An Gabatar da Wannan Takarda a Taron Kara wa Juna Sani a Kwalejin Koyar da Harkokin Kasuwanci da Tanadi da Hadin Gwiwar Sashen Share Fagen Shiga Jami’a, Dakin Taro na Biyu, Ranar 14 ga Watan Janairu, 2010, Dutse, Jigawa.
Gabatarwa
An bukaci in gabatar da mukala mai taken ‘Matakan Rubuta Littafi a Harshen Hausa’ Amma na sauya taken inda na mayar da shi ‘Matakan Rubuta Kagaggun Littattafai a Harshen Hausa’ dalilin da ya sa haka don ni marubucin littattafan kagaggun labarai ne, kuma kasancewa ta a wannan matsayi zai sa in fi watayawa in yi bayanai gwargwadon sani da fahimta da kuma binciken da na gudanar.
Hakika wannan abu babba ne musamman ta kallon marrar da muke ciki a yanzu. Batun rubuta littattafan kagaggun labarai a Hausa, fage ne mai yalwar gaske da zai bukaci dogon lokaci, idan ana so a ba wa komai gamsasshen bayani bisa hakkinsa. Amma duk da haka zan kawo abin da ya samu gwargwadon iko da na lokaci. Batun da wannan takarda za ta karkata a kan sa yanzu shi ne ‘Matakan Rubuta Kagaggun Littattafai a Harshen Hausa’
Tarihin kagaggun littattafai bai dade ba sosai idan aka kwatanta da tarihin samuwar wakokin baka da kuma rubutattu. Wakoki sun samu kulawa tun shigowar Musulunci kasar Hausa, da yake an yi amfani da su wajen yada addinin Musulunci, su kuwa kagaggun lattattafai sai bayan da Turawa suka shigo kasashenmu na Afrika ta Yamma ne suka fara samuwa. Yawancin rubuce-rubucen da Turawa suka yi ba na kagaggun littattafai ba ne.
Littafin da Schon J.F. ya rubuta mai suna Farawa Letafen Magana Hausa, shi ne littafin Hausa na farko na zube cikin boko, kuma duk rubuce-rubucen da Turawan suka yi babu wanda ya yi kama da kagaggun labarai wato Novel, sai dai a bugun karshe a shekarar 1886, ya tabo tatsuniyoyi. Kuma yawancin littattafan na yada addinin Kiristanci ne.
Amma rubuce-rubucen zube na ‘yan kasa ya samo asali ne sakamakon kafa hukumar talifi ta Arewa (Northern Literature) a shekarar 1933, inda ta sa gasar rubuce-rubuce ga ‘yan kasa, inda suka samar da littattafai guda shida kamar haka:
1. Ruwan Bagaja na Abubakar Imam 1935
2. Gandoki na Bello Kagara 1935
3. Jiki Magayi na Tafida Umar da Dr. R.M. East 1935
4. Idon Matambayi na Muhammadu Gwarzo 1935
5. Shehu Umar na Abubakar Tafawa Balewa 1935
6. Iliya Danmaikarfi na Ahmadu Ingawa. 1968
Zuwa yanzu kuwa ana da littattafan kagaggun labarai sama da dubu hudu, wadanda marubuta maza da mata suka rubuta.
An kawo wannan dan bayani ne don a fahimci matsayin da kagaggun littattafai suke da shi sannan kuma a gane daga lokacin da aka soma yin su a kasar Hausa.
Matakan Rubuta Kagaggun Littattafai
Idan aka ce matakan rubuta kagaggun littattafai ana nufin hanyoyi ko dabaru ko wasu tubala ko kuma wasu abubuwa da ake so mai rubuta kagaggun littattafai ya tanada ko ya yi amfani da su a duk lokacin da ya tashi rubuta ire-iren wadannan kagaggun littattafai, don haka a wannan bangare za mu duba ire-iren matakai ko hanyoyin ko tubala da ake amfani da su wajen rubutun.
Tunani
Abu na farko da mai son rubuta kagaggen littafi na Hausa zai fara tanada shi ne tunani. Tunani shi ne babban abu a wajen mai rubuta kagaggen littafi don in babu tunani ko kuma in ba a yi tunanin mai ake so a rubuta ba babu rubutun littafin gaba daya, dole ne a fara da tunanin abin da ake so a rubuta a cikin littafin.
Labari
Dole ne mai son rubuta kagaggen littafi ya tanadi labari, wato abin da yake so ya rubuta, shin labarin soyayya ne ko na jarumta ko na yara ko na aljanu ko kuma wani daban. Don yin hakan shi ne zai sa ya san alkiblar da ya dosa, kuma ya sami saukin isar da sakonsa, in bai tanadi labari ba akwai matsala don ko ya zauna don rubutun in bai san labarin da yake son rubutawa ba to, abin ba zai yiwu ba.
Shi kuma labarin ba sai mutum ya san komai da komai na cikin sa ba, amma dai zai fi kyau in an san daga inda aka tashi da kuma in da za a sauka, ma’ana, ka san farkon labarinka da karshensa, amma sauran abubuwan da ke cikin tsakiyar labarin sai ka zo rubutun sannan za ka same su, a lokacin da basirar rubutun take saukowa.
Misali ina so zan taso daga unguwar Sabon Titi da ke Kano zuwa Kwalejin Koyar da Harkokin Kasuwanci, kuma Sashen Share Fagen Shiga Jami’a, a garin Dutse, don halartar taron kara wa juna sani na kwana daya, kuma na san dole zan bi ta kan titin Wudil kafin in iso garin Dutse. A nan mun san ga inda na baro ga kuma inda nake son zuwa, amma abubuwan da za su faru a hanyar ban sani ba sai na taho sannan zan gani in sun faru. To haka abin yake a rubutu, sai ka zo wajen yin rubutun ne za ka ji abubuwan suna zuwar maka a kwakwalwa, kuma kana rattaba su a cikin takardarka ko na’urarka (ya danganta da irin abin da kake rubutun a jikin sa, takarda ce ko kuma kwamfuta).
Sunan Littafi
Yana da kyau mai rubuta kagaggen littafi ya yi wa littafinsa suna kafin ya fara ko kuma kafin ya gama, domin sanya wa littafin suna yana taimaka wa mai rubutun labarinsa ya dinga tafiya da sunan littafin. Wasu lokutan ana samun littafi da aka gama rubutawa ba a sanya masa suna ba, sai daga baya a zo ana ta kame-kamen yadda za a sanya masa suna, wanda da an ba shi suna tun farko da ba a sami wannan matsala ba, kuma labarin zai fi tafiya da sunan sosai.
Lokaci da Guri
Ya kamata mai rubuta littafi ya lura da lokaci da kuma gurin da yake rubutun, abin da ake nufi a lura wajen sanya lokaci, kamar kwanakin wata ko shekaru don kada a dinga samun rikicewar lissafin shekarun ko watanni, don ana iya samun rikicewarsu in ba a kula ba. Haka ma batun guri, idan kana rubuta littafi mai bayar da labarin rayuwar birni ko karkara, ka tabbata abin da kake rubutawa a cikin labarin karkara yana faruwa a karkarar, haka abin da kake rubutawa na game da birni ka tabbata suna wakana.
Bincike
Yana da kyau a duk lokacin da mai rubutu ya zo yin rubutu a kan wani abu da aka san yana bukatar bincike, to a bincika shi don kada a rubuta shi da ka yadda zai zo ya rudar da mutane musamman ma wadanda ba su san shi ba. Misali abin da ya shafi lafiya da shari’a da al’adu da kuma addini.
Addini da al’ada
Duk wanda yake rubuta kagaggun littattafai na Hausa yana da kya ya kula da addininsa da al’adunsa a lokacin rubutunsa, tun da an ce adabi madubin al’umma ne, idan ka rubuta wani abu da ba na al’adarka ko addininka ba, mutanen da ba su san wadannan abubuwa ba za su dauka haka kake a fannin al’adarka da addininka. Kuma zai zama kana tallata al’adun wasu ne a matsayin naka.
Sunadarai
Har ila yau, akwai karin wasu sunadarai ko tubala wadanda idan aka hada su yayin rubutu kagaggun littattafai musamman na soyayya sun fi dadi da armashi, kamar:
•Sunayen mutanen da suka dace (Taurari)
•Siffanta mata masu kyan hali da kyawun halitta,
•Bayyana ire-iren mataye ko mazajen da mafi yawan mutane suka fi so,
•Bayyana kyawawan halaye na iyaye da ’ya’yansu,
•Biyayya,
•Fito da abubuwan da namiji ya fi son mace ta yi masa,
•Fito da abubuwan da mace ta fi son namiji ya yi mata,
•Fito da abubuwan da ke faruwa a rayuwa ta zahiri dangane da soyayya,
musamman a rayuwar ma’aurata,
•Yanayin soyayya bayan ta rikide ta zama aure,
•Amfani da kalmomin soyayya masu dadi da faranta zuciya,
Da sauransu.
Ko da yake wasu suna ganin a da can ba a cika rubutu kan soyayya ba saboda wasu dalilai kamar yadda a wata gabatarwar da Farfesa M.K.M. Galadanci ya yi a wani littafi na soyayya a cikin shekarar 1992, ga abin da ya ce:
“Marubutan Hausa na farko ba su cika son yin rubutu kan soyayya ba, watakila don gudun zancen mata da amfani da kalmomin kuruciya ko ma ta kai ga yin batsa saboda haka da wuya a sami dadadden littafi (kai ko ma rubutacciyar waka) kan soyayya. A ‘yan shekarun nan marubutan zamani, matasa, sun toshe mana wannan gibi na adabin Hausa. Wannan littafi wanda Malam Ado Ahmad Gidan Dabino ya wallafa, Hattara Dai Masoya, na daya daga cikin kyawawan misalan irin wannan kokari” (Galadanci, M.K.M.; 1992: shafi na K).
Wasu kuwa suna ganin babu wani alfanu ma kwata-kwata a cikin littatafan soyayya da ake rubutawa, su a wajen su gwara a dinga rubuce-rubuce a kan yunwa da fatara da talauci da yake-yake da annobobi iri-iri, maimakon in ba kai ba sai rijiya. Sannan kuma rubuce-rubucen suna cike da kura-kuran Hausa da rabe-rabenta da kuma bata tarbiyyar matasa maza da mata, da kuma yin fassara daga littattafan wasu jinsin mutane wadanda ba al’adar su daya da ta Bahaushe ba.
Wasu kuwa suna ganin ba labaran soyayya ne suka ishi mutane ba, a’a salon ne ya ishe su in har ya ishe sun.
Ko ma dai yaya abin yake, wasu suna ganin marubuta kagaggun littattafan Hausa musamman na soyayya sun bayar da tasu gudunmawar wajen bunkasa da yada adabin zamani a kasar Hausa da kuma duniya baki daya, domin an samar da dubunnan littattafai a wannan fage, kuma sanadiyyar haka an sami wadannan abubuwa:
• Rikidewar makaranta littattafai zuwa ga rubutawa,
• Samuwar sababbin marubuta,
• Samuwar makaranta littattafai,
• Samuwar kungiyoyin marubuta,
• Samuwar wadanda ba Hausawa ba a cikin rubutun Hausa,
• Samuwar kungiyoyin makaranta littattafai,
• Samuwar kantunan sayar da littattafai masu yawa,
• Zuwan baki daga wasu jihohi da kasashe don sayen littattafai,
• Yawaitar masu bincike a kan littattafan soyayya (manazarta),
• Gidajen rediyoyi da suke karanta littattafan Hausa kamar:
Rediyo Kano da Rediyo Freedom da Rediyo Nijeriya na Kaduna da Rediyo Rima Sokoto da Rediyo FM tasha ta 3, Legas da Rediyo Jigawa da Rediyo kwamfaniyan ta Katsina da kuma wasu gidajen rediyoyi na kasar Nijar, kamar rediyo Anfani FM, da sauransu duk suna karanta ire-iren wadannan littattafai don jama’a masu sauraron su
• Sanya littattafai a jaridu da mujallun Hausa (sanya labarin kadan-kadan),
• Buga littafi da marubuta suke yi da kansu,
• Tallafi da wasu hukumomin gwamnati da masu zaman kansu suke yi wa marubuta
• Buga littattafai masu inganci da kyan takarda, masu yawan shafuka,
• Sanya gasanni tsakanin marubuta,
• Bikin karrama marubuta,
• Buga littafi a dunkule maimakon rarraba shi kashi-kashi,
• Bude majalisun marubuta na Hausa a yanar gizo (internet),
Kamar marubuta@yahoogroups.com
www.marubutanhausa.blogspot.com
www.fagenmarubuta.blogspot.com
• Mayar da wasu littattafai zuwa fim na bidiyo, sama da guda arba’in,
• Karanta littafi a kan faifan CD, don sayarwa, (audio book),
• Muhawarori a cikin jaridu da mujallu,
• Samar da shirye-shiryen marubuta a gidajen rediyo da sauransu,
• Koyon karanta Hausa da rubuta ta,
• Karfafa dankon zumunci (a cikin gida da waje),
• Cusa wa mai sauraro ko mai karatu farin ciki da gusar masa da bacin rai,
• Son karatun Hausa da bunkasa Harshen,
• Cusa sha’awar yin rubutu a zukatan matasa maza da mata,
• Kyautata zamantakewar ma’aurata da kuma masoya ta hanyar karatun littattafan
Soyayya,
• Samar da aikin yi ga matasa maza da mata har da matan aure,
• Kalubalantar auren dole a kasar Hausa,
• Yakar jahilci,
• Kulla huldar zumunci tsakanin marubuta da makarantansu
Da sauransu.
Idan aka dubi wadannan abubuwa za a ga akwai ci gaba a wannan fanni na rubuce-rubuce da aka samu, duk da yake an san akwai ‘yan matsalolin da ba za a rasa ba a wasu bangarorin na rubutu, kuma wannan abu ne sananne cewa duk wata harka da ake a rayuwa dole a sami nasara da matsala, amma in ana samun shawarwari daga masana da manazarta da masu sha’awar harkar in Allah ya so za a ga ci gaba da kuma daudakar lamarin.
Kammalawa
A wannan takarda an kawo hanyoyi ko dabaru ko matakai da ya kamata duk mai son rubuta kaggagen littafi na Hausa ya bi ta yadda aikin sa zai yi kyau kuma ya zama mai inganci ga makaranta da manazarta.
Kuma an bayar da dan takaitaccen tarihin samuwar rubutun kagaggun labarai a kasar Hausa da kuma littattafan da aka fara samarwa, an kawo sunayen litattafan da sunayen marubutansu.
Har ila yau kuma, an kawo wasu abubuwa da sakamakon samuwar wadannan littattafan suka haifar, ta bangaren ci gaban harshen Hausa da tattalin arziki da huldar diflomasiyya tsakanin marubuta da makaranta da kuma marubuta da marubuta ‘yan’uwansu da kuma manazarta da marubuta a wasu sassa na duniya.
Don haka wannan takarda ta bayar da karfi ne ga ci gaban da rubuce-rubucen suka haifar ba, sai kuma dan tsokaci da aka yi na abubuwan da wasu suke gani na rashin ci gaba da su marubutan suka haifar wa harshen Hausa. Fatanmu dai wannan harshe ya samu ci gaba da daukaka a duniya baki daya, amma hakan ba za ta samu in ba mu taimaki harshen ba, in ba mu karfafa wa marubutanmu gwiwa ba? In muna sukan su a kafafen yada labarai da manyan makarantu, alhali ba ma kiran su mu zauna mu nuna musu kurakuransu? Wannan ita ce hanyar samun ci gaban harshenmu da al’adunmu? Ya kamata mu sake tunani. In ba ka so naka ba duniya sai ta so shi. Kuma in mun ki sharar masallaci, to za mu yi ta rumfar kasuwa. Allah ya kyauta!
Manazarta
Adamu, A.U. (2006) Hadin Kai Tsakanin Marubutan Harsunan Gida Na Kasashe, An
Gabatar da Wannan Takarda a Taron Kasa da Kasa na marubutan Nijeriya da Nijar, Wanda Kungiyar Marubuata ta Nijeriya Reshen Jihar Kano Suka shirya, a Birnin Yamai, Nijar.
Furniss. G., Buba. M. (2004) Bibliography of Hausa Popular Fiction 1987-2002.
Germany. Rudiger Koppe Verlag, Koln.
Gidan Dabino, A.A, (1995) Muhimmancin Marubuta a Cikin Al’umma,
Takardar da Aka Gabatar a Bikin Kaddamar da Littafin Karshen Mai Zalunci. Koko, Jihar Kebbi: Makarantar Sakandare.
Gidan Dabino, A.A, (1993) Gudummawar Adabin Hausa ga Addinin Musulunci,
Takardar da Aka Gabatar a Taron Kara wa Juna Sani na Dalibai Musulmi na Babbar Makarantar Sakandaren Dawakin Tofa.
Gidan Dabino, A.A, (1992) Tasirin Labaran Soyayya ga Al’umma, Musamman ta
Hausawa, An Gabatar da Wannan Takarda a Taron Kara wa Juna Ilimi Mai Taken “Rubutu Don Al’umma’’ Wanda Kungiyar “Writers Forum” ta Gudanar, a Majalisar Matasa ta Fagge, Kano.
http://hausa.soas.ac.uk/
Malumfashi, I. 2004. Ta’aziyyar Adabin Kasuwar Kano Makalar da Aka Gabatar a Taron
Kara wa Juna Sani a Taron Kasa da Kasa na 6 Wanda Cibiyar Harsunan Nijeriya ta Jami’ar Bayero, Kano ta Shirya.
Muktar, I. (2004) Jagoran Nazarin Kagagaggun Labarai. Kano: Benchmark Publishers
Limited.
Sa’id, B. 1980. Dausayin Soyayya. Zariya: Gsakiya Corporation.
Yahaya I.Y, (1988) Hausa a Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa. Zaria: NNPC.
Sunday, February 21, 2010
Subscribe to:
Posts (Atom)