Thursday, September 25, 2008

Tsarin Doka a Kasar Hausa Kafin Zuwan Musulunci

Wannan takarda wani bangare ne na kundin binciken NCE a Sashen Hausa na Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Kano, Agusta 2006. Dalibai hudu ne suka rubuta, kuma sun karanta Hausa/Arabic:

Auwalu Yahaya Abdu da Aminu Ahmad Sa’id da Muhd. Ibrahim Sani da kuma Hamisu Hassan Abdullahi


Tarihin Kasar Hausa a takaice:
Kasar Hausa ita ce yankin nan na kasar Sudan wanda ke wajen yammacin kasar Afrika, daga gabas da ita akwai Kasar Borno, daga yamma kuma kasar Dahoma (Jamhuriyar Benin a yanzu), daga Arewa ga hamadar sahara, daga kudu kuma akwai kasashen Nufe da kasashen da ake kira “Middle Belt” a takaice.

Kasar Hausa wata bangare ce ta Arewacin Najeriya da kudancin Nijar, tana da fadin kasa tare da bishiyoyi dogaye da gajeru a mafi yawan wurare, kuma kasa ce mai ni’ima tare da albarkar wajen shuka, kuma tana da tsayayyun yanayi guda hu]u duk shekara su ne Sanyi, da Zafi, da Rani, da kuma Damina.

Irin sana’o’in da ake da su sun hada da Noma, da Kiwo, da Rini, da Kira, da Jima, da Sassaka da dai sauransu. Kuma a wancan lokaci ba su da wani abu tsayayye da za a kira da suna kudi illa iyaka ban gishiri na ba ka manda (Cikin Furfure).

Misali Manomin da yake bukatar wuka, ko Fartanya, ko Lauje, sai ya dauki Hatsinsa ya kai wa Makeri.

Haka ma Makerin idan yana bukatar a yi masa wani aiki kamar yabe, to sai dai ya ba da abubuwan da yake kerawa kamar su Garma, ko Takobi ko makamancinsu, a ladan aikin.

Da haka sai ka ga kowa ya samu biyan bukatunsa, kuma rayuwa ta saukaka.

Irin wannan nau’in ciniki shi ake kira cinikin ‘Furfure’. Amma ko ba a fadi ba irin wannan rayuwa, tana bukatar kowa ya yi aiki tukuru, tare da nusar da mutum ya zuwa ga yin tsimi da tanadin abin da ya yi saura don gaba.

Wannan ya sa tsarin tattalin arzikin Hausawa a wancan lokaci ya ginu a kan sana’o’insu.

Kafuwar Al’ummar Hausawa:
Kafuwar al’ummar Hausa ta faru tun can zamani mai tsawo. Zamanin da jahilci da duhun kai suka yi wa duniya kanta. Yayin da kowacce daga cikin al’ummomin duniya ba ta san da zaman kowa ba, in ka ]ebe ita kanta da ‘yan kabilu daya ko biyu masu makwabtaka da ita. Wato lokacin da dan Adam ke bautawa dukkan wani abin da ke ba shi tsoro ko mamaki, saboda ya wuce hankalinsa. Ma’ana ya kasa fahimtarsa. Irin wannan matsayi na sa Dan’adam ya bauta wa abubuwa da dama kwatankwachi su rana, da wata da itatuwa da rafuka da duwatsu, da aljanu, har ma da dabbobi. Kaico! Ke nan bautawa aljanu (Bori) da kangida da su ‘Dodo’ su ne nau’o’in addinin Bahaushe na tun farko-farkon kafuwar al’ummarsa.

Al’adun Hausawa Ta Bangaren Shugabanci:
Shugabanci na nufin rikon ragamar al’umma da ba su umarni da yi musu jagoranci bisa tafarkin da suka amince da shi, da tsara musu dokoki da sasanta tsakaninsu, da makamantan wadannan.

Shugabanci ta bangaren al’adun Hausawa kuwa, ya faro ne daga tsarin zaman iyali inda Maigida yake kamar Sarki a gidansa, a kullum shi ne babba, daga nan sai matarsa da sauran yaran gida. Yayin da aka samu gidaje biyu ko fiye da haka akan zabi wani dattijo a matsayin shugaba, ko kuma wani jarumi wanda ya nuna ya fi kowa sadaukantaka da jaruntaka da dauriya.

Wasu dalilai kamar halin kunci a cikin gida ko bukata irin ta tsaro ko rashin zaman lafiya, kan sa Maigida ya fitar da wasu daga cikin ‘ya‘yansa zuwa wani guri na daban, kamar gona ko garke. Ta haka ne iyali kan yadu su yawaita su hada wani kauye.

Saboda haka ne sai a kara zabar wani shugaban da zai shugabanci wannan kauye. Wannan shi ya haifar da mukamin MAI UNGUWA kuma shi zai dinga tsara musu dokoki.

Kauye yakan bunkasa ya zama gari sosai, a sakamakon haka sai a kara zabar wani mutum a matsayin Maigari (Fagaci) don kula da wannan gari.

Da aka samu ci gaba kuma, garuruwa suka kara yawaita sai aka samar da mukamin Hakimi, ana ba wa Hakimi garuruwan Maigari akalla biyar don ya kula da su.

Da tafiya tai tafiya, sai aka samar da mukamin Sarki inda ake hada wa Sarki masarautar Hakimi akalla biyar ko fiye domin ya shugabance su ya kuma shimfida musu dokoki domin zaman lafiya.

A takaice dai ajin shugabannin da ke tsara dokoki a tsakanin talakawansu sun hada da Maiunguwa, da Fagaci, da Hikimi, da Sarki, don haka a tsarin zaman Hausawa komai dukiyar mutum in ba ya cikin wannan jeri to talaka ne.

3.1 MA'ANAR DOKA DA MASU KAFA TA:
Dangane da ma'anar Doka masana sun yi bayana da dama a kan ta daga cikin su akwai Farfesa Neil Skinner (1980), ya bayyana ta da cewa "Doka wata tsarrriyar hanya ce da akan gindaya ta ga mutanen gari, da kuma horo ga duk wanda ya ketare ta don samar da tsaftatacciyar rayuwa ga wannan al'umma".

Dangane da masu kafa doka kuwa sun hada da Maigida wanda yake kafa doka a tsakanin iyalinsa domin suna karkashin kulawarsa, a wannan bangare na cikin gida ana yin amfani da doka ta ina gaba da kai dole abin da na umarce ka ka bi ki da so.

Sannan sai Maiunguwa wanda ke sasanta rikicin da ya afku tsakanin makwabta.

Sannan sai Fagaci (Dagaci) wanda ke sasanta rikicin da ya fi karfin Maiunguwa wato kamar kauyuka da unguwanni.

Hausawa na cewa ‘Komai tsawon wuya kai ne a samansa’, wato Sarki shi ne sama da kowanne daya daga cikin wadannan shugabanni da aka ambata, wanda ya kasance Sarki yakan zamo mutum ne mai kwarjini da girman sha'ani, kuma ba a kawo masa wargi saboda matsayinsa na bango madafar bayi.

Alhaji Mamman Shata Katsina a wa}ar da ya yi wa Sarkin Bauci Sulaimanu Adamu yana cewa:

"Kowas-Sarki ya darma sa’a

Wasa da aboki ba shi yiwo".

A takaice Sarki shi ne karshen mai yanke hukunci a tsakanin dukkan wadannan rukunai na shugabanni.

3.2 RABE-RABEN DOKA
Dangane da rabe-raben doka kuwa, za mu iya cewa doka ta rabu zuwa kaso uku kamar haka;

i. Doka a bangaren cikin gidan Hausawa;

ii. Doka a bangaren masu mulki;

iii. Doka a bangaren masu sana'o'in gargajiya.

Wadannan su ne manyan rukunai ko azuzuwan da doka ta kasu gare su. Ga kuma bayanin su kamar haka:

3.3 DOKA A BANGAREN CIKIN GIDAN HAUSAWA:
A gargajiyance gidan Bahaushe yakan kunshi Maigida da matansa, da 'yan uwansa, da kuma 'ya'yansa. Iyali shi ne ainihin ginshikin da aka kafa al'ummar Hausa a kansa. Daga iyali ne jama'a kan faru, har su zama 'yar kungiya, daga nan kuma su hadu su samar da 'yar unguwa, wadannan unguwoyi su ke haduwa su kafa kauye, daga nan kuma sai garuruwa su samu.

A zaman iyalin Bahaushe, babba ne kan yi kokarin sadaukar da kansa, ya kyautatawa na kasa da shi. Shi kuma karami ya yi masa biyayya, da kaucewa duk wani abu da ka iya kawo raini ga na gaba. To akasari za ka tarar irin wannan gida, gida ne na gado, wato wanda aka gada tun kaka da kakanni kuma ba a raba shi ba. Sau da yawa irin wannan gida a tukunya guda ake girka abincin da za a ba wa kowanne.

A bangare guda kuwa, Kaka na wajen uwa ko na wajen uba, shi ne mai yin hukunci na farko a tsakanin danginsa, kuma shi ne zai fadi abin da za su yi. Idan ka ga an jingine kaka, to ya tsufa ne ko kuma ba shi da cikakkiyar lafiya, ko ta Allah ta kasance akansa(ya mutu).

A wannan bangare ana yin amfani ne da Doka ta ina gaba da kai, don haka dole abin da na umarce ka shi za ka bi, ki da so.

A lokacin da mai gida ba ya nan, wansa ko kaninsa shi sai zama a makwafinsa, kuma ko mahaifi (Maigida) yana nan zai iya zama a makwafinsa, misali zai ce "Kai wane mun samu labari kana neman auren 'yar gidan wane, ba za ka aure ta ba". Shi ke nan ba ka da ta cewa, don yana cikin masu fada a ji a cikin danginku. Kuma sannan wadannan 'ya’ya ba za su zama manya ba ko da kuwa an yi musu aure, har sai sun hayayyafa. Kun ga ke nan na gaba yana wucewa na baya na maye gurbinsa, shi ma wancan kakan a da jika ne na wani, ya zama da, ya zama uba, kana ya zama kaka. Don haka Kaka shi ne tsani na farko da za a taka wajen bin Doka ta cikin gida.

Idan muka juya banagren aure kuma, Hausawa suna da Al'adar wanda duk aka ba wa yarinya ta bayu, ko tana so ko ba ta so, dole ne su zauna tare. Haka shi ma mijin ba kasafai ake bari ya zabi wacce yake so ba, yana yin uhn! Za a ce "Kai! Da ubannika za ka yi jayayya?. Ko kuwa wannan ba kanin ubanka ba ne? Wato ba shi da iko a kan ka ke nan?". Haka nan a kan dole zai zauna da wannan mata, in da rabo ma sai ka ga sun hayayyafa. Su ma idan suka tashi aurar da 'ya'ansu irin wancan auren da aka yi musu (Na zumunta) za su yi wa 'ya'yansu.

3.4 DOKA A BANGAREN MASU MULKI:
Mulki a Kasar Hausa ya danganci rikon ragamar al'amuran jama'a, wanda ya hada har da ba su umarni, da kafa Doka, da sulhunta tsakaninsu da sauran hakkokinsu na yau da kullum.

A karkashin wannan aji na bangaren masu mulki muna da Sarki da Hakimi, da Dagaci (Fagaci) da kuma mai unguwa. Ga bayanin yadda kowanne daga cikinsu ke zartar da Doka a bangarensa.

1. MAI’UNGUWA: Shi ne sabon shugaban da talakawa suka zaba a yayin da suka fuskanci sun soma yawa, dole tafiyar sai da jagora, daga baya ne abin ya zama gado.

To shi Mai’unguwa yana cikin masu kafa Doka a bi dole, ko ya hana don karfin mulkinsa, sai fa idan abin ya fi karfinsa ne zai tura shi gaba.

2. DAGACI (FAGACI): Shi ne mutumin da ke mulkar unguwanni da ke karkashin masu unguwanni kamar biyar ko fiye, ana kiran sa Maigari saboda yankinsa ya fi karfin unguwa.

To shi ne mai zartar da hukuncin da ya gagari masu unguwannin da ke karkashinsa.

3. HAKIMI: Ya samu wannan suna ko mukami ne a yayin da aka samu ci gaba, kuma garuruwa suka kara yawaita. Sai aka ba wa Hakimi garuruwan Fagaci a kalla guda biyar don ya kula da su.

To shi ma Hakima idan abu ya daure masa kai yakan tura shi kai tsaye ga shugaban kasa na gargajiya (Wato Sarki).

4. SARKI: Shi ne shugaban koli ga dukkan mahukuntan da aka yi bayaninsu a baya, shi ya sa ma wasu ke yi wa sarki kirari da "Bango madafar bayi".

Tsarin sarakuna, shi ne tsarin shugabanci a tsarin gargajiya na zaman Hausawa. Kuma ya samo asali ne tun zamani dadadde. Kuma duk wanda ya kasance Sarki ya kan zamo mutum ne mai }warjini da girman sha'ani, Jarumin gaske, kuma ba a kawo masa wargi.

Kuma Sarki shi ne mai zartar da Doka na karshe, daga kansa Magana ta kare, babu wani maganar kotu ko Alkali, don kuwa sun samu ne bayan zuwan addinin musulunci da kuma Turawan Mulkin Mallaka.

A lokacin wadannan shugabanni da muka yi bayani, suna zartar da Doka ne da abin da shugaba ya yi tsinkaye a kai, wato a matsayinsa na wanda ya ga jiya da yau, kuma yake shirin ganin gobe. Dama Hausawa na cewa "Abin da babba ya hango yaro ko ya hau Rimi ba zai gano ba".

3.5 DOKA A BANGAREN MASU SANA'O'IN GARGAJIYA:
Al'umma, tamkar jikin dan adam ne, wanda baya ga aikin da tilas ne kowace ga~a ta yi, don tabbatar da rayuwarta cikin inganci, akwai kuma gudunmawar da take ba da wa don kasancewar dan Adam ]in jiki guda. Ga kuwa sauran aikace-aikace da suke da mahimmanci fiye da saura, wadanda in ba a yi su ba, sai ta kai ga katsewar rayuwa. Wannan siffa ta al'umma, ta tilasta wa kowa daga cikin jama'arta yin wani aiki, domin tabbatar da wanzuwar al'ummar, baya ga wasu aikace-aikace da suka zama dole ga kowa, domin rayuwarsa shi kansa.

Sarakuna a kowanne gari, sun bai wa shugabannin sana'o'i da manyar Bokaye, da jarumai har ma da dattijan gari matsayi na musamman wajen gudanar da mulkinsu. A hakika ma, bincike ya tabbatar da cewa wadannan rukunonin jama'a ne suka zamo mataimakan Sarki, wajen tafiyar da mulkin yankinsa.

Don haka a gargajiyance ana zabar dattijo da ya fi kowa yawan shekaru da kwarewa a kan sana’ar da mazauna wurin suke yi. Irin sana’o’in da ake da su a wancan lokaci sun hada da Noma, da Kiwo, da Kira, da Jima, da Saka, da sauransu.

Bisa ga tsarin zama na gargajiya, Hausawa sun amince da zaman cude-ni-in-cude-ka. Kowanne mai sana'a, yakan yi la'akari da cewa kamar yadda yake bukatar wasu abubuwa don nasarar sana'arsa, haka ma wasu ke bukatar wani abun daga gare shi. Wannan fahimtar ta sa kowanne mai sana'a yakan yi fiye da abin da yake bukata, ta yadda zai iya amfana daga abin da ya saura, don mallakar wasu abubuwa da ba zai iya yi da kansa ba.

Misali, Manomin da ke bukatar wuka, ko fartanya, ko lauje, sai ya dauki Hatsinsa ya kai ga Makeri. Haka shi ma makerin zai ba da garma ko takobo don a yi masa yabe ko jinka ko dinki. Da haka sai ka ga kowa ya sami biyan buktarsa kuma rayuwa ta saukaka. wannan, nau’in ciniki shi ake kira cinikin furfure.

Amma ko ba a fada ba, irin wannan rayuwa, tana bukatar kowa ya yi aiki tukuru, tare da nusar da mutum zuwa ga yin tsimi da tanadi na abin da yai saura don gaba. Wannan ya sa tsarin tattalin arzikin Hausawa ya ginu a kan sana'o'insu.

To idan kuma ya kasance a bangaren sana'a kamar ga Mahauta wani ya ci bashin dabbar wani ya ki biya, to shi wanda aka ci bashin nasa ba zai ja wancan da rigima ba, a'a sai ya tafi wajen Sarkin fawa ya yi kararsa. Shi kuma Sarkin fawa zai tura daya daga cikin fadawansa su yi kiran wanda ya ci bashin, a nan za a kashe rigimar, ko Sarkin fadawa ya biya, ko a yi wa wanda ake bi bashi lamuni ya kawo. To haka ma abin yake ga sauran masu sana'o'in gargajiya da suke da sarakuna.

4.1 BAUTAR HAUSAWA (ADDINI) NA GARGAJIYA DA DOKOKINTA:
Addini hanya ce ta bauta, wadda tilas dukkan Dan’adam ya bi. Allah (S.W.A) ya ce 'Ban halicci mutum da Aljani ba sai don ya bauta mini'. Amma kuma ya ba su na su bauta wa Allah da ya hallicce su. Ko kuma su bauta wa waninsa. Abin da kuwai dan Adam ba zai samu ba, shi ne ya zauna bai yi bauta ba, ko ba komai ya bauta wa cikinsa, ko wani ra'ayi nasa Allah ya tsare mu, amin.

A matsayinsa na hanyar bauta addini shi ne yake daidaita tunanin Dan’adam da dukan al'amuransa na rayuwa, ko da kuwa kowanne addini mutum ya zabi ya yi, to kuwa za ka tarar addinin nasa yana da kwakkwaran tasiri dangane da yadda yake tafi da harkokin rayuwarsa.

Idan kuwa muka koma dangane da bauta, addinin Hausawa na gargajiya za mu tarar yana da dokoki, da tsare-tsare da mabiyansa ke bi. Misali ga alama ‘Kan-gida’ shi ne abin bautar kowanne iyali na Hausawa ‘Dodo' kuwa, abin bauta ne na jama'ar gari, kowanne gari suna da Dodon da suke bautawa, za a iya cewa Tsunburbura ita ake bautawa a Kano.

Daura kuwa, suna bauta wa macijiya. Zariya kuwa suna bauta wa dodanni da ake kira ‘MADARA' Da ‘KUFE’, shi kuwa Bori addini ne da Hausawa suke bautawa "Ubangiji' ta hanyar iskoki. Shi kansa addinin bori, duk da cewa ya yadu akasar Hausa, ba kowa da kowa ne ya karbi addinin yake bi ba. Ma'ana ba kowane Bahaushe ne dan bori ba, sai wanda ya yarda da addinin, kuma shugabanni addinin na bori suka karbi yardar tasa, suka yi wasu al'adu na shigar da shi addinin nasu. Misali, mutumin da ya zabi ya abutawa kar, zaka same shi yana kaffa-kaffa da karen tare da yin dukkan abinda kare ke so, da kuma barin dukkan abinda karen bazai so ba. Haka zaka sami wannan mutum ya cika da bakin ciki a duk lokacin da wani ya sabawa karen, ko ya sa shi fishi, sannan ya yi farin ciki da wanda duk wanda ya kyatatawa karen ko ya ganshi cikin koshin lafiya da annushuwa dan haka duk wata harka da bata shafi karen ba bai damu da ita ba. Karen nan ya sani, shi ya tsare aikinsa ke nan hidimar kare. Dan haka baya sake da duk wata doka da ya kafawa kansa game da karen.

4.2 MISALIN WASU DAGA CIKIN DOKOKIN Kasar HAUSA TA BANGAREN BAUTA; Kasar KANO DA Kasar DAURA:
Kamar yadda bayani ya gabata Tsunburbura ita ake bautawa a Kano, a matsayin bautarsu ta gargajiya a waccan lokacin. Dan haka zamu kawo bayanin yadda ake bauta mada da dokokin da masu bautarta ke bi.

Akwai wani Hatsabibi da ake kira Barbushe wanda shi ke jan talakawa zuwa wurin bautawa Tsunburbura, ance murgujejen kato ne na gani na fadi, an ce yakan kashe giwa ya rataya ta a wuya shi kadai, kuma shi ke karbo sakon shekara daga wajen Tsunburbura, kuma duk wani horo ko umarni da Tsunburbura take yi yana biyowa ta hanyarsa.

To, an ce a wannan lokaci idan mutum ya yi laifi, saia a sanar da Barbushe irin laifin da mutumin ya aikata, shi kuma sai ya shiga wajen Tsunburbura, wato Dutsen Dala inda fadarwa take, idan ya shiga yana daukan lokaci mai tsawo kafin ya fito. Idan ya fito ba zai fadi irin Dokar da aka yanakewa mai laifin ba, har sai shi mai laifin ya gabatar da wani abu da ya danganci dabbobin gida kamar rago, ko tunkiya, ko akuya da sauransu.

Idan aka kawo wannan dabba shi Barbushe zai hau da ita kan dutsen kusa da fadar Tsunburbura, daga nan sai kowa ya tafi gida sai washe gari, za a yo dafifi a biyo bayan Barbushe shi kuma sai ya hau kan dutsen wado inda ya ajiye dabbar, idan ya taras babu wannan dabba, to shi ke nan an yafewa mai laifin.

Amma idan ya taras da wannan dabba kamar yadda ya bar ta, hakan na nufin Tsunburbura ba ta karbi tuban mai laifin ba, don haka zai ci gaba da bawa Tsunburbura wata dabba a matsayin fansar mai laifin da ya aikata har sai ta ji kansa koda kuwa garkensa da na danginsa zai kare.

A Kasar Daura kuwa tsarin bautarsu a samo asali ne daga wata macijiya da ake kira Sarki. Yadda abin ya samo asali kuwa shi ne, akwai wani makiyayi da ke kiwon shanu, a cikin shanun da yake kiwo akwai wani sa wanda kullum sai ya fice daga garken ya shiga wata 'yar duhuwa, can jimawa kadan sai ya fito.

Ana nan ana nan sai wata rana makiyayin nan ya ce "Bari dai na bi san nan na ga wurin da yake zuwa". Shi ke nan sai ya bi shi, ya shiga nan ya fita can har suka dangane da wata 'yar duhuwa, sai ya ga san ya cusa kansa ciki, can jimawa sai ya ga ya dago kansa jike da ruwa, sai makiyayin nan ya tabbata akwai rijiya a gurin.

Bai ya kasa a gwiwa ba, sai ya kai wa Sarauniya Daurama labari, shi ke nan sai ta sa aka gyara wurin aka digan diban ruwan rajiyar, to ashe a cikin rijiyar akwai wata macijiya, sai ta hana mutane diban ruwa sai sau daya a sati, sai ta zama uwargijiyarsu su kuwa suka zama bayinta, ba su suka samu fita daga kanginta, sai bayan da Bayajidda "Abu Yazid" ya iso Kasar Daura ya kashe macijiyar kamar yadda tarihi mai tsawo ya nuna.

5.1 MATALOLIN DA AKA FUSKANTA:
Bahaushe na cewa "SAI AN SHA WUYA AKAN SHA DADI", babu shakka wannan magana gaskiya ce, domin kuwa muma mun fuskanci matsaloli da ba za a rasa ba a yayin gudanar da wannan aiki, dama an ce "Zomo ba ya kamuwa daga zaune", hakan ce ta sa muka ta shi haikan wajen nemo bayanai ingatattu.

Babbar matsalarmu ita ce ta kudi masu gidan rana, musamman kasancewar daibai ba mai saye ko sayarwa, kuma dukkanmu babu dan 'in service'. Amma cikin yardar Allah wannan matsala ta kau.

Matsala ta biyu ita ce karancin littattafai masu magana a kan wannan batu namu, wato "Doka a Kasar Hausa kafin zuwan musulunci". Su kan su masana tarihi sun yi mamakin wannan batu da muke bincike a kansa, domin suna ganin kamar shirin daukar dala ba gammo ne, ko kuma diban ruwa kwado. Saboda haka mun samu matsalar rashin samun cikakkun bayanai kan irin dokokin Hausawa na wancan lokaci, sakamakon rashin bayyanar rubutu da karantu kafin zuwan musulunci.

Matsala ta uku ita ce ta ke ka ka dawo da muka yi ta samu daga masana, bayan da muna ganin kamar kayan mu ya tsinke a gindin kaba, hakance ta sa mu matsala lamba har sai da hakanmu ya cimma ruwa.

Wadannan da ma wasu da ba mu ambata ba, suna cikin dinbin matsalolin da muka fuskanta a yayin gudanar da bincike kan "Doka a Kasar Hausa kafin zuwan addinin musulunci".

5.2 SHAWARWARI:
Babu shakka akwai shawarwari da ya kamata mu ba wa 'yan uwanmu dalibai masu sha'awar yin binciken da ya danganci doka da rayuwar Hausawa kafin zuwan musulunci. Shawarwarin sun hada da:

1. A yi tambaya ta kai tsaye maras rikitarwa, kuma a cikin ladabi da biyayya don masanin ya gane inda aka dosa.

2. A samu hadin kai ga rukunin masu gudanar da bincike

3. A dinanci jurina da na ci wajen gudanar da bincike

4. Ya zama dole a kai zuciya nesa, wato ban da yin fushi

5. A tsara tambayoyi kafin a je wajen wanda za a tambaya

6. Duk littafi da aka samu wani bayani komai kankantarsa, a dauki sunansa, da na marubuci, da kuma shekarar bugu.

7. A rubuta kwanan wata da lokaci da ka ziyarci wani masani

8. Masu bincike su dauki abin da suke da sha'awa ko masaniya a kansa ko yaya take.

9. A guji yin tambayar da za ta kawo bacin rai ga wanda aka yi wa ita, ko kuma za ta bukaci ya fadi sirrinsa.

10. lallai ne masu gudanar da aikin bincike su samu cikakken lokaci, kuma su tanaji kudi da kayan aiki.

Allah ya sa mu dace amin.

5.3 KAMMALAWA:
Muna mika godiyarmu ga Allah subhanahu wa ta'ala da ya kawo mu karshen wannan aiki da muka sa wa suna "Doka a Kasar Hauwa Kafin zuwan musulunci".

Ya zama wajibi mu mika godiyar ta musamman ga malamanmu, wadanda suka taimaka mana wajen wannan aiki namu, musamman Malam Bashir Ibrahim saboda gudunmawa da ya ba mu da shawarwari masu amfani da ba za su misaltu ba, Allah ya saka masa da Alherri ya daukaki zuciyarsa, amin.

Wannan aiki ya ba mu damar ganawa da masana daban daban wadanda ko a mafarki ba mu yi tunanin saduwa da su ba, amma sai ga shi a dalilin wannan aiki har hira mun yi da su ta baka da baka. Daman Alhaji (Dr.) Dan Maraya Josa yana cewa:

Ina ruwan wani da wani

In ba dalili tai ba

To mu dai kan ta yi dalilin saduwarmu da fitattun masana na cike da wajen Kanon Dabo. A karshe muna fatan wannan aiki namu zai amfani dalibai masu nazari da kuma masu niyyar gudanar da aikin bincike a wannan fage. Amin.

5.4 MANAZARTA:
1. Adamu Mahadi, (1978): The Hausa Factor in West African History A.B.U Zaria.

2. Umar A.A, (1981): Hirarsu da jaridar Gaskiya ta fi Kwabo ta ranar 24 ga Afrilu, 1981

3. Ibrahim M.S., (1982): Dangantakar Al'ada da Addinin Musulunci kan Rayuwar Hausawa ta gargajiya, (M.A Thesis) sashen Nazarin Harsunan Najeriya, B.U.K

4. Muhd. N.I, (1986): Tsarin Sarautar gargajiya jiya da yau, B.A Hausa Yuni, 1986

5. nuwa Sale, (1987): Matsayin Harshen Hausa jiya da yau, Kundin Digiri na farko, Sashen Nazarin Harsunan Najeriya, B.U.K.

6. Hassan Y.A, (1992): Tsarin gargajiya na zaman iyali da Dangantaka: B.A (hons) Hausa Yuli, 1992

7. Ibrahim Idrin, (2002): Al'adun Hausawa nag ado: Nazarin Hanyoyin zaman tare a al'umar Hausawa: B.A (Hausa).

8. Dahiru Hadi, (2002): Ire-Iren Yanayi na shekara da abubuwan da Hausawa ke yi a cikinsa. B.A (Hausa)

9. Hira da Dr. Ahmad Magaji na Jami'ar Bayero ta Kano, ranar Labara 19 ga watan Yuli, 2004.

10. Hira da Muhd. Tahir Adam (Baba Impossible), ranar 4 ga watan Augusta, 2004.

5 comments:

DANDALIN BASHIR ZARIA said...

Ina alfahari da mahaliccina ya yo ni a Bahaushe!

Unknown said...

Hakika godiya ta tabbata ga Allah mahalicci da Ya halicci yaruka daban daban, domin haluttu su fahimci juna, da kuma yin alfahari da asalin su. Yau na kara alfahari da yaren hausa. Allah Ya kara tsare yaren daga facewa sanadiyar zamani da ake canja lafuza da furucin kalmoni.

Unknown said...

Tabbas gaskiyar 'yan magana da suke cewa " mai madi ke talla,mai zuma ido yaka saws ".Nuraddeen sabo ringim

naseer adamu said...

Abubakar Ado Ali daga ABU Zaria ina addu`ar Allah ya kara daukaka Hausawa da al`adunmu a duniya baki daya, kuma muna addu`a ga wannan gidauniya Allah ya daukakata ya sanya albarka a cikinta.
ina mai tsananin san Hausa sannan kuma ina mai alfahari da ita zan kuma kare martabarta. Hakika wannan aiki ya yi mini amfani matuka domin kuwa har wani abu na samu ta silar haka..

Unknown said...

Ina son sanin yadda tsarin rabon gado yake a kasar hausa kafin zuwan musulunci