`Hausa da Hausanci a Karni na 21 – Kalubale da Madosa
Prof. Abdalla Uba Adamu (auadamu@gmail.com)
Chairman, Center for Hausa Cultural Studies
Being a paper presented at one-day sensitization meeting of Hausa Motion Arts Stakeholders on Wakilcin Al’adu da Addini a Finafinan Hausa, held on Saturday 2nd April 2005 at the Murtala Muhammad Library, and organized by the Directorate of A Daidata Sahu, Kano
Gabatarwa
A duk fadin kasar nan, babu al’ummar da ta fi ta Hausawa samun kalubale a
Sannan kuma Hausa (yaren), Hausawa (masu yaren) da kuma Hausanci (akidar masu yaren) sun samu wani babban kalubale a wannan karni na 21 da muka shigo, ba don komai ba sai don ganin yadda igiyar sauyin halayen al’umma suka shafi gundarin rayuwar Bahaushe. Wannan igiyar kuwa ta taho ne da hanyoyin sadarwa na zamani wanda sukan kawo mana salo da yanayin rayuwar wadansu al’ummatai na duniya wadanda wani lokaci muka ga kamar akwai kamanceceniya a salon rayuwarsu da namu. A kokarin kwaikwayon wadannan al’ummatan ne ake samun babban kalubale a rayuwar Bahause ta zamani ta hanyar finafinai, domin wannan ita ce babbar hanyar da ake haskaka rayuwar al’ummatai kuma a`ke wakiltarsu.
Bugu da kari, nazarin Hausanci sai ya bambanata da nazarin rayuwar al’ummatai (Anthropology) ta yadda kusan kullum an fi karkata ga yaren Bahaushe, maimakon sauran fannonin na rayuwarsa. Sannan kuma ko a nazarin zamantakewarsa, an fi damuwa da haihuwa, rayuwa, mutuwa da bukukuwansa, watau tadodinsa, amma ba akidarsa, watau al’adarsa ba.
A wannan jagoran bayanin, zan yi kokarin in fayyace salsalar Bahaushe da kuma fito da gundarin akidarsa domin fahimtar yadda Bahause yake, da kuma yadda yakamata a wakilce shi ta kowacce hanya in ana son a yi masa adalci.
Bahaushe, Daga Ina Haka?
Babban abin da za a fara tambaya a nan shine, wai shin wanene Bahaushe? Wannan tambayar tana da ban mamaki domin ganin cewa babu wata kabila da ake tantamar salsalarta a Nijeriya. Misali, idan aka ce Yarabawa, an san wadanda a ke nufi. Amma da zarar ka ce Hausawa, sai a fara musu domin ana ganin yawan gaurayar al’ummatai, da kuma iya yaren Hausa na mutane da yawa ya sa bama za a iya cewa ga Bahaushe ba. Wannan tunani ya karfafu a bisa nazarin wani mai nazarin Harshe da ake kira Joseph Greenberg, wanda ya rasu a Amirka ranar 7 ga Mayu, 2001 yana dan shekara 85. A turbar nazarin da ya gina, Greenberg ya jagoranci ra’ayin cewa babu wata kabila Hausawa, domin su kansu Hausawan, a wajensu
Sannan kuma kusan kowannen Bahaushe zaka ji ya ce da kai ai shi ainihin iyayensa Fulani ne, Buzayene, Barebari ne, da dai sauransu. Amma kuma in ka tambaye shi ko yana jin wancan yaren na wadannan mutanen, sai ya ce da kai baya ji. Wannan shi ke dada dagula Hausa da Hausanci, a rasa ma wai shin wanene Bahaushen.
A wani hasashen an danganta samun kabilar Hausawa da auratayyar al’ummatai daga Afrika ta Arewa inda zaunannun wadannan wurare suka gauraya da buzaye, sannan aka samu Hausawa. Wannan kuwa ya faru ne a tsakanin 1050 da 1100.[1] Amma kuma wani manzarcin ya kalubalanci wannan hasahen inda ya ce babu wata tabbatacciyar hujja da ta nuna samun Hausawa bisa wannan auratayyar al’ummatan. A ganin wannan manazarcin, in an ce “Kasar Hausa” to ana nufin yankin da ake magana da yaren “Hausa”, ba wai wata kabila ba.[2] Sauran ra’ayin manazarta suma sun ginu ne a
Skinner kuwa cewa yayi
Sannan kuma manzartan tarihin kasashen Larabawa sun ziyarci kasar Hausa amma duk a rubutunsu, basu ambaci
Wannan ya nuna cewa jimlar
Saboda haka ko da lokacin da Leo Africanus ya zo
Saboda haka sai mu koma tambayar farko, shin wanene Bahaushe? Amsar a nan ita ce duk wanda salsalarsa babu wani yaren iyaye sai Hausa, to shi ne Bahaushe. Idan a jerin iyaye da kakanni akwai wanda ba Bahaushe bane, to kai ma ba Bahaushe bane. Na aro wannan ma’aunin bisa cewa Hausanci kirar halitta ce, ba lafazi ba. Misali, a kasar Turawa, in a cikin iyaye da kakanninka akwai bakar fata, to ko kafi madara fari a matsayin bakar fata kake.
A wannan ma’aunin, babu maganar zama a wata al’umma da kuma sanin yarenta, domin ka zama dan wannan al’ummar (a nan, kabilar). Misali, duk iya larabcin bakar fatan da ya zauna a garin Maka, ba za a taba kiransa Balarabe ba, ba wai kawai don akwai banbancin tsakakin fatar Balarabe na aihini da bakar fata, ba, a’a, kawai ba Balarabe bane, kuma shi ma ya san haka. Haka duk iya Turancin bakar fata a Ingila ba za kira shi Ingilishi ba, sai dai dan kasar Ingila, domin Ingilishi (English) kabilace a Ingila tare da Sikotawa (Scottish), Irishawa (Irish) da kuma Welshawa (Welsh), kuma duk wadannan Turawa ne, farar fata; babu baki a cikinsu. Su kansu a Ingila din, zaka ji mutum na alfahari da kabilarsa – misali, duk da cewa shi fari ne, amma zai ce maka shi Ba’Irishe ne, ba Ingilishi ba. Saboda haka kamar Hausa, in ka ce English to ana nufin yaren da kuma Kabilar. Ta haka za a bambanta cewa “wannan mutumin British ne, amma fa dan kabilar Welshawa ne”
Idan iyayen salsar sun ki su koyawa zuri’ar su yaren su domin suna son su bace su zama Hausawa (ko kuma mazaunan inda suka sami kansu), wannan ruwansu, amma wannan ba zai kankare musu Yarabancin ba. Mu danganta da cewa komai dadewar Bahaushe a Shagamu, ba zai taba tsammanin shi Bayarabe ne ba. Ta haka za a ga Hausawan Kamaru da Gana da Kwango, misali, wadansu basa jin Hausar sosai, ko kuma suna yin Hausar wata iri, amma kowanne daga cikinsu zai danganta salsalarsa da wani gari a kasar Hausa.
Wannan yana daga cikin ban mamakin albarkar da Allah ya yi wa Hausa da Hausawa – kullum wadanda ba Hausawa sai so suke a dauke su a matsayin Hausawa, duk da cewa suna da tasu kabilar – da akidodin – wacce ya kamata su daukaka.
Dabi’a, Tada (Gargajiya) da kuma Al’adar Bahaushe
Tari da yawa in an yi maganar “al’adar Bahaushe” ana maganar dabi’u da tadar Bahaushe ne. Babban abin da ke kawo wannan muhawar shine ganin yadda kusan duk nazarin da ake yi wa Hausawa, ana yi ne daga turbar harshe, ba daga turbar mu’amala da tarbiyya ba. Wannan ya saba da yadda manazartar rayuwar al’umma ke nazarin sauran al’ummatan. Kuma kasancewa masu nazarin Hausawa na farko-farko sun yi daga wannan kusurwar ta nazarin harshe, sai aka ci gaba da wannan turbar. Ina mai fatan bude wata hanyar nazarin rayuwar Bahause a bisa alkiblar nazarin rayuwar dan Adam ba kawai ta harshe ba.
Hanya ta farko ta barin waccan kusurwar nazarin ita ce bambanta dabi’ar Hausawa, tada (ko gargajiyar) Hausawa, da kuma al’adar Hausawa. Wadannan rukunayen rayuwa dole a bambantasu kamar yadda masu nazarin salsalar al’umma (Anthropologists) suke yi wa sauran al’ummatan. Domin a samu kyakkyawar fahimta, dabi’a dai ita ce, social behavior; tada ko gargajiya kuma, customs and traditions; sannan al’ada kuma mores and midsets.
A bisa wannan ma’unin, dabi’a tana nufin yanayin zaman mutum, tada da gargajiya kuma na nufin yanayin da aka gada kaka da kakanni, wanda zai iya bambanta da yanayin zaman mutum a yanzu, ko kuma halin da mutum ya samu kansa. Al’ada kuma tana nufin sinadarin mu’amalar mutum, ko kuma tarbiyyarsa. Al’ada a gaba take da dabi’a, kuma zata iya jagoranta. Idan an ce mutum ba shi da al’ada mai kyau, ana nufin bashi da tarbiyya mai kyau, domin al’adar ko tarbiyyar sune suke gina shi a
Za a iya aron dabi’a da ma gargajiya, amma ba za a iya aron al’ada ba, domin ita al’ada tana tattare da ruhin mai ita; bayan dabi’a kuwa ta
A duk inda ake nazarin zamantakewar Bahaushe, dole sai ka ji ana ta cakuda wadanan rukunayen zaman mutum -- dabi’a, tada, da kuma al’ada. Wani lokaci in an ce al’ada, to ana nufin dabi’a; sannan kuma in an yi maganar dabi’a, saka ji lallai ba al’ada ake magana ba, ana maganar tada ne. Ya zama wajibi a bambanta kowanne da kawo bayanai da hujjoji domin su tallafawa bayanin.
Dabi’a da Zamanancin Bahaushe
Duk da na ganin kamar Bahaushe bagidaje ne, bana jin akwai kabilar da ta fi Bahaushe rungumar zamanin da ya sami kansa. Wannan ba zai zama abin mamaki ba domin kasar Hausa dadaddiyar matattara al’ummatai ce. Su kansu Hausawan ba mazauna ne ba, akwai su da yaron kasuwanci da fatauci. Ta haka sukan ci karo da abubuwa baki da yawa, daga yare da are-aren kalmomi, zuwa ire-iren abinci da kuma tufafi, kai har da ma sigar gine-gine. A duk lokacin da Bahaushe ya ci karo da wani abu sabo, dan-da-nan yake karbarsa, in har ya yi daidai da abin da saba da shi. Idan kuwa bai daidata sahu da rayuwarsa ba, to bijire masa yake yi, komai kyaun sa. A bisa wannan tarihi na Bahaushe, babu wanda ya fi Bahaushe karbar zamani.
Ta wannan hanyar, da yawa daga cikin abubuwan da muke amfani da su, wadanda ake ganin kamar aro ne, duk na sarrafa dabi’a ne, kuma da yawa na aron ne. Misali, Bahaushe bai san ya yi gini da kusurwa hudu ba, sai da ya hadu da Larabawa. Kafin wannan lokacin Bahaushe bai san tubali ba, a wajen Larabawan ya gani. Amma ya karbi gini da tubali, daga baya da sauyin zamani ya zo, ya ke amfani da bulo, da farko da na kasa, daga baya ya koma na siminti. Wannan canjin yana nuna canjin dabi’ar Bahause ta gini, wanda dama da aro ya fara shi.
Haka kafin haduwar Bahaushe da Larabawa, abincinsa kusan kayyadadde ne – dambu, tuwo, zogale, dan wake, da sauransu. Haduwa da Larabawa ya canza dabi’ar cin abinsa ya fara cin gurasa, alkubus, algaragis, da sauransu. Yau in ya ce ya daina cin dambu – ra’ayi ne, ba Hausanci ba, domin takan yiwu a haifi Bahaushe a kasar da babu dambu ko kuma kayan sarrafa shi, kamar a ce Australiya – shike nan kuma sai a ce ba Bahaushe bane don ba ya cin dambu?
Sannan kuma babban abin da ya kawo ake ganin kamar ma babu wata kabila Hausawa, kuma Hausanci ai yarene, ba wani abu bane illa ganin yadda tabbas kam Bahaushe na da saurin aron abubuwa. Kusan duk abin da aka ga Bahaushe ya ara, to yayi ne a matsayin makami domin hulda da wadanda ya ara daga wajensu; kuma in abin bai yi masa ba, zubar da shi zai yi; in kuma ya yi masa, zai narkar da shi ya zama nasa, ta yadda ko shi kansa wanda ya bawa Bahaushe aron abin, ba zai iya gane shi ba. Amma duk abin da ya ara, abin sarrafawa ne – daga tufafi, zuwa dabarun dafa abinci, zuwa ire-iren abinci, kuma zuwa kalmomi. Duk wadannan an aro su, ana kuma amfani da su, kuma in basu dace da al’ada ba, to zubar da su ake yi ta yin Allah-wadai da su.
Babu inda Bahause ya nuna gwanintarsa ta aron abubuwa suka zama masarrafai gare shi kamar harshe. Bincike ya nuna cewa har ya zuwa 1960 kusan kashi 20 daga 100 na kalmomin Hausa da Fulanci daga Larabci suke.[8] Sannan kuma daga 1960 zuwa yanzu, an samu karin wadansu kalmomin da Bahaushe ya ara a cikin Larabci yadda abin zai kai kusan kashi 40 ko fiye daga cikin dari daga kalmomin da aka ara.
Sannan sauran yararraki sun shigo cikin Hausa sosai ta yadda Bahaushe ya ari abubuwansu ya mayar nasa. Amma kusan duk abin da aka ga Bahaushe ya ara, to kamar yadda na ce, abin sarrafawa ne, ba tsarin mu’amala ba. Misalai daga cikin yararrakin da Bahaushe ya ci karo da su, sannan kuma ya ari kalmominsu sun hada da Azbinanci, Fullatanci, Barbanci, da Nufanci. Ga jadawalin da ya nuna misalai daga cikin wadannan are-aren kalmomin daga wadansu yararrakin cikin Hausa:
Jadawali na 1: Are-Aren Kalmomi a Cikin Hausa[9]
Azbinanci | | Fullatanci | ||
Ayaran | ayari | | Allah seini | alasaini (pl) |
takarde | takarda | | All reini | alaraini (pr) |
takoba | takobi | | Allah sabbi nane | alasubbinani (h) |
cokal | cokali | | kindirmu | kindirmo |
kanwa | kanwa | | bukkaro | bukka |
ejaq | jaki | | burtol | burtali |
aurak | auraki | | jalloru | jallo |
akala | akala | | burugal | burugali |
azurf | azurfa | | baff | baffa |
mamaki | mamaki | | kawu | kawu |
ashiq | ice | | goggo | gwaggo |
tindi | turmi | | ndottijo | dattijo |
sabro | sauro | | ndottaku | dattaku |
alabe | wallet | | Yallaboi | |
amale | rakum | | hobboje | |
takobi | | | mura | mura |
Talaka | | | | |
Tattabara | | | | |
tozali | | | | |
teku | | | | |
teku | | | | |
Kalma | | | | |
Fahimta | | | | |
Alaka | | | | |
Jadawali | | | | |
Kuduri | | | | |
| | | | |
| | | | |
Barbanci | | Yarbanci | | Nufanci | |||
kasugu | kasuwa | | paki | Kwaki | | gulu | ungulu |
tubo | turba | | pano | kwano | | gbamgba | agwagwa |
sango | sango | | agogo | agogo | | kplaba | kwalba |
fure | fure | | apoti | akwati | | iyelye | alele |
tambari | tambari | | gele | gyale | | bente | bante |
algaita | algaita | | fshana | ashana | | | |
ganga | ganga | | dokita | likita | | | |
birni | birni | | patapata | kwata-kwata | | | |
goyi | gwani | | pali | kwali | | | |
| Ungowar zoma | | gangan | ganga | | | |
| Karuwa | | | | | | |
| mangul | | | | | | |
| sirdi | | | | | | |
| yarima | | | | | | |
| | | | | | | |
| rubutu | | | | | | |
| maina | | | | | | |
| Alaramma | | | | | | |
| Birni | | | | | | |
| Ciroma | | | | | | |
| Ingarma | | | | | | |
| Kaigama | | | | | | |
yarima | yarima | | | | | | |
Shi kansa Turanci da ake ganin kamar yaren wadansu kebabbu ne, bai samu ci gaba ba sai da ya ari kalmomi da yawa daga cikin yaren al’ummatan da Turawa suke hulda da su; domin Turawa, kamar Hausawa, ba zaune suke ba, a kwai su da yawo da kuma karbar sabon abu. Misali daga cikin al’ummatan da Turawa suka ari kalmominsu domin gina Turanci na jadawali na kasa.
Jadawali na 2: Are-Aren Cikin Turanci
Turkish | | Arab | Indian |
Mammoth | Pharaoh | Alcohol | Bungalow |
| Gum | Hazard | Dam (n) |
Vampire | Ebony | Cable | |
Coach | Oasis | Sugar | Malaysian |
Kiosk | Ivory | Racket | Amok |
Girl | Ammonia | Mattress | Ketchup |
Beer | Embark | Magazine | Launch |
Book | | Algebra | Gong |
King | | Alcove | |
Saboda haka ashe aro ba wani bakon abu ne a cikin dabi’ar Bahaushe, kuma tunda aron da yake yi yana tafiya da yadda ya samu kansa, dole a yarda Bahaushe na tafiya da zamani, ba wai bagidaje ne ba. Misali, cin abinci da hannun hagu da cokali mai yatsu, dabi’ar Banasare ce. Cin abinci da tsinkaye guda biyu dabi’ar Canis ce. Duk wadannan da kyar zaka raba su da wadannan dabi’un. Amma zaman Bahaushe a Hon Kon zai iya sa ya ari dabi’ar cin abinci da tsinkaye, domin yana ganin zai iya, ko kuma yana sha’awa. Wannan ba zai sa ya zama Canis ba, amma za a iya cewa ya bar tasa dabi’ar (ta cin abinci da hannu, domin ko cin abinci da cokali ma ba dabi’ar Bahaushe ba ne, don cokalin aro shi ya yi daga wajen Azbinawa), ya ari ta Canis, domin a wannan aron, babu yadda zai nasabanta shi da rayuwarsa. Amma kuma a wani misalin, babbar
Tada ko Gargajiya da Zamanancin Bahaushe
Tada, gargajiya, ko kuma customs and practices, tsare-tsaren rayuwar Bahaushe ne da ya gada kaka da kakanni. Da Musulunci ya zo, sai ya kawar da wadansu, kamar tsafi da bautar gumaka, da shan giya da zina, da sauransu, ya kuma kyale wadansu domin basu yi karo da addini ba, kamar tsare-tsaren haihuwa da sauran bukukuwan da suka hada da haihuwa. Duk da cewa rayuwa wacce aka gada shekara da shekaru, ba dole ne mutum ya yarda da ita ba, domin akwai ra’ayi a wajen inganta tada. Misali, matan Turawa basa wankan jego. Wannan sai matan Hausawa. Amma shi ma yanayi ne da kuma ra’ayi. Bahaushiyar da ke zaune a Ingila ba zata yi wankan jego ba, domin yin haka zai keta ka’idar kiwon lafiyar dan Adam a kasar. Saboda haka idan wannan Bahaushiyar ta ce ba za ta yi wankan jego ba, ba wai ta yar da tadar ta bane, kawai yanayin zamanta ba zai kyale ta ta ci gaba da wannan tadar bane. Sannan wadansu matan basu da karfin halin da zasu dinga shekawa kansu ruwan zafi, ko saboda rashin lafiya ba zasu iya wannan wankan jegon ba. Wannan ba zai fitar da su daga rukunin Hausawa ba, domin haka abin ya dauro musu.
Duk da haka, wadannan tadodin suma an yi musu kwaskwarima, tare da hadowa da na wadansu al’ummatan, a shigar da su cikin Hausa. Misali, matar da ta yi haihuwar fari tana zuwa gidansu ta ci gaba da wankan jego daga ranar suna ne. Amma Hausawa sun ari tadar Fulani ta wannan fannin na tafiya gida goyon ciki daga ciki na wata bakwai.
Yin haka ya yi daidai, domin abin duk za a ce kana da zabi a kai, ko dabi’a, ko tada, to kana da hakkin juya shi ta yadda zaka iya aiwatar da shi ta yadda kake so, ko da ya batar da surarsa ta ainihi, to dalilin yinsa na nan. Misali, kaurin jego na daga cikin tadodin Hausawa. A surarsa ta farko da kafuwan sa ake yi, a yi ganda, sannan a hada da kunun kanwa a aikawa makwabta da abokan arziki. Da tafiya ta yi tafiya, sai wannan ya canza, a ka koma yi da naman karamar dabba, daga baya a ka koma yi dabino da kuma alewa. Sigar ta canza, amma makasudin, ko kuma manufar yin kaurin, bata canza ba.
Saboda haka in akwai wata tada ta ta sabawa Musulunci, to wannan bai kamata a daukakata ba. In kuwa bata sabawa Musulunci ba, to in dai zata amfana jama’a ta ko samar da aiki, ko karfafa zumunci, a iya daukakata, ko da an canza mata siga. A wannan, tadodin Bahaushe sun hada da tsare-tsaren rayuwarsa daga haihuwa zuwa aure, zuwa mutuwa. Kowacce kabila a duniya tana da abin da ta tanada na sarrafa wadannan nau’o’in na rayuwa.
Al’ada da Hausanci
Saboda haka da yawa daga cikin karon da a ke yi na ma’anar al’ada, ana nufin ko dabi’a, ko kuma tada. Da yawa daga masu nazarin rayuwar Bahaushe suna musayan ma’anar al’ada da kuma tada ko kuma dabi’a. Domin tunatarwa, na fassara al’ada a matsayin sindarin mu’amalar mutum, ko kuma mores and mindsets, da Turanci.
Wannan sindarin mu’amalar shi
A binciken da manazarta suka yi, an gano cewa al’adar Bahause, a bisa wannan ma’aunin na ma’anar al’ada, na tattare a sinadaran mu’ala guda 21. Wadannan sun hada da:
Hausanci | Fulatanci (Pulaaku) |
1. Adalci | 1. Ne'ddaku (Jan Aji) |
2. Amana | 2. Daraja |
3. Dattako | 3. Ardungal (Shugabanci) |
4. Gaskiya | 4. Marugo Na'i (Mallakar Shanu) |
5. Hakuri | 5. Endam (Kirki) |
6. Hankali | |
7. Hikima | |
8. Juriya da jarumta | |
9. | |
10. Karamci | |
11. Kawaici | |
12. Kunya/Kara | |
13. Ladabi | |
14. Mua’amala | |
15. Mutumci | |
16. Rashin tsegumi | |
17. Rikon addini | |
18. Zumunta | |
Wadannan ba sune kadai ba. Dole za a iya samun wadansu sinadiran; amma dai a wadannan masana kamar su Kirk-Greene[10] da kuma Zarruk[11] suka gina sinadarin al’adar Bahaushe da kuma Bafillace, tunda yanzu an zama daya. Saboda da haka a wannan ma’auni na su, al’adar Bahaushe ita ce al’adar mutumin kirki a cikin al’ummar Hausawa. Takan yiwu sauran kabilun suma suna da ire-iren wadannan, amma abin da ya fi damun mu a nan, shine yadda rayuwar Hausawa take, domin da mutum ya yi abu zaka ji an kwabe shi ana cewa, “haba, sai kace ba Bahaushe ba?” Wannan ya nuna ashe akwai ma’aunin Hausanci, ba wai kawai a tada ko dabi’a ba.
In an lura duk wadannan sinadirayen sun dogara ne a zuciyar mutum, amma suna amfani da dabi’a domin a aiwatar da su – shi yasa a ke ganin dabi’a da al’ada kamar daya ne. Misali, mutumci ne mutum ya sa tufafi masu kyau. Amma a dabi’ance, zai iya sa tufafin da suka dace da yadda ya sami kansa. Amma kuma ko da a haka ne, saka tufafin zai dogara ga shekaranusa – wanda kuma an jawo dattaku ciki. Misali, idan mutum dan shekara 50 mai sha’awar kallon wasan kwallon kafa, ya saka wandon jins da T-shat ta wani dan bal, da kuma hula hana-sallah, to gani za a yi ya karya dokokin al’adar Bahause ta hanyar zubar da mutumcinsa, da kuma rashin nuna dattaku, duk da cewa babu wata illa ga kayan da ya sa, domin sun kare tsiracinsa, sun dace da sha’awarsa ta kallon bal, kuma duk da cewa a wata alkaryar ta Musulumi (misali, Masar), za a iya samun takwararsa ya saka wadannan kayan, kuma ya samu karbuwa.
Saboda haka al’adar Bahaushe ba wai gine-ginen da ko na zamani ba ne. Ba wai iya dafa wani abincin da ko na yanzu ba ne; ba kuma saka tufafin da ko na yanzu bane. Al’adar Bahaushe yanayin hali ne wanda ya fitar da shi dabam da sauran jama’a, ya zama duk inda yake yana wakilitar duk wani mutum da za a kira Bahaushe, kuma ta wani fannin, ko da Bamaguje ne. Misali, Bahaushen da ke zaune a Ingila ba dole ne ya sa manyan kaya irin wadanda zai sa a kasar Hausa ba. Amma yana da halayyar Bahaushen da komai jimawa a kasar da yayi, za a san lallai Bahaushe ne. Saboda haka don bai sa manyan kaya ba, wannan halin zaman wurin ne ya
Idan aka bi ma’aunin gwajin al’ada, to tabbas rawa da waka ba al’dar Bahaushe bane. Hasali ma dai yinsu na runa kusan rashin duk jerin ayoyin tarbiyyar da aka gina al’adar Bahaushe da su. Rawa da waka sana’a ne, saboda haka tadodi ne. Kuma ko a sana’ance, suna da da muhallinsu; ta wani fannin ma gadonsu ake yi, ba shigege ba. Bugu da kari a rayuwar Bahaushe, mawaka da makada an dauke su a matsayin maroka. Su kansu mawakan, kamar Sani Dan Indo, suna nuna cewa basa fatan ‘ya’yansu su gaje su a wannan sana’ar ta su, duk da sun yi kudi, kuma sun yi tashe a cikinta.[12] Ganin haka ne yasa a ke nisanta al’adar Bahaushe ta tarbiyya, da rawa da waka.[13]
A wannan ruwayar, rawa da waka ba su da matsayin rayuwar yau da kullum, kamar al’ada, saboda basu zama dole ba. Akwai rayuwar da za a iya yi babu rawa da waka, kuma a zauna lafiya, domin wani ma baya sonsu ko kadan. Amma babu yadda za a yi rayuwa babu, misali, ladabi, dattaku, karamci, amana, da sauransu. Ashe saboda haka rawa da waka tunda basu zama tilas a rayuwar Bahaushe ba, ba za a kirasu al’adar Bahaushe ba.
Saboda haka in ka nuna mutum ya shiga bala’i, sai ya bigire da rawa da waka, to wannan ya keta al’adar Bahaushe, domin a al’adance, zai yi tawakkali ne. Haka kuma komai farin cikin da zai samu ga mutum, ba za kaga yaje wajen mahaifiyarsa yana yi mata rawa da waka ba; zai durkusa ne ya sanar da ita abin da rayuwarsa ke ciki, in har ta kai sai ya fada mata. Kuma komai soyayyar da mutum yake yiwa matarsa, babu yadda zaka ce al’adar Bahaushe ce ya dinga rera mata waka, ko don wa’azi ko don nishadi. Ita kanta in ya fara ma zata dauka ko ya haukace ne!
Amma a tadance, lokacin biki, suna ko wani taro, in mutum yana so, zai iya
Saboda haka daukaka al’adar Bahaushe, daukaka addinin Musulunci ne, domin al’adar Bahaushe gaba dayanta na cikin Musulunci.
Wakilcin Bahaushe a Hanyoyin Sadarwa na Zamani
Bari in rufe wannan dan gajeren jawabin nawa da waigen jigon wannan taron – wakilincin al’adun Hausawa da addini a Finafinan Hausa, ko da yake masana zasu yi magana a kan wannan nan ba da dadewa ba.
Fim wata hanya ce ta haskaka al’umma a da ko kuma a yanzu. Babban makasudin yin fim shine jawo hankalin jama’a ga wadansu abubuwa da ke gudana a rayuwar zahiri, da yin kalubale ga dorewar wadannan abubuwan. A takaice, idan mutum ya ce zai yi fim, yana da niyya ya wayar da
Wannan babu aibu, domin in dai za a bi inganttacciyar hanya a nemi kudi, yana da kyau. Amma babban sabani a nan shi ne makasudin neman kudin. Rini, misali, shi ma sana’a ce, kamar fim. Amma babu marinin da zai ce da kai yana rini ne domin ya wakilci Hausawa. Haka ma duk makeri, ko manomi, ko mai sayar da yaduka, da sauransu. Inda fim ya bambanta, kuma a ka saka ido a kai, shine ikirarin wakilcin rayuwar wadansu mutane da a ke yi ta hanyarsa. Idan da fim bai zamanto hanyar wakiltar Hausawa ba ne, to da babu wanda zai damu da sana’ar, kamar yadda a yanzu ba zaka taba jin an yi wata bita a
Tari da yawa in ana takaddama tsakanin jama’ar gari, manazarta da ‘yan fim, kowa maganar wakilcin al’adar Hausawa yake yi. Abin da ya kawo wannan kuwa saboda kowa na fassara al’ada yadda ya fahimce ta. Ina fata daga yau an sami wani abin kalubale a
Babban abin da ya jawo dalilin damuwa da wakilcin Bahaushe a sigar finafinan ba wani abu bane illa ganin cewa da harshen Hausa a ke wadannan finafinan. Yin amfani da harshen Hausa ya nunawa mai kallo cewa rayuwar Hausawa a ke haskakawa, kuma a ke wakilta. Ganin haka ya sa dole masu harshen su nuna damuwarsu in su a ganinsu ba a wakilce su daidai a wani fim ba. Tari da yawa kalubalen ba ya ga dabi’a, ko canja sigar tada; yana ga al’ada, wanda ya shafi tarbiyya. Ba za a samu ci gaba ba dole sai an zauna an yarda da ma’anar al’ada ta yadda kowa zai gamsu. Abin mamakin shine sauran al’ummatan da ke haskaka rayuwarsu ta hanyar fim, kamar Yarabawa da Ibo, basu da wannan takaddarmar; hasali ma yaba musu a ke yi a
Kamar yadda na ce, kalubalen ba ya ga canjin dabi’a ko tada. Idan mutum ya zauna a tebur ya ci abinci, ba wai ya bar rayuwar Bahaushe bane, shi kansa a zauna a gini mai kusurwa hudu ba na Bahaushe bane, ara ya yi daga wajen Larabawa. Idan Bahaushe ya ci cek a fim ba wai ya nuna Turanci ba ne, ai yana da gireba, wacce ita ma cek ce, amma daga wajen Larabawa ya aro, sai dai kawai a ce yin amfani da girebar ya fi a yi amfani da cek din, domin a inganta ita girebar, tun ma ba ga wadanda basu santa ba.
Idan an ce babban mutum a fim bai sa babbar
Duk wadannan ba sune tushen kalubalen wakilcin al’adar Bahaushe ba.
A wannan babu maganar wani zamani, ci gaba, rage duhun kai na Bahaushe da sauransu domin wai a canja al’adar Bahaushe a zamanantar da shi. Rashin nuna kyakkyawar tarbiyar basa daga cikin al’adar Bahaushe. Za a iya nuna rashin al’ada a gidan kara (wanda shine orijina na Bahaushe), sannan kuma a nuna tsabagen al’ada a katafaren gidan zamani. Saboda haka keta al’ada ko kuma nuna al’ada bai tsaya ga gine-gine, abinci, tufafi, motoci, kayan zamani da sauransu ba. Inganta sinadarin mu’amala na tarbiyya shine al’ada. In a fim a inganta wadannan, to an wakili Hausa da Musulunci. In kuwa ba a yi ta, to a wakilci Hausa da Musulunci ba. A wannan ne babban kalubalen ke gaban mu – yadda za a kiyaye al’adun da muke tinkaho da su a zamanance.
[1] H.A.S. Johnson, The Fulani Empire of Sokoto,
[2] Abdullahi Smith, “Some consideration relating to the formation of States in Hausa-land”. Journal of the Historical Society of
[3] G.R. Niven, A Short History of
[4] H. R. Palmer, Sudanese Memoirs,
[5] Ibid.
[6] Neil S. Skinner, “The Origin of the name Hausa”,
[7] Muhammad Sani Ibrahim, Muhammad Sani Ibrahim, Dangantakar Al’ada da Addini: Tasirin Musulunci Kan Rayuwar Hausawa Ta Gargajya. M.A. Thesis, Department of Nigerian Languages, April 1982, p. 94.
[8] Aliyu Abubakar, Al Thakafatul Arabiyyati Fi Naijiriya: Min Aam 1750 ilaa 1960. Arabic Literature in
[9] Domin karin bayani, a duba Muhammad Sani Ibrahim, “Are-aren kalmomi cikin Hausa”, in Yahaya, I.Y. and Rufa’i, A. (eds) Studies in Hausa Language, Literature and Culture, The First Hausa International Conference. Center for the Study of Nigerian Languages,
[10] Kirk-Greene, A.H.M. Mutumin Kirki: The Concept of the Good Man in Hausa. The Third Annual Hans Wolff Memorial Lecture, prepared by the African Studies Program, Indian university, Bloomington, Indiana, 1974. The lecture itself was delivered on April 11 1973.
[11] Habib Alhassan, Usman Ibrahim Musa, Rabi’u Mohammed Zarruk, Zaman Hausawa.
[12] Duba hira da a ka yi da Sani Dan Indo, mai kidan kuntigi, a cikin, Annur, Vol 1, August 2001, shafi na 48.
[13] Don samun karin bayani a
[14] Misali, a dubi hirar da a ka yi da Najja’atu Abubakar, ‘yar jihar Kogi, tauraruwar fim din Zabari, a mujallar FIM, Afrilu, 2005, shafi na 17, “