Saturday, December 20, 2008

Littattafan Soyayya: Samuwarsu da Bunkasarsu da kuma Tasirin su ga Al’umar Hausawa a Nijeriya


Na gabatar da wannan takarda a Sashen Koyar da Harsunan Afrika da Nazarin Al’adun kasar Itofiya, a Jami’ar Hamburg, Kasar Jamus. Ranar Laraba рей ga watan Disamba, 2008


1.0 Gabatarwa
Ta hanyar rubutu ne marubuta suke fitar da abubuwan da suke cikin zuciyoyinsu, wadanda suka faru da kuma wadanda suke hasashen za su faru nan gaba, don jama’a masu karatu ko sauraro ta hanyar rediyo su ji kuma su karu da abubuwan da ke cikin rubutun wanda ya shafi ilmantarwa ko tarbiyyantarwa ko nishadantarwa ko kuma akasin haka.
Rubutu rayayyen al'amari ne da kan wanzu matukar wanzuwar duniya, kuma tamkar shuka ce wadda in har an yi ta za a girbi abin da aka shuka.
Bisa la’akari da irin wannan tunani na sama ya sa na shiga fagen tattauna soyayya da yadda take da tasiri a rubuce-rubucen Hausa, sai dai kamar yadda yake abu ne sananne ga jama’ar da suka san Hausawa ko suke jin labarin su, cewa tun tuni Hausawa suna da tsarin soyayyarsu kafin su cudanya da sauran jama’a kamar Larabawa da kuma Turawa, har kuma suka dinga kwaikwayar wadannan baki a wajen tafiyar da soyayyarsu da auratayya, da sauran mu’amaloli na yau da kullum.
A gargajiyance, Bahaushe a fagen soyayya mutum ne mai kunya da hakuri da dauriya da kuma kau da kai da bin maganar magabatansa, sau da kafa misali, Bahaushe ko Bahaushiya na zamanin baya can, ana iya aura masa mata ko aura mata mijin da ba su san juna ido da ido ba, wato sai an daura auren an kawo matar sannan za su ga juna. Sannan kuma Hausawa suna da wata al’ada ta tsarance inda masoya biyu (saurayi da budurwa) suke kwana a kan gado daya su kuma tashi ba tare da wani abu ya shiga tsakaninsu ba, ba don ba su da sha’awar juna ba, a’a, saboda akwai al’adar kasa wadda ta hana yin haka. Ashe ke nan su masu biyayya ne da juriya da hakuri da yarda da juna da amana. Idan budurwa suna soyayya da saurayi, ba za ta iya zuwa gidan su saurayin ba, wai don ta gan shi ko kuma ta kawo masa ziyara, sai dai in da wata matsala mai karfi kamar mutuwa ko haihuwa ko duba marar lafiya, ko bikin aure ko salla. Bayan haka idan yarinya ta san za ta hadu da saurayinta a hanyar da za ta bi ta je wata unguwa, to da wuya ta bi hanyar sai ta canza wata, duk don kada su hadu. Sannan budurwa ba ta iya ambatar sunan saurayinta kai tsaye, sai dai ta dinga kiran sa da wani suna a maimakon sunansa na gaskiya, in kuwa ta aure shi shi kenan ta yi sallama da fadin sunansa. Wannan dalili ne ma ya sa wasu suke daukar Hausawa ba su san soyayya ba ko kuma ba su iya ta ba, ba haka ba ne, soyayyar Bahaushe ba ya bayyana ta a fili sai in an yi aure a wajen zamansa da matarsa, domin a lokacin ta zama mallakarsa.
Idan aka dubi wasu daga cikin tatsuniyoyin Hausawa za a fahimci wasu al’adun Hausawa nagartattu, misali a cikin littafin Yahaya (1971:1-12) tana nuna mana yadda Bahaushe ba ya son rashin gaskiya da karya da cin amana, kamar yadda Gizo ya yi a lokacin da aka ba shi aikin tsinke baure, ya dauki alkawarin ba zai sha ko daya ba, amma ya zo ya sha ya ce bai sha ba. A karshe da aka gano ya sha sarki ya fasa ba shi auren ‘yarsa, wadda har an kai ta gidansa da kayan gararta masu yawa, aka fasa a ka dawo da ita gidansu.
Sannan in aka duba tatsuniyar Musa Dan Sarki (Yahaya, 1972:21-28) ita kuma tana nuna yadda budurwa Bahaushiya take jin kunyar fadin sunan masoyinta, tun kafin a yi aure, bare kuma in an yi auren.
A gabatarwar da Farfesa M.K.M. Galadanci ya yi a wani littafi na soyayya a cikin shekarar 1992, ga abin da yake cewa:
“Marubutan Hausa na farko ba su cika son yin rubutu kan soyayya ba, watakila don gudun zancen mata da amfani da kalmomin kuruciya ko ma ta kai ga yin batsa saboda haka da wuya a sami dadadden littafi (kai ko ma rubutacciyar waka) kan soyayya. A ‘yan shekarun nan marubutan zamani, matasa, sun toshe mana wannan gibi na adabin Hausa. Wannan littafi wanda Malam Ado Ahmad Gidan Dabino ya wallafa, Hattara Dai Masoya, na daya daga cikin kyawawan misalan irin wannan kokari” (Galadanci, M.K.M.; 1992: shafi na K).
Saboda Hausawa sun cudanya da wsau al’umma baki kamar Larabawa da Turawa shi ya sa suka sami nason wasu al’adu da dabi’un wadannan mutane musamman a zamantakewar yau da kullum, kama tun daga kan soyayyarsu da auratayyarsu da bikin suna da abinci da suturarsu da sauransu.
Karuwar Hausawa da wadannan al’adu daga baki na nesa da na kusa da su ya sanya suka iya rubutu da karatu cikin harshen Hausa। Daga nan suka sami dabarun dauwana al’adunsu da adabinsu a rubuce a cikin littattafai na binciken ilmi da wadanda ake kagawa na zube da wasan kwaikwayo da kuma wake-wake da sauran dangogin ilmi.


2.0 Labaran soyyaya
Labaran soyyaya suna da wasu sinadarai wadanda idan aka hada su yayin rubutun ya fi dadi da armashi, idan kuma labarin bai same su ba to labarin ba zai yi armashi ko dadi ba, kuma rashin sa zai sa a kasa cim ma manufar da ake son gina labarin a kai, matukar babu wadannan abubuwa labarin ba zai zama labarin soyayya ba, wato ba za a kai ga babbar manufa ba.
Kamar yadda aka sani soyayya ta kasu iri daban-daban, musamman yadda take wakana tsakanin saurayi da budurwa, ko miji da mata, ko ‘ya’ya da mahaifinsu, da sauransu. To amma babbar manufarsu (jigo) daya ce wato soyayya, sai dai kananan jigoginsu wadanda a kansu ne babban jigon ya ta’allaka, sun sha bamban da juna, wadannan kananan jigogi kuma su ne ake kira tubalan gina babban jigo. To amma duk da haka a iya kawo wadannan jigogi a dunkule tun da yake babban jigonsu daya ne (soyayya) wato ke nan a dunkule a iya bayyana tubalan ginin labarin soyayya, musamman tsakanin mace da namiji kamar haka:
• Sunayen mutane da suka dace (taurari)
• Siffanta mata masu kyan hali da kyawun halitta
• Bayyana ire-iren mataye ko mazajen da mafi yawan mutane suka fi so
• Bayyana kyawawan halaye na iyaye da ’ya’yansu
• Tunani
• Biyayya
• Fito da abubuwan da namiji ya fi son mace ta yi masa
• Fito da abubuwan da mace ta fi son namiji ya yi mata
• Fito da abubuwan da ke faruwa a rayuwa ta zahiri dangane da soyayya,
musamman a rayuwar ma’aurata
•Yanayin soyayya bayan ta rikode ta zama aure
• Amfani da kalmomin soyayya masu dadi da faranta zuciya
• Halayyar wurin da labarin zai wakana
• Da sauransu.
A halin yanzu da an ji an ambaci labarin soyayya, watakila nan da nan za a tuna cewa ko ana nufin labaran da matasan yanzu suka fi so a zuciyarsu fiye da kowane labari. Labari wani abin da aka rawaito ne da ya wuce mai dan tsawo cikin shafuka, aka gina shi bisa gaskiya ko bazama a mafarke-mafarken rayuwa Shi labarin soyayya shi ne abin da yake wakana tsakanin saurayi da budurwa, ko mata da miji, ko ko?
Rubutattun labaran soyayya shiryayyun zantuka ne da yawanci akan kaga, ko aka kara wa gishiri, da ake shinfidawa a fasalin zube ko wasa ta bin babi-babi ko fitowa-fitowa ko kashi-kashi, cikin azanci da ke dauke da wani salo na musamman zuwa ga al’ummar da aka rubuta shi domin ta.


2.1 Samuwar Littattafan Soyayya
Sabanin yadda wasu suke dauka a ransu cewa a ’yan shekarun nan ne Hausawa suka soma rubuce-rubucen wakoki ko kuma labarai a kan soyayya. Bincike ya nuna cewa a wajen karshen shekarar 1880, an sami wata waka da aka rubuta cikin Ajami wadda wani mutum mawaki mai suna Aikau ya rubuta kuma ya ba ta suna Begen Mariya. Shi kuma wani Bajamushe Dr. Rudolph Prietze (1854-1933), daga baya, ya tattara ire-iren wakokin da aka yi da ajami ya mayar da su littafi. An buga wannan littafin a shekarar 1927 da sunan littafin Lieder des Haussawolks, (Wakokin Al’ummar Hausawa).
Shi kuma Farfesa Umaru Balarabe Ahmed ya fassara su, aka buga a shekarar 2002, aka sanya wa littafin suna Jiya A Yau: Dadaddun Wakokin Hausa.
Ga wasu daga cikin baitocin wakar Aikau:
Mai kyaun ido na barewa,
Mare Gudaliya, ‘yar Ranau!,
Ni ban san ana kamna ba,
Sai a wurin ki jikal Ranau,
In nai rawa na juya,
Dukka domin ki ne’yar Ranau.

Begenki ya ci raina, Mare,
Tilas ne nake yi mi ki bege,
Mare Gudaliya ‘yar Ranau!

Arme yakinku ne ‘yan mata,
Ya ci Gudaliya ‘yar Ranau,
Kafal da bat takalmi,
Ita tsidau yake fudawa.

Wanda ba masoyi,
Shine na ya zo duniya don wofi,
Ni Mare ta fi uwata,
Mare ta fi ubana,
Don raina yana son Mare,
Mare Gudaliya ‘yar Ranau.
(Ahmad;2002:4-6)

Sannan a lokacin da aka gabatar da gasar farko ta rubuce-rubucen Hausa a Arewacin Nijeriya, wanda Hukumar Talifi ta yi a tsakanin shekarar 1932-1933, an sami littafin soyayya a cikinsu, wato littafin Jiki Magayi na J. Tafida da R. East, an buga littafin a shekarar 1935. Littafin yana bayar da labarin daukar fansa a kan wata soyayya da aka sami kasayya bisa danniya a cikinta.

A shekarar 1978 kamfanin NNPC sun buga wani littafi mai suna Sihirtaccen Gari, wanda Malam Amada Katsina ya fassara daga cikin harshen Larabci zuwa Hausa, sunan littafin da ya fassara Ikra na Sayid Kutub. Shi ma na soyayya ne.
A shekarar 1978, kamfanin dab’i da wallafa mai suna Kamfanin Buga Littattafai na Arewacin Nijeriya da yake a Zariya, kuma wanda ya shahara a buga littattafan Hausa, yau sama da shekaru Hamsin da suka shude, ya fito da gasar kagaggun labarai, makamanciyar gasar farko wadda aka yi a shekarar 1933.
A wannan gasa ta shekarar 1978, an sami littattafan soyayya guda uku a ciki, wato So Aljannar Duniya na Hafsatu Abdulwaheed da Amadi Na Malam Amah na Magaji Danbatta da Mallakin Zuciyata na Sulaiman Ibrahim Katsina, duk wadannan littattafai an buga su a shekarar 1980, kuma kamfanin wallafa da dab’i na Arewa ne ya buga su.
Babban abin mamaki shi ne daya daga cikin wadanda suka yi nasara din mace ce, wacce ta yi nasara da kagaggen labarinta na soyayya mai suna So Aljannar Duniya, wato Hafsat Abdulwaheed। Wannan littafin ba karamin tubali ne ba a wajen gina harsashin samuwar mata Hausawa kuma Fulani marubuta ba. So Aljannar Duniya shi ne littafi na farko da mace ta rubuta a cikin harshen Hausa. Bugu da kari, shi ne littafin farko na adabin soyayya, wanda mace ta rubuta a Arewacin Nijeriya.


Hotunan littattafan:
Mallakin Zuciyata
So Aljannar Duniya
Amadi Na Malam Amah


A cikin shekarar 1980 Hukumar Al’adu Ta Kasa ta shirya gasar rubuce-rubuce cikin harsunan Hausa da Yorba da Ibo, amma Hausawa ne kawai suka shiga gasar da sauran harsunan ba su kawo littafi ko daya ba, inda aka samar da littattafai guda shida wato
• Zabi Naka
• Karshen Alewa Kasa
• Turmin Danya
• Tsumagiyar Kan Hanya
• Soyayya Ta Fi Kudi
• Dausayin Soyayya.
Wadannan littattafai sun hada da na zube guda ukun da wasan kwaikwayo guda daya da na waka guda daya da kuma na wasa kwakwalwa guda daya, kuma cikinsu guda biyu ne suka karkata kan soyayya, wato Soyayya Ta Fi Kudi na Hadi Abdullahi Alkanci wanda yake wasan kwaikwayo ne da kuma Dausayin Soyayya na Bello Sa’id shi kuma na wakokin soyayya ne zalla.
Wata gasar kuma da aka yi ita ce ta cikin shekarar 1988 wadda Hukumar Raya Al’adun Gargajiya ta Jihar Kaduna ta yi inda aka sami littattafai guda shida wato Kowa Ya Bar Gida, na Mahmud Barau Bambale da Kifin Rijiya na Ibrahim Sheme da kuma Dukan Ruwa na Yusuf M. Adamu, a rukunin rayuwa ta zamani ke nan. Sai kuma rukunin rayuwa ta soyayya an sami, Jamilu Mijin Jamila da Kome Nisan Dare da kuma Dabaibayi, a matsayin zakaru.

Littattafan da aka buga daga cikin wadannan guda shida, marubutansu ne suka dauki nauyin abinsu da kansu. Daga cikinsu, marubucin Kifin Rijiya Ibrahm Sheme ya buga nasa littafin a kamfani Nation House, Kaduna, a shekarar 1991. Shi kuwa marubucin Kowa Ya Bar Gida da Kome Nisan Dare, wato Mahmud Barau Bambale, ya fara buga littattafan nasa ne da wani kamfani mai suna Ibramud Nigerian Limited, Zaria, a 1994. Sauran littattafan guda uku har yau ba a buga su ba.
Kafin wannan gasa ta 1988 an sami wani marubuci, matashi ya bayyana da wani sabon littafinsa mai suna In Da Rai…, wanda aka buga shi a shekarar 1984.

Wata matashiyar mai suna Talatu wada Ahmed ta fito da nata littafin mai suna Rabin Raina, ta buga littafi na daya a shekarar 1985, littafin da ya yi tsokaci a kan ilmin mata da kuma muhimmancin kyale ‘ya mace ta zabi masoyinta, maimakon a tilasta mata a kan wanda za ta aura.

Ba a jima da fitowar Rabin Raina ba, sai Ibrahim Hamza Abdullahi Bichi marubucin Soyayya Gamon Jini, littafin da ya fito a shekarra 1986, sai kuma Balaraba Ramat Yakubu ta fito da nata littafin, mai suna Budurwar Zuciya, a shekarar 1987 wanda ya fadada sakonnin da suke cikin So Aljannar Duniya da kuma Rabin Raina, ta nuna illar auren dole. Amma littafin da ya fito da sakon Balaraba Ramat Yakubu fili shi ne Wa Zai Auri Jahila? a inda ta nuna illar auren dole da kuma muhimmancin ilmin ‘ya mace.

Wadannan kagaggun labarai na soyayya su ne suka bude kofa ta rubuta littattafan soyayya na Hausa।



Hotunan littattafan
Rabin Raina 1, 2, 3
Budurwar Zuciya
Wa Zai Auri Jahila?


Sakonnin da littattafan farko suke dauke da su sun nuna muhimmancin bai wa mata ‘yancin ra’ayinsu a kan abin da ya shafi rayuwarsu tun ma ba a kan aure ba da kuma muhimmancin ilmi ga mata, sannan kuma ga yadda mata masu ilmi suka fi mata marasa ilmi da wayewa da gogewa a zama na rayuwa.
Lokacin da maza suka dada shigowa fagen rubutun kagaggun labaro na soyayya, sun tallafa wa mata ne ta wajen nuna muhimmancin kyautata wa mata da kuma ba su hakkinsu। Wasu maza marubuta da suka biyo baya su ne, Ahmad Mahmood Zaharadden Yakasai Kogin Soyayya (1988) da Yusuf Muhammad Adamu Idan So Cuta Ne (1989) da Ibrahim Saleh Gumel Wasiyar

Baba Kere (1989).



Wasiyar Baba Kere
Inda Rai Da Rabo
Soyayya Gamon Jini
Kogin Soyayya
Idan So Cuta Ne



Daga shekarar 1980, wasu marubuta sun sami sa’ar kamfanonin wallafa na Arewa sun buga musu littattafansu, wasu kuma sun buga littattafan da kansu। A iya tsawon shekaru goma da fara samun matasa marubuta littattafan soyayya, wato daga 1980 zuwa 1990, ba a buga littattafan soyayya na Hausa guda dari a duk fadin arewacin Nijeriya, har a gan su a kasuwa ana sayarwa ba। Manyan kamfanonin buga littattafai a lokacin ba su amsar rubuce-rubucen soyayya su buga, sai lttattafan da aka shigar da su a manhajar koyarwa a makarantu suka fi damuwa da su, don sun fi samun kudi a kansu।


Shekarar 1990 a wannan lokaci ne sababbin jini, matasan marubuta suka bayyana a farfajiyar rubutun soyayya, sahun farko na marubutan wannan lokaci su ne Ado Ahmad Gidan Dabino da Dan’azimi Babba Chediyar ‘Yan Gurasa da Aminu Abdu Na’inna da Badamasi Shu’aibu Burji da Hamisu Bature da Aminu Hassan Yakasai da Abdullahi Yahaya Mai Zare da Bala Muhammad Makosa da Bashir Sanda Gusau da Bala Anas Babin Lata Kabiru Muhammad Assada Kabiru Ibrahim Yakasai da Abdullahi Muhammad Gusau da Kabiru Hassan Illelah da Yusuf Aliyu Lawan Gwazaye da Hauwa Aminu da Zuwaira Isa da Abba Bature Kawu da Safiya A. Tijjani da Ashiru Bala Bichi da Ibrahim M. Mandawari da Bilkisu S. Ahmed Funtuwa da Muhammad Usman da Laila Zaharaddeen da Hassana Ibrahim Daneji da Abubakar Ishaq da Balarabe Abdullahi da Hajiya H.K.A. Gusau da Sahanunu Garba da Binta Bello Dambatta da Binta Maiwada da Jummai Mohammed Argungu da Mamman Nasiru Zungeru da Karima Abdu D/Tofa da Lami Tijjani Maiatamfa da kuma Usman K. Muhammed
Nason wadannan littattafai ya zama kugiyar da ta makalo zuciyoyin makaranta, maza da mata, suka shiga karatun littattafai gadan-gadan। Sannan kuma gidajen rediyoyi, kamar Rediyo Kano da Rediyon Nijeriya na Kaduna da Rediyo Rima Sokoto da Rediyo FM tasha ta 3, Legas da kuma wasu gidajen rediyoyi na kasar Nijar, kamar rediyo Anfani FM, da sauransu duk suna karanta ire-iren wadannan littattafai don jama’a masu sauraron su.


In Da So D a Kauna na 1 da 2
The Soul of My Heart


Daga shekara ta 1978, lokacin da aka fara samun littattafan soyayya na Hausa zuwa wannan shekara ta 2008, bincike ya nuna ana da ire-iren wadannan littattafai sama da dubu uku। Kuma har yanzu ana nan ana tattara bayanai kan wadannan littattafai na Soyayya.
Kasar Nijar ba a bar ta a baya ba wajen samar da littattafan karantawa cikin harsunan gida wadanda suka shafi soyayya da wasu al’amura na rayuwa. A cikin shekarar 2000 an kafa wani sashe na buga littattafai mai suna Albasa wanda yake karkashin 2peb da ke Ma’aikatar Ilmi ta Jamhuriyyar Nijar wanda ya sami tallafin kudi daga GTZ na kasar Jamus, inda suke buga littattafai cikin harsunan gida, kamar Hausa da Zarma da Kanuri da Tamajaq da Fullanci, sannan har da Faransanci. Wannan hukuma ta buga littattafai mabambanta sama da iri sittin, kuma na soyayya suna da yawa a ciki. Wannan aiki an yi shi ne daga shekarar 2000 zuwa 2004, wato na tsawon shekara hudu. Hukumar sukan sanya gasanni tsakanin marubuta cikin harsunan gida a zabi zakaru a ciki a buga musu littattafansu kyauta, sannnan a ba su wasu kudi a kuma ba su kyautar wasu litattafan. Wannna madaba’a ta Albasa tana sayar da littattafanta ne cikin farashi mai araha don littattafan su sami isa ga masu karatu. Sukan rage kudin littafin da wajen kashi hamsin cikin dari na kudin da aka buga shi .
Bayan an gama aikin da aka shata a ma’aiktar 2peb da madaba’ar Albasa a cikin shekarar 2004 sai kuma aka sake kafa wani aikin karkashen ma’aikatar ilmi ta kasa wanda aka sanya masa suna SOUTEBA, a cikin shekarar 2004 har zuwa yau, shi kuma wannan aiki na SOUTEBA yana samun kudin gudanar da wannan aiki nasu daga kungiyar kasashen EUROP, suna samar da littattafai cikin harsunan gida da kuma koyarwa cikin harsunan gida a wannan kasa ta Nijar baki daya. Zuwa yau bincike ya tabbatar da cewa daga 2000 zuwa yau an buga kwafin littattafai 380,000 cikin harsunan da muka bayyana a sama.
Hotunan littattafan Kasar Nijar
A cikin shekarar 2006 hukumomin UNESCO da OIF suka nemi kamfanonin buga littattafai da marubuta cikin harsunan Afrika, don su rubuta littattafai cikin harsunan Hausa da Zarma da Fulfulde da Songhai. An zabo kamfanin wallafa na Gashingo da yake a Niamey, a Nijeriya kuma an dauki kamfani na Gidan Dabino International Nigeria Limited da yake a Kano, sannan an dauko kamfanin Edis da ke Bamako ta kasar Mali. Daga nan, aka hadu a Mali da Nijar da Cotonou aka yi tarurruka inda aka tattauna, aka tabbatar da za a buga littattafai takwas, uku daga Nijar, uku daga Mali, biyu daga Nijeriya. Kuma hukumomin nan na UNESCO da OIF sun bayar da tallafin kudi na buga wadannan litttattafai.
Hotunan littattafan UNESCO/OIF, na Hausa
Yawancin marubutan wadannan littattafai matasa ne wadanda shekarunsu suka fara daga ashirin zuwa talatin da biyar (20-35). Littattafan da aka rubuta cikin harshen Hausa sun hada da Maza Gumbar Dutse na Yusuf M. Adamu da Bakin Karfe na Zainabu Gonde .
Yawancin matasa marubuta suna da sha’awar kallon finafinan da suka danganci soyayya, a gidajen kallo na silima ko bidiyo ko kuma talbijin, don haka, ba za a raba su da tunanin soyayya a zuciyoyinsu ba. Haka in suka zo yin rubutu, dole wannan tasiri ya yi aiki a cikin tunaninsu da rubutunsu. Kuma yawancin marubutan suna da sha’awar shirin fim amma rashin karfin aljihun shirya fim ya sa suka tsaya a fagen rubutu. Za a tabbatar da haka in aka lura sosai yadda a cikin ‘yan shekaru wasu littattafan an mayar da su fim, haka nan kuma, wasu marubutan suka tsunduma cikin harkar fim gadangadan.
Kasancewar rubuce-rubucen matasa na soyayya ne, mafi yawa makarantansu ma matasa ne, ko da a kasuwanni ka je za ka iske su matasan maza da mata ne suka fi zuwa sayen litattafan, kuma su kansu ‘yan kasuwar sun fi son litttattafan soyayya don ya fi amsuwa ga abokan cinikinsu। Idan ma ka kawo musu littafin da ba na soyayya ba ba su ciki murna su amshe shi hannu biyu ba, don ba sa samun ciniki sosai in ba wanda ya kunshi soyayya ba. Kadan daga cikin marubuta wadanda sunansu ya yi fice, suka shahara, su ne kawai suke canza salon rubutunsu daga soyayya zuwa wani fannin su kuma samu amsuwa ga masu karatu da kuma masu sayar da littattafai.


Hotunan Wasu littattafa


2।2 Bunkasar Littattafan Soyayya

Daga shekarar 1991 zuwa 2000, marubuta matasa maza da mata sun rubuta tare da buga littattafai Hausa na zamani masu sunaye mabambanta sama da guda dubu daya (1000). A cikin littafin Furniss da wani (2004) da http://hausa.soas.ac.uk/ an fadi yawan littattafan soyayya da ya tattara kimanin guda dubu daya da dari takwas da talatin da biyar (1835). Daga iya inda wannan binciken ya tsaya an ci gaba da dorawa, kuma ya zuwa yau (2008) akwai littattafan Hausa na soyayya sama da dubu uku (3,000).

Wannan ci gaba ya samu ne saboda wasu dalilai wadanda suka hada da:
• Samuwar na’ura mai kwakwalwa (computer)
• Samuwar matasa masu sha’awar rubuce-rubuce
• Samuwar makaranta littattafai
• Samuwar kungiyoyin marubuta
• Samuwar kantunan sayar da littattafai masu yawa
• Zuwan baki daga wasu jihohi da kasashe don sayen littattafai
• Gidajen rediyoyi da suke karanta littattafan Hausa
• Sanya littattafai a jaridu da mujallun Hausa (sanya labarin kadan-kadan)
• Buga littafi da marubuta suke yi da kansu
• Tallafi da wasu hukumomin gwamnati suke yi wa marubuta
• Buga littattafai masu inganci da kyan takarda, masu yawan shafuka,
• Samuwar kamfanonin buga littattafai na ‘yan kasuwa
• Sanya gasanni tsakanin marubuta
• Bikin karrama marubuta
• Buga littafi a dunkule maimakon rarraba shi kashi-kashi
• Samar da aikin yi ga matasa maza da mata
• Bude majalisun marubuta na Hausa a yanar gizo (internet)
• Mayar da wasu littattafai zuwa fim na bidiyo
• Karanta littatafi a kan faifan CD, ana sayarwa, 2008 (audio book)
• da sauransu
Harkar rubuce–rubucen littattafan Hausa na soyayya ta samu bunkasa kwarai da gaske. Saboda yawan dalilai da suka habakar da rubuce-rubucen soyayya, a wannan takarda an dan fadada bayanai a kan wasu daga cikinsu kamar haka:

2.2.1 Buga littafi da marubuta suke yi da kansu: wannan ba karamin babban yinkuri ne marubuta suka yi ba, domin lokuta da dama marubuci zai rubuta littafi ya yi ta neman wani babban kamfani ya dauki nauyin buga masa, don ya dinga ba shi wani kaso na ribar da aka samu (royality) amma abin ya gagara, ko da sun karbi littafin sai ya yi shekara da shekaru ba a buga ba, kai in ma ba a yi sa a ba sai littafin ma ya bata gaba daya, ko kuma in ma sun yarda sun buga maka, wajen biyan hakkin marubuci sai an ji kansu da shi don ba za su biya shi daidai ba. Wannan shi ya jawo marubuta suke yin aikin su kai tsaye, wato sun tsara su buga kuma su kai kasuwa, da haka ne harkar rubuce-rubucen Hausa musamman na soyayya suka bunkasa suka kai matsayin da suka kai, wato (sefl publishing)

2.2.2 Gidajen rediyo da suke karanta littattafan Hausa: wannan wata babbar hanya ce
da litttafan soyayya na Hausa suka samu bunkasa da yaduwa da kuma shiga zuciyoyin masu sauraro, a wajen Hausawa da ma wadanda ba Hausawa ba amma suna sha’awar harshen Hausa, kai a sanadiyyar haka ma an sami mutane da yawa da suka fara sha’awar yin rubutu, har ma suka rubuta yi din suka buga shi ya shiga kasuwa, musammam ma matan aure. Ba kuma a gidajen rediyon Nijeriya ne kawai ake karanta wadannan litattafai ba, in ka shiga kasar Nijar kusan duk gidajen rediyoyin kasar sama da guda goma suna da filin karanta littattafan Hausa na soyayya wanda suke kira da suna Dandalin Soyayya.

2.2.3 Samuwar kungiyoyin marubuta: sakamakon kafa kungiyoyin marubuta a cikin jihohin Nijeriya musammam a Arewa, rubuce-rubucen Hausa na soyayya sun bunkasa saboda yawan tarurruka da wayar da kan jama’a da kungiyoyin suke yi a kan muhimmanci rubuce-rubuce cikin harshensu na haihuwa da kuma bai wa marubutan shawarwarin yadda za su inganta harkar rubuce-rubucensu.

2.2.4 Tallafi da wasu hukumomin gwamnati suke yi wa marubuta: babu shakka wasu daga cikin hukumomin gwamnati na jihohin Nijeriya suna tallafa wa marubuta, misali a jihar da nake wato Kano, hukumar A Daidaita Sahu wadda Dr. Bala Muhammad yake jagoranta, a cikin shekarar 2004 ta shirya wani taro da marubutan jihar Kano, musammaman marubuta cikin harshen Hausa inda ta yi musu wata bitar sanin makamar aiki ta kwana biyar don marubuta su yi mata rubutu na canza hallayyar matasa a kan munanan dabi’u, kamar shaye-shaye da ha’inci da zaman banza da soyayya da dogaro da kai da harkokin daba da dai sauransu. Kuma sakamakon wannan bita an rubuta litttafai goma sha bakwai wadanda suka yi magana a kan batutuwa mabambanta, wadanda aka buga su har kwafi dubu tamanin da biyar, ana raba su a makarantun sakandare da kuma sauran jama’a masu sha’awar karatun littattafan Hausa. Ba kuma a nan suka tsaya ba kawai suna tallafa wa marubuta da dama wadanda ba su da halin iya daukar nauyin buga littattafansu. Bayan haka kuma takan tallafa wa kungiyoyin marubuta na jihar Kano in za su yi wasu tarurruka ko za su yi tafiya zuwa wata jiha ko kasa. Misali, a duk lokacin da kungiyar marubuta ta Nijeriya Reshen jihar Kano suka kai mata takardar neman taimako zuwa wani taro sukan taimaka, a lokacin da za a tafi Jihar Imo da Bayelsa da kasar Nijar duk wannan hukuma ta taimaka wa ANA, sannan a cikin wannan shekara ta 2008, kungiyar marubuta mata zalla, wato Kallabi Writers Association da za su kaddamar da kalandarsu, A Daidaita Sahu sun taimaka musu kwarai da gaske.
Sannan kuma hukumomin Uensco da OIF su ma sun tallafawa marubuta da kamfanonin dab’i don a samar da littafai cikin harsunan Afrika, a kasashe uku, wato Nijeriya da Nijar da kuma Mali.

2.2.5 Bikin karrama marubuta: kungiyoyin marubuta suna bikin karrama marubuta da kuma mutanen da suke taimakon harkar rubutu cikin harshen Hausa, shekarar da Ta gabata 2007 kungiyar Hausa Authors Forum (HAF) ta karrama wasu tsofaffi kuma fitattun marubuta da kuma matasa da wadanda suka taimaki adabi. Wasu daga cikin mutanen da aka karrama akwai, marigayi Abubakar Imam da Sa’adu Zungur da Malam Aminu Kano Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau Abdulkadir Dangambo da Dandatti Abdulkadir. Kungiyar marubuta mata ta kallabi ma sun kaddamar da kungiyar tare da kalandarta. Su ma sun karrama wasu mutane da suka taimaka wa harkar Adabi.

2.2.6 Bude majalisun marubuta na Hausa a yanar gizo (internet): Farfesa Abdalla Uba Adamu shi ne ya fara bude wa marubuta majalisa a yanar gizo don su sami wata mahada da za su dinga tattauna matsaloli da nasarorin marubuta, marubuta@yahoogroups.com sannan ana sanya sharhi na littattafai ko kuma wata sanarwa da ta shafi marubuta, game da bikin aure ko suna, don sada zumunci a tsakaninsu, ko kuwa rasuwa ko rashin lafiya. Bayan wannan Dr. Yusuf M. Adamu ya bude wani blog mai suna www.marubutanhausa.blogspot.com, wanda yake bayar da tarihin marubutan Hausa, tare kuma da hotunansu a ciki. Har ila yau kuma Ado Ahmad Gidan Dabino ya bude wani blog din mai suna www.fagenmarubuta.blogspot.com wanda ake sanya gajerun labaran marubutan Hausa musamman ‘ya’yan kungiyar marubuta ta Nijeriya reshen jihar Kano (ANA).

2.2.7 Sanya gasa tsakanin marubuta: baya ga wadancan gasanni da aka yi a Arewacin Nijeriya don bunkasa harkar rubuce-rubucen littattafa na Hausa, an ci gaba da samun ire-iren wadannan gasanni kamar yadda e Kamfani Fisbas Media da ke Kadun ya sanya gasar marubuta a shekara ta 1994 inda aka samu littattafai guda uku, amma har yanzu ba a buga su ba kuma ba a bayar da kyautukan ba. A shekarar 2007 an sanya gasar marubutan Hausa wadanda suke rubutun zube, don tunwa da marigayi Injiniya Bashir Karaye, kuma an ware kudi Naira dubu dari uku N300,000 ga mutane uku, na farko N150,000 na biyu N100,000 na uku N50,000. a wannan shekara ta 2007, shekarar da aka fara gasar Littafin ‘Yartsane na Ibrahim Sheme ne ya yi na daya, sai kuma Matar Uba Jaraba na Hajiya Balaraba Ramat ya yi na biyu, littafin Kankana na Maje El- Hajij shi ne ya yi na uku.

A wannan shekara da muke cikin2008, an sake yin wannan gasa, kuma littafin Baki Abin Magana na Dala’ilu Bobboji ne ya na farko aka ba shi N150,000 sai kuma Bakin Kishi na Muhammad Lawan Barista ya yin a biyu aka ba shi N100,000, na uku kuma shi ne Garinmu Da Nisa na Ibrahim Birniwa.

2.2.8 Mayar da wasu littattafai zuwa fim na bidiyo: da tafiya ta yi tafiya a cikin rubuce-rubucen matasa sai kuma sha’awar nan ta harkar fim ta dada karuwa gare su har kuma wasu daga cikinsu suka tsunduma tsundum cikin harkokin finafinan Hausa. Ga Jerin sunayen wasu marubuta da suka shiga harkar fim da kuma littattafan da aka mayam fim:

Marubuci Sunan Littafin da aka Mayar Fim
1 Abba Bature- Auren Jari
2 Abdul’aziz Sani Idaniyar Ruwa
3 Abdullahi Yahaya Mai Zare ........
4 Abubakar Ishak Rigima Uban Wa T7a Kashe? Da Da Kyar Na Sha
5 Adamu Muhammad Kwabon Masoyi
6 Ado Ahmad Gidan Dabino In Da So Da Kauna
7 Alhamis D. Bature ...........
8 Aminu Aliyu Argungu Haukar Mutum
9 Aminu Hassan Yakasai (marigayi)- Madubi
10 Aminuddin L. Abubakar (Ala) - Bakar Aniya
11 Auwalu Muhammad Danborno........
12 Auwalu Y. Hamza- Gidan Haya
13 Bala Anas Babinlata- Tsuntsu Mai Wayo
14 Bala Muhammad Makosa- Halimatu Ko Jummai
15 Balaraba Ramat - Ina Son Sa Haka da Alhaki Kwikwiyo
16 Bashir Sanda Gusau- Babu Maraya Sai Rago da Auren Zamani
17 Bilkisu Salisu Ahmad Funtuwa - Ki Yarda Da Ni da Sa’adatu Sa’ar Mata
13 Dalhatu Ibrahim Basawa- Cizon Yatsa
19 Dan’azumi Baba Cediyar ‘Yangurasa- Bakan Damiyar Rikicin Duniya
20 Habibu Hudu .........
21 Halima A.D. Aliyu - Muguwar Kishiya
22 Ibrahim Birniwa - Maimunatu
23 Ibrahim M. Mandawari- Aminu Mijin Bose
24 Ibrahim Mu’azzam Indabawa- Boyayyiyar Gaskiya (Ja’iba)
25 Ibrahim M. K/Nassarawa- Soyayya Cikon Rayuwa
26 Jamilu Abubakar Kundila ................
27 Kabiru Ibrahim Yakasai- Suda da Turmi Sha Daka
28 Kamilu Gwammaja- Rabi’a
29 Khalid Musa- Kadaura (Hannun Da Ya Ba Da Kyautar Fure)
30 Lubabatu Ya’u.......
31 Maje El-Hajij- Sirrinsu
32 Muhammad .B. Zakari- Komai Nisan Dare
33 Nazir Adam Sale- Naira Da Kwabo
34 Rabi’u Abdullahi Sharfadi- Halak
36 Sadiya Garba Yakasai.........
37 Sani Yusuf Mararraba .........
38 Sunusi Shehu Daneji- Bankwana da masoyi
39 Yusuf Aliyu Lawan Gwazaye- Cinnaka
40 Zilkifilu Mohammed- Su Ma ‘Ya’ya Ne
41 Zuwaira Isa - Mowar Mata

3.0 Tasirin Littattafan Soyayya ga Al’ummar Hausawa:
Tasirin littattafan soyayya ga al’umar Hausawa, ba kadan ba ne. Amma duk da haka za a yi kokari a bayyana kadan daga cikinsu.

Alal hakika al’umma kan amfana sosai da karanta ko sauraron littattafan soyayya a rediyo. A takaice dai ga yadda aka karkasa ire-iren wannan tasiri ko amfani da al’umma kan samu a sakamakon karantawa ko sauraron littattafan soyayya a gidajen rediyo:

• Bunkasa tunani
• Karfafa dankon zumunci
• Cusa wa mai sauraro ko mai karatu farin ciki
• Tausayi
• Jarumta
• Dauriya/hakuri
• Son karatun Hausa da bunkasa Harshen
• Cusa sha’awar yin rubutu a zukatan matasa maza da mata
• Kyautata zamantakewar ma’aurata da kuma masoya ta hanyar karatun littattafan soyayya
• Samar da aikin yi ga matasa maza da mata
• Kalubalantar auren dole a kasar Hausa
• Yakar jahilci
Da sauransu.

Bari mu dan yi bayanin wasu daga ciki wadannan abubuwa da muka jero a sama don a dan fahimci yadda tasirin da littattafan soyayya suka yi ga jama’ar Hausawa.

3.1 Son karatu da bunkasa Harshen: sakamakon samuwar littattafan soyayya cikin harshen Hausa, irin dabi’ar nan da ake cewa Hausawa suna da ita ta rashin son yin karatu ta fara raguwa, domin matasa maza da mata da kuma matana aure za ka tarar da su suna yawan karanta wadannan littattafai dare da rana, ko a cikin mota, kai wani lokacin a matar aure tana girki idan ta san za ta sami wasu mintina ba tare da ta yi wani aiki da hannunta ba za ka ga ta dauki littafi tana karantawa, domin kada ta bar wannan mintinan su tafi a banza ba tare da ta yi wani abu ba. Haka ma a cikin kasuwanni idan babu abokan ciniki a wajen da mutum yake kasuwancinsa za ka tarar yana ko kuma tana karatun littafi kafin abokin cinikin ya zo.

3.2 Cusa sha’awar yin rubutu a zukatan matasa maza da mata: Karanta littattafan Hausa da kuma sauraro lokacin da ake karantawa a gidajen rediyo sha’awar yin rubutu ta shiga zukatan mutane da yawa, domin ni da kaina na san mutane da yawan gaske, maza da mata wadanda suka zama marubuta sanadiyyar karatun da littattafai da suke yi.

3.3 Samar da aikin yi ga matasa maza da mata: littattafan soyayya sun samarwa da matasa maza da mata aikin yi, wasu matasan a da can ba su da wata tsayayyiyar sana’a, amma sanadiyyar samuwar wadannan littattafai sun samu abin yi. Misali wasu marubutan ba su da wata sana’a da ta wuce rubuta littattafai da shi suka dogara, shi ne sana’arsu, da shi suke ci da sha a rayuwarsu ta yau da kullum. Wasu kuwa a buga littattafan suka dogara, wat sun kafa dan karami kamfanin wallafa da suke bugawa ire-iren wadannan marubuta littattafansu, kuma cikin sauki, sabanin irin yadda manyan kamfanoni suke zabga kudi in ka kai musu buga littafi. Wasu kuwa kantunan sayar da littattafan suka bude, yadda in an buga littafi ake kai musu su sayar. Kai da tafiya ta yi tafiya ma, sai su ma marubutan suka fara bude kantunan sayar da littattafai da kansu. Wasu kuma daga cikin marubutan sun kafa wajen wallafa littattafai don su dinga wallafa nasu, daga baya kuma suka shiga wallafa na wasu marubutan.

3.4 Kalubantar auren dole a kasar Hausa: marubuta littattafan Hausa musamman ma na soyayya ba karamin aiki suka yi ba a wajen kalubalantar auren dole a kasar Hausa, domin abu ne sananne cewa a lokutan baya ana yi wa ‘yanmata auren dole, kara zube amma a ‘yan shekarun nan sakamakon rubuce-rubuce da ake ta yi yi ana nuna wa iyaye illar yin hakan da kuma irin yadda ake jefa ‘yanmata cikin mummunar rayuwa ta shiga bariki da yin karuwanci, ko kuma yarinya ta halaka kanta ta wasu hanyoyi da ba su dace ba, a yanzu abin ya ragu (auren dole) sosai.

3.5 Yakar jahilci: kamar yadda muka sani jahilci muguwar cut ace, mai hana mutane su ci gaba, to marubuta sun taimaka wajen yakarsa a kasar Hausa, domin da yawa mutanen dab a su iya karatunda rubutu ba amma don son su da sha’awarsu da ire-iren wadannan littattafai na soyayya, sai ka ga sun dage wajen koyon hada bakaken Hausa har ta kai su ga iya karatun littafin soyayya. Wasu kuma in ana karantawa a rediyo ne suke neman wanda ya iya karatun Hausa ya dinga nuna musu wurin da ake karantawa, suna bi, wato suna saurara kuma suna bin sun hada harufan da ake karantawa, wata rana sai ka ga mutum ya karanta shi kadai, domin an ce himma ba ta ga raggo.

4.0 Kammalawa
Wannan takarda ta yi kokarin bayyana tarihin ginuwa da habakar rubuce-rubucen soyayya na Hausa wadanda suka fara samarwa tun daga shekara ta 1916 zuwa yau. Haka kuma an duba ire-iren gasannin da aka shirya ga marubuta a Nijeriya ta Arewa. Sannan an bayyana wasu dalilai wadanda suka dada ruruta rubuce-rubucen litattafan soyayya da suka yi tasiri a rayuwar al’ummar Hausawa musamman a Nijeriya. Har wa yau, an dada fito da yadda wadannan dalilai suka yi naso a zukatan marubuta har suka bad a damar juya wasu littattafan izuwa shiri na fim na Hausa.

A dunkule, wannan takarda ta waiwayi littattafan soyayya wadanda aka rubuta cikin Hausa ta tsatstsefe tarihinsu da yanye-yanensu da halayinsu da dabi’unsu da kuma nasonsu a rayuwar Hausawa, tun ma ba matasa ba, a Nijeriya da kuma duniya baki daya.

5.0 Manazarta
Adamu, Y. M. (1994) Wane Ne Marubuci? Mujallar Zamani, Ta 1, Fitowa Ta 1, Maris. Kano:
Gidan Dabino Publishers.

Adamu, Y. M. (2002) Print and Broadcast Media in Northern Nigeria. www.kanoonline.com.

Adamu A.U. (2006) “Loud Bubbles from a Silent Brook: Trends and Tendencies in Contemporary Hausa Prose Writing” in Research in African Literatures Volume 37, Number 3, fall, Indiana University Press.

Adamu, Y. M. 1999. Hausa Literary Movement, Media and the City. Being a paper presented at Kano
Millennium Conferance

Adamu, Y. M. (1994) Hausa Novel at the Cross-road, ANA Review, October.

Adamu, Y.M. (1998) Long Live the Hausa Novel, New Nigerian Weekly, 6-12 June.

Adamu, Y.M. (1996) Hausa Writing and Writers Today. Being a paper presented at the 16th
Annual convention of the Association of Nigerian Authors, November, Arewa House.

Adamu, A.U. (1999) Literary Expressions in the 1990s

Adamu, A.U. (2006) Hadin Kai Tsakanin Marubutan Harsunan Gida Na Kasashe, An Gabatar da
Wannan Takarda a Taron Kasa da Kasa na marubutan Nijeriya da Nijar, Wanda Kungiyar Marubuata ta Nijeriya Reshen Jihar Kano Suka shirya, a Birnin Yamai, Nijar.

Adamu, A.U. (2005) Rawar da Matan Hausawa ke Takawa Wajen Bunkasa Adabin Hausa, an
Gabatar a Bikin Kaddamar da Littattafan Muradin Mata da Madafa – Kicin Sirrin Mata,
a Dakin Karatu Na Murtala Muhammad, Kano.

Abdulwaheed, H.1980. So Aljannar Duniya. Zariya: NNPC.

Ahmad, T. W. 1985. Rabin Raina. Kaduna: Ogwu Printers.

Ahmad, U.B. 2002. Jiya A Yau: Dadaddun Wakokin Hausa. Zariya: ABUPL.

Alkanci, H.A. 1980. Soyayya Ta Fi Kudi. Zariya: Gsakiya Corporation.

Ayagi, S. Y. (2005) WaKar Shirin AlKalami Ya Fi Takobi. Kano: Freedom Rediyo.

Danbatta, M. 1980. Amadi Na Malam Amah. Zariya: Gsakiya Corporation.

East, R. & Tafida, J.1935. Jiki Magayi. Zariya: Gsakiya Corporation.

Furniss. G., Buba. M. (2004) Bibliography of Hausa Popular Fiction 1987-2002. Germany.
Rudiger Koppe Verlag, Koln.

Galadanci, M.KM. (1992) Gabatarwa a Littafin Hattara Dai Masoya 1 & 2. Kano:
Gidan Dabino Publishers Enterprises.

Gidan Dabino A.A (1993) The Soul of My Heart,. Kano: Gidan Dabino Publishers.

Gidan Dabino, A.A, (1995) Muhimmancin Marubuta a Cikin Al’umma,
Takardar da Aka Gabatar a Bikin Kaddamar da Littafin Karshen Mai Zalunci. Koko, Jihar Kebbi: Makarantar Sakandare.

Gidan Dabino, A.A, (1993) Gudummawar Adabin Hausa da Addinin Musulunci, Takardar da
Aka Gabatar a Taron Kara wa Juna Sani na Dalibai Musulmi na Babbar Makarantar
Sakandaren Dawakin Tofa.

Gidan Dabino, A.A, (1992) Tasirin Labaran Soyayya ga Al’umma, Musamman ta Hausawa,
An Gabatar da Wannan Takarda a Taron Kara wa Juna Ilimi Mai Taken “Rubutu Don Al’umma’’ Wanda Kungiyar “Writers Forum” ta Gudanar, a Majalisar Matasa ta Fagge, Kano.

http://hausa.soas.ac.uk/

Katsina, S.I.1980. Mallakin Zuciya. Zariya: NNPC.

Katsina, A.1978. Sihirtaccen Gari. Zariya: NNPC.

Malumfashi, I. (2007) Behind The Veil of The Silent Sisters: The Images of Space, A Paradox
of Plenty And Women's Writing From Northern Nigeria. Leventis Fellow, Being a paper Presented at SOAS University, London, Weekly West Africa Seminar, Department
of Anthropology University College, London.

Malumfashi, I. & Aliya A.A, 2006. Writing Competitions and The Development of Hausa
Novel: The Colonial Legacy. Being a paper presented at the 4th Conference of Literature in Northern Nigeria, organized by the Department English and French, Bayero University, Kano.
Malumfashi, I. 2004. Ta’aziyyar Adabin Kasuwar Kano Makalar da Aka Gabatar a Taron Kara
wa Juna Sani a Taron Kasa da Kasa na 6 Wanda Cibiyar Harsunan Nijeriya ta Jami’ar
Bayero, Kano ta Shirya.

Muktar, I. (2004) Jagoran Nazarin Kagagaggun Labarai. Kano: Benchmark Publishers Limited.

Prietze, R. 1916. Lieder des Hausawolks. Germany.

Sa’id, B. 1980. Dausayin Soyayya. Zariya: Gsakiya Corporation.

Usman, B. (2005) Taskar Tatsuniyoyi na 1 zuwa 12. Kano: Gidan Dabino Publishers.

Yahaya, I.Y., (1971-72) Tatsuniyoyi da Wasanni 1 zuwa 6. Ibadan: Oxford University Press.

Yahaya I.Y, (1988) Hausa a Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce Ciin Hausa. Zaria: NNPC.

Yakubu, B.R. 1987. Budurwar Zuciya. Zariya: Gsakiya Corporation.

Yakubu, B.R. 1990. Wa Zai Auri Jahila? Zariya: Gsakiya Corporation.