Tuesday, June 15, 2010

ZIYARA ITALIYA DA FARANSA: NA JE KALLO NA ZAMA ABIN KALLO

Sashen kula da ilmi na hukamar da ke kula da kasashe masu amfani da harsunan faransanci, wato OIF da ke kasar Faransa, wanda Waziri Amadu dan kasar Nijar yake jagoranta su ne suka shirya wannan tafiya.

A kashin farko na wannan tafiya, wasu kamfanonin wallafa guda biyar ne suka fara zuwa kasar Italy da Faransa daga kasar Nijar da kuma Afrika ta tsakaya, kwanaki biyar su ma a suka yi a tsakanin Faransa da Italiya.

Bayan sun koma kasashensu ne mu kuma muka je wannan ziyara, a wannan karon shugabannin kamfanoni wallafa littattafai uku ne suka je wannan ziyara, wato Dan bourgami Magaouata, shugaban kamfanin Danbourgami (Niger)da Issouf Oumarou Alzumma shugaban kamfani Alpha (Niger) sai kuma Ado Ahmad Gidan Dabino shugaban kamfanin International Nigeria Ltd. (NIGERIA).

Mutum biyu da suka taho daga Nijar sun riga ni zuwa da kwana biyu, ni na bar Nijeriya ranar Lahadi 8 ga watan 11 da dare misalin karfe goma sha daya in da muka wayi gari a birnin Paris wajen karfe shida muka sauka, wato mun yi kamar awa shida muna tafiya kenan.

Daga nan muka shiga layin da jami’an tsaro za su duba passport dinmu. A nan na ga abin mamaki da ban haushi wato fasfot din Nijeriya ba a daraja shi a kasashen duniya, domin ni kadai na ga an dade ana duba fasfot dina sannan aka nemi in nuna takardar gayyata da aka ba ni ta zuwa wannan ziyara a kasar Italiya kafin a buga min hatimi a kan fasfot dina, abin ya ba ni mamki har na shiga tambayar kaina da kaina, shin ta yaya shi wannan jami’in tsaro zai ce in kawo takardar gayyata ta ya gani, bayan ga biza a ba ni ta kasar Italiya, shin ofishin jakadanci Italiya zai ba ni biza ne ba tare da na cika sharudan da suka tanada ba? Wannan abu ya ba ni takaici kwarai da gaske, don ganin babu wanda aka yi wa wannan abu sai ni kadai dan Nijeriya. Amma babu yadda zan yi don na san wasu daga cikin ‘yan Nijeriyar ne suka zubar mana da kima da martabar da muke da ita a da, na san lokacin da in dan Nijeriya zai tafi Ingila ba ya bukatar biza sai in ya je filin jirgin saman London a nan za a buga masa hatimi ya shiga, kamar yadda in mutum zai shiga kasar Nijar yana da fasfot ake yi masa.

Haka dai muka wuce muka je wajen jiran wani jirgin da zai dauke mu zuwa kasar Italiya, Mun yi jira na wajen awa daya sannan muka sake shiga wani jirgin muka nufi Italiya. Nan kuma a cikin jirgin ni kadai ne bakar fata, duk jajaye ne daga Turawa sai mutanen kasar Sin da Indiyawa da Italiyawa da dai sauransu.

Bayan kamar awa biyu muna tafiya sannan muka sauka a kasar Italiya. A nan ban gamu da wata matsala ta duba fasfot ko wani abu ba, illa kawai jinkirin daukar babbar jakata da aka dan samu, don na fi minti talatin ban ga jakar ta iso daga ramin da ake turo kayan ba.

Tun lokacin da muka sauka daga jirgi na kira wayar shugaban tafiyar, wato Waziri Amadu, ya amsa min da cewa shi ma yanzu ya sauka, don haka yana nan yana jira na a wajen fita, na shaida masa ni kuma ina so in dauki kayana tukunna.

Da na ga kayan sai na sake kiransa na ce ga ni nan fitowa ina za mu hadu? Ya shaida min. Muka hadu muka hau tasi muka nufi masaukinmu. Tsakanin masaukin da filin jirgi ya kai nisan kilomita ashirin.

Bayan mun isa masauki ba mu fi minti goma sha biyar ba sai direban kamfanin da muka zo don ziyararsu wato Arti Grafiche ya zo ya dauke mu don ya kai mu kamfanin, domin su abokan tafiyar tamu da suka zo daga Nijar suna can kamfanin. A kan hanya ne direban yake shaida mana ai ya je filin jirgi don ya dauko mu ya kasa samun mu.

Bayan wasu ‘yan mintina muka isa kamfani Arti Grafiche da ke unguwar masana’antu ta Pomezia, muka iske Magawata Danbourgami da Umar Alzumma, daga nan muka ci gaba da tattaunawa game da abin da ya kawo mu, wato kulla huldar yin aiki tare a bangaren wallafa littattafai, a nan dai muka wuni a kamfanin, sai da yamma bayan karfe biyar sannan jami’ar kasuwanci ta wannan kamfani wato Ms Nelly ta dauke mu mu hudu ta kai masauki.

Washegari muka sake komawa kamfanin don ci gaba da tattauna batutuwan ayyukan wannan kamfani na wallafa littattafai. Abubuwan da muka tattauna shi ne batun farashi da kuma yadda in an buga littattafan za a debu su a jirgin ruwa ko na sama da kum sauran wasu batutuwa da suka shafi kulla hulladar aiki tare da su da mu da muka zo daga Afrika ta yamma.

Da lokacin cin abincin rana ya yi muka koma masaukinmu tare da manajar kasuwanci Ms Nelly. Daga baya kuma mutane biyu daga cikin manajojin kamfanin suka zo don mu ci abincin rana tare das u, wato Mr. Poulo da Mr Luciano. Gaskiya an baje kolin abinci amma kash! Irin wanda zan iya ci kadan ne a ciki, wato kamar biredi da kifi sai kuma nama, amma sauran sun gagare ni. Haka dai aka yi wannan cin abinci aka gama, amma in na kalli wani abincin sai in ji zuciyata na tashi saboda kwamacalar da aka hada a cikinsa. Lallai abincin wani ba na wani ba.

Bayan an gama muka sake dawowa kamfanin don mu ga injinan da ake buga littattafai na zamani. Mun dade a cikin wannan bangare na buga littattafai kuma mun ga injinan da ba mu taba gani ba sai dai a cikin mujallu ko a finafinai na Turai. A nan muka ga wani inji mai saurin buga littafi, wanda kafin awa guda zai buga madaidaicin littafi guda 10,000. Lallai aiki ga mai kare ka.

A rayuwar duk wani mai harkar buga littafi ya ga ya mallaki mada’a, haka shi kuma dan jarida ya ga ya kafa kamfanin mujalla ko jarida, mai harkar yada labarai na rediyo kuma ya ga ya kafa gidan rediyo ko talbijin. Haka dai muka fito muna ta addu’ar Allah ya gwada mana lokacin da za mu mallaki ire-iren wadannan kayan aiki na dab’in littattafai. Da yamma bayan karfe biyar aka dawo da mu masauki.

A wannan rana da dare ya yi muka tafi wani gidan cin abinci, ga katon littafi an kawo don mu zabi abincin da za mu ci amma da Italiyanci aka rubuta kuma Italiyanci suka iya sai Faransanci da Turanci dan kadan wanda ba a rasa ba. Ni dai na ce ina son a kawo min shinkafa da kifi, da yake yarinyar mai kawo abincin ta fi fahimtar Faransanci sai aka shiga yi min tafinta, wato fassara daga Hausa zuwa Faransanci ana gaya mata abubuwan da nake so, mai yi min tafinta ya gaya wa yarinyar irin abin da nake so na ci da kuma da sha.

Assha! An kuma mace ta haifi mace. Bayan mun yi zama fiye da minti talatin muna jiran abincin, tun da dama a lokacin da ka fadi abin da za a kawo maka sannan ake dafawa. Can aka kawo abinci, na kalli shinkafar da na ce a kawo min na kau da kai, don abubuwan da na ga an zubu a ciki, an yi dafa duka da su, wato kaguwa da dodon kudi da wasu abubuwa masu kafafu kamar gizogizo su ne aka yi wannan dafa dukar shinkafa da su. Nan fa na kama fada, cewa a gaya mata a garinsu haka ne shikafa da kifi, ai duk duniya kifa guda daya ne, ba kaguwa ko dodon kudi ne ba. Wani abin haushi dodon kodin har da kwanson sa (kokonsa) aka zubu shi turmis.

Mai yi min tafinta ya ce, ta koma ta kawo kifi da dankalin Turawa. Kuma abincin ga tsadar tsiya, kowane filet daya ya fi Naira dubu uku a kudin Nijeriya, ga shi kuma dan kadan, (ita dai wannan dafadukar da ba za ta ciyu a gare ni ba). Nan dai shugaban tafiyar tamu wato Waziri Amadou da yake mai barkwanci ne, sai ya ce, ‘Ai kuwa Malam Ado ya kamata ka ci ka ji ka ga sai ka rubuta a rubutun ka nan gaba ko?’ Na ce, ‘Ai in na ci wannan abubuwan ban san yadda za mu kare da su ba, maganin kada a ji kada a fara, don haka ba zan fara ba.

Washegari kuma muka tafi yawon ganin gari, inda direban kamfanin Arti Grafiche mai suna Alkabeer, wani dan kasar Marocco ya dauke mu ya nufi birnin Roma don mu ga toshon birnin Roma da kuma fadar Fafaroma da ke Batikan.

Nisan birnin Roma daga Pomezia wato inda muka sauka ya kai kilomita ashirin da biya. Muna dosowa kofar shiga birnin Alkabeer ya ce wannan ita ce kofar shiga birnin Roma.

Haka dai muka yi ta ganin gine-gine tsofaffi wadanda suka yi shekaru dubunnai kamar yadda ake shaida mana. A nan muka ga ginin da maza ke gwada karfi, wato fadar Siza na Roma, wato wajen da aka yi fim din nan na Giladiyeto.

Daga nan bayan mun gama da wadannan wuraren sai muka nufi fadar Batikan. Muna zuwa muka dinga ganin mutane masu kai ziyara don kallo, wato irin mu da kuma masu zuwa don yin ibada. Kofar shiga wajen ibadar akwai jami’an tsaro da motocinsu suna kai komo don tabbatar da wani abu bai faru ba. Tsofaffi da ba za su iya tafiya ba ana tura su a kan keken guragu, ga kuma masu cin kasuwa nan a wajen harabar suna ta karakaina.

Wani abin dariya da aka yi, mu muna daukar hotuna tare da abokan tafiyar mu, ni kuma baki suna dauka ta hoto, na kati da bidiyo, saboda doguwar riga ta shadda da hula da na sanya. Wasu ma zuwa suke yi su ce don Allah muna so mu dauki hoto da kai, wani ya zo shi kadai wani ya zo da matarsa wani saurayi da budurwa ne suke zuwa.

Nan fa shugaban tafiyar tamu, da yake mutum ne mai barkwanci, Waziri Amadou sai ya ce “To kai Malam Ado ka zama wani gidan tarihi ko gidan zoo, ko kuma gidan kallo ga shi sai baki ne suke ta daukar ka hotuna, to ko kudi za mu sanya ne duk mai son daukar hotonka sai ya biya?” Sai na yi dariya na ce masa “Ka ga kuwa da mun tara kudi, ko da Euro biyar muka ce duk mutum daya zai biya, daga nan zuwa yamma ai da mun tara kudi da yawa” Muka yi dariya mu duka. Na ce “To Danbourgami Magaouata kai za ka zama mai amsar kudi ko?”

Muna cikin wannan magana sai ga wata mata da miji su ma sun zo sun ce “Don Allah za mu dauki hoto da kai” Na ce “To ba komai ku dauka”. Na tsaya matar ta zo ta tsaya kusa da ni mijin ya dauke ta” Sai ni ma na ce “To bari in bayar da kyamarata a dauke mu”. Ta tsaya aka dauke mu tare, suka yi godiya suka tafi, suna fara’a da dariya. A karshe sun ce min daga Barazil suka zo, ni kuma fa, na ce daga Kano, arewacin Nijeriya.

Da muka gama muka dawo, a kan hanyarmu ta komawa masauki dorebanmu Alkabeer ya ce zai kai mu wajen cin abinci na Halal, wato na musulmi. Haka aka yi kuwa. A nan ne na san na ci abinci sosai saboda na sami irin abincin da zuciyata ta yi na’am da shi.
Washegari ranar 12 ga wata muka dawo birnin Paris, in da za mu yi kwana biyu kafin kowa ya koma kasarsa.

Mutanen Nijar jirgin su ya riga namu tashi, bayan karfe bakwai na safe suka taso, ni kuma sai bayan karfe goma sha daya na taso, kuma tafiyar awa biyu ce tsakanin Italiya da Paris, kuma da yake an sami jinkirin jirgi sai bayan sha biyu muka tashi, don haka ba mu iso Paris ba sai bayan karfe biyu na rana. Nan ma a wajen jiran kayana sai da mutane hudu mace biyu namiji biyu suka zo don neman su dauki hoto da ni, wannan karon mutanen Jafan da Cana ne suka zo.

A Paris kuma abin da ya faru gare ni shi ne, na ci wani abinci da ya sa ni atini na wuni a daki, na kasa fita ko’ina sai dai zaman otel, sai da abokan tafiyata suka sayo min magana na sha, sannan na samu ‘yar sa’ida.

Sai washegari ne muka sami damar fita muka zaga gari muka je wajen dugon karfen nan da ake kira Tawa Elfe. Sannan kuma muka je ofishin hukamar da ta shirya wannan tafiya wato OIF, inda muka mika musu rahoton wannan tafiya da muka yi da kuma irin matsayar da muka cim ma da su wadannan kamfani na Arti Grafiche don su ajiye a ma’adanar su ta hukamar OIF.

Wannan tafiya dai ta ba mu wata dama da muka hada huldar yin aiki da wannan kamfani na wallafa kuma mun karu da ilmi mai yawa a wadannan kasashe biyu, sannan kuma a cikin rubutun da nake na littafina na tafiye-tafiye mai suna GANI DA IDO… na dada samun abubuwan da zan sanya a cikinsa kamar yadda na samu a bara lokacin da na je kasar Jamus.

Fatanmu dai Allah ya sa wannan ilmi da muka samu ya zama ya amfanar da jama’armu marubuta da mawallafa da kuma sauran jama’a masu karatu.

1 comment:

Unknown said...

Nakarance wannan ziyara tsaf,(kamar a idona akayi) Nayaba da sassaukan salon rubutu mai armashi da dadin karatu da akayi amfani dashi. Kuma a maganar rashin daraja fasfonmu da kace anayi gaskiya hakane ko'ina,kuma ba wasu bane suka ja mana illa abokan zamanmu aljihwan baya 'yan kudu. Domin sanda na taho nima nahadu da wannan abun ta'ajibi da ban haushi, da ike sai da muka yada zango a egypt na kwana guda tukunna muka karaso. Ana ganin koran fasfo sai ayi waje guda da mu, kai harma dai abin ya fara isata. Bayan mun iso abin da har yau idan na tuna yaken ban haushi shine, a inda za'a buga mana stanfin shigowa kasar muna isa gurin sai jami'an suka ce ai mu sai an kaimu cikin ofishinsu gurun manyansu. Haka muka rankaya kamar shanu aka tusamu agaba. Bayan sungama batamana lokaci sa'annan ni nayi sa'a makarantarmu sukazo suka daukeni, nanma saida wakilin makarantar yayi da gaske. Saurankuwa ban ma san yadda suka karkeba, sai daga baya muka hadu a waya. Wato irin kallon da akewa dan najeriya a kasashen waje abin bakyan gani, sai dai ace Allah ya kyauta. Nayi murna da karanta wannan ziyara mai cike da Ilimi.
Allah ya samu a danshinku.