Wednesday, June 20, 2007

MUHIMMANCIN MARUBUCI A CIKIN AL’UMMA

Na Gabatar da Wannan Jawabi a Wajen Taron Gangamin Marubuta, Wanda Kungiyar ‘Brigade Authors Forum’ Suka Shirya, Ranar Lahadi 21/05/2006, a ‘Government Girls Secondary School’ Gama Tudu, Kano.



Gabatarwa:
Rubutu rayayyen al'amari ne da kan wanzu matukar wanzuwar duniya, kuma tamkar shuka ce wace in har ka yi za ta girma ta ba ka inuwa ka kuma ci 'ya'yanta. Yana kuma iya zama tamkar dan kunama ko kuwa kaikayi wanda Hausawa ke cewa "koma kan mashekiya".

Manyan masana tuni sun bayyana abubuwa masu yawan gaske game da murubuci da kuma shi kansa rubutun, don haka duk abin da zan fada an riga ni fada sai dai na dan tsakuro abin da ya samu daga ire-iren abubuwan da suka ce.

An nemi in gabatar da takarda mai taken Muhimmancin Marubuci A Cikin Al’umma, ina godiya ga masu shirya wannan taro da suka ba ni wannan dama. Kuma ina yi musu fatan alheri da samun nasara a kan manufar wannan taro.

Wane Ne Marubuci?:
MARUBUCI Dan BAIWA NE, haihuwarsa ake yi ba yin sa ake ba. Marubuci shi ne wanda ta hanyar amfani da fasahar rubutu yakan kirkiri wani yanayi na gaske ko na almara ko tunani ya kuma yi amfani da shi don gina wasu mutane da abubuwa wadanda yake amfani da su don isar da sako ga al'ummar da ke karatun rubutunsa. Shi wannan sako ana tsara shi ne ta hanya ta musamman mai cike da hikima da hazaka don isarwa a saukake, kamar ta hanyar yin amfani da haruffa zuwa kalmomi zuwa jimloli zuwa si]arori da shafuka har zuwa cikakken littafi.

Wani ana haihuwarsa da rubutu wani kuma koyo yake yi, amma duk marubuta za mu kira su. Shi marubuci mutum ne na daban, ba wai ya fi sauran rukunonin bil'adama ba ne, a'a, shi dai daban yake da sauran mutane, wato dan baiwa ne. Marubuci na yin tunani ne iri na daban, yana kuma kallon rayuwa da al'amuran rayuwa da wata irin fahimta tasa ta daban, sannan ya bayyana ta a rubuce. Kamar yadda aka ambata a sama shi marubuci dan baiwa ne, sannan shi kansa rubutun baiwa ne.

Muhimmancin Marubuci A Cikin Al’umma:
Abu ne sananne ga al’umar da take da ilmi cewa marubuci yana da matukar muhimmanci da tasiri. Saboda haka ya wajaba a kan al'ummar da ta sami marubuci a cikinta ta yi kokaririn jawo ra'ayinsa ko yin tasiri a kan tunaninsa don ya yi rubutu na kwarai, in ba haka ba duk abin da ya rubuta zai yi tasiri a kan ita al'ummar.

Marubuci kan yi rubutu saboda dalilai da dama ko wani hali ko yanayi da ya sami kansa ko wani tarihi na kasa ko dadadde ko kuma wata manufa ko ra'ayi. Don haka marubuci na iya yin rubutu don ilmantarwa ko wayar da kai ko kyautatawa ko fadakarwa ko farfaganda ko ta da zaune tsaye ko cin zarafi ko kuwa tsokana. Yana iya yin rubutu don gina wata akida ko rusawa ko kuwa don ru]ar da jama'a ko kawo sauyi ko kuma don tabbatar da wani ra'ayi ko manufa. Saboda haka marubuci na iya zama dan kwarai ko kuma baragurbi, sai dai a koyaushe yana kokariri ne ya ga cewa ya shawo kan makaranta su amince da shi. Domin kuwa zai yi iya kokaririnsa ya nuna musu cewa sakon nan nasa gasgatacce ne, amintacce ne kuma dauwamamme ne mai farin jini.

Wani mawaki Sani Yusuf Ayagi, a cikin wakarsa ta Alkalami Ya Fi Takobi, ga abin da yake cewa:
Alkalami mai hagun da dama,
Mai haske ga duhu ku duba.

Mai zaki alkalam da daci,
Ko ba ku san me nake nufi ba.

Ai ma’ana gaskiya da karya,
Babu guda wadda bai iya ba.

In ya so yanzu ai zumunci,
Sai ya matsa can ya kulla gaba

In an so, sai a kulla yaki,
Ku hargitse ba da kun sani ba.

Da shi masoya ka daukaka,
Da sun rubuta ba a musa ba.

Da shi akan sa a kassara ka,
Da dai ba ka kara daukaka ba.

Da an rubuta ana yabonka
Ko kai sata ba a sani ba.

Da shi sukan bata dan adam kaf,
Akan abin shi dai sani ba.

Yana da kyau mu fahimci cewa marubuci na da matukar muhimmaci ga duk al'ummar da yake zaune a ciki domin kuwa kadara ne ga wannan al'umma kuma yana iya jawo wani ci gaba ko dakushewa da alkalaminsa. In har ba ka fahimci manufar marubuci a rubutunsa ba, to ka dauka cewa ka jahi1ci fahimtarsa. Don haka duk irin abin da marubuci ya rubuta akwai manufa a cikinsa sai dai ko ba a fahimta ba. Amma fa ba dole ne a ce koyaushe marubuci na yin rubutu mai ma'ana ba.

Wani abin lura shi ne, zama marubuci wani al'amari ne babba. Duk lokacin da mutum ya zamo marubuci ko yake son zama marubuci, to yana shiga wani hali ne mai wuyar gaske. Na farko marubuci a kullum cikin tunani da kokaririn fahimtar al'ummarsa yake. Na biyu duk lokacin da yake rubutu dole ne ya rinka sanya tunaninsa da kuma mutuntakarsa. Shi ne zai zama na kwarai yanzu, wani lokacin kuma ya zama mugu. Ya zama yaro ya zama babba ya zama namiji ya zama mace, kuma duk lokacin da yake rubutu yana tunani ne na irin mutumin ko halin da yake rubutu a kansa.

Wani lokaci kuma marubuci tamkar dan-leken asiri ne domin kuwa muddin zai yi rubutu in har marubucin kwararre ne sai ya yi bincike don gano wasu bayanai ko fahimtar su. In da za ku gamu da shi a irin wuraren da yake neman bayanansa sai ka rantse ba wani abu yake yi ba. Alal misali idan marubucin yana yin rubutun da a ciki sai an yi maganar karuwai ko mashaya, kada ka yi mamaki don ka gan shi a mashaya ko yana tattaunawa da karuwa neman bayani ne ya kai shi. Ta haka yakan bi sauran hanyoyi don gudanar da binciken sa.

Babban muhimmancin da marubuta ke da shi ga al'umma shi ne, na yin amfani da alkalaminsu wurin sauya al'umma. Ya zama lallai a fahimci cewa ayyukan marubuta kan yi tasiri ga al'umma kai tsaye ko kuma ta rashin sani.

Don haka ya zama wajibi ga al'umar da take da marubuta a cikinta ta ga ta taimaka musu ta kuma yi tasiri na kwarai ga tunaninsu don rubutunsu ya yi tasiri nagari ga al'uma.

Gwagwarmayar Da Ke Gaban Marubutanmu:
Babu shakka a 'yan shekarun nan mun sami wadatuwar marubuta littattafan Hausa daga kowane sashe a arewacin kasar nan, amma akwai kalubale mai yawan gaske a kan su marubutan, wato wajen rashin ingancin bugu da rabe-raben kalmomi da satar fasaha da maimata suna da kuma dagewa a kan jigo daya wanda a kansa ne yawa-yawan manazarta ake ta gwagwarmaya da su, wato jigon soyayya. Tun a shekarar 1992 aka fara wannan muhawara a cikin jaridu da mujallun Hausa kan dacewa ko rashin dacewar jigon da ake rubutu a kansa. Don haka wannan wata dama ce da su marubuta za su yi amfani da ita su gyara kurakuran da ake cewa suna yi, in sun san suna yi din. Domin idan mutum bai samu masu gane masa kuskure a aikinsa ba, to bai yi dace ba.


MANAZARTA:
Adamu, Yusuf M. (1994) Wane Ne Marubuci? Mujallar Zamani, Ta 1,
Fitowa Ta 1, Maris. Kano: Gidan Dabino Publishers.

Adamu, Yusuf. M. (2002) Print And Broadcast Media In Northern Nigeria.
www.kanoonline.com

Ayagi, Sani Yusuf, (2005) Wakar Shirin Alkalami Ya Fi Takobi, Freedom,
Rediyo

Gidan Dabino, A.A, (1995) Muhimmancin Marubuta a Cikin Al’umma,
Takardar da Aka Gabatar a Bikin Kaddamar da Littafin Karshen Mai Zalunci, Koko, Jihar Kebbi.

Gidan Dabino, A.A, (1993) Gudummawar Adabin Hausa Ga Addinin
Musulunci, Takardar Da Aka Gabatar a Taron Kara Wa Juna Sani Na Dalibai Musulmi Na Babbar Makarantar Sakandaren Dawakin Tofa.

No comments:

Post a Comment