko. Haka kuma cikin fitattun marubuta a kan fannin magani wadanda suka biyo bayan masu fassarar farko, har da su, Ali Al-tabari da Al-Razi da Ali Ibn Al-abbasi Al-Majusi.

Shaihun masana, kamar yadda aka yi masa take a lokacin, Abu-Ali AI-Husayyn. Ibn- Sina shi ne wanda ya rubuta littattafai fiya da 200 (dari biyu) a kan falsafa da Addini da aikin magani da hisabi da ilimin taurari da ilimin harshe da kuma sauran sana’o’i. Fitattun littattafan sa da suka fi suna su ne; Kitab al-shifa (littafin warkarwa), wanda kundi ne na falsafa da kuma Qanun fi al-Tebb, ‘The Canon’ kamar yadda Turawa kan kira shi, wanda shi ma babban kundi ne na ilimin aikin lafiya. An fassara wannan littafi zuwa harshen Latin, sannan Turawa sun yi amfani da shi wajen koyar da likitoci har zuwa karni na 17 (goma sha bakwai). A cikin shekaru talatin na karshen karni na 15 (goma sha biyar) an buga wannan littafi sau 15 (goma sha biyar) Shi wannan littafi ya fi kowane dadewa ana amfani da shi a fagen aikin lafiya, a duniya.

A jerin su lbn-Sina akwai manyan malamai kamar su Abu Yusuf, Yakub lbn lshaq Al- Khindi da Muhammad lbn Muhammad lbn-Tarkhan Abu Nasr Al-Farabi wadanda su ma sun yi fice a fagen falsafa da hisabi da magani da siyasa da aikin ido da ilimin taurari da fasalta kida.

Wajen nazarin taurari an yi shaihunan malamai wadanda suka kiyasta yanayin taurari da duniyoyi da bigirensu, irin su Abu Abdullahi Muhammad lbn Ahmad al-biruni (ca 1050), da Umar al-khayya (ca 1124) wanda saboda tsananin sanin taurari da iya hisabi, ya yi gyara a kalandar Rumawa, ta kasance sai bayan shekara dubu biyar (5000) za ta rasa kwana daya a madadin kwana takwas da takan rasa a duk shekara.

Tarihi na nan cike da sunayan masana wadanda suka yi aikace-aikacen da a yau muke cin albarkacinsu. Duk da kokarin dakusar da sunayansu, duniya ba za ta manta da su ba. Ta fuskar ilimin addini akwai irin su Al-Numan Ibn Thabit Abu Hanifa (ca 767) da Malik lbn Anas (ca 795) da Muhammada lbn ldris Al-Shafi’i (ca 820) da Ahmad lbn Hanbali (ca 855). Ta fuskar Hadisi akwai su Muhammad lbn lsma’il Al-Bukhari (ca 870) da Muslim lbn Al-Hajjaj (ca 875) da Abu Dawud (ca 888) lbn Majah (ca 86) da Al-Nasa’i (ca 915) da Al-Tirmidhi (ca 892).

Ba za to yiwu mutum ya lissafa dukkan wadanda suka yi wannan gagarumin aiki ba, amma ban da wadanda muka fada a baya akwai wasu ma kamar su Jabir lbn Hayyan da Al-fargani da Thabil lbn Qurra da Al-Mas’udi da Al-Tabari da Abul wafa da Ali lbn Abbas da Abul-Qasim da lbn Al- Jazzar da lbn Yunus da Al-Karhi da lbn Al-haitham da Ali lbn Isa Al-Ghazzali da Al-Zarqali da lbn Rushd da sauran masana masu yawan gaske. Wadannan mutane sun yi aiki a kan fannoni masu yawa kamar labarin kasa da tarihi da siyasa da addini da hallitar dabbobi da halittar jikin mutum da gine-gine da Hadisi da shari’a da harsuna da shuke-shuke da wakoki da falsafa da labarai da fasalin kida da dai sauran fannonin ilimi.

Tushen Wayawar Kan Turawa Na Wannan Zamani
Bayan kwace birnin Toleda, a lokacin da daular Andalusiya (Spain) to fara kubucewa daga hannun musulmi, limaman kirista karkashin Arch Bishop Raymon, sun bude makarantar fassara inda aka yi ta aikin fassarar har zuwa karni na 13 (goma sha uku). An tara masana masu yawa daga kowane sashe na Turai, wadanda suka yi kusan shekaru dari da hamsin suna wannan aiki. Zuwa karshen karni na 13 (goma sha uku) kusan an fassara dukkan muhimman aikace-aikacen da musulmi suka yi, kuma an watso shi a kowane sashe na Turai. Wannan ta kawo mu yau, inda Turawa suke rike da tutar wayewar kan wannan zamani.

Nadewa
A nan ya kamata mu gane cewa, amfanin nazarin tarihi shi ne al’umma ta san inda ta fito, da inda take, da kuma inda ta dosa game da harkokinta na yau da kullum. Wannan kuwa sun hada da al’adunsu da addininsu da mulkinsu da ilimi da sana’o’i da siyasa da tattalin arziki da alakarsu da sauran jama’a. Sannan kuma a san cewa, muhimmin amfanin tarihi, kamar kowonne irin ilimi, shi ne aiki da shi. Ana nazari ne don a karu ta wajen fahimtar gaskiya da karya, Adalci da zalunci, kwazo da ragwanci, tattali da al’mubazzaranci. Wannan shi ne zai yi mana nuni da inda al’umma ta kai a nata kokarin; kuma shi ne ma’auninta na shahara ko gazawa gwargwadan kwazon da ta yi (Abubakar Dakaji). ldan muka dubi irin ci gaban da yake kewaya da mu a yau, ta fuskar ilimi da kere-kere, mu Hausawa da sauran mutanen nahiyar Afrika muna da jan aiki a gabanmu. Amma idan muka duba tarihi, kuma muka yi aiki da darasin da ya kunsa, to da ikon Allah; ba wani abu da zai gagare mu.

Misali a halin yanzu duk abubuwan taimakon mutum wajen tafiye-tafiye kamar su kekuna da babura da motoci da jiragen kasa da na ruwa da na sama duk ba mu da su. Kusan dukkan wadansu kayayyakin aiki na zamani wato injina da na’urori sai dai mu dogara da wadansu wajen kera su da kuma gyara su. Haka kuma, ba mu iya biya wa kanmu bukatu ta fannonin aikin lafiya da hada magunguna da gine-gine da ilimi da dai sauran bukatu na yau da kullum. Idan aka yi la’akari da wannan sai mu ga duk wani kirari na ci gaba da muke yi, dori-difiri ne, domin a jingine muke jikin wadansu.

Dago misalan da na bayar na farko muna iya gane muhimmancin harshe da al’ada wajen samara wa al’umma wayewar kai da ci gaba. Muddin harshe da al’ada ba ilimi a cikinsu to wadannan mutanen masu su ba yadda za su ci gaba domin dole su dogara da wadansu wajen samun biyan bukatunsu. Gwagwarmayar da take gaban Hausa shi ne a mai da Hausa harshen ilimi da harshen kimiyya da sana’a, ta zama harshen aiki da ci gaba. Wannan aiki ya shafi kowa da kowa. Shugabanni da masu kudi da sauran jama’a kowa zai bayar da irin tasa gudummuwar gwargwadon iko. Haka kuma wannan aiki na masu ilimi ne. Wato ke nan irin aikin sashen harsuna na wannan jami’a, da makamantan ta da kuma Hausawa da masu jin Hausa masana a fannoni daban-daban na ilimi da sana’o’i. Wannan gagarumin aiki ne ba na makaranta daya ko hukuma daya ko mutum daya ba. Ina ganin zai yi kyau a ce akwai kungiyoyi na masana kamar kungiyar masana aikin lafiya da lissafi (hisabi) da hadin magunguna da ilimin taurari da injiniya da siyasa da tattalin arziki, haka dai, a ce a kowane irin fanni a sami kungiyar Hausa wadda za ta yi kokarin habaka wannan ilimi a cikin harshen. Dole mu share wa marigayi Abubakar Imam hawaye mu sake kafa wani ofishin fassarar, a Zariya da sauran wuraren da suka cancanta don ci gaba da aikin wallafe-wallafe, daga inda suka tsaya. Idan har muna son ci gaban a karni mai zuwa, to dole mu zage dantse mu kawar da jahilci daga cikin harshenmu. Yin haka ya zamo wajibi damin ba za ta yiwu a dogara ga gwamnati wajen aiwatar da wannan aiki ba.

Gwamnatin wannan zamani, kamar sauran na bayanta, tun zuwan Turawa, ita ma Baturiya ce. Sabada haka dole mu yi damara mu fara canjin da kanmu, a hankali, har ta kai mu ga canja gwamnatin ita kanta, yadda za ta dace da bukatunmu.

Wannan manufa tawa ba sabuwa ba ce domin masana da dama sun jawo hankalin jama’a a kanta. Sai dai da yake ni na fito ne kururu ba kamar yadda manyan malamai sukan yi ba, wato a sakaye.

Za a fahimci irin wannan ra’ayi idan aka duba makalar Marigayi Waziri Junaidu wadda ya gabatar a lokacin da aka ba shi digirin girmamawa a wannan jami’a. Shaihun Malami Abdullahi Smith, wanda sunansa ne aka sa wa wannan dakin taro don girmamawa, ya yi irin wannan fadakarwa a cikin shahararriyar makalarsa da ya kira “Muhimmancin akidar ilimi ta jihadin Shehu Danfodiyo a wannan zamani”.

Haka ma Shaihun Malami lsma’ila Tsiga, ya yi irin wannan hasashe a makalar da ya gabatar a taron shugabannin makarantun sakandare wanda aka yi a Katsina a 1993, Wannan makala, kari ce a kan irin wadannan kiraye-kiraye, wadanda na san akwai su da dama, da fatan Allah ya sa a amsa kiran. Sannan kuma a yi aiki da shi, Amin.

Alhamdu Lillahi. Wasalamu Alaikum wa Rahmatullahi Ta’ala wa Barakatuhu.

Friday, June 15, 2007

SU WA MUKE Yl WA RUBUTU?

Ibrahim Malumfashi, Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usman Danfodiyo, Sokoto

An gabatar Da wannan Takarda a Taron Shekara-shekara Na Kungiyar Marubuta Ta Kasa Reshen Jihar Kano, a Dakin Taro Na Dakin Karatu Na Murtala Muhammad, Kano, 31 ga Watan Janairu, 2003


1.0 Gabatarwa
Harshe kamar yadda aka sani, shi ne injin din aiwatar da duk wani tunani na kowace irin al’umma. Shi ne ke tafiya da al’adu da adabi da ma duk wani ilimi na rayuwar dan Adam, a ka ne ko kuma a rubuce. Kila wannan dama cc ta sa ake ba harshe muhammanci, ta yadda wadanda ba su da shi sukan kasance nakasassu, wadanda kuma suke amfani da wani abu makamancin sa, ake musu kallon wadanda ba su cika ba a cikin al’umma. A nan ina magana ne kan bebaye ko kuma masu kama da su da kuma masu amfani da hito a matsayin hanyar sadarwa a tsakanin mutane, misali al’ummar Mazatec da ke kasar Mexico, haka wannan yanayi yake ko a cikin rubutaccen harshe. Duk wadanda ke da hanyar rubuta harshensu, an yi musu kallon wadanda suka ci gaba, suka fi sauran al’ummomi na duniya wayewar kai da sanin abin da duniya take ciki. Wannan shi ne fasali na farko da aka fara amfani da shi wajen gane bambancin da ke tsakanin Turawa da bakaken fatar Afirka, dab da za a yi mana mulkin mallaka. Rubutu, ko kuma in ce harshe shi ne ya sanya wa Turawa ji da kai da kuma tokabo, har suke ganin cewa ba wata hujja da bakaken fatar Afirka za su kyamace su dangane da zuwan su nahiyar a madadin ‘yan jari hujjar wancan lokaci. Ba sai an fada ba, harshe a magance da kuma rubuce ya kara gibi tsakanin Turawa da mutanen Afirka, domin kuwa ko da alburusai da bindigogi da suka yi amfani da su wajen cin wannan nahiya, daga cikin rubutaccen harshe aka samo tunanin.

Saboda haka ko da masana irin su Janh (1963) ke bayanin cewa, ai ko da Turawa suka zo Afirka sun iske mu da wayewar kanmu da tunaninmu da kuma ci gaban zamani irin namu. Shi kuma Rodney (1973) ya kara jaddawa ta hanyar cewa ai zuwan Turawan ya dakushe ne a maimakon ya taimaka wajen ciyar da nahiyar Afirka gaba, kuma ko kafin zuwan Turawa akwai wasu al’ummomi da suke da harshensu a rubuce, akwai kuma wadanda ke da hanyar sadarwa ta gargajiya, irin ‘yan ma’abba da kuma kida da ganguna ko makamantan haka, wannan ba ta nuna mana irin yadda tunanin jama’ar ya kasance ba a zahiri. Domin kuwa mulkin mallaka abin da ya mayar da hankali shi ne sanya mutumin Afirka ya dinga tunani da rubutu a cikin harshen da ba nasa ba, a cikin harshen da zai sanya ya dinga ci gaba da mulkinmu ko da kuwa bayan ya nade tabarmarsa da tsawon shekaru.

Wannan shi ne a halin yanzu ke faruwa a yawancin kasashen da ake yi wa lakabi da masu tasowa ko kuma wadanda ba su ci gaba ba, ba wai a nahiyar Afirka kadai ba, har da sassan duniya da makincin mulkin danniya da mallaka ya shiga cikinsu ya yi kaka-gida. Shi ya sa yau kasar Ingila da masu magana da rubutu da harshen Ingilishi a matsayin harshen uwa ba su wuce ka kwana ka kirge su ba, amma kuma masu magana da Ingilishi a duniya sun fi kowa yawa a doron kasa, shi ya sa ma ake wa harshen lakabi da harshen duniya, ni ko na cc ko dai harshen danniya!
Na fadi haka ne saboda sanin irin yadda tunani da Ingilishi da rubutu da Ingilishi yake nakasa kowace al’umma da ta ba wannan abu niuhimmanci. Ba yadda za a yi al’umma ta ginu ta kuma ci gaba ba tare da kare harshenta da kuma rubuce-rubucenta ba, duk irin yadda mutum zai yi ya ciyar da kasarsa gaba ta hanyar amfani da ilimi da ke cikin littafin da ba a harshensa yake ba, zai kasance cikin matsala da kuma kunci, domin zai zamanto mai yaki da tunani iri biyu, na baki da kuma nasa na gida, wannan na daga cikin abubuwan da suka cunkushe harkar iliminmu da kuma halin da ilimin yake ciki a yau. Wannan abu da muke fama da shi yau, shi ne kuma Turawa suka yi fama da shi tsakaninsu da Larabci, a lokacin da Larabcin yake cikin ganiyarsa. Kusan duk wani ilimi na kimiyya ko fasaha ko kuma na ci gaban al’umm a Larabce yake, kuma dole ta sa Turawa suka yi amfani da nakaltar Larabci don cin moriyar ilimin da ke kumshe a cikin littattafan Larabawa da ke mulkin duniya a wancan lokaci. Daga baya ne Turawa suka fahimci cewa ai yawancin ilimin da Larabawa ke takama da shi su ma sun kwaso wasu ne daga littattafan Girkawa, don haka suka yi watsi da na Larabawa suka koma wa na ainihin, ta haka ne mallakar da Larabawa suka yi wa duniya ta subuce ta koma ga Turawa, musamman na Ingila. Wannan ba wani abu ya nuna mana ba sai cewa gadon gida halal ne ga raggo. Ba ta yadda za a kai ga kololuwar ilimi da ci gaba ta amfani da bakon harshe, domin kuwa komai iya nakaltar harshen wasu da ka yi, ba za ka taba zama kamar su ba, kuma za ka kasance ne a kullum kana magana da su bakin, ba mutanen cikin gida ba, domin kuwa kashi 7 cikin 10 na mutanenmu ba su san da wannan bakon harshen ba, idan kuwa haka ne, to mu da wa muke magana a rubuce-rubucenmu? Shin marubutan baya haka suka yi? Yaya tasirin wannan abu yake ga ci gaban mu da al’ummarmu da kuma kasarmu?

2.0 Ko Kafin Ka Ga Biri....
Su kan su Turawan mulkin mallaka sun san irin da Larabci ya yi wa sauran harsunan duniya kafin su durkusar da shi, su maye gurbinsa da nasu, shi ya sa duk inda suka sami kan su a matsayin masu mulkin mallaka, a Afirka ko Asiya ko Amurka ba su yi wasa da cusa tunaninsu da kuma akidojinsu ga al’ummomin da suka ci karo da su ba. Sun yi haka ne da sani, domin ta haka ne kurum za su iya yin zaman darshen a cikin harkokin kasashen da suke yi wa sukuwar salla a wancan lokaci. Shi ya sa tsarin ilimin nasu da littattafan da suka shigo da su domin horaswa, suka kasance cikin harshen ‘yan mallakar, a wasu wurare suka matsa sai a yi komi tamkar a Turai, a wasu wuraren kuwa a kaikaice, wasu kuma ba ka iya bambanta su da masu mulkarsu ta kowace irin fuska, dubi Amurkawa ka kwatanta su da mutanen Indiya ko Pakistan da kuma bakaken fatar Afirka, musamman a tsakanin inda Faransa ta yi turke da kuma inda Birtaniya ta kafa tata lemar. Ma ana, wannan rarrabuwar ita ce ta taimaka wajen gane illar mulkin mallaka da kuma yadda aka rarraba kawuna domin a ji dadin mulki. Bisa wannan tafarki ne Leopord Senghor na Senegal ke nuna bakin cikinsa game da irin ilimin da ya samu ta hanyar Turawan Faransa, yana cewa: A lokacin da nake fafutukar karatu a gida da waje, ‘yan uwana da na bari a gida ba su yi boko ba, sun kasance ‘yan kasa na gari, ni kuwa a kullum da na bar firamare na shiga sakandare, na wuce zuwa jami’a, sai kara hannun riga na yi da al’ummata da kuma kasata. A kullum sai na kara sanin tarihi da yanayin kasashen Turai, ina kuma kara jahilcewa game da tarihin al’ummata da kuma kasata. A lokacin da na dawo gida daga Faransa, sai na ga na kasance bako cikin jama’ata, tsararrakina da na bari ba su yi karatu ba, suka kasance malamaina.

Wannan haka ya kasance dangane da marubuta da shugabanni a nahiyar Afirka, musamman wadanda suka kasance karkashin mulkin Faransa. A bangare daya kuwa, wadanda suka zauna cikin inuwar mulkin Birtaniya ba haka abin ya kasance ba, ga wasu, kamar yadda Mista East ya bayyana game da Abubakar Imam a matsayinsa na marubuci, ya cc:

Ya kasance daya daga cikin ‘yan kalilan da ya kasance duk da cewa ya sami iliminsa ta hanyar horaswa cikin Ingilshi da littattafan Ingilishi, daga kuma Turawan Ingilishi, bai yi watsi da harshensa ba, domin kuwa yana bayyanar da tunaninsa cikin harshen nasa, ba cikin Ingilishi ba kamar yadda saura ke yi.

Me ya bambanta Senghor da Imam? Ba wani abu da ya ya wucc cewa shi Imam bai yarda Ingilishi ya kasance masa harshen tunani ba, ba ma Ingilishi kadai ba, kusan duk wani harshe da ya ci karo da shi a lokacin da yake nadar ilimi da ya gina masa rayuwa. Shi kuwa Senghor ya tashi ne cikin wani tsari da ya fifita tunanin Faranshi bisa na bakar fata, haka al’adu da addini da kuma tsarin ilimin baki daya. Bai sami damar bambance barcin makaho ba ko kuma duma daga kabewa, ba don komi ba kuwa saboda irin yadda ak rene su tun daga gida.

Imam ya sami ilimin addini mai zurfi ko kafin ya hadu da Bature da makircin da ya shigo da shi, saboda haka bai yarda wani makiri ya yi masa wayon wanikiki ba, tun yana karami. Ko da ya shiga dakin ajiyar littatafai na makarantar Midil a Katsina domin ya yi nazarin da zai shiga gasar kaga littattafai da aka shirya a 1933, bai yarda ya yi amfani da duk abin da ya ci karo da shi ba, sai ya karanta, ya auna da abin da addininnmu da kuma tadojinmu na kwarai suka aminta da su, sa’annan yake kattaba shi a cikin nasa aikin, kuma bai taba yarda da tasirin bakin al’adu ko addinai sun ja masa akala ba. Haka su Tabawa Balewa da Ahmadu Bello da Aminu Kano da Sa’adu Zungur da wasu da dama, kuma wannan shi ya haifar da akidar nan ta NEPU da neman canji a wannan yanki da muke ciki.

Bari mu yi bitar wasu daga cikin ayyukan Imam, mu gani ko za mu iya samun haske dangane da irin abubuwan da aka yi a da, kafin mu koma ga shin mu wa muke yi wa rubutu?

3.0 Sai Gida Ya Samu…
A cikin ayyukan da Abubakar ya yi na adabi ba wanda ya zauna ya shirya a cikin ransa da nufin ya nishadantar ko ya burge ko kuma dai a san da shi a cikin harkar rubutu ko kuma rayar da ilimi. Bai yi haka a lokacin rubuta Ruwan Bagaja ba, duk da cewa a lokacin da ya yi rubutun yana da shekara 21 a doron kasa. Ko da ya shiga dakin ajiyar littattafai na makarantarsu domin ya sami samfur na irin yadda zai tsara labarin nasa, ya kuma ci karo da littafin The Water Of Cure na ‘yan uwa Grimms, ba haka nan ya bi shi ya kwashe komi da komi ba kamar yadda labarin yake a kasar Jamus, tun asalinsa, sai da ya bi ya yi masa kwaskwarima ya debe al’adun Jamusawa, ya shigar da na Hausa, ya cire addinin kiristanci ya shigo da Musulunci. Da wannan ne kuma ya shiga cikin littafin Alfu Lailah ya debo hikayar Abdussamad da ‘yan uwansa, ita kuma ya kwashi wani gefe da ya dacc da tunanin malam Bahaushe ya jefa a cikin Ruwan Bagaja, ya yi watsi da tadar Larabawa da ya san cewa ba ta da wani alfanu ga mai karanta Hausa. Ya kuma shiga cikin gonar adabin baka na Hausa inda ya tsamo tatsuniyoyi da labaran Hausa da suka yi tashe a wancan lokaci ya gina zubin littafin. To amma ba inda ya fi fiddo da tsarin kyautatawa fili irin yadda ya nemi Malam Zurke da Alhaji Imam daga rayuwa ta yau da kullum. Shi dai Zurke wani mahaukaci ne da aka yi a cikin birnin Katsina, Alhaji Imam kuwa marubucin ne, amma kuma wadannan mutane a zahiri ya same su ne daga littafin Maqamatul Hariri, inda Harisu da Abu Zaid suka taka rawa irin ta Zurke da Alhaji Imam, sai dai su Harisu dabarun da wayon wanikiki da suka yi a cikin Maqama cike suke da al’adun Larabawa, dole ta sa Imam ya mayar da su na Hausawa, cikin ban dariya da sosa rai

Idan kuma muka dubi Magana Jan Ce (1-3) sai mu ga cewa nan Imam ya nuna gwanancewa fiye da a Ruwan Bagaja, ko ba komi a nan ya san da wa yake magana, ya kuma san dalilin yin rubutun da abin da yake son rubutun nasa ya yi ga wadanda aka yi wa rubutun. Tun da farko, nan ba gasa ba ce, an nemi a yi rubutu ne don yara ‘yan firamare, domin a samar musu abin karatu da kuma tarbiyya. Nan ma Imam sai da ya nemi samfur da zai gina nasa tunanin, amma kamar kullum sai da ya canza wa duk wani tubali da ya tsinto daga wasu wurare sifa ko kuma kama, don su dace da yara ‘yan kasar Hausa. Ya dubi tsarin Alfu Lailah, ya gina budewar Magana Jari Cc, ya kuma yi amfani da littafin The Parrot ya gina batun Aku mai Magana, ya nemo Andersen Fairy Tales da Aesop Fables da Grimms Fairy Tales da kuma tatsuniyoyin Hausa domin su kasance masa ‘ya’yan da ke tafiya da uwar labarin Magana Jari Ce. Ya yi haka ne cikin tunanin makarantarsa, duk inda ya hadu da maganar barayi sai ya yi huduba kan sat da rashin kyan sat, yana kuma bayyana cewa bai son bayar da labarin barayi ba don komi ba sai don gudun kada yara su sami abin kwaikwaya, kuma duk inda ya kawo labarin barayi to bai barin su yi nasara. Kai ba wannan kadai ba, duk inda aka yi mugun abu sai ya nuna horon da aka yi wa wanda ko wadanda suka yi mugun abun, kamar yadda ya fada a cikin tarihinsa, East ya koya masa cewa kada ka yarda ka bar mugu ya yi nasara a cikin gina labarinka, domin tasirin barin haka zai iya rusa al’umma. Wannan shi ne ke cikin zuciyar dukkan ayyukan adabin da Imam ya gina a cikin Magana Jari Ce. Inda ya ji ana maganar itaciyar yeuw (mai kwankwamai) sai ya mayar da ita itaciyar tsamiya. Gidan Turawa na ginin bene, ba zaure don baki da sa kwat da duk wasu abubuwan jin dadi nà rayuwa, irin na Turawa, canza su yake yi da na Hausawa, bai yarda bakon malam Bahaushe ya shigo har cikin gida ba, domin masaukin bako ai zaure ne in ji Hausawa. Haka abinci da abin sha da abin hawa da sauran makamantan su, ba don komi ba sai don wadanda yake wa rubutun su karu da ilimin da ke ciki da kuma inganta kyawawan al’adu.

Imam bai yarda ya bar mugu ya sha ba, bai bar azzalumi ya wuce da zaluncinsa ba, bai kuma bar kunci ya tabbata a cikin rayuwa ba. Duk yadda zai yi ya nuna wa yara kyau da rashin kyawun abu, shi ya bi ya gina tunanin nasa adabin, wannan kuma har yau har kwanan gobe ayyukan nasa suke kasancewa kamar yau ne aka yi su duk da cewa sun yi fiye da shekaru saba’in da da dabbakawa. Darussan da ke ciki har yau suna da tasiri a rayuwar jama’ar yau din ba wa sai na jiyar ba, za su kuma ci gaba da wanzuwa a haka har gobe.

4.0 Kai Wa Kake Wa Rubutu?
Tambayar da kila wasu ke faman yi har yanzu ina jin ba ta wuce to mu wa muke wa rubutu? Kanmu ko gwamnati ko talakawa ko masu ilimi ko kuma madaidaita ilimi ko kuma dai kowa da kowa? Kafin na bayar da wannan amsa, zan so dan mazaya tukun, domin ta haka ne nake jin cewa za mu sami haske game da irin rubutunmu da wadanda muke wa.

Ko da aka gayyace ni da in ce wani abu a wannan taro, na amsa cewa zan zo ne, amma idan an aiko man da takardar gayyata, ba wani abu ya sa na dage kan haka ba sai don ina son in ga inda masu shirya taron suka sa gaba, domin kuwa tun ranar da na cika shekara 40 a watan Oktoban da ya wuce, na sha alwashin cewa ba zan sake mu’amala da Ingilishi ba. Na kuma sha wannan alwashi ne da nufin ganin na bada tawa gudunmuwa wajen kara habaka harshe da adabi da al’adun Hausawa gaba. Ban ce ba na bada gudunmuwa a inda aka fito ba, amma sai na fahimci cewa duk tsawon lokaci muna maganar bebaye ne, ba mai jin abin da muke fada da harshen Ingilishin, ni kuma ga shi ba don neman suna nake abin da nake yi ba.

Taro in na raya adabi ne, rubutu in na raya adabi, magana in ta raya adabi ce, in ni ne zan je ko zan yi ko kuma zan ce, to da Hausa zan yi, sai dai a yi mani aikin gafara.

Da na sami wasikar gayyatar na gan ta cikin Ingilishi sai na ce to wannan ba da ni za a yi ba, karanta takardar ne ya canza mani ra’ayi, domin an ce in yi laccar cikin Hausa, abin da ya kawo ni ke nan.

Kila wasu su ce ai ba sai na bi wannan mataki ba, in yi wake-wake mana, wato in an dama da Ingilishi in sha, in kuma an dama da Hausa in sha. Ba zan iya haka din ba. Ba don komi ba sai don ina son in san wadanda nake wa rubutu. Ba kuma wanda nake wa rubutu face malam Bahaushe. Saboda haka ban ga dalilin da zan zauna ina magana da Bature ba. Ina amfanin badi ba rai.

Kai da ke nan tare da ni a yau wa kake yi wa rubutu? Bahaushe ko Bature? Idan da malam Bahaushe kake magana ko kuma rubutu, to ya dace rubutun nan naka a cikin a cikin jarida ko mujalla ko kagaggen labari ko waka ko kuma wasan kwaikwayo ne ka gwanancc to ya kasance a cikin hasrshen da mutanenka za su gane, za su fahimta, za su kuma yi aiki da shi. A da ban dauki wannan da muhinmanci ba sai da na rubuta From The Eyes Of My Neighbour a 1992, na saki littafin a kasuwa a kan Naira 10 kacal, na rarrabar da dubbai kyauta domin sakon ya kai ga jama’ar da nake jin za su amfana da shi, yau sama da shekara 10 da fitar littafin, ba wanda ya kama ni ko ya ce da ni uffan, duk da cewa zagi da batunci da neman tashin-tashina su ne jibge a cikin littafin. Gwainnatin da wasu ke ganin cewa za ta sa kafar wando da ni ko bihim ba ta ce ba, ba don komi ba sai don wadanda nake bukatar su tashi su yi boren daga zaluncin da ake tafkawa a cikin kasar, ba su ma san da littafin ba. Amma da na rubuta wakar Jigida Ta Ta Tsinke, na rera ta a gaban jama’a a shekarar 1995, ba a yi kwana bakwai ba sai da na yi bakin dare da kuma aka buga a cikin jaridar Nasiha, sai da aka nemi na yi bayani a gaban jami’an tsaro, ba wani abu ya jawo haka ba sai zakin harshen da na yi amfani da shi da kuma damar da harshen yakc da shi na isa ga wadanda ake son bayanin ya isa gare su. A wannan lokaci ne na fara fahimtar wadanda ya kamata in yi wa rubutu na.

Da kurna muka kwashe shekara muna ta hadiyar miyau tsakanina da Abdalla da Sheme sai na fahimci cewa muna jifa ne a cikin duhu, su wadanda ake yi domin su ba su san ana yi ba, idan kuma sun sani, ba abin da za su iya yi, domin dogon Turanci ne kurum ake ta faman yi, domin haka a kai kasuwa. Wannan ma ya sanya man tunani game da shin wa nake yi wa rubutuna.

Saboda haka kai da ke nan wa kake wa rubutu? Mutumin Garun-Ali ko kuma Yorkshire ko Manchester? Kai da ke ta fafutukar rera wakar Ingilishi, kai da ke Ni tsara da kuma aiwatar da wasan kwaikwayo cikin Ingilishi, kai da ke ta faman zayyana labarai cikin Ingilishi, kai da ke ta faman rubutu cikin jarida da harshen Ingilishi, kai da ba ka da abokiyar hira irin jarida ko mujallar Ingilishi ba ruwanka da na Hausa, shin wa kake taimakawa? Malam Mande da ke Kaura-Namoda ko kuma Clement da ke Bradford. Kai da ke faman sai ka wallafa littafi cikin Ingihshi. Don me kake wannan hankoro, domin kedafare ko kuwa don a san ka a Ingila ko Amurka, ba ruwanka da kasar Hausa? Me ya sa kake rubutu? Wa kake wa rubutun? Wace ribar kake nema? Ni dai ba zan ba ka amsa ba, amma na san tawa, sai ka yi tunani, idan mun hadu a wani jikon, zan so in san wa kake wa rubutu? Sai dai fatata ita cc, mu hadu a taron Kungiyar Marubuta Ta Jihar Kano, ba taron ANA ba. Na gode.