Monday, November 5, 2007

Tarihin Hausawa:

Addinin Gargajiya da Hanyoyin Yada Labarai da Kayan Sawa da Al’adu da Sana’o’i da Muhalli da kuma Tattalin Arzikinsu


Asalin Hausawa abu ne da aka sha kuma ake kan tambaya a kullum, sai dai abin takaici har yanzu ba a sami wata cikakkiyar amsa mai gamsarwa ba. Kafin mu yi nisa ya kamata mu san ko su wane ne Hausawa. Hausawa dai su ne mutane wadanda harshensu shi ne Hausa sannan dukkan al’adunsu na Hausa ne. Haka kuma addinin musulunci ya yi cikakken tasiri a kansu.

Mutane dabam-daban sun yi bincike sosai a kan ilmin harsuna da abubuwan da aka kattaba da kuma zantukan baka. Ta hanyar irin wannan bincike ne aka gane cewa wadansu harsuna suna da kama da juna ainun, wanda ya haifar da kara zurfafa nazarce-nazarce. Sakamakon haka ne kuwa aka karkasa harsunan Afrika ta yadda kowane kaso ya kunshi harsuna wadanda bisa dukan alamu tushensu guda. Ma’ana a asali su wadannan harsuna harshe ne guda daya wanda wasu dalilai irin su bambancin wurin zama, sanadin kaurace-kaurace da yake-yake da dai wadansu dalilai suka sanya ya karkasu ya kasance harsuna iri-iri a halin yanzu.

Akwai dangunan harsuna da dama a cikin Afrika. Misali akwai dangin Bantu a can wajen tsakiyar Afrika wadanda tushensu duka daga wani tsohon harshe ne wai shi Bantu; akwai kuma dangin Kwa wanda ya kunshi Yarabanci da Ibo da Nupanci da dai sauransu. Ita kuwa Hausa tana cikin harsunan iyalin Cadi. Ko da yake shi wannan harshe babu shi a yanzu, wannan suna na Cadi suna ne kawai da masana ilmin harsuna suka kirkiro. Dalili kuwa shi ne yawancin iyalin wannan harshe ana samunsu a farfajiyar tafkin Cadi. To saboda rashin sanin ainihin sunansa sai aka kira shi da sunan Cadi. Harsunan iyalan Cadi suna da yawa. Akwai Angas da Bacama da Bade da Bolanci da Bura da Hausa da Kanakuru da Karekare da Mandara da Margi da Miya da Ngizim da Tera da dai sauransu. A sakamakon kamanni da wadannan harsuna suke yi da juna ya sanya aka danganta su ga tushe guda.

A bisa wannan dan bayani muna iya cewa Hausawa da harshensu sun fito ne daga cibiya daya da sauran harsunan iyalin Cadi. Wannan kuwa zai ba mu damar cewa mutanen da suka zama Hausawa sun fito ne daga Gabas ko arewa maso gabas da wurin da suke a yanzu

Daga nan sai mu duba abubuwan da aka kattaba. A nan an samu mutane dabam-daban sun yi rubuce-rubuce a kan asalin Hausawa da harshensu. A wani littafi da ya wallafa a kan Daular Usmaniyya, Johnston ya bayyana cewa a tsakanin shekarar 1050 zuwa 1100 ta Miladiyya wadansu, Berbers, (Buzaye) sun ratso sahara suka zauna cikin Tukururu kuma suka yi auratayya da su. Wai a sanadin wannan cudanya ne aka sami Hausa da harshen Hausa.

Shi ma wani marubucin dangane da tarihin Hausawa da harshensu, M.G. Smith, yana da ra’ayi kusan iri daya da na Johnston. Wato ya amince da cewa akwai kaura da ta auku daga gabas zuwa kasar Tukururu, wanda ya yi sanadin samuwar Hausawa da harshensu. Ya kare da cewa wannan kaura ta auku ne wajajen shekarar 1350 ta Miladiyya.

Shi kuwa Abdullahi Smith nuna rashin amincewarsa ya yi da wannan bayani da aka yi dangane da asalin Hausawa da harshensu. Musamman ma cewa wai nan da shekara dubu da suka wuce babu Hausawa. Shi yana ganin cewa kasa rarrabewa tsakanin asalin Hausawa da harshensu da kuma asalin daular mulkin da suka kafa shi ne dalilin rashin fahimtar. Haka kuma bai amince ba da cewa Hausawa sun samu a sakamakon auratayya tsakanin Berbers (Buzaye?) da kuma Tukururu da suka taras a wurin. Hasali ma ra’ayinsa ya fi karkata ga cewa Hausa tana da alaka da harsunan iyalin Cadi, har hakan ma kuwa yana ganin cewa sun raba hanya shekaru dubbai da suka wuce.Ya kuma kara da cewa mai yiwuwa da can akwai dangantaka tsakanin harshen Berber da na Cadi, wato tun kafin Sahara ta zamo hamada.

Babu shakka ba abu ne mai karbuwa ba a ce nan da shekaru 950 da suka wuce babu Hausawa da harshensu, musamman idan aka dubi tarihin garuruwan Hausa da jerin sarakunan da suka mulke su. Misali an ce tun karshen karni na 9 na Miladiyya wadansu maharba suka zo suka zauna a duwatsun da ke kewaye da sararin da ake kira Kano yanzu. Idan haka ne wannan ya nuna cewa akwai Hausawa a wannan wuri fiye da shekaru 1,000 da suka wuce.

Addinin Gargajiya na Bahaushe

Adinin gargajiya wata hanya ce ta bautar da mutane dabam-daban kan sama wa kansu. Babu wata kabila da za ta bugi kirji cewa ita ta koya wa wata bauta wa (Ubangiji). Kusan kowace kabila nan take take ta kago hanyoyin bautarta. Wadannan hanyoyin bauta ana ganin sun samu tun farkon samuwar dan’adam. Masu binciken tarihi na ganin cewa makasudin bautar gumaka shi ne ganin cewa wasu abubuwa kamar rana da wata da kogi ko duwatsu suna yi dabi’a irin ta mutum wato in an faranta musu rai su ji dadi in kuma an bakanta musu su yi fushi. Masu bauta wa kogi ana ganin sun yi imani da shi ne saboda ganin cewa wani lokaci sai ya yi ambaliya su sami amfani mai yawa, wani lokaci kuma ya bushe. Daga ya bushe sai masu bautar su dauka cewa sun yi wani laifi ne, sai a sami wani babbansu ya kasance mai yin magana da gunkin, shi kuma zai rika gaya musu sakon gunki. Makasudi na biyu da ake zaton ya sa mutane yin bautar gunki shi ne ta wajen ciwo. Wani lokaci ciwo kan kama mutum a yi ta magani a rasa yadda za a yi ciwon ya warke. To, in aka yi katari wani ya zo ya ba da magani majinyacin ya warke, sai a dauka cewa wannan mutumin yana da wata daraja ta musamman. Saboda haka duk abin da ya faru, shi za a dosa, shi kuma ya rika dangana cuce-cucen da iskoki. Ta nan ne sai mutane su yi imani da iskoki.

Tun da yake za a yi magana ne a kan addinin gargajiya na Bahaushe, ya kamata a dan bayyana wasu misalai na tsafe-tsafen Hausawa a lokacin da suke yin Maguzanci da kuma barbashin tsafe-tsafen har zuwa yau. Amma tun da ba Bahaushe ne kadai yake yin irin wadannan tsafe-tsafe ba, za a bayar da takaitaccen misalin bautar gumaka a wasu kasashen. Misali a kasar Masar suna da nasu gumakan kafin zuwan musulinci, sanannu daga cikin gumakan su ne Ra da Osiris. Ra shi ne gunkin rana shi kuma Osiris shi ne mai kula da kogin Nil, kogin da shi ne kashin bayan rayuwar mutanen Masar. Idan muka matso wajen makwabtanmu za mu ga cewa Ashanti na kasar Ghana su ma suna da sanannen gunkin da suke kira Abosomi. Yarabawa kuma suna da Orisha. Orisha din nan shahararren gunki ne wanda Yarabawa ke wa bauta sosai. A duk lokacin da suka ga wani abu ba ya tafiya daidai, sai manyansu su kai kukansu ga wannan gunki. Daga nan sai a yi yanke-yanken dabbobi don Orisha ya sha jini. Da an ga wani canji sai a dauka cewa Orisha ya yarda. Mutanen Jukun ma suna da nasu gunkin da suke kira Jo. Barebari kuma na da nasu gunkin da suke kira Sanama. Kabilar Tangale da ke Bauchi ma ba a bar su a baya ba wajen bautar gumaka, suna da babban gunkinsu da suke kira Yeku. Ban da babban gunki Yeku akwai kuma kananan gumaka a kowane gida da ake bautawa, haka kuma a kowace unguwa.

Daga wadannan bayanai da aka yi za a fahimci cewa addnin gargajiya ya mamaye kasashe da yawa kafin zuwan addinin Almasihu da na musulunci. Kuma kusan kowane irin addinin gargajiya, sai an sami wani mutum wanda shi ne mai wucewa gaba don nemo bayani daga gunkin sa’annan ya sanar wa da mabiya.

Tun da yake an dan ji bayanan addinan gargaji na wasu mutane, sai kuma mu tsunduma ga na Hausawa. Hausawa ma kamar sauran mutane suna da addininsu na gargajiya tun kafin zuwan addinin musulunci. A gaskiya ba wanda zai ce ga lokacin da Hausawa suka fara bautar gumaka da tsafe-tsafe. Tarihi ya nuna cewa tun da aka halicci dan’adam, bautar iskoki ta cusu a zuciyarsa. Wannan shi ya sa yake da wuya a bayyana tun sa’ad da abin ya fara. Dalilai na biyu da ake jin su suka haifar da addinin gargajiya, ba kuma ga Hausawa kadai ba har ma da sauran jinsi iri-iri na duniya. Dalili na farko shi ne, shi dai dan’adam ya dauka cewa kowane abu a duniya yana dabi’a irin tasa, wato wani lokaci zai ji dadi musamman in an faranta masa rai, ya kuma ji zafi in an bakanta masa, har ya kai ga ramuwar gayya. Alal misali, lokacin da Kanawa ke bautar Tsumburbura a gindin Dala, zamanin Barbushe, duk shekarar da ta zo da wani bala’i sai mutane su dauka cewa lallai an saba wa Tsumburbura. Saboda haka sai a yi yanke-yanken awaki da karnuka don dodon ya sha jini wai ko ya huce. To wasu lokutan kuwa sai a yi sa’a abin ya yi sauki shi ke nan sai a dauka wannan sauki ya faru ne saboda yanke-yanken da aka yi wa gunkin ne.

Dalili na biyu da ake zaton shi ma ya taimaka wajen kago bautar gumaka shi ne ciwo. Sau da yawa akan sami ciwo ya ki ci ya ki cinyewa ga mutum, a yi ta neman magani, amma a banza, sai a dauka ba mai warkar da majinyacin sai dai mutumin da Allah ya yi wa wata daraja ta musamman. Ana nan har a sami wani boka ya nuna cewa iska kaza ce ta taba mutum amma shi zai warkar da shi. Idan aka yi katari sai kuwa mutumin ya warke. Da zarar haka ta faru fa sai mutane su yi imani da wannan iska da boka ya ambata, shi kuma boka kasuwa ta bude ke nan.

Ana yin bauta ta hanyoyi dabam-daban. Wasu sukan sassaka gunkinsu da kansu, su yi wani mutum-mutumi su rika bauta masa. Wasu kuma sukan bauta wa iskokai.

Dangane da bautar gumaka wajen Hausawa, su ba sa sassaka gunki don yi masa bauta, a’a, sai dai bautar iskokai ta hanyar bori. Kanawa suna bautar Tsumburbura a dutsen Dala.

Akwai wasu gumaka makamantan wadannan a wasu wurarae a kasar Hausa. A kasar Katsina, akwai mutanen Kainafara, arnan Birci a kasar Dutsin ma, masu bautar wani gunki mai suna Dan talle. Sunan mai kula da wannan gunki shi ne Sarkin Noma. Kamar Barbushe Sarkin Noma shi ne mai ba da labarin sakon da Dan talle ya yi ga mabiyansa. Su ma mabiyan Dan talle kabilar Kainafara na yin bikinsu ne shekara-shekara kuma suna yin yanke-yake kamar dai mutanen Barbushe.

Akwai kuma wasu maguzawa masu bautar wani gunki mai suna Magiro a dutsen Kwatarkwashi a cikin jihar Sakkwato. Mai kula da tsafin shi ne Magajin Ranau. Shi ma ana yi masa yanke-yanke kamar yadda ake yi wa Tsumburbura sai dai su bakin sa ake yanka masa ko bakar akuya.

Bayan wadannan gumaka kuma, Hausawa Maguzawa kan yi tsafe-tsafe na gida. Misali shi ne, kusan kowane Bamaguje ya ajiye wata halitta wadda ya dauka ita ce kan gidansa. Wasu sukan dauki dabbobi kamar damisa, kura ko zomo ya zama kan gidansu. Duk abin da aka dauka ya zama kan gida to ba hali wani dan gidan ya ci namansa, ko ya kashe shi ko kuma ya cuce shi ko ta wace hanya.

Tasirin Addinin Gargajiya

A halin da ake ciki yanzu, ko da yake mafi yawan Hausawa sun karbi addinin musulunci hannu bibiyu, har ma ta kai fagen da an ambaci sunan Bahaushe sai a kawo addinin musulunci ciki, don ganin cewa Hausa da musulunci sun kusa zama abu daya duk da haka akwai Hausawa wadanda har yanzu tasirin addinin gargajiya bai bar su ba. Sanin kowa ne cewa har yanzu akwai Maguzawa a kasashen Kano da Katsina wadanda ba su daina yin tsafi da bautar gumaka ba. Wadannan Maguzawa har yanzu sukan yi bukukuwa da tsafe-tsafe iri-iri. Ta hanyarsu ne wasu Hausawan musulmi kan nemi taimako wajen dodo don neman biyan bukata. Irin wannan da’awa ta sa na sami wani tsohon Bamaguje a Jammawa ta kasar Dawakin Tofa wanda ake kira Zuga don ya tabbatar min ko Hausawa musulmi sukan nemi taimako a wurinsu, Zuga ya bayya min cewa a matsayinsa na makeri, ya sha karbar ziyarar makera Hausawa kuma musulmi wadanda suke zuwa wajensa don neman taimako kan yadda za su sarrafa wuta. Ya ce yakan fayyace musu fa lallai sai an kauce kuma sun yarda suna kuma bin dukan abin da ya nuna musu na game da tsafi.

Haka kuma na sadu da wani dattijo a wani kauye mai suna Katsardawa ita ma a kasar Dawakin Tofa take. Shi wannan Bamaguje sunansa Girbau kuma gawurtaccen manomi ne, ya bayyana min cewa ya ba mutane da yawa Hausawa kuma musulmi asirin dodo don kawai su tara hatsi da yawa.

Idan muka juyo ta fannin bori (wanda al’ada ce ta Maguzawa masu bin addinin gargajiya), za mu ga cewa har kwanan gobe Hausawa musulmi suna yi kuma duk mai yi ya ba da gaskiya.

Hanyoyin Yada Labarai Na Hausawa

Hanyoyin yada labarai abubuwa ne da suke tattare da kowacce al’umma, kamar yadda Hausawa kan ce ‘tun ran gini tun ran zane’. Hanyar yada labarai hanya ce tsararriya da ake bi domin isar da sako ga daidaiku ko kuma jumlar mutane ba tare da wani tarnaki ba. Babu shakka hanyar yada labarai ta dade a cikin al’umma amma, tun tuni, mun dade a kasar Hausa muna da tsarin isar da sako ta hanyar yekuwa ko shela da sankira yake yi domin fadakarwa ko sanarwa ko kuma nusarwa ga mutane ko ilmantar da su dangane da wani muhimmin abu da ya shafi rayuwarsu. Irin wannan yekuwar (shela) tana daga cikin tushen kafafin yada labarai a kasashen Afrika, musamma ma kasar Hausa.

Kayan Sawar Hausawa
Hausawa a da can ba su da wata sutura da ta zarce warki sai kuma ganye, amma zuwan addinin musulunci kasar Hausa ya canza rayuwarsu ta hanyoyi da dama, misali, ko wajen sutura ma musulunci ya canza tsarin adon Hausawa, zuwan Larabawa da wasu kabilun Masar suka kawo wa Hausawa suturu masu rufe al’aura, kamar su riga ’yar Tambutu da jabba da Kaftani da Kubta da wanduna iri-iri da hular dara. Aka kuma tanadar wa mata zane (gyauto) da mayafi (gyale) da dankwali da riga. Saboda samun irin wadannan suturu su ma Hausawa suka kago irin nasu suturun don maza da mata kamar ’yar-shara da taguwa da aganiya da fatari da bante. Wasu sun ce bante Hausawa sun aro shi daga wajen Nufawa ne.

Ire-iren Suturun Da Hausawa Suke Amfani Da Su
Luru, Gwado-babbar kwarya da karamar kwarya
Babbar riga da ’yar ciki-gari
Shakwara da jamfa da wando
Doguwar riga

Launukan Babbar Riga
Gari da Sace da Shakwara da Aganiya- akwai wadanda ake yi musu ado a ba su wasu sunaye:
Kamar Aska tara mai cibiya da Aska takwas malummalun da Aska biyu mai wau da Girke da Girken Zazzau da Girken Nufe da Sace mai adda da Sace mai gafiya.
’Yar Tambutu da Doguwar riga da Fanjama da Hartin da Jallabiyya da Zuleka da Kaftani
’Yar ciki dahariya da ’Yar shara da Zuhuni da kuma Falmaran

Wanduna
Tsala da Fanyama da Bulus da Dan itori da Dantunis mai kamun kafa da kuma Kwarjalle.

Huluna
Dankwara da Bakwala da Damanga da Habar kada da Facima da Zanna da Kube da kuma Zita

Rawani
Harasa da Bakin fara da Dankura da kuma Mubarrashi

Takalma
Dangarafai da Sambatsai da Fade da Mai gashin jimina da Dan Maroko da kuma Huffi.

Zanin Mata
Saki da Bunu da Bakurde da Gam Sarki da Tsamiya da Dantofi da Fatari da Saro da kuma Mukuru

Sana’o’in Hausawa
Kasuwaci da Fatauci da Saka da Rini da Farauta da Jima da Noma da Kiwo da Kira da Sassaka da Dukanci da Gini da Fawa da kuma Wanzanci.

Muhalli
Bukka da Tsangaya da Dakin Hayi da Shigifa ko Soro da Kudandan ko Rudu da kuma Kago.

Al’adun Hausawa
Hausawa mutane ne musu tsananin rikon al’adunsu na gargajiya, musamman wajen tufafi da abinci da al’amuran da suka shafi aure ko haihuwa ko mutuwa da sha’aninmu’amala tsakanin dangi da abokai da shugabanni da sauransu, da kuma al’amuran sana’a ko kasuwanci ko neman ilmi.

Tun daga zuwan Turawa har yau, Hausawa suna cikin al’ummomin da ba su saki tufafinsu na gargajiya sun ari na baki ba. Galibin adon namiji a Hausa ba ya wuce riga gari da wando musamman tsala, da takalmi fade ko kafa-cik, da hula kube, ko dankwara, ko dara. In kuma saraki ne ko malami ko dattijo, yakan sa rawani. Adon mata kuwa, zane ne da gyauton yafawa, wato gyale da kallabi da taguwa da ’yan kunne da duwatsen wuya wato tsakiya.

Yawancin abincin Hausawa kuwa, ana yin sa da gero ko dawa ne. Sai kuma sauran abubuwan hadawa, da na marmari, kamar su wake da shinkafa da alkama da kayan rafi da sauransu.

Yawancin Hausawa Musulmi ne saboda haka yawancin al’adunsu da suka shafi aure da haihuwa da mutuwa duk sun ta’allaka ne da wannan addni, sai dan abin da ba a rasawa na daga al’adun gargajiya musamman a wajen Maguzawa.

Haka kuma wajen mu’amala da iyaye ko dangi ko abokai ko shugabanni ko makwabta ko wanin wadannan, yawanci na Musulunci ne. Haka nan sha’anin sana’a da kasuwanci da neman ilmi duk a jikin Musulunci suka rataya..

Da can, sana’a da kusuwanci da neman ilmi suna bin gado ne, wato kowa yana bin wadda ya gada kaka da kakanni. Kuma idan mai sana’a ya shiga bakon gari zai je ya sauka a gidan abokan sana’arsa ne. In ma koyo ya zo yi, zai je gidan masu sana’ar gidansu ne. Saboda haka kusan kowace sana’a akwai sarkinta da makadanta da mawakanta, kai har ma da wasu al’adu na musa yinta da suka sha bamban da na sauran jama’a.

Tattalin Arzikin Hausawa
Kalmar tattali tana nufin kula ko ririta ko tanadi da kula ko adana wani abu, wato tsiminsa. Ita kuwa kalmar arziki a nan tana nufin tajirci ko dukiya ko samu ko hali ko gafi ko kudi ko sukuni ko daula ko wadata ko abin hannu wato mllakar dukiya mai yawa fiye da sauran abubuwan bukata.

Daga wadannan bayanai za a ga, a ma’ana ta gama-gari, tattalin arziki yana nufin kula da dukiya. A fagen nazari kuwa, tsari ne na sarrafa al’barkatun kasa da sauran ni’imomin da Allah ya yi wa mutum, yadda za a samar da muhimman abubuwa da dan’adam yake bukata a kuma sarrafa su ga jama’a.

Dangane da haka, dan’adam tilas ne ya yi aiki ya sarrafa wasu abubuwa don ya kai ga biyan wadannan bukatu, amma kuma mutum bai iya wadatar da kansa da dukkan bukatunsa, don haka dole ya dogara da ’yan’uwansa wajen samun wadannan abubuwa, kamar yadda su ma suka dogara da shi.

Tattalin arzikin Hausawa na gargajiya abu ne kara zube inda ake barin abubuwa kara zube, ma’ana kowa yana ba da gudummawa gwargwadon karfinsa kuma yana samun abubuwa gwargwadon irin sana’arsa da kwazonsa da kuma sa’arsa. Ita kuma hukuma ta sa ido don tsaron mutunci da dukiyar al’aumma.

Sana’o’i su ne mafi girman tafarkin da Hausawa suke bi don samar da abubuwan bukata. Ta hanyar sana’o’i suke sarrafa albarkatun kasa da sauran ni’imomin kuma rarar da suka samu suke musanyawa su mallaki abubuwan da ba za su iya samar wa kansu ba. A takaice dai sana’o’i su ne kashin bayan tattalin arzikin Hausawa na gargajiya wadanda suka hada da noma da kira da wanzanci da fawa da saka da jima da dukanci da sassaka da rini da dillanci da bokanci da dibbu da dinki da magori da tuggu da kwarami da banbadanci da kuma koli da dai sauran su.

Daga cikin wadannan sana’o’i noma shi gidan kowa da shi, a gargajiyance duk Bahaushe manomi ne amma kuma yakan kara da wata sana’ar don tallafawa. Dangane da haka ne ake karkasa mazauna gari bisa tsarin sana’o’in kowane gida ko unguwa, don haka ne ma a Kano aka sami unguwannin Makera da Dukawa da Mahauta da unguwar gini da makamantansu.

Manazarta

Adamu, Muhammad Tahar; 1997: Asalin Hausawa Da Harshensu. Kano: Dan Sarkin
Kura Publishers Ltd.

Alhassan, Habibu da Musa, Usman Ibrahim da Zarruk, Rabi’u Mohammed; 1982. Zaman
Hausawa, Bugu na Biyu: Lagos:Islamic Publications Bureau.

Adamu, Muhammad Tahar; 1997: Asalin Magungunan Hausawa Da Ire-ire-iresu. Kano:
Dan Sarkin Kura Publishers Ltd.

Dawaki, Alahassan Muhammad; 1983. Tasirin Addinin Gargajiya Kan Hausawa:
Takardar da Aka Gabatar a Taron Malamai da Dalibai na Jami’ar Bayero, Kano,
Sashen Harsunan Nijeriya.

Gidan Dabino, A.A.; 2001. Gudummawar Finafinan Hausa Game da Addini da
Al’ada: An gabatar da Wannan takarda a Bikin Makon Hausa na 23 Wanda
Kungiyar Hausa ta Jami’ar Bayero ta shirya, a Tsakanin 5 zuwa 8/1/2001.

Gusau, Sa’idu Muhammad; 1982.Wasanni Don Yara. Kano:
Jola-Ade Printers.

Gidan Dabino, A.A.; 2003. Ta Leko ta Koma: Mujallun Hausa Ina Mafita: An gabatar da Wannan Takarda a Taron Shekara-shekara na Mujallar Ar-Risala, a Harabar Makarantar Farhan, Kabuga Jan Bulo, Kano.

Magaji, Ahamad; 1986. Gudummawa a Kan Kokarin da Ake yi na Samar da Cikakken
Tarihin Hausawa: Takardar da Aka Gabatar a Taron Malamai da Dalibai na
Jami’ar Bayero, Kano, Sashen Harsunan Nijeriya.

Nazari A Kan Harshe Da Adabi Da Al’adun Hausawa Na Farko.1978: Kano: Uniprinters
Ltd.

Nazari A Kan Harshe Da Adabi Da Al’adun Hausawa Na Uku.1993: Zariya: Gaskiya
Coporation Ltd.

Nazari A Kan Harshe Da Adabi Da Al’adun Hausawa Na Biyar. 2002: Kano: Benchmark
Publishers Ltd.

Yahaya, Ibrahim Yaro da Zariya, Mu’azu Sani da Gusau, Sa’idu .Muhammad;
1992. Darussan Hausa 1,2,3, Don Makarantun Sakandare. Ibadan: University Press,
PLC.