Friday, August 7, 2015

Me Ya Sa Muke Rubutu?
Wace Irin Gudummawa Muke Bukata?

Daga
Ado Ahmad Gidan Dabino
Shugaban Kamfanin Gidan Dabino International Nig. Ltd., Kano

An Gabatar Da Wannan Takarda a Bikin Cika Shekara Hamsin a Duniya na Farfesa Ibrahim Malumfashi da kuma Bikin Cika Shekara Tamanin da Biyar da Fara Rubutu Kagaggun Labarai na Hausa, Wanda Aka yi a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harshe, Jami’ar Jihar Kaduna, a Ranar 8 ga Watan Disamba, 2012.


Tsakure
‘Nakan ji dadi a duk lokacin da na zo wucewa na ga wani ko wata suna karanta abin da na rubuta a cikin littafi, nakan ji kamar babu ya ni a wannan lokaci, ba don komai ba sai don na cika buri na, wato na isar da sakon da nake so ya isa ga jama’a, wanda kuma shi ya sa nake rubutu’.

Gabatarwa

Wadannan kalamai su ne suke fitowa daga ruhina zuwa zuciyata daga nan kuma har bakina ya furtawa a lokacin da na fara buga littafi ya shiga kasuwa, wato In Da So Da Kauna na daya a shekara ta 1991, wanda ake sayar da shi Naira biyar kacal ga masu karatu. Ba ni da wani buri ko bukata da suka wuce haka a wannan lokaci. Lokaci ne na samartaka, wanda babu wani abu da yake damun rayuwa ta face abin da na sa a gaba in ga na cim ma burina. Babu tunanin samun kudi ko suna a cikin zuciyata a wancan lokacin, fatana kawai ciwon da ke cikin zuciyata in bayyana shi ga jama’a, wadanda ba su sami kansu a irin wannan yanayi ba kada su sake su shiga, in kuma tsautsayi ya kai su sun shiga to, ta wace hanya za su bi su fita.

Na bukaci gudummuwoyi da dama a wancan lokacin, wadannan gudummuwoyi sun hada da neman shawarwari da duba min littafin a gyara Hausar da rabe-raben kalmominta kasancewar farin shiga ne ni a lokacin, kuma na sha wuya sosai wajen zirga-zirga a cikin birnin Kano da kewayenta. Ba dare ba rana ina bisa kekena don zuwa wajen mutanen da na bai wa wannan littafi don su duba kuma su yi min gyare-gyare a cikinsa.

Zirga-zirga ta aure ni. Je-ka-ka-dawo ba a magana. Hakuri dole ya zama abokin zamana saboda na yi ta samun sabanin lokaci na kammala aikin dubawar daga wasu mutanen da na bai wa karantawa da yin gyaran littafin.

Amma da ya kasance a kullum hakuri muka zama abokai da shi sai na ga alfanun abin, domin ko yanzu (yau shekara ahirin da daya) in aka dauko littafin aka karanta ba za a ga gyare-gyare rakwacam ba kamar yadda marubutan yanzu suke barin gyara a cikin littattafansu, wanda ba wani abu ne yake kawo hakan ba face rashin hakuri da juriya wajen kai wa a duba littafin.

Taken mukalata shi ne Me Ya Sa Muke Rubutu? Wace Irin Gudummawa Muke Bukata? Wadannan tambayoyi guda biyu suna da amsoshin su, kuma na san kowa ya tashi bayar da amsa za a ji ya fadi gwargwadon fahimtarsa da kuma ra’ayinsa. Don haka in muka ce tambaya ce mai sauki ba mu yi kuskure ba. Domin in dai kai marubuci ne kana da amsar da za ka bayar.

Me Ya Sa Muke Rubutu?

Wannan tambaya tana iya zama mai saukin gaske ga duk marubuta tun da kowa da irin dalilin da ya sanya ya shiga fagen rubutu, don haka ra’ayi ko amsar wannan tambaya ma za su bambanta. Amma don ba na son arar bakin marubuta in ci musu albasa sai na je kai tsaye ga marubuta don in ji waka a bakin mai ita, wato su marubutan su gaya min da kansu daga wasu jihohi kamar Kano da Kaduna da Bauchi da Jigawa, na kuma yi musu tambaya kamar haka:

Salam. Ina rubuta wata takarda a kan rubutu da marubuta don haka nake son a ba ni wannan amsarzan yi amfani da ita, Me ya sa kuke rubutu? Wace gudummawa kuke bukata?

Marubuta goma sha uku, maza guda 4 da kuma mata guda 12 na aikawa wannan sakon, duk sun ba ni amsoshinsu, kuma cikin mabambantan ra’ayoyi, wasu sun yi daidai da junansu wajen amsar, wato ra’ayinsu ya zo daya. Sannan kuma kamar hadin baki babu wata amsa da na same ta da safe, duk lokacin da na sami sakonne da yamma ne, sun fara daga 4.18  zuwa 11.26 na dare, a ranar farko, haka kuma a sauran ranaikun, duk da yamma na same su. Ga amsoshin da suka rubuto min kamar haka:

Da farko dai ni na fara rubutu domin sha'awa, ina jin dadi kawai idan ina rubutu, lokaci guda kuma sai nake amfani da damar domin na wa'azantar cikin nishadi.
Nazir Adama Saleh, Kano, ranar 10/11/2012, karfe 4.18 na yamma.

In muka dubi abin da Nazir Adam Saleh ya bayyana game da dalilinsa na fara yin rubutun littafi, za mu ga sha’awa ce kawai ta kai shi ba wani abu ba, sai kuma jin dadin yin rubutun, sannan kuma ya gane cewa ashe baiwar rubutun da yake da ita hanyar wa’azantarwa ce ta samu gare shi, wanda kuma har zai iya nishadantar da masu karatu.

Don fadakarwa da nishadantarwa da kuma akida.
Alawiyya Wada Isa, Kano ranar 10/11/2012, karfe 4.37 na yamma.

Malama Alawiyya Wada Isa kuwa don ta fadakar da al’ummrta ta nishadantar da kuma akida su suka jawo ta afka fagen rubuta littafi.

Ni dai ina yin rubutu don tallafa wa adabi da inganta al'ada da kuma ba wa mata gudummawa ta zamtakewa da mazajensu da kuma yadda za su yi girki mai kyau da tarbiyyar yaransu da hakuri da juriya da yin sana'a. Sannan shi Rubutu babbar cuta ce da ba shi da magani tilas sai ka yi shi muddin saboda Allah kake don karuwar jama’a ba don kudi ba.
               
Sadiya Garba Yakasai, Kano  ranar 10/11/2012, karfe 5.20 na yamma.

Sadiya Garba Yakasai ta lallabo da nata hujjojin shiga fagen rubutu ne saboda agaza wa adabi da al’ada da kuma bayar  da gudummawa ga ‘yan’uwanta mata don su iya girki don kada a dinga samun sabani tsakanin magidanta da matansu wajen abinci domin wasu matan ba suiya dafa abinci ba, da tarbiyyar yaransu da nuna hakuri da juriya a rayuwa da kuma son a dogara da sana’a, bn das a ido a kana bin hannun mutane.

Ina rubutu ne saboda girmama harshena.
       
Asama’u Lamido, Kaduna, ranar 10/11/2012, karfe 6.23 na yamma.

Asama’u Lamido, ra’ayinta ya bambanta da wasu don ta bayyana cewa harshenta da take girmamawa shi ne ya sa take rubutu.

Kishin harshe na da yada al'adata, sannan na isar da sakona na fadakarwa cikin nishadi.
Rabi Talle Maifata, Kano, ranar 10/11/2012, karfe 7.21 na dare.

Ita ma Rabi Talle Maifata sun hada hanya da Asma’u Lamido, inda ta nuna kishin harshen Hausa ne ya ya tsoma ta a tekun rubutu, sannan ta kara da son yada al’ada da fadakarwa hard a nishadantarwa.

Dalilin da ya sa ake rubutu yana da yawa, daga ciki akwai: Ilmantarwa da nishadantarwa da neman suna da neman kudi da sha'awar rubutu da soyayya da sauransu.
Umma adamu, Hadeja, ranar 10/11/2012, karfe 7.52 na dare.

Umma Adamu Hadeja ta hado abubuwa da yawa da take ganin suna sawa a shiga rubutu, wadanda suka kunshi ilmantarwa da nishadantarwa da neman suna da neman kudi da sha’awar rubutun shi kansa da kuma soyayya.

Muna rubutu don fadakarwa da nishadantarwa da nema wa al'umma mafita a al'amuran yau da kullum, kamar zamantakewa da neman ilimi da gyaran halaye da sauransu.
Bilkisu Yusuf Ali, Kano, ranar 10/11/2012, karfe 8.39 na dare.

Ita kuwa Bilkisu Yusuf Ali, mun fahimci saboda ta nema wa al’umma mafita wajen al’amuran da suka shafi zamantakewa da gyaran halaye da neman ilmi da fadakarwa har ma da nishadantarwa, su ne suka kawo ta cikin farfajiyar yin rubutu. Kuma sun yi tarayya a wasu ra’ayoyin tare da Umma Adamu da wasu marubutan.

Ta hanyar rubutu nake sadar da sako ga dubban mutane ba tare da na yi tattaki zuwa inda suke ba.

Bala Anas Babinlata, Kano ranar 10/11/2012, karfe 8.52 na dare.

Bala Anas Babinlata, ya nuna don isa da sako ne, wanda rubutu yake isar wa wanda ba sai ya je kafa da kafa ba sakon sa yake isa ga jama’a.
Ni ina yin rubutu don na fadakar da kan al’umma game da zamansu, musamman aure da kishi da tarbiyyar yara.

Balaraba Ramat Yakubu, Kano, ranar 10/11/2012, karfe 9.44 na dare.

Yaya babba kuwa wato Balaraba Ramat Yakubu, ta bayyana nata dalilan shiga taskar rubutu da cewa fadakar da al’umma wajen zamantakewa musamman ‘yan’uwanta mata a kan batun kishi da tarbiyyar ‘ya’yansu.

Babban abin da ya sa ni yin rubutu shi ne, kishin al'adunmu da kokarin fadakarwa da ciyar da yarenmu na Hausa gaba. Sha'awar rubutu ta karfafa a zuciyata ganin cewa hanya ce ta watsa manufofi, ta saukakakkiyar hanya, kuma mutum zai iya yin gargadi da wa'azantarwa da dora mutane a kan kyakkyawar hanya, walau ta hanyar tsoratarwa ko nishadantarwa. Wadannan dalilai su suka dasa min sha'awar rubutu. Don wani lokacin marubuci har kankanba yake yi, ya shiga rigar malamai ta hanyar wa'azantarwa. Kuma yin rubutu hanya ce ta kaifafa kwakwalwa, shi ya sa a duk inda marubuci yake za ka gan shi tamkar tsuntsun da yake yawo a sama, da zarar ya hango kuskure a kasa sai ya zaro biro da takarda ya shiga tunanin hanyar warware matsalar ta ruwan sanyi, yadda al'umma makaranta za su gano bakin zaren. Duk wadannan abubuwan su suke ba ni sha'awa a harkar rubutu.
Lubabatu Ya’u Babura, Kano, ranar 10/11/2012, 10.01 na dare.

Lababatu Ya’u Babura, ta dada karfafa ra’ayoyin da wasu suka bayyana cewa kishin harshen Hausa da al’adu suka sagalo ta zuwa farfajiyar fasiha, marubuta don ta ba da tata gudummawar, kuma ta kara da cewa shi rubutu hanya ce sassauka ta yada manufa ga jama’a, sannan ta nuna marubuta ma suna tarayya da malamai wajen wa’azi ga jama’a ta hanyar rubutunsu. Wadannan da ma wasu dalilan su ne suka jagorarta ta ci gaba da rubutwa da bugawa, jama’a suna karantawa.

Na fara rubutu da nufin gyara yadda wasu marubuta suka kalli mace da alkalaminsu, nufin ya fadada zuwa sakonni mabambanta.

Rahma Abdul Majid, Minna, ranar 10/11/2012, karfe 10.06 na dare.

Rahma Abdul Majid, ta sirnano nata jawabin ne da cewa, marubuta suna kallon mace da alkaminsu a baibai, shi ya sa ita kuma ta shigo don ta rubuta su daidai, a daina kallon mata a baibai kamar yadda wasu ‘yan’uwanta marubutan suka rattaba a littattafansu, daga wannan niyya kuma sai abubuwan suka fadada suka yi rasa har take rubutu na’u’i daban daban har da na masu aikata laifuka

Yana daga dalilan rubutuna, tsintar baiwar rubutun da na yi a tare da ni. Ka ga ya zama wajibi. Raba dannin jigo kuma sun hada da; bayyana abin da ke cikin zuciya da fadakarwa da tallar harshe da kuma neman kudi.

Aminu Abubakar Ladan (ALA), Kano, ranar 10/11/2012, karfe 11.26 na dare.

Shi kuma mai rumbun kalmomi, mahirun waka, Aminu Abubakar Ladan (ALA), ya ce tsintar biwar rubutun ya yi a tare da shi kawai don haka ya zama wajibi ya yi. Sai kuma ya kawo wasu raba-danni ko kananan jigogi na musabbabin yin rubutun, inda ya bayyana cewa fitar da abin da ke cikin zuciya da fadakarwa da da tallar harshe da kuma neman kudi.

Ni mai son isar da sako ga al’umma ce, sai na zabi hanyar rubutu wajen kai sakon.

Jamila Adamu Yaro, Bauchi, ranar 11/11/2012, karfe 2.41 na yamma.

‘Yar mutan Bauchi kuwa, Jamila Adamu Yaro ta nuna tuni take da son isar da sako ga jama’a amma sai ta zabi hanyar rubutu wajen isar das akon.

Ina rubutu ne don isar da sako tare da ilmantar da mutane da wayar musu da kai.

Adamun Adamawa, Bauchi, ranar 12/11/2012, karfe 2.50 na yamma.

Dan mutan Adamu, wato Adamun Adamawa ya bi hanya guda da Jamila Adamu yaro, da ma kuma dukkansu suna jihar Bauchi a yanzu, shi ma dai son isar da sakon ne ya ingiza shi cikin harkar rubutu.

Ina rubutu ne domin na isar das ako ga jama’a ta yadda za su rike aure da zumunci da zama da kishiya da sauran mu’amalar yau da gobe.

Aisha Abdulhamid Alhaji (Lawash), Bauchi, 25/11/2012, 9.20, dare.

Ina rubutu saboda yada harshena da al’adunmu na Hausa da fadakarwa da nishadantarwa ga masu karatu da kuma wayar da kan jama’a dangane da zamantakewar yau da kullum musamman auratayya wadda take jigon rayuwa

Sa’adatu Saminu Kankiya, 26/11/2012, 10.37, dare.

Idan muka lura da ire-iren dalilan da marubutan suka bayyana na abubuwan da suka sanya suka shiga fagen rubutu, za mu ga mafi yawa don son gyaran tarbiyyaar al’umma ne ba don neman kudi ba. Kuma dukkanin maubutan da na aika wa da  rubutaccen sakon (SMS) sai da na kira wayarsu muka yi magana baki da baiki, wasu sun ce in rubuta abin da suka fada min da bakinsu, amma na ce a’a, su aiko min a rubuce kamar yadda na aika musu a rubuce, don gudun idan gaya min aka yi da baki kila in rubuta abin da ba haka marubutan suke fadi ba, amma ta hanyar SMS, ba za a sami wannan sabanin ba. Kuma hakan aka yi suka rubuto da hannunsu.

Wace Irin Gudummawa Muke Bukata?

Game da wannan batu na abubuwan da marubuta suke bukata ta fannin gudummawa a wannan harka ta rubutu, ita ma amsar a bayyane take, kuma ba wuya gare ta ba, tun da duk marubuta sababbi da tsofaffi (na Hausa) sun san matsalar da marubuta suke fuskanta a fagen rubuce-rubuce da inganta shi da buga shi da tallata shi da sama masa tagomashi a wasu wurare, don haka da an tambayi marubuci kila zai fadi wannan miki da ya dade a zuciyarsa cikin hanzari. Ga abubuwan da marubutan suke ce:

Asamau Lamido, Kaduna:
Gudummawar da nake so, a sa mana ido a kan dillalan da ke safarar littattafai, suna cika riba kuma ba su da alkawari wajen biyan kudin littattafanmu.

Sadiya Garba Yakasai, Kano:
Muna mutukar son taimakon gwamnati ta san da mu marubuta, ta rinka tallafa mana, kuma muna bukatar manyan marubuta irin ku kuna yi mana gyara da sa mu a hanyar da za mu inganta rubutunmu, mu ma duniya ta san da mu, idan rubutu ba inganci tamkar shan shayi ne ba madara ko sukari. Ina son na ga ana yi mana gyara, ana kula da abin da muke yi, saboda ita rayuwa in har ba ka da mafadi, to, ba za ka ga da kyau ba, ina jin ciwon yadda manyan marubuta irin ku kuka bar mu kara zube babu mai sa mu ko hana mu, muna bukatar tallafin ku don bunkasa harkar.

Alawiyya Wada Isa, Kano:
Muna bukatar jagora na gari wanda zai tsaya mana a kan al’amuranmu, da kuma tallafawar gwamnati.

Nazir Adama Saleh, Kano:
Taimakon da muke bukata shi ne, mu sami hanyar da za ake yi mana dab'i mai inganci, sannan muna bukatar kara samun karfin gwiwa da kuma kauna daga gwamnati, ba tsangwama ba.”
 
Bilkisu Yusuf Ali, Kano:
Muna bukatar samun shugabanni tsayayyu da shigowar hukuma inda za ake hukunta wanda ya karya doka, kuma muna bukatar a sami wani ko kungiya ko kuma kamfani karbabbe wanda zai zama yana duba littafi wanda kuma in ya duban littafn zai sami yarda gun kowa, har malaman jami’a, sannan muna son littattafan ake nazarin su a matakinkaratu kowane.

Rahma Abdul Majid, Minna:
Bukatata ita ce a fahimci sakona.

Umma Adamu Hadeja, Jigawa:
Tallafin da marubuci ke bukata a wajen masu kudi da gwamnati shi ne jari da agaji da bashi. Sai kuma ingantaccen aiki da rikon amana da cika alkawari daga ma'aikatan madaba'a.”

Aminu Abubakar Ladan (ALA):
Muna bukatar goyon bayan hukuma da mazhabobin ilimi.

Adamun Adamawa, Bauchi:
Tallafin yada rubutun da yayata shi, shi ne bukatata.

Jamila Adamu Yaro, Bauchi:
Gudummawar da nake bukata ta kudi ce (hahaha).

Balaraba Ramat Yakubu, Kano:
Ina bukatar taimako ta kowace hanya a kan rubutu, kudi don buga littafin, ko kayan aikin bugawa, kuma hukumar ilmi ta tallafa  ta sa littattafan a manhajar karatu don mu fadakar da yaranmu”

Rabi Talle Maifata, Kano:
Gangamin wayar da kan marubuta daga lokaci zuwa lokaci. Iyaye su gane ba tarbiyyar yara muke batawa ba. Su karanta littafinmu kafin su yi hukunci a kanmu. A sanya littattafanmu a manhaja domin kada a manta da al’adunmu, amma littattafan da suke sun danganci hakan.

Lubabatu Ya’u Babura, Kano:
Hakika marubuta suna neman dauki ta hanyar a taimaka musu da kudade ko da rance ne don farfado da harkar rubutu, kuma yana da kyau a ce gwamnati ta samar da injinan dab'i ingantattu. Sannan a yi kokarin wayar wa da marubutanmu kai ta yadda marubuci zai bazama ya karo ilimi. Inganta shawarwari a tsakaninmu don kamo bakin zaren a kan abin da ya tabarbara harkar kasuwar littafi. Samar da wani fili a yanar gizo (internet) domin tallata hajar fasahar rubutun zube. Kana manyan marubutan da suka fara kawo salon rubutun da a yanzu aka fi raja'a a kan sa, su rinka jan mu kananan marubuta suna dada tunasar da mu irin nauyin da yake kan marubuci. Da darfafa gwiwar su ringa zurfafa tunaninsu ta hanyar zakulo matsalolin da suka addabi al'umma a rinka rubutu a kai, ba wai sai na soyayya ba. Manyan namu kuwa su ne irin su Dr. Yusif Adamu da Ado Ahmad Gidan Dabino da Bala Anas babinlata da Hajiya Balaraba Ramat da sauransu. Abu na gaba kuma shi ne sama wa marubuta kariya wajen yada manufofinsu.”      

Sa’adatu Saminu Kankiya, Katsina:
Taimakon da nake ganin muna bukata shi ne, na farko hadin kan mu marubuta, sai kuma samun jagoranci nagari da kuma tallafi daga hukumomi da kunguyoyi ta yadda za mu iya tsayawa da kafafuwanmu, ba tare da mun dogara ga ‘yan kasuwa ba. Kusan wannan ita ce babbar matsalar marubuta a wannan lokacin, saboda har yanzu ban taba jin wata kungiya ko hukuma da ta taba ba da tallafi ga sana'armu ba.

Tun da mun ji bayanai daga bakin marubuta ta hanyar rubutaccen sakon wayar hannu (SMS), ya kamata kuma a ji ta bakin zabiyar, wato shi mai rubuta wannan takardar, domin kila shi ma yana da nasa ra’ayin, wanda tun a farkon wannan takarda ya fara furtawa a cikin gabatarwarsa ta wannan takarda.

Ga ra’ayin mai gabatar da wannan takarda kamar haka:
Ni ina rubutu ne saboda ya zama jinin jikina kuma ya zama abokin rayuwata, wanda babu garin Allah da zai waye ban yi rubutu ba ko kuma na duba na wani na yi gyara ko ba da shawara ba, tun da ya zama aikina kuma sana’ata, ba ni da wani aiki da ya wuce rubutu da wallafa.

Gudummawar da ake bukata a harkar rubuta, akwai batun tsayayyiyar kungiyar marubuta wadda za ta kare hakkokinsu da nema musu daraja da kima a idon duniya. Kungiyar da za ta dinga kimanta harshen gida fiye da bakon harshe, wadda za ta dinga nema wa marubuta hanyoyin samun tallafi na sana’arsu, a wajen gwamnati ko masu hannu da shuni ko sha’awar rubutu ko kungiyoyi masu zaman kansu ko bankuna, a cikin gida da wajen Nijeriya, don bunkasa hanyoyin rubuce-rubuce musamman na Hausa. Wadda za ta nemo hanyoyin sanya gasanni don zaburar da marubuta su yi rubuce-rubuce masu inganci da nagarta da shirya taruka don kara musu sani da koyar da su dabaru na harkokin rubutu.

Mun ji ra’ayoyin masu ruwa da tsaki na ma’aikatar rubuta da wallafa, game da abubuwan da suka sa su suka tsunduma cikin rubuce-rubuce da kuma ire-iren gudummawa da suke bukata don bunkasa wannan sana’a tasu ta rubutu da wallafa. A duba kasa an takaita wadannan ra’ayoyi zuwa kasha hudu, kuma za a ga isar da sakon fadakarwa shi ne a kan gaba a zukatan marubuta daga nan sai girmama harshe da yada al’ada sannan batun neman kudi da a sha’awa su ne suke kafada da kafada da juna.

In muka dawo kuma batun irin gudummawar da narubuta suke bukata za  mu ga cewa batun samun tallafi daga gwamnati da hukumomi ne ya baibaiye wannan faifai na bayyana ra’ayi ko kididdiga sai kuma batun samun jagoranci yake biye masa sannan batun dillanci da dab’I ya zo na uku, sai abu na hudu batun kudI, wato taimako ko aro ko jari.

Kila yanzu daga wadannan bayanai da aka samu an gane ko kuma an soma gane su wane ne marubutan Hausa kuma don me suke rubutu, amma na san wasu a da can kafin su ji ta bakinsu suna ba su wata fassara ta daban, wato kila a ce don neman kudi ko bata tarbiyya suke yi, amma kila wadannan bayanai da aka ji daga gare su zai sa wasu su sauya tunani game da marubutan Hausa musamman na adabin zamani. Masu iya magana suna cewa, hange ba ya kawo nesa kusa, kuma ba ka gane mutum kila sai ka zauna da shi ko ka ji kalamansa.

A cikin watan Nuwamba na shekarar 2004, Shaihin Malami, Farfesa Graham Furniss ya ziyarci jihar Kano a Nijeriya daga London don ya yi hira da wasu marubuta na adabin zamani inda ya tattauna da su ya ji ra’ayoyinsu da kuma dalilan fara yin rubuce-rubucensu, wannan kuma ya sa ya gabatar da takarda wadda za a buga a cikin: Research in African literatures Vol. 43 No. 4, 2012. Takardar tana da shafuka sama da ashirin, kacokan ya mayar da hankali ne a kan wasu daga cikin ‘ya’yan kungiyar marubuta ta Raina Kama, kamar Badamasi Shaaibu Birji da Alkhamis D. Bature da Amina Abdu Na’inna da Dan’azumi Baba da Balaraba Ramat da kuma Ado Ahmaad. Wadannan mutane sun yi dogayen bayanai game da dalilai da manufofin yin rubutunsu da kuma matsaloli da suke fuskanta a wancan lokaci, yau kimanin sheakara takwas kenan, kum har yanzu wasu daga cikin matsalolin da suka bayyana ba su sauya ba sai ma karuwa da suka yi. Ga wadanda Allah ya sa suka karanta wannan takarda za su ga cikakkun bayanai

Kammalawa
An yi kokarin bayyana ra’ayoyin wasu daga cikin marubuta maza da mata daga jihohin Katsina da Kano da Kaduna da Bauchi da Neja da Jigawa maa hudu mata goma sha uku, wadanda suka bayyana dalilan da suka sa suka shiga farfajiyar rubuta littattafai da kuma ire-iren gudummawar da suke bukata don inganta wannan sana’a tasu ta rubutu da kuma neman a samar da wata hadaddiyar kungiya ta marubuta harsunan gida musamman ma Hausa don ta dinga samar wa da marubuta hanyoyin da a su inganta ayyukansu da sama musu tallafi da kara musu ilmi a bisa wannan sana’a.  


Manazarta

Furniss, Graham da Adamu A.U (2012) “Go by Appearances at Your Peril”: The Raina Kama Writers’ Association in Kano, Nigeria, Carving out a Place for the “Popular” in the Hausa Literary Landscape” Research in African literatures Vol. 43 No. 4, 2012 (forthcoming)


Sakonnin Wayar Hannu (SMS) da Aka Samu Daga Marubuta Don Amsa Tambayoyin da Aka yi Musu:

Nazir Adama Saleh, Kano, ranar 10/11/2012, karfe 4.18 na yamma.

Alawiyya Wada Isa, Kano ranar 10/11/2012, karfe 4.37 na yamma.

Sadiya Garba Yakasai, Kano  ranar 10/11/2012, karfe 5.20 na yamma.

Asama’u Lamido, Kaduna, ranar 10/11/2012, karfe 6.23 na yamma.

Rabi Talle Maifata, Kano, ranar 10/11/2012, karfe 7.21 na dare.

Umma adamu, Hadeja, ranar 10/11/2012, karfe 7.52 na dare.

Bilkisu Yusuf Ali, Kano, ranar 10/11/2012, karfe 8.39 na dare.

Bala Anas Babinlata, Kano ranar 10/11/2012, karfe 8.52 na dare.

Balaraba Ramat Yakubu, Kano, ranar 10/11/2012, karfe 9.44 na dare.

Lubabatu Ya’u Babura, Kano, ranar 10/11/2012, 10.01 na dare.

Rahma Abdul Majid, Minna, ranar 10/11/2012, karfe 10.06 na dare.

Aminu Abubakar Ladan (ALA), Kano, ranar 10/11/2012, karfe 11.26 na dare.

Jamila Adamu Yaro, Bauchi, ranar 11/11/2012, karfe 2.41 na yamma.

Adamun Adamawa, Bauchi, ranar 12/11/2012, karfe 2.50 na yamma.

Aisha Abdulhamid Alhaji (Lawash), Bauchi, 25/11/2012, 9.20, dare.

Sa’adatu Saminu Kankiya, Katsina, 26/11/2012, 10.37, dare.



No comments: