Masu iya magana suna cewa, tafiya sannu-sannu kwana nesa, wannan haka yake, ga shi har na yi kwanaki ashirin da shida a kasar Birtaniya, a kan tafiyata don rubutun littafin GANI DA IDO...da kuma nuna fim din SANDAR KIWO.
Filin jirgin saman Amsterdam da Heathrow
Lokacin da muka sauka a filin jirgin saman Amsterdam inda za mu sauka mu hau wani jirgin da zai karasa da mu London, ba mu jima ba muka sauya jirgi muka tashi zuwa filin jirgin Heathrow na London, misalin karfe 7. 40 muka fito muka nufi wajen jami’an kula da shige da fice, aka fara duba fasfot dinmu, sai da suka tambaye ni me na zo yi nan London, na shaida musu ni marubuci ne kuma na zo ne a kan rubutun littafi da nake yi a kan tafiye-tafiye a Afrika da turai, aka kuma nemi a ga tikitina na komawa da kuma kwanakin da zan yi, duk na nuna su, sannan na wuce.
Da na fito wajen da masu zuwa tarbar baki suke, sai na tsaya don in ga wadda ta zo tarba ta wato Katrin Schulze, wata Bajamishiya da take karatun digiri na uku, wato tana neman takardar shaidar dakta a fannin zane-zane. Bayan wasu ‘yan mintina sai ga ta nan ta karaso inda nake, don lokacin da na fito ita kuma tana wani bangaren.
Daga nan muka nufi wajen shiga jirgin kasan karkashin kasa don isa gida. Mun kai minti arba’in muna tafiya kafin mu isa gidan, don gidan yana arewacin London. Gidan yana lamba 46 Park Road, Turnpike Lane, London N15 3HR. Gidan dalibai ne a cikinsa su bakwai, mata uku mazu hudu, daliba daya mai suna Alina Demitron daga Balgeriya, sai Katrin Schulze daga Jamus dayar kuma Caroline dag Finland, su kuma mazan biyu Dr. Abdullahadi Bala Yahaya daga Kano- Nijeriya, da Dr. Isa Jibril jihar Neja-Nijeriya, akwai kuma Khairul Islam da kuma Reza dukkansu daga Bangaladash dukkansu suna karatun digiri na uku ne.
Bayan na dan huta ne muka nufi jami’ar SOAS, don in hadu da manyan shaihunnan malaman Hausa na wannan makaranta, kamar Farfesa Graham Furness da Philips Jigger da sauransu, sannan kuma in ga Dr. Lindiwe Dovey da ke sashen koyar da finafinan Afrika.
Ashe Filashin a nan London batsa ce?
Wani abin dariya da aka yi ranar farko da na sauka a birnin London wajen karfe uku na rana. Mun je na sayi sabon layin waya da zan dinga amfani da shi mai suna lyca sai na ce da wadda ta raka ni wato Katrin, bari in yi miki filashi ki ga lambar tawa, sai ta kece da dariya tana cewa, kai ka yi a hankali wannan kalmar ba mai dadi ce ba a nan garin. Sai na ce kamar yaya? Sai ta ce ai ina ka ce za ka yi filashin kamar ka ce bari in budi jikina ki gani ne.
Sai na ce wani irin jiki? Sai ta ce kamar ka yi tsirara ko kuma makamancin haka, a kan hanyar da mutane suke wucewa ko a cikin mota ko kuma ga wata mace, shi ake nufi da filashin. Na ce to, ai kuwa ba zan kara fadi ba har wani ya ji.
Da muka isa jami’a, mun hadu da mutane da yawa malamai da dalibai wadanda nake sa rai zan gani da kuma wadanda ma ban zata ba, cikinsu akwai Farfesa Ahmad Halliru Amfani na jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto, ya zo yin wasu na labintis harkoki na ilmi na tsawon wata uku, da wani malami daga jami’ar jihar Kano mai suna Ibrahim Abdullahi wanda yake karatun digiri na uku a fannin kididdigar lissafi, dukkanmu mun yi farin cikin haduwa da juna. A wannan rana aka sanar da ni akwai liyafar cin abinci ta maraba da wani Dr. Usman Ladan da ya zo daga jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, zai yi irin zaman da Farfesa Amfani zai yi na wata uku, za a yi liyafar ranar litinin 01/03/2010 da karfe 12.30 na rana.
Kowace rana mukan zo jami’ar SOAS sannan in kuma muna da tsarin fita ganin gari mu fita tare da Katrin, ko Farfesa Amfani don a nuna min gurare. Duk da yake ana yin ruwan sama jefi jefi, ga kuma sanyi, a haka dai muke fita mu zagaya don in an ce ba za a fita ba don ruwa, to kuwa ba za a yi komai ba kenan, don haka duk da ban saba ba a haka nake fita cikin ruwan.
Wasu daga cikin wuraren da muka ziyarta akwai
London Planetarium da Madame Tussaud da British Museum da Trafalgar Square da Natural History Museum da Buckingham Palace da Tottenham court Road da Oxford Street da Middlesex Street da Houses of Parliament da Tower Bridge da London Bridge da Brixton da Alexander palace da kuma Old Street.
Mun ziyarci Sashen Hausa na gidan rediyon BBC
Ranar 25/02/2010, wajen karfe uku na rana muka nufi gidan rediyon BBC ni da Farfesa Ahmad Halliru Amfani, inda aka yi hira da shi a kan harshen Hausa, kuma mun sami haduwa da wasu daga cikin ma’aikatansu kamar Sulaiman Ibrahim Katsina da Suwaiba Ahmad da Muhammad Jamil Yusha’u da Ahmad Abba Abdullahi da Mansur Liman da kuma Aminu Abdulkadir da kuma Jamila Tangaza shugaba sashen. Mun dade a gidan rediyon, har sai da aka yi sallar magariba sannan muka taho makaranta. A lokacin ne Sulaiman Ibrahim ya gayyace mu cin abinci gidansa da ke wajen garin London wato Forest Gate.
Da ranar ta zo muka je muka ci abinci a gidansa, muka yi sallar magariba da isha’i. Na lura da wani abu da ya birge ni sosai a gidan Sulaiman, wato batun addini, gaskiya bai yi sake zaman Turai ya sa ya manta da addini ba, haka nan iyalinsa, duk ya sanya su bisa turbar addini, sannan kuma suna yin Hausa sosai a cikin gidan, sabanin wasu da in sun fita suke mantawa da duk wadannan abubuwa, wato tarbiyya da al’ada da addini da kuma harshensu, don cikin ‘ya’yansa mata har da wadanda suka sauke Alkur’ani a nan birnin London. Abin dai sai son barka.
An nuna fin din Sandar Kiwo
A ranar Talata 2/03/2010 aka nuna fim din Sandar Kiwo ga dalibai da malaman sassa biyu wato masu koyon Hausa da kuma finafina Afrika, har ma da baki daga wajen makarantar. Cikin mutanen da suka halarci wannan wajen kallon fim sun hada da Farfesa Philips Jagger da Farfesa Ahmad Halliru Amfani da Farfesa Miry Las (sananne a fannin tarihi) da Dr. Lindiwe Dovey da Barau na Chedi wato Williams Barry Burgerss tsohon shugaban BBC, yanzu kuma malamiN Hausa a jami’ar SOAS da Dr. Chege Githiora mai koyar da harshen Swahili da Jamila Tangaza shugabar sashen Hausa na BBC da Jamilu Mustapha Chedi, Kano, wanda yake karatun digiri na biyu a kan wani sabon fanni a Nijeriya, mai suna ‘designing and ergonomics’ a jami’ar Coventry sai kuma Ibrahim Abdullahi, Kano da ke Jami’ar London yana yin digiri na uku a fannin kididdigar lissafi.
Kafin a fara nuna fim din sai da Farfesa Philips Jagger ya gabatar da ni da kuma gajeren bayanin abin da fim din ya kunsa, sannan ni kuma na karanta dan gajeren jawabin dalilin yin fim din da kuma abin da ake fata a yi in an gama kallon fim din, duka cikin harshen ingilishi aka yi jawaban.
Bayan an gama kallon fim din Sandar Kiwo na tsawon awa daya da minti talatin da shida sai aka bayar da dama in da masu son cewa wani abu wanda ya danganci gyara ko shawara ko kuma suka. Mutum na farko da ya yi magana shi ne Dr. Chege Githiora wanda ke koyar da harshen Swahili, ya ba da shawarar cewa ya kamata mu masu shirya finafinan Hausa mu dinga sanya fassara da harshen Swahili don ya samu karbuwa ga wasu sassa na duniya masu amfani da wannan harshe, kuma ya ce kofa a bude take gare mu a wajensa don gudanar da wannan aiki.
Jamila Tangaza wadda take shugabancin sashen Hausa na BBC London, cewa ta yi, an yi kokari wajen shirya wannan fim kuma ya kamata a kara wani kokarin wajen taba wasu fannoni na rayuwar Hausawa musamman na karkara.
Sauran abubuwan da mutane suka bayyana su ne, sun ji dadin ganin wannan fim kuma yana da ban tausayi sosai, ga shi kuma labarin ana gane shi da abubuwan da yake kunshi da shi, cikin sauki ba tare da sarkakkiya ba.
Na Ziyarci garin Oxford
Ranar Laraba 3/3/2010 ne na tafi garin Oxford don ganawa da wata mata mai suna Mary Jay, sakatariyar masu shirya gasar Noma Award for publishing in Africa, wadda ake bayar da fan dubu goma #10,000 (na Ingila), kimanin Naira miliyan biyu da rabi kenan kudin Nijeriya, ga wanda duk ya yi na daya. Tsakanin birnin London da garin Oxford tafiyar awa daya da minti arba’in 1.40 ce, a cikin irin doguwar motar nan mai hawa biyu. Kuma kudin motar fan 16 ne, kamar Naira dubu hudu kenan (4,000) kudin Nijeriya. Mun bar birnin London da misalin 11.19 na safe kuma mun isa Oxford bayan karfe daya na rana. Sai dai lokacin da muka yi da farko za mu hadu da ita sai ya zama tana da wani mitin a lokacikin don haka da na isa sai na kira ta, sai ta gaya min in dan yi hakuri ta gama mitin din.
Lokacin da nake zaman jiran ta ne na shiga kantin sayar da kayan shaye-shaye da ciye-ciye da ke Gloucester Green bus station, na ce a ba ni shayi da madara da ‘meat-pea’ wato fanke a hausa ke nan. An ba ni shayi da madara da wani dan karamin fanke, na tambaya nawa kudin, aka ce fan uku da wasu ‘yan sulalla, kudin Nijeriya kusan N1000 kamar Naira dari takwas kenan, na biya, na zo na zauna ina sha ina ganin gari. Na kalli fanke da shayin nan, na ce Allah daya gari bamban, shayi da madara da dan wannan fanken su ne a kan wannan kudin, da a garinmu ne na sayi shayin wannan kudin Naira dari takwas ai da an ga ire-iren hadin da ke cikin sa, kuma komai da komai sai ka gani a tare da shayin. Na yi dariya na ce haka dai kasashen Turai suke da tsadar rayuwa, amma babu kamar Ingila. Don a tafiye-tafiyen da na yi zuwa Italiya da Faransa da Jamus ba su kai tsadar nan ba.
Da na gama ne na tashi na shiga wata ‘yar kasuwa da aka baje kolin kayan abinci da sauran kayan bukatun yau da kullum har da kayan sawa. Bayan na gama da kasuwar sai na kara yin gaba na biyo layi ina ganin yadda garin Oxford yake. Ban jima ban a koma, wajen wannan kantin daman an muka yi za mu hadu.
Ban jima da komawa wannan kantin ba na ji ta kira ni tana tambayar ina ina, na shaida mata. Ba a yi minti biyar ba kuwa ta iso wajen da nake. Ta yi min tayin shan shayi ko kofi, na ce ai na sha shayi yanzu, don haka muka je ta kabo shayi ta zo muka zauna, muka fara tattauna abubuwan da suka kawo ni, sannan ta tambaye ni me na zo yi London, na shaida mata na taho ne a bisa dalilin rubutun wani littafi da nake yi mai suna Gani Da Ido…, da kuma fim dina da aka nuna a jami’ar SOAS. Ta yi murna kwarai da jin wadannan dalilai na zuwana. Sannan kuma muka shiga tattauna batun wallafa littattafai a kasashen Afrika da kuma wani aiki da take yi a African Books collective. Ta ba ni labarin kasashen da ta je a Afrika, ni ma na gaya mata kasashen Afrika da Turai da na ziyarta.
Mun dade muna hira, da muka gama, sai ta ce na san garin Oxford, na ce a’a wannan ne karo na farko, ta ce na shiga gari na ga yadda yake?, na ce a’a. Daga nan ta ce mu zaga in gani, in dauki hotuna tun da rubutu nake yi na sami wanda zan sa a ciki.
Da yake a kasashen Turai tafiya a kasa an mayar da ita dabi’a, sai muka fara dukan sayyada muna zaga gari, ta nuna min tsufaffin jami’o’in garin da kuma wani kantin sayar da littattafai wanda ya fi kowane dadewa a Birtaniya, wato Blackwell, wanda aka kafa a shekarar 1897.
Bayan mun gama zagawa da daukar hotuna sai muka yi bankwana da ita na dawo wajen da zan hawo motar da za ta dawo da ni birnin London. Mota za ta tashi da misalin karfe 4.10 na yamma, lokacin yana cika kuwa motar ta tashi ba tare da kara lokaci ba.
Na bata a birnin London
Mun iso London kusan karfe shida na yamma, lokacin dare ya yi tun da an yi sallar magariba. Ashe zan bata ban sani ba, lokacin da muka isa garin kafin mu karasa tashar da ya kamata direba ya kai mu sai ya yi sanarwa a cikin motar cewa ba zai karasa Burkingham Palace Road ba a nan Victoria zai tsaya, kuma bai shiga cikin tashar da motocin suke tashi ba, a hanya kafin ya karasa ya tsaya, ni kuma waccan tasah na fi ganewa ban gane nan inda zai ajiye ni ba, amma babu yadda zan yi sai na sauka, na je wajen da ake shiga motoci masu zuwa wurare daban-daban, wato wurin tsayawar motoci. Na duba duk taswirar da ke makale a jikin allon sanarwa amma ban ga wajen da zan je ba, wato Russell square, don haka sai na ce to bari in kira mai masaukina ta gaya min yadda zan yi, na kira ba ta dauka ba sai salular ce ta amsa da kanta, na bar mata sako, sai na kira Farfesa Ahmad Halliru Amfani don ya gaya min ta yadda zan yi in koma jami’a, sai ya ce gaskiya bai san wace mota zan hawo ba amma in shiga tashar jirgi in hawo jirgin da zai zo Russell square in da jami’ar take kenan, wato shi ya fi sanin hanyar jirgi fiye da mota. Na sake karasawa can inda tashar take na tambayi wani ma’akiacin wajen, bakar fata ne, ya duba taswira ya ce in yi nan zan ga wajen, da na zo wajen hanyar da zan bi in hau jirgi na dauko katina na sanya a shingen da aka yi a kan hanyar, amma karfen ya ki budewa, don haka na tambayi wani ma’aikacin wajen, sai ya karbi katin nawa ya kara a wani waje sai ya ce sai na zuba kudi a ciki, ga wajen da zan je can in biya a kara min.
Na yi turus, na kadai ina cewa, ni da nake da kudi a ciki yaya za a ce sai na kara kudi bayan kudina ba su kare ba, fan 25 na fara sawa lokacin da na zo, sannan na kara fan 21 gaba daya ina da fan 46, kimanin Naira 11,500 na sanya a katin don hawa mota. Sai na ce gaskiya ba zan kara ba bari in nemi inda mota take in hau.
To fa! Ashe na yi gudun gara na cim ma zago, da na sani ma kara kudin na yi in hau jirgin kawai. Da na tafi a kafa na samu inda zan hau mota amma ba mai zuwa inda za ni kai tsaye ba, sai an sake hawa wata motar, na hau mota ta sauke ni a Holborn, nan ma ba a sauke ni a daidai inda zan gane ba, amma na tambayi matar da take tuka wannan babbar motar, da zan sauka ta yi min wani baubawan kwatance wanda ban gane ba, na yi ta bilinbituwa da buliya a tsakanin wajen, mahadace kamar biyar, na yi ta safa da marwa a wajen ban gane ba, na yi ta kokarin kuma in kira lambobin wayar Katrin ko Farfesa Amfani amma baturina ya mutu, don haka babu sauran gyaran mai kalangu ya fada ruwa, wato dai ba sauran sadarwa tsakanina da masu yi min kwatancen hanya, don haka yanzu sai abin da hali ya yi dan daudu a kiyama. Don haka ya zama wajibi in san yadda zan yi in dawo da kaina makaranta ko ta halin kaka, don haka sai na cire tunanin kiran kowa a waya, na shiga neman mafita.
Na fi minti goma sha biyar ina ta bin wajen tsayawar motoci ina karanta taswira don in ga motar da zan hau. Ina nan ina dubawa sai na ji murya ta bayana an ce, da gani wannan bai san inda za shi ba, na waigo sai na ga Sulaiman Ibrahim Katsina yana murmushi, muka gaisa, na ce kai amma dai Allah ya taimake ni. Na ba shi labarin abin da ya faru, ya yi dariya ya ce ai ka kusa da wajen tsallaka can bangaren ka hau mota mai lamba 73, ita za ta kai ka Russell Square. Muka yi bankwana da murmushi, na tsallaka na hau mota shi ma ya hau mota ya nufi unguwarsu wato Forest Gate.
Ina zuwa makaranta na tarar Katrin ba ta nan ta bazama nema na, amma ta bar sallahu in na zo in jira ta a dakin masu binciki, inda na’urori masu kwakwalwa ne tirmis a ciki da injin juyar takardu ‘photocopy’ da sauran kayan bukatun masu bincike. Na zauna na ci gaba da zaga duniya a cikin yanar gizo.
Bayan na share kusan awa daya ina cikin ofishin tare da wani dalibi dan kasar Bangaladash, sai ga Katrin ta shigo a jigace, ta fi awa biyu tana nemana ba ta same ni ba, ta yi ta kiran wayata a rufe sai murya salular ce take amsa mata. Tana ganina ta yi turus ta dafe kirji ta koma kan kujera ta zauna, tana nuna abin mamaki a fuskarta. Muka shiga tattaunawa kan irin yadda ta damu da kuma rudewa ta rashin gani na da ta yi, har nake tsokanarta ina cewa, ko tana tsoro kada mutanena su ce ta batar da ni a London? Muka yi barkwanci muka gama sannan muka nufi gida.
Na ziyarci yankin Hammers Smith a yammacin London
Ibrahim Abdullahi Kano wanda yake malami ne a jami’ar kimiyya da fasaha ta Kano, yana zaune a gundumar Hammer Smith a yammacin London, unguwar White City da ke Shaferds Bush, kusan shekara uku kenan yake zaune a garin tare da iyalinsa, ya gayyace ni cin abinci a gidandsa. Ranar Alhamis bayan na je BBC an yi hira da ni a filin Taba Kidi Taba Karatu, wajen karfe bakwa na dare ya zo BBC muka tafi tashar jirgin kasa muka je unguwar tasu. A can muka yi sallar magariba da isha’i, sannan muka tsaya muka gaisa da wasu ‘yan Nijeriya, muka dawo gidan muka ci tuwon suman bita miyar kuka da yaji da kuma man shanu. Da muka gama hirar da za mu yi ya rako ne tashar jirgi na dawo Holborn (inda na bata wata rana) na hawo mota na dawo jami’a. Shi ma Ibriahim mutum ne mai riko da addini sosai. A wannan unguwa ta White City gidan talbijin na BBC yake don haka kafin in bar unguwar sai da muka je ginin gidan talbijin din, sannan kuma a wanna unguwa ne babban kantin sayar da kayayyaki da ya fi kowane girma da zamananci a nan London yake, ana kiran sa da suna Westfield. Ibrahim ya nuna min shi, ya ce ba don ba lokaci ba da mun je mun shiga, na ce ba komai tun da ana can ana jira na a jami’a.
Hira da kafafen yada labarai
Tun lokacin da zan taho London na sanar da abokaina da ke kafafen yada labarai na rediyo da jaridu, don haka da na zo nan London sai muka yi ta yin hira da su, ciki kuwa har da sashen Hausa na BBC, su zuwana gidan sau uku. Sannan Rediyo Faransa su ma wakilinsu na nan London Idris Muhammad Aminu, ya same ne har masaukina muka yi hira da shi. Su kuma gidan rediyoyin Kasar Nijar, wato Sarauniya da ke Maradi sau biyu muna yin hira da su kai tsaye tare da Laminu Gwanda, haka nan gidan rediyon Altanative da ke Yamai, mun yi hira shi ma ta kai tsaye da Sule Maje Rejeto. Rediyo Freedom ma mun yi za mu tattauna da Baharu mai gabatar da filin Finafinan Hausa amma matsalar layin waya ya hana mu samu damar yin hirar.
Sai kuma wani gidan talbijin mai suna Success TV, ta wani dan Nijeriya, wadanda suke gudanar da shirye-shirye a cikin harshen Hausa da Turanci, mun yi za a yi wata tattaunawa da ni amma saboda lokacin da za a yi hirar ni kuma na bar birnin London, na taho garin Telford, don haka hirar ba ta yiwu ba.
Na yi kwanaki goma a cikin birnin London, sannan yanzu kuma na kara gaba zuwa ina garin Telford.
Garin Telford
Garin Telford shi ne zangona na biyu a wannan tafiya, kuma a nan garin na yi kwanaki goma sha biyar, sannan na dawo gida Kano-Nijeria, wato ranar Asabar 20/03/2010.
Garin yana da mutane 125,000 a cikinsa, muna iya kiransa karkara, yana kusa da garin Birmingham, gari ne mai yawan ma’aikatu, shi ne garin da aka fara kafa masana’anta a Birtaniya don haka ma suke yi masa kirari da Birth place of industry. Ba mutane da yawa, don haka ma ba za ka dinga ji ko ganin zirga-zirgar mutane kamar birnin London ko Birmingham ko Oxford ko Coventry ko kuma Sheffield ba, wato sauran garuruwan da na ziyarta kenan.
Birmingham
Mun je garin Birmingham ranar Talata ni da mai masaukina Umar Dan’asabe Barde a cikin motarsa don ya sayo rago sannan kuma in ga gari. Bayan tafiyar kamar minti ashirin da biyar muka isa Birmingham, muka isa wani kamfanin sayar da yankakkun raguna na mutanen Pakistan, musulmai. Muka sayo daga nan kuma muka dan zaga gari sannan muka dawo gida Telford.
Garin Coventry
Ranar Juma’a na hau jirgin kasa daga garin Telford na kai ziyarci garin Coventry don in gani da idona, wajen wanda na je kuwa shi ne Jamilu Mustapha Chedi, wanda yake karatun digiri na biyu a jami’ar Coventry. Tafiyar kusan awa da ya ce ta kai ni garin. Da yake mun yi alkawari zai zo tarba ta, ina sauka kuwa na gan shi a tsaye yana jira na, na tarar da shi tare da wani abokinsa mai suna Nasiru Garba Anka wanda yake karatun digiri na uku, wato zai zama dakta kenan a fannin tsara birane.
Haka dai muka tako a kafa mu uku, muna tafiya muna labarin duniya, har muka isa makaranta, Nasiru ya tsaya a makaranta, ni da Jamilu muka isa gidan da yake muka yi alwala muka fito muka nufi masallaci don sallar juma’a. Wajen da ake yin sallar filin wasan kwallon hannu da na Kwando ne, in kuma a daidai lokacin sallar juma’ar akwai wani wasa da za a yi a wajen sai dai masu sallar juma’ar su nemi wani wajen su yi sallar. Yau dai an yi sa’a ba wani wasa da ya zo daidai da sallar juma’a don haka a nan muka yi salla.
Da aka idar da salla muka fito waje muka hadu da wasu ‘yan’uwa ‘yan Nijeriya daya daga Kano, Bashir da Adamu Gwani Yola, daga Katsina kuma akwai Yakubu da Abdulaziz, sai Idris Ahmad Adamawa, muka gaisa muka dauki hotuna tare sannan muka yi bankwana da juna. Daga nan muka nufi wasu wurare da muke ganin za mu iya samun damar ziyarta, tun da ba ni da lokaci sosai, tun da a ranar zan kara gaba zuwa wani garin. Mun je gidan abinci na Nando’s inda muka ci abincin rana.
Wuraren da muka ziyarta su ne, Transport museum da West Ochord da Coventry Cathedral (wajen da Hetila ya yi waruwan bamabama) da IKEA da Coventry University da City Centre da Lower Precincts da Shoping Centre da Coventry Rail Station da kuma Pool Meadow.
Bayan mun gama ziyarar gari mu uku sai muka hadu da wasu dalibai Abubaka Rabi’u Yola daga Adamawa da kuma Binta Umar daga jihar Kebbi, muka zama mu biyar kenan, muka zo tashar mota na sayi tikitin tafiya garin Sheffield inda zan ziyarci Muhammad Jamil Yusha’u na gidan rediyon BBC Hausa. Mun dade muna hira a wajen jiran mota, don sai bayan karfe shida motar za ta tashi. Tafiyar awa uku da rabi za mu yi kafin mu isa garin.
Da mota ta zo muka yi bankwana na shiga mota. Kafin motar ta tashi na kira Jamilu Yusha’u na sanar da shi ga motarmu nan za ta taso yanzu. Ya ce da na zo in kira shi sai ya zo tasha ya tare ni.
Garin Sheffield
Bayan awa uku da rabi muka isa garin Sheffield, muka sauka a tashar mota ta Sheffield Interchange. Na kira na sanar da Jamil. Bayan wasu ’yan mintuna ya zo muka tafi gidansa. A lokacin da muka isa gida wani makocinsa mai suna Dr. Kabiru Abdul Katsina, ya kawo min abinci. Sannan mun hadu da Dr. Sani Damban, wanda yake daga jihar Bauchi.
Washegari da muka fito daga gida mun fara da Royal Hallanshire Hospital inda muka duba matar Jamilu inda take kwance ba ta da lafiya. Daga nan muka je masallaci (Muslim welfare house) muka yi sallar azahar da la’asar, sannan muka je dakin Dr. Bichi wani malami daga jami’a kimiyya da fasaha ta Kano, inda muka dan yi hira, kafin mu fita daga dakin wani malamin ya shigo shi kuma daga unguwar Chiranchi ta cikin birnin Kano yake. Sannan muka fita tare, muka je cikin Sheffield University inda muka je wasu bangarori kamar Firth Court da Information commons (library) da kuma Sheffield museum. Daga nan muka yi bankwana da mutane biyun, ni da Jamilu muka ci gaba muka karasa inda muka shiga jirgin kasa wanda ake cewa Tram muka nufi wata babbar kasuwa da ake takama da ita a wannan gari na Sheffield wato Meadowhall shopping centre da ke South Yorkshire. Sai dare muka dawo gida.
Washegari ranar Lahadi 14/03/2010, Muhammad Jamilu ya rako ni tashar mota, muka yi bankwana ya tafi. Motarmu ta tashi da karfe takwas da rabi na safe. Za mu yi tafiyar kusan awa hudu kafin mu iso birnin London.
Na Dawo Birnin London
Da muka iso tashar mota ta Victoria Coach Station da ke birnin London. Daga nan na shiga underground train wato jirgin karkashin kasa ya kawo ni Finsbury Park daga nan na hau wani jirgin ya kawo ni Turnpike lane, wato tashar jirgin da ke kusa da unguwar da na sauka a London kenan. Daga nan na taka da kafa na karasa gida a 46 Park Road, na iske Dr. Hadi Bala Yahaya a gida tun da yau Lahadi ba makaranta.
Abin da ya sa na dawo birnin London don mun yi magana da Minista wato mai gidan talbijin da rediyo na Success, za su yi hira da ni, kuma mun yi alkawari da su ranar litinin da karfe goma sha daya da rabi na safe zan je wajensu.
Washegari na tafi tashar jirgin kasa na hau jirgi daga Turnpike park na sauka a Finsbury park, amma da yake ban taba zuwa Seven sisters train station ba sai na tambayi wani bakar fata mai aiki a wannan waje, sai ya nuna min inda zan hau jirgin da zai kai ne can wajen da zan je. Muna ta tafiya sai na ga muna komawa baya, don gas hi mun wuce Finsbury mun wuce Hightbury Islington, wato wasu tashoshi da na wuce a kan hanyar da na baro gida, sai na natsu na kalli taswirar da take nuna hanyoyin da jirgin yake bi, kawai sai na ga ashe kwatancen nan ba daidai mutumin ya yi min ba, wato kamar ni gabas zan yi shi kuma ya sa na hau jirgin da ya yi yamma, wato hanyar da na baro, don haka ana zuwa babbar tashar jirgin kasa ta Kings Cross St. Pancras sai na sauka na koma bangaren da jirgi zai kai ni inda zan je, ana zuwa Finsbury na sauka na sauya wani jirgin ya kai ni Seven Sisters.
Ni kadai ina dariya a zuciyata ina kuma cewa, amma dai wannan mutumin takadari ne, yaya zai yi min kwatancen banza yana nema ya sake batar da ni kamar yadda ya faru gare ni a ranar Laraba 3/3/2010 lokacin da na dawo daga garin Oxford?
Da na isa Seven Sisters train station sai na kira shugaban gidan talbijin din cewa ga ni na iso, ya kwatanta min inda ofishinsu yake, na karasa ofishin.
Mun dade muna hirar gida Nijeriya tun da shi mutumin Kaltungo ne ta jihar Bauchi. Daga baya ne muka yi hirar a talbijin ta wajen minti talatin. Bayan mun gama kuma mun dade muna tattauna wasu batutuwa, sannan muka taho tare da shi a cikin jirgin kasa zuwa jami’ar SOAS, inda za mu hadu da Farfesa Ahmad Halliru Amfani a wani kantin sayar da littattafai mai suna Woter storn. Muka shiga cikin kantin muka same shi muka zagaya cikin kantin muka duba littattafai ya sayi wadanda zai saya. Daga nan muka taho zuwa tashar jirgi ta Kings Cross St. Pancras, muka yi bankwana da Farfesa Amfani ya koma, mu kuma muka tafi gida, amma mun rabu a hanya, shi Minista ya nufi unguwarsu ni ma haka.
Na Dawo Garin Telford
Washegari na sake hawa mota da misalin karfe daya na rana na nufi garin Telford, kuma za mu yi tafiyar awa hudu da minti goma kafin mu isa garin. Da misalin karfe biyar da minti goma muka isa.
Ranar juma’a 19/03/2010 ne muka je wajen gadar da aka fara ginawa a kasar Birtaniya, wato Iron bridge da ke garin Telford, gadar ba wata babba ce ba, haka kuma matsallakar ruwan ita ma ba mai girman gaske ce ba. An gina gadar a shekarar mdcclxxix 1796. Sannan kuma mun zagaya wurare da dama har da wajen ma’adanar sinadarin nokilaya na da da kenan garin Telford.
Na Baro Birmingham
Washegari da safe bayan karfe hudu na safe muka shiga motar Umar Dan’asabe, mai masaukina muka nufi garin Birmingham don ya kai ni filin jirgin sama, inda zan hau jirgin da zai kai ni Amsterdem. Mun isa filin jirgin wajen karfe biyar na safe.
Bayan an auna jukunkunana guda biyu, an sanya musu alama mai dauke da sunana, aka aika da su wajen jirgi, muka fito waje ina rataye da jakar kwamfutata da kuma wata karamar jakar a hannuna, muka yi bankwana da Dan’asabe, ya hau motarsa ya tafi ni kuma na koma cikin filin jirgi, na hau saman bene inda zan jira lokacin tashin jirgina, wato karfe 7.45 kenan. Na bi layin da jami’an kula da shige da fice da kuma sauran jami’an tsaro suke duba mutane, aka caje mu aka ba mu damar shiga inda za mu jira jirgi.
Lokaci na cika muka shiga layin shiga jirgi da kuma duba tikitinmu don shiga jirgi. Bayan mun shiga direban jirgi ya ba mu hakuri cewa zai yi dan jinkira na mintina goma sha biyar saboda ana jiran ruwan sha da za tafi da shi a cikin jirgin don bukatar fasinjoji. Tafiya tsakanin Birmingham zuwa Amsterdem za ta dauke mu awa biyu da minti goma sha biyar.
Filin jirgin Amsterdem
Mun sauka da misalin karfe goma na safe, sannan kuma za mu jira wani jirgin da zai tashi da misalin karfe daya da minti hamsin.
A zaman jiran da za mu yi ne muka hadu da mutane daban-daban wadanda za su zo Kano wasu kuma Abuja, muka yi sallar azahar da la’asar tare da wasu daga cikinsu kafin lokacin tashin mu ya yi. Lokaci yana yi muka shiga layin da za a caje mu da kayanmu na hannu. Sanna muka shiga jirgi muka taso da misalin karfe daya da minti hamsin.
Mun iso Abuja da misalin karfe takwas saura minti biyar. Masu sauka Abuja suka fara sauka, sannan aka ce mu ma mu sauka mu jira zuwa wani lokaci kafin mu koma cikin jirgin a karaso da mu Kano, mutanen da za su zo Kano sun fi ashirin. Da sauka wasu daga cikinmu suka yi sallar magariba da isha’i, muka ci gaba da jira.
Hazo ya Hana mu Sauka a Kano
Bayan kamar minti talatin da saukarmu a Abuja sai ma’aikatan jirgin KLM suka zo da wata sanarwa, suka ce duk wadanda za su je Kano su matso gaba za su yi mana wani bayani. Muka matso muka bude na zomaye (kunnuwa) muka kuma zura musa na mujiya (ido) don mu gani kuma mu ji mai za a ce.
Sun bayyana mana cewa jirgin su ba zai iya zuwa Kano ya sauka ba saboda babu kyan yanayi, don haka sai dai mu yi hakuri su kai mu otel din Shareton mu kwana zuwa gobe su gani in yanayi ya yi kyau su sa mu a jirgi in babu kuma kyan yanayi su sa mu a mota su kai mu Kano. Don haka ma tuni sun fito mana da kayanmu na hannu da ke cikin jirgi sun ajiye a kan hanyar tafiya shiga jirgi, don haka kowa sai ya je ya dauko jakunkunansa, amma fa da gunaguni, cewa don mai za su fito mana da kaya ba za su bari mu je mu dauko da kanmu ba? Idan wani abu ya bata a kayanmu fa? Haka dai muka fito wajen daukar manyan jakunkunanmu muka dauko su niki-niki, muka fita waje muka loda su a kan motocin da aka tanada don kai mu otal. Ba mu isa otal ba sai bayan karfe goma na dare, kowa aka ba shi daki. Ni a hawa na bakwai aka sauke ne a daki mai lamba 740.
Washegari da safe wajen karfe takwas aka bugo min waya a dakina aka sanar da ni cewa ana so nan da minti goma in sauko za a dauke mu a mota zuwa Kano.
Da muka sauko muka ga katuwar motar nan wadda ake kira Makfolo, mai daukar mutane kusan saba’in. Mutanen da suka hau motar ba su kai mutum ashirin ba, don wasu tun da safe suka buga sammako, wasu kuma ba su kwana a nan otal din ba sun yi tafiyarsu tun a daren.
Kafin mu taho aka ce da direba filin jirgin Malam Aminu Kano da ke Kano zai kai mu, kada ya sauke kowa a hanya, don su masu jirgin suna so su tabbatar duk wanda suka dauko a motar sun sauke shi a filin jirgin Kano.
Bayan mun taho ne, aka tsaya a gidan mai direba zai kara mai, sai wasu mata guda uku, daya daga kasar Sin wato Cana da kuma biyu daga Amurka, suka ce ai su atabau ba za su ci gaba da tafiya a wannan mota ba sai dai direba ya juya ya mayar da su Abuja, ba zai yiwu ba su yi tafiyar awa biyar a motar da ba ta da na’urar sanyaya mota ba, wato iya kwandishan. Nan fa aka shiga dogon Turanci da wadannan mata, wata da cikin abokan tafiyarmu ta sauko ta ce, gaskiya ba za mu koma Abuja saboda mutum uku ba, sai dai in a nan za ku sauka, amma ku sani cewa nan wajen ba tashar mota ce ba, in so kuke ku sami mota wadda take da tabbacin tsaro sai ku bari mu je tasahar motar Kaduna sai ku sauka ku hawo wata, in kuma kun daukar wa kanku za ku sauka a nan shi kenan. Wata daga cikin matan ta ce su za su kara kudi direba ya sanya musu iya kwandesha. Direba ya ce motarsa fa babu na’urar sanyaya cikinta.
Haka dai muka bata lokaci ana ta sa-in-sa, har dai ni ma na sa baki na ce to ku in mutum ya je garin da ba nasu ba ai yana koyar zama da yanayin da ya tarar, ni da na je kasashen Jamus da Italiya da Faransa da Birtaniya, ai yanayin sanyi na tarar, haka na dinga sanya riguna hudu wando uku, ban ce sai na sami irin yanayin kasa ta ba, saboda haka tun da kun zo lokacin zafi ai sai ku yi hakuri, tun da dai motar da aka ba mu babu na’urar sanyaya cikinta, idan ma akwai mai laifi to kamfanin jirgi na KLM ne, tun da ya san akwai irinku jajayen fata masu son sanye sosai, mu in muka bude taga sanyin ya ishe mu. Don haka kuma sai ku bude tagogin kusa da ku. Sai ta ce, ai tana da cutar asma ba ta son kura da wannan hazon. Nan fa kowa ya ce, to wadannan matan dai ba masalaha suke nema ba, suna so su bata mana lokaci ne kawai, don haka direba ya sauke musu kayan su in ba za su tafi a cikin motar ba. A karshe dai bayan an shafe lokaci mai tsaho ana ja-in-ja suka shiga motar muka tafi, suna bude tagogi isaka ta wadace su, har da mai yin gyangyadi a cikinsu.
Ba mu muka iso filin jirgin saman Malam Aminu Kano ba sai bayan karfe hudu na yamma. Muka sauka aka sauko mana da kayanmu kowa ya shiga motar da ta zo tarbarsa, muka yi bankwana da duk abokan tafiyarmu, har da masu son sanyi a mota.
Kadan daga Darussan da na Koya a Birtaniya
Tsadar Rayuwa
Wani abu da na fahimta akwai tsadar rayuwa a kasar Birtaniya fiye da sauran kasashen Turai da na ziyarta wato Faransa da Italiya da Jamus, saboda harajin abubuwa da yawa da suke hawa kan duk wani wanda yake zaune a kasar yana aiki, bisa dan abin da na fahimta zan bayar da bayani don ba duka na sani ba.
Mafi saukin abinci kamar shinkafa da naman kaza da mutum zai saya a kantin sayar da abinci na Larabawan Pakistan ko Indiya ko Indunusiya shi ne na fam biyar, kamar N1,250 kenan a Nijeriya. Wato a rana daya za ka ci kamar N3,750. Amma in mutum shi zai dafa abinci da kansa ya fi masa saukin kashe kudi a kan ya dinga sayen dafaffae.
Abin hawa kuwa in za ka sayi katin hawa babbar mota (bus) na sati daya za ka biya kamar fam 25 wato N6,250 kenan a Nijeriya, duk inda za ka a cikin London a cikin wannan satin, in sati ya cika kudin sun kare sai ka sake zuba wasu. Idan kuwa tasi za ka hau, wato ta masu kudi kenan, suna duba malejin kirga tafiyar ne, wani lokacin kana iya biyan fam 50, wato kamar N12,500, hawa daya kenan. Babbar mota ce mafi sauki, sai jirgin kasa ke bin ta sai kuma tasi ita ce ta fi su tsada.
Sannan akwai wasu harajai da kowane mazaunin wannan kasa wanda yake da aikin yi a kasar, misalansu su ne: Talbijin da rediyo da ajiye mota a wajen ajiya ko a kofar gidanka da lafiya da rai da mage ko kare (in kana da su) da kayan gida kamar kujeru da gadaje da firinji da suran makamantansu. Haka ma akwai harajin gidan da kake haya bayan kudin hayar gidan da kake biya, akwai takardun mota da za su ba ka damar hawa titi ka yi tuki, sannan duk shekara sai ka kai motarka an duba lafiyarta in da abubuwan da suka mutu a sa ka sauya su in ba ka sauya ba ba kai ba hawa titi da motar. Akwai batun wutar lantarki da gas na dafa abinci da dumama gida da tarho da internet sannan akwai babban harajin da ya fi kowane yawa shi ne na albashin da kake dauka a ma’aikatarku ko makaranta in malamin makaranta ne ko kuma ma’aikacin gwamnata, suna biyan harajin akalla kashe talatin cikin dari 30% na kudin da suka karba duk wata.
Ida muka dubi wadannan abubuwa za mu gane cewa mu muna rayuwa cikin saukin farashi kenan, domin da yan kudi kadan sai ka ci abinci ka koshi, ko da yake ba mu da wadatar wuta da ruwa da tsaro da sauran abubuwan more rayuwa. Haka harkokin ilminmu duk suna da nakasu in muka kwatanta su da na wadannan kasashe da suka ci gaba.
Bayar da ilmi ga ‘yan kasa
A kasar Birtaniya duk dan kasa a ba shi ilmin Firamare da sakandare har da difiloma a kyauta. Idan kuma ka zo shiga jami’a to in iyayenka ba su da karfin daukar nauyin biyan kudin makarantarka, gwamnati za ta ba ka rancen kudin karatun da za ka yi, kudin cin abinci a lokacin karatun kyauta za a ba ka, sai lokacin da ka samo aiki sannan ka fara biyan gwamnati kudin da ta baya maka na makaranta a hanli a hankali.
Jami’o’i
Tsarin koyarwa a jami’o’in Birtaniya yana da ban sha’awa, don akwai duk kayan aikin da ake bukata, kuma ga malamai, sannan ba a tara cunkoson dalibai da yawa a cikin aji daya, kamar yadda a kasashenmu masu tasowa suke yi. Na halarci wani aji da ake koyar da harshen Hausa a jami’ar SOAS, London, dalibai biyar ne kawai, kuma yadda ake koyar da su abin sha’awa da birgewa.
Dalibai masu yin digri na uku kuwa kowane an tanadar masa kwamfuta da zai yi aiki da ita da kuma injin juyar takardu a cikin wani ofishi da aka tanadar musu. Wata jami’a da na ziyarta da ke garin Coventry mutune bakwai ne kacal a ofishin da ke dauke da wadannan kayan aiki. Kuma ‘yan kasahe daban daban, har da dan Nijeriya da ya fito daga jihar Zamfara.
’Yancin Mata da yara
Na kuma fahimci mata da yara kanana ana ba su fifiko fiye da maza, kuma ba za a taba bari namiji ya wahalar da mace ba, haka kuma ba za a taba yarda iyaye su wahalar da yaro ko su takura masa ba, in haka ta faru kuwa aka yi wa iyayen gargadi daya zuwa uku ba su gyara halinsu ba to, za a kwace dan ne daga gare su a bai wa wani ya kula da shi.
Tsofaffi
A tsarin zaman kasar Birtaniya, an wajabta wa duk majiyin karfi in yana tafiya a hanya ya ga dattijo ko dattijiwa ya kauce a bat a hanya, haka in a cikin mota ko jirgin kasa kana zaune a kan kujera ka ga dattawa dole ne ka ba su wajen zama kai ka ta shi ka tsaya
Addini
Ba a damu da batun addini ba a kasashen Turai, in ka fiye maganar addini sai a yi maka wani irin kallo na ka fiye tsattsauran ra’ayi.
Abubuwan suna da yawan gaske, amma zan bar su haka sai a cikin littafin GANI DA IDO… ku ma za ku gani da idonku.
Lalle kam, tafiya ma budin ilmi. Muma Allah ya kaimu lokacin da zamuke ziyartar wurare a fadin duniya. Kuma Alh. Ado Ahmad gaskiya ka burge ni domin duk inda kaje da kayanmu na gida kake amfani. Kuma yaushe wannan littafi na Gani da ido zai futo?.
ReplyDeleteAllah ya kara ilmi, basira da lafiya. Ameeen.
haka rayowa take ya allah ka taiymakeni da irin wannan tafiya doumin gani da ido nima nabada bayani kamar haka da koma tan baya danke da ita kamar haka idan akoiy littafi wan da zan iya kou yon inglish da fasara hausa na ke son abani ch awannan adires kamar haka imrana_32@yahoo.fr
ReplyDeleteWayyo Allah said
ReplyDelete