Tuesday, January 1, 2008

Tasirin Labaran Soyayya ga Al’umma, Musamman ta Hausawa

Wannan ce Mukalar da na Fara Gabatarwa a Rayuwata Cikin Harkar Adabi

An Gabatar da Wannan Takarda a Taron Kara wa Juna Ilimi Mai Taken “Rubutu Don Al’umma’’ Wanda Kungiyar “Writers Forum” ta Gudanar Ranar Lahadi 2/12/1992, A Majalisar Matasa ta Fagge, Kano.

1.0 Gabatarwa
Godiya ta tabbata ga Allah mai kowa mai komai, wanda yake sanar da dan’adam abin da bai sani ba, ya kuma ba shi baiwa da hikima ta yadda zai ji dadin sarrafa rayuwarsa. Sannan ya hore wa wasu daga cikinsu hange a kan al’amuran da kan je su komo, su yi amfani da basirarsu su fadakar da al’ummar da suke ciki. Tsira da aminci su tabbata ga shugaban manzanni cikamakin Annabawa, manzon rahama, sallallahu alaihi wasallama.

Kamar yadda aka bukaci in gabatar da mukala mai taken ‘Tasirin Labaran Soyayya da na Jarumta ga Al’umma’ Hakika wannan abu babba ne musamman ta kallon marrar da muke ciki a yanzu. Labaran soyayya da na jarumta, fagage ne masu yalwar gaske da za su bukaci dogon lokaci, idan ana so a ba kowane daga cikinsu gamsasshen bayani bisa hakkinsa. Don samun saukin fayyace bayanansu dalla-dalla bisa gwargwadon iko da na lokaci, na dauki sashe daya da nufin magana a kansa, wato batun da wannan takarda ta karkata a kansa yanzu shi ne ‘Tasirin Labaran Soyayya ga Al’umma, Musamman ta Hausawa’

Tasiri dai yana karkata ne bisa ma’ana ga ire-iren canjin da wani abu ya kawo ko ya haifar a kan wani abu. Nason wani abu ne a kan wani abu domin haka Bahaushe yake cewa, zama da madaukin kanwa shi ke kawo farin kai, to, burbushin saukar danshin kanwar nan kan wanda ke kusa da mai daukarta shi ne tasiri a takaice. Tasiri yana iya zama mai amfani, nagartacce ko akasin. Ita wannan takarda za ta karkata ne ga fito da tasirin da rubuce-rubucen labaran soyayya kan haifar wajen inganta ko hannunka mai sanda ga dangogin rayuwa a al’ummar Hausawa. An bi zancen tunanin wannan batu daki-daki, bisa matakai kamar haka:

2.1 Ma’anar Soyayya
Soyayya aba ce mai wuya, mai rikitarwa, mai kuma dadi, saboda haka kowa ya tashi ba da ma’anarta zai fadi gwargwadon fahimtarsa da ita. Mutane da dama sun yi mata fassara kamar haka: Kawa zuci ko tsananin kauna da bukatar kusanta ga wani mutum ko wani abu daban. Shi kuma so wata iska ce mai kadawa wadda take babu wani dan’adam da bai shake ta ba. Tilas ne kowane mahaluki ya kasance yana da dabi’ar son wani abu a ransa, wanda galibi son nan yakan tsananta har ta kai idan bai sami abin nan ba ya fada cikin wani hali ko kuma ya kasance ya sami abin amma yana gani a hana shi saboda wasu dalilai (Sa’idu, 1982).

Ga ra’ayin wani kuma abin da yake cewa, Bahaushe na asali na iya fahimta kalmar so da cewa, kauna ko sha’awa. Amma ma’ana ta fahimta na iya bayyana SO da cewa, wani maganadisu ne da yake yawo a jinin mutum, a duk lokacin da ya yi arba da abin da ya shiga raywarsa sai wannan maganadisu ko ‘ya’yan halitta su sakar masa kauna ko sha’awa ko kma ra’ayi zuwa ga wannan abu. Wasu na ganin cewa soyayya kamar cuta ce mai sosa zuciya, kuma takan yi ale-ale, wato kane-kane a gadon zuciyar mutum, tun ma ba in ya yi kacibis da abin da zai iya sa lale marhaban a dukkan bangaren hankalin dan’adam ba, dada (wato) mutum ne ko dabba ko akasin su. Amma da za ka tambayi mutumin yau dangane da ma’anar soyayya ba mamaki ya ce da kai ana nufin wata mace ta share fage ta kwanta har ma ta yi kwai ta kyankyashe a filin farfajiyar zuciyar wani mutum ko akasin haka. Gaba daya soyayya wani tsuntsu ne da ke dauke da iskar sha’awa da ra’ayi da kauna wanda kuma ke zirga-zirga tsakanin samari da ‘yan mata (Aliyu, 1990).

Wasu kuma suna fassara soyayya da cewa, wata aba ce ta farin ciki da ke shiga cikin zuciyar mutum, ta yi kaka-gida, a sakamakon haka sai mutum ya ji yana cike da farin ciki. Hatta a tsakanin dabbobi ko tsuntsaye ma ana samun soyayya.

2.1 Mene ne Labarin Soyayya?
Tun da mun ji wasu fassarori a kan ma’anar soyayya, bari kuma mu juya ga bayyana shi kansa labarin soyayya. A halin yanzu da an ji an ambaci labarin soyayya, watakila nan da nan za a tuna cewa ko ana nufin labaran da matasan yanzu suka fi so a zuciyarsu fiye da kowane labari. Labari wani abin da aka rawaito ne mai dan tsawo cikin shafuka da ya wuce, aka gina shi bisa gaskiya ko akasinta. Shi labarin soyayya shi ne abin da yake wakana tsakanin saurayi da budurwa, ko mata da miji, ko ko?.

Bisa abin da masana labarai suke cewa, rubutattun labaran soyayya shiryayyun zantuka ne da yawanci akan kaga, ko aka kara wa gishiri, da ake shinfidawa a fasalin zube ko wasa ta bin babi-babi ko fitowa-fitowa ko kashi-kashi, cikin azanci da ke dauke da wani salo na musamman zuwa ga al’ummar da aka rubuta shi dominta. Daga cikin ire-iren rubutattun labaran soyayya da akwai:
So Aljannar Duniya
Amadi Na Malam Ama
Mallakin Zuciyata
Idan So Cuta Ne
Budurwar Zuciya
Kogin Soyayya
Kaddara Ta Riga Fata
Rabin Raina
In Da Rai
Soyayya Gamon Jini
Soyayya Dankon Zumunci
Amintacciyar Soyayya
In Da Alkawari
So Marurun Zuciya
Son Maso Wani
In Da So Da Kauna
Da sauransu


2.2 Tubalin Ginin Labarin Soyayya
Idan aka ce Tubalin gina labari, to ana nufin wani muhimmin abu wanda idan babu shi a labari, to labarin ba zai yi armashi ko dadi ba, kuma rashin sa zai sa a kasa cim ma manufar da ake son gina labarin a kai, shi ma labarin soyayya , kamar kowane irin labari, yana da wadansu tubala da ake amfani da su wajen gina shi, wadanda idan babu su labari ba zai zama labarin soyayya ba, wato ba a za cim ma babbar manufa ba.

Kamar yadda aka sani soyayya ta kasu iri-iri, kamar yadda take wakana tsakanin saurayi da budurwa ko miji da mata ko ‘ya’ya da mahaifinsu da sauransu. To amma duk haka babbar manufarsu (jigo) da ya ce wato soyayya, sai dai kananan jigoginsu wadanda a kansu ne babban jigon ya ta’allaka, sun sha bamban da juna wadannan kananan jigogi kuma su ne ake kira tubalan gina babban jigo. To amma duk da haka a iya kawo wadannan jigogi a dunkule tun da yake babban jigonsu daya ne (soyayya) wato kenan a dunkule a iya bayyana tubalan ginin labarin soyayya musamman tsakanin mace da namiji kamar haka:
• Sunayen mutane da suka dace (taurari)
• Siffanta mata masu kyan hali da kyawun halitta
• Bayyana irin mataye ko mazajen da mafi yawan mutane suka fi sha’awa
• Bayyana kyawawan halaye na iyaye da ’ya’yansu
• Tunani
• Biyayya
• Fito da abubuwan da namiji ya fi son mace ta yi masa
• Fito da abubuwan da mace ta fi son namiji ya yi mata
• Fito da abubuwan da ke faruwa a rayuwa ta zahiri dangane da soyayya
• Amfani da kalmomin soyayya masu dadi da faranta zuciya
• Halayyar wurin da labarin zai wakana
• Da sauransu.

2.3.0 Amfani/Muhimmancin Labarin Soyayya ga Al’umma
Daga jin bayanin matsayin labarin soyayya ga al’umma, an san amfaninsa ma ga al’umma ba kadan ba ne. Amma duk da haka za a yi kokari a wannan mukala a bayyana kadan daga cikin amfaninsa ko muhimmancinsa ga al’umma musamman al’ummarmu ta Hausawa.

Alal hakika al’umma kan amfana sosai da karanta ko sauraron labarin soyayya. A takaice dai ga yadda aka karkasa ire-iren wannan amfani da al’umma kan samu a sakamakon karanta ko sauraron labarin soyayya a wannan mukala:
• Bunkasa tunani
• Karfafa dankon zumunci
• Cusa wa mai sauraro ko mai karatun farin ciki
• Tausayi
• Jarumta
• Dauriya/hakuri
• Son karatun Hausa da bunkasa Harshen

2.3.1 Bunkasa Tunani
Akan sami wani abu ko wasu mutane su yi kokarin hana mutum samun wani abu da yake matukar so(ko kuma raba masoya) a sakamakon haka sai ka ga mutum ya ya shiga tunanin ire-iren hanyoyin da ya kamata ya bi don ganin bai rasa wannan abin da yake so ba. Akwai kuma wadanda ba su san hanyoyin da za su bi su nemo ko su sami wadansu abubuwa da suke so ba, musamman idan akwai masu yi musu kafar ungulu a wannan kokari nasa, ire-iren labarun soyayya da suke karantawa ko sauraro ne suke taimaka musu wajen warware matsalolin da suke addabar su dangane da soyayya, musamman tsakanin da namiji ko saurayi da budurwa ko miji da mata. Domin a labari za a yi musu bayanin wasu matsaloli makamantan nasu da kuma hanyoyin da aka bi aka warware su. Ta haka ne al’aumma kan bi su fadada tunaninsu ta hanyar karanta ko sauraron labarun soyayya.

2.3.2 Karfafa Dankon Zumunci
Kamar yadda wani dan’uwa ya kira littafinsa da sunan ‘Soyayya Dankon Zumunci’ Hakika haka ne, kuma labarin soyayya yana karfafa dankon zumunci. Idan muka duba yadda samari da ‘yan mata suke musayar littattafai a junansu, haka kawa da kawa, ko kuma aboki da aboki, a duk lokacin da wata kawa ko aboki ya ari littafi da wuya a ce wani bai ara ya karanta ba, da sannu in dai ana aron littattafai ga wannan mutum wata rana takanas zai nemi a hada shi abota da mai littafin domin ya dinga ara a wajensa kai tsaye, a nan da tafiya ta yi nisa sai zumunci ya karfafa, abota ta kullu, kowa ya san labarin soyayya ne sanadiyyar wannan zumunci. Haka kuma idan saurayi ne yake bai wa budurwa aron littafin labarin soyayya, da sannu dankon zumunci zai karfafa tsakaninsu, mai yiwuwa ma nan gaba su zama masoya, in da rabo ma su zama ma’auratan juna, a nan ba wani abu ne mujaza ba sai labarin soyayya.

2.3.3 Cusa wa Mai Sauraro ko Mai Karatun Farin Ciki
Da yawa marubuta labarin soyayya suna samun takardun yabo da godiya daga wajen makaranta littattafansu saboda jin dadi da farin ciki da ya dabaibaye su sakamakon karanta wani littafi da suka yi. Wasun su suna cewa, ire-iren wadannan labaru suna zamar musu tamkar ruwan wankin duk wani bacin rai da suka sami kansu a ciki. Haka su ma masu sauraro a kafafen yada labarai, har dauka suke yi a ‘kaset’ su ajiye da zarar wani bacin rai ya same su su kunna don su sami sa’ida a zuciya.

Bayan haka kuma, kafin ire-iren wadannan littattafai su wadata ko kuma mu ce kafin a same su da yawa, matasa (maza da mata) ba su san yadda za su yi magana da junansu ba, musamman ma maza tun da dama su aka sani suna fara ambata soyayya ga mata, kuma ba su san yadda za su tsara musu wasikar soyayya ba, balle har t a kai ga yin waka, wanda kuma wannan abu biyu yana daga cikin hanyoyin da ake kama zuciyar wanda ake so (namiji ko mace) sannan kuma wani lokaci za a sami saurayi da budurwa sun yi aure amma ba su fahimci juna ba, wata kila saboda jin kunyar juna ko kuma daman can yarinya ba ta son sa, ko kuma shi ba ya son ta, amma saboda wasu dalilai kawai sai a hada su, idan ba a yi sa’a ba yana shiga dakin ta fito, in ya fito ta koma, haka za su yi ta zaman doya da man ja, amma a yanzu saboda tasirin da labarin soyayya ya yi ga al’umma an fara samun damar fahimtar juna sakamakon karance-karancen da suke yi da sauraron labarun soyayya. Da yawa wadanda suka karanta irin wannan labaru suna fada da kansa cewa, sun warware wata matsala da ta shige musu duhu sakamakon karanta littafi kaza.

2.3.4 Tausayi
Sau da yawa ana samun labarin soyayya mai ban tausayi, sakamakon haka masu karantawa ko sauraro ba sa iya jurewa har sai sun yi kuka da hawaye, wata kila tauraron labarin ko kuma tauraruwar labarin ce, ko ma su duka ne suka sami kansu a wani hali, a nan masu karatu ko saurare za su yi iya bakin kokarinsu nan gaba kada irin abin da ya faru a cikin labarin nan ya faru a kansa, a nan labarin soyayya ya yi amfani a kan su, kuma an cusa musu tausayi da yin taka-tsantsan da abin.

2.3.5 Jarumta
Soyayya tana sa jarumta, jarumta kuma tana sa soyayya, misali mutum ne yake tafiya da masoyiyarsa sai suka ci karo da wani abin tsoro, a zahiri idan babu wannan masoyiya tasa a kusa guduwa zai yi, amma don kada ya gudu ya ji kunya, sai ya tsaya aka yi ta gumurzu har Allah ya taimake shi ya kori abin nan. A nan mun fahimci abin da ya sa ya zama jarumi , soyayya ce.

Idan muka dubi bangaren da jarumta take sa soyayya, sai mu tafi fagen kokowa da dambe da shadi, duk wadannan fagage ne na jarimta muddin ka zama jarimi sai ka ga maza da mata suna son ka, a nan ma jarumta ta jawo soyayya.

2.3.6 Hakuri
Da yawa wadanda ba s u shiga fagen soyayya ba, ba za su san dadi ko wuyarta ba, wasu kuma sun dauka dadi ne da ita kawai, amma da sun shiga sai su ga abin banbarakwai, nan da nan sai su ce sun daina yi. Hakika soyayya ba ta yiwuwa sai an hada da hakuri, kuma da yawa masu karantawa ko sauraron labarin soyayya sun fahimci hakan ne ta hanyar ire-iren labaran soyayya da ake yi, ba don labaran soyayya suna tasiri ga al’umma ba da an ta samun tabargaza kamar yadda ake yi a da, idan saurayi ya rasa yarinya ya je ya yi mata asiri, ko kuma ya je ya nemi tashin hankali da wanda za ta aura, wani lokaci ma har ta kai ga yin kisan kai, wanda rashin hakuri ne ya kawo haka. Amma a halin yanzu su masu karanta ire-iren wadannan labarai, da kansu suke cewa, ba don mun karanta wannan labarin ba haka ta faru a kanmu ba za mu yi hakuri ba, ashe a nan labarin soyayya ya yi tasiri har ya jawo hakuri ga wanda ya karanta ko wadda ta karanta.

2.3.7 Son Karatun Hausa da Bunkasa Harshen
Littattafan soyayya sun taimaka wajen cusa wa matasa son karatun Hausa, nesa ba kusa ba. A da sai ka ga yaro ko yarinya ya kai aji hudu ko biyar na sakandare amma ba zai iya karanta maka Hausa dalla-dalla ba saboda bai damu da ita ba, alhali kuma harshensa ce. Amma a yanzu da wuya a ce yaro ko yarinya sun kai aji biyar bas u iya karanta Hausa ba, saboda me? Saboda suna karanta littattafan soyayya. Ko da bai koyi karatun Hausa don ya yi amfani da ita a aji ba, ya koya don ya karanta littattafan soyayya. A nan labarun soyayya sun yi amfani, don kuwa an cusa masa son harshensa.

Har ila yau an dada bunkasa Harshen Hausa fiye da da, an kuma kakkabe son littattafan Turai a zukatan matasa fiye da da. Bayan haka kuma kudin da za ka sa ka sayi littafin kasar Turai guda daya su ne za su sai maka littattafan Hausa na soyayya guda hudu ko shida. Saboda haka a nan ma littattafan soyayya sun kawo saukin kashe kudi da matasa suke yi wajen sayen littattafan kasar waje.

2.4 Nadewa
Labarin soyayya yana da babban matsayi ga al’umma. Domin al’umma kan yi amfani da shi don maganin bakin ciki da bacin rai. Buga da kari suna amfani da shi don faranta wa juna rai da debe kewa. Dubi yadda al’ummar Hausawa a gargajiyance suke kirkiro labarin soyayya suna gaya wa abokan hirar su don nishadi. Alal misali Tatsuniyar Bora da Mowa inda aka nuna wa daya soyayya sosai da kuma tatsuniyar Daskin Daridi inda ake ba da labarin wasu ‘yan mata da suke kokarin gano sunan Daskin Daridi don su aure shi, wanda a karshe wata da ake kira Burtuntuna ta fadi sunansa daidai, da dai sauran wasu tatsuniyoyi na labarin soyayya. Haka ma abin yake a zahiri, misali dubi yadda idan saurayi matashi ya hadu da abokinsa, ko kuma mace matashiya ta hadu da kawarta, babu wani labari da suka fi yi fiye da na soyayya. Shi ya sa ma a yanzu babu wani littafi da ya fi cin kasuwa fiye da na labarin soyayya domin kuwa kashi casa’in cikin dari 90% na masu karanta littattafai a wannan zamani matasa ne.

A takaice dai a iya cewa saboda muhimmin matsayin da labarin soyayya (kowane iri) yake da shi a wajen al’umma, kusan shi ne labarin da dan’adam ya fi sha’awa fiye da sauran labarai a zamanin yanzu.

Bayan haka, akwai ra’ayoyi da suka sha bamban daga mutane daban-daban, wasu suna cewa labaran soyayya sun ishi mutane haka nan, wasu kuma suna cewa labarn soyayya suna bata tarbiyyar matasa, suna hana su karatu, wasu kuma suna cewa ya kamata a tarkata littattafan soyayya gaba daya a kona su domin ba su da amfani, kuma nakiyoyi ne wadanda nan gaba za su fashe su tarwatsa mana zuri’a masu zuwa nan gaba. Har ila yau wasu suna cewa, yawancin marubutan matasa ne masu jin tashen balaga, kuma iliminsu bai wuce cikin cokali ba, saboda haka suke ta rubuta shirme a ciki.

Masu ganin labarin soyayya yana da matsayi ga al’umma sun fadi nasu ra’ayin kamar haka: Rayuwa a bayan kasa zango-zango ce, kowane zango da yadda ya dace a bi a yi wa ahalinsa fadakarwa da jawo hankali kan tafarkin rayuwa madaidaiciya, saboda haka, marubutan Hausa na farko ba su cika son yin rubutu kan soyayya ba, wata kila don gudun zancen mata da amfani da kalmomin kuruciya ko ma ta kai ga yin batsa, saboda haka da wa sami dadadden littafin (kai ko ma rubutacciyar waka) kan soyayya, amma a ‘yan shekarun nan marubutan zamani, matasa, sun toshe mana wannan gibi na adabin Hausa. Matasan yanzu akwai masu kokarin kallon rayuwa da nufin kyautata ta, kuma suna yi wa matasa da sauran mutane hannunka mai sanda kan mas’alolin da suka dabaibaye su musamman ta fuskar aure.

Har ila yau wasu kuma suna cewa, ba labarin soyayya ne ya ishi mutane ba, a’a, yadda ake bi wajen rubuta shi ya kamata a inganta duk lokacin da aka zo rubuta labarin soyayya a yi kokarin cusa tarbiyya da fadakarwa a ciki, tun da an fahimci ga alkiblar da masu karanta littattafan suka bi, saboda haka sai a bi su a ja hankalinsu da taken soyayya, amma a cusa musu kishin kasa da rikon amana da tsoron Allah da tausayi da zumunci, kai da duk wata manufa da ake ganin za ta gyara rayuwar matasa, domin an ce Karen bana shi ke maganin zomon bana, matashi shi ne ya kamata ya ja hankalin dan’uwansa matashi zuwa tafarki mai kyau.

Wani ra’ayi kuma cewa ya yi, ai don an yi rubutu a kan soyayya mene ne laifi? Wanda ya zakalkale wajen rubutu kan talauci da yunwa da yaki da sauran tashe-tashen hankali bai yi laifi ba, sai wanda ya yi a kan soyayya? Kuma idan aka ce za a tsaya a yi tawili, tsakanin yunwa da talauci da yaki da sauran tashe-tashen hankula da kuma soyayya wane ya fi karbuwa ga al’umma? Sannan kuma kowa ya san soyayya ita ce kashin bayan zaman lafiya da ci gaban kasa da kwanciyar hankali da bunkasa arziki, shin me yake kawo fadace-fadace tsakanin unguwanni har a zo ana kasha-kashen mutane? Me yake kawo yaki tsakani kasa da kasa? Shin kiyayya ce take kawowa ko kuma soyayya?

Kafin a kammala wannan takarda a nade ya-nata-ya-nata za a ba da shawarwari kamar haka:

Ya kamata marubuta su yi kokarin hada kawunan su domin hada wata babbar kungiya wadda za ta dinga tafiya har wasu kasashe na duniya don bunkasa wannan harshe na Hausa. Sannan kuma kamar yadda muke samun kalubale daga wasu wurare, ya kamata mu yi kokari domin mu ba su mamaki wajen taka rawa a fannin wannan rubuce-rubuce, kuma kada mu dauka kalubale da ke kusantar mu wani abu ne da zai firgita mu, a’a, sau da yawa wata kalubalantar tana sa marubuci ya shiga bincike da bin kwakkwafi domin gano gaskiyar lamari, wata kalubalantar ta hassada ce kawai, saboda haka idan muka ci karo da irin wannan sai mu yi watsi da ita waje daya.

Amma duk da haka Hausawa suna cewa, wake daya shi ke bata gari, ba mamaki a cikinmu a sami wadanda suke ya kamata a yi musu tambihi, domin an ce makaho bai san ana ganin sa ba sai, an taba shi. Saboda da haka muna maraba, kuma a shirye muke mu amshi shawarwari masu kyau.

2.5 Karin Bayani
Ina mika godiyata da ta kungiyar da nake shugabanci, wato ‘Raina Kama’ da ‘Writers Forum’ wadanda suka dauki nauyin shirya wannan taro na kara wa juna ilimi, mai taken Rubutu Don Al’umma. Haka kuma ina gode wa Dr. Sa’idu Muhammad Gusau da Farfesa M.K.M. Galadanci da Hassan Yahaya bisa muhimman shawarwari da suke ba ni a ko da yaushe, na gode.

2.6 Mazarta
Sa’id, Bello. 1982; Dausayin Soyayya
Lagos: Nigeria Magazine.
Ahmad Rufa’I, Aliyu, 1990; Fitilar Soyayya
An Buga Shi a Kan Keken Rubutu.
Gusau, Sa’idu Muhammad. 1992; Tsari Da Manufar Karamar Taska.
An Gabatar da Ita a Bikin Kaddamar da Littafin

1 comment:

Anonymous said...

asslm alaikum

gaisuwa tareda fatan alkahiri ga jagoran marubutan hausa na zamani, mr ado ahmed godan dabino
ina tinawa cewa, littafin sumayya da muhammad shine farkon littafin hausa dana karanta ina yaro, kuma har yanzu littafin yana cikin zuciyata,
ina tayaka murnar bude shafin yanar gizo, fatan zaka bari na kuma karanta wannan littafin a shafinka da sauran littafanka
ina godiya
ALLAH ya taimaka
Naka
mustapha sbarnoma