Saturday, August 2, 2008

MARUBUTAN HAUSA BA JAHILAI NE BA

Masu iya magana suna cewa, idan hankali ya bata hankali ake sawa ya nemo shi, kuma mayar da martani cikin fushi babu abin da yake haifar wa mai yin sa illa aiwatar da kuskure, shi ya sa ake cewa kada ka mayar da martani a cikin fushi, kuma gagggawa tana daga aikin shaidan.

Na karanta rubutun Malam Buhari Daure, wanda aka buga a cikin jaridar Leadership Hausa ta ranar Juma’a 25-31 ga watan Agusta na wannan shekara ta 2008, kuma abin akwai ban mamaki kwarai da gaske a ce a matsayin Buhari na marubuci kuma mai hankali da ilmi da karatu, wanda yake ganin marubuta ba su da ilmi kuma mai ganin marubuta ‘yan’uwansa a matsayin ‘mahaukata ‘yan banza ‘yan iska’ kamar yadda ya rubata a takardarsa, a sakin layi na bakwai, layi na karshe.
Na yi zaton zai dauki kanun bayaninsa guda daya kamar yadda ya yi wa takardar take da cewa ‘MARUBUTA A KAN SIKELI’, amma sai ya shiga kame-kame yana hado tsaba da tsakuwa, yana yin wake da shinkafa, sannan kuma yana bayar da bayani yana kuma karyata kansa da kansa, ko kuma mu ce yana yin amai yana lashewa, sannan maganar tana kama da tafiyar gwamen jaki. E haka ne mana, ai ga duk wanda ya karanta bayanin nasa zai ga wuraren da ya yi magana amma ya rusa ta da kansa.
Ba so nake in yi dogon bayani ba, don ba so nake in bas hi amsar duk wasu abubuwa day a yi Magana ba illa ina so in dauki wasu wurare in ba shi amsa, sauran wasu sa bas hi amsa, don gudun kada in maimata irin abin da ya yi a rubutunsa, domin an ce ‘mafi alherin magana shi ne abin da ya karanta kuma ya shiryar, bai yi tsayi ba balle ya kosar’
1. Sakin layi na goma, ya bayyana cewa ‘ana maganar Hausa a majalisar dinkin duniya, zaune tare da Faransanci da Larabci da Turanci’.
Abin tambaya me kake nufi da ana yin maganar Hausa a majalisar dinkin duniya?
2. Sakin layi na goma sha daya, ya bayyana cewa ’Kalli irin takardar da ake buga wasu littattafan da kwalayen da ake buga bangon, kai wata takardar ko kosai da tsire ba za su iya zama a cikin ta ba, to ta yaya wadannan littattafan za su je Abuja ko Yamai balle Legas, bayan ba su da lamba?’
A tunanina da can, na yi zaton Buhari ya fahimci kyan bugun littafi da takarda da kwali mai kyau ba su ne kyan littafi ba, a a, kyan abin da ke cikin littafi shi ne muhimmi, domin kana iya samun littafi ya samu bugu da takarda mai kyau amma abin da ya kunsa ba shi da kyau, wannan ya zama kyan dan miciji kenan. Haka nan yawan shafuka, su ma ba su ne muhimman ababen dubawa ba, abin da ke ciki shi ne abin lura kawai, amma fa ban sani ba shi a wajen sa, mene ne kyan littafi?.
Kuma batun Yaya wadannan littattafan za su je Abuja ko Yamai balle Legas, bayan ba su da lamba?’
Amsa a nan ita ce, ya je ingila wajen Divid Hogarth, zai iske yana sayar da wadannan littattafai ta hanyar aika wa ta gidan waya, kuma duk shekara yana zuwa Nijeriya, musamman Kano ya sayi wadannan littattafai na marubutan da Buhari ya dauka a matsayin ‘mahaukata ‘yan banza ‘yan iska’, sannan ya je Yamai kasuwar ‘Giran marshe’ wato babbar kasuwa, zai iske ana sayar da wadannan littattafai, balle kuma Abuja ko Legas. Kai ba ma nan ba, ya ma je Library of Congress ko British Library da dakunan karatu na manyan jami’o’I na Ingila da Amurka da Jamus da sauran kasashen duniya, zai ga littattafan kuma ba kyauta muka bas u ba. Don haka rashin lamba ba ita ce za ta hana su zuwa ko’ina ba, tuni sun je inda Buhari bai sani ba.
Sannan kuma kana iya zuwa jami’ar SOAS da ke Landan inda Farfesa Graham Furniss yake, za ka iske littattafan Hausa na zamani har guda 1835, an adana su an kauwame su, don masu neman ilmi, kuma an bude musu yanar gizo mai adireshi kamar haka: http://hausa.soas.ac.uk// har ila yau kuma, shi dai Farfesa Graham Furniss tare da Dr. Malami Buba sun rubuta littafi mai suna Bibliography of Hausa Popular Fiction 1987-2002, wanda kamfanin Rudiger Koppe Verlag Koln suka buga a kasar Jamus, a shekarar 2004. Yawan shafukan littafin 179. Kuma za ka iske har da naka littattafan guda biyu, Zakanya, wanda aka ba shi lamba 643, wanda kamfani Mashi, Kano suka buga shi a shekarar 2001, yana da shafuka 42, sai kuma Karnukan Farauta, wanda aka ba shi lamba 653, wanda kamfanin Gizo, Kano suka buga shi a shekarar 2001, yana da shafuka 116. Don haka tunanin da kake yi da kuma bayananka iya fahimtarka ne da kuma inda ka sani ne kawai a game da wadannan litattafai da kuma marubutansu.
3. Sakin layi na goma sha uku, ya bayyana cewa ‘Mutane nawa ne suke da digiri a cikin marubutan? Da kyar in sun kai mutane 30, balle a ‘yan fim wadanda ba su kai rabin marubuta ba, kai mata nawa masu fim suke da difiloma? Sannan me shugabannin kungiyoyin marubuta suka yi? Me masu wallafa littattafai suka yi wajen kawo karshen wannan matsala?
Amsa a nan ita ce babu shakka ko tantama, kungiyoyin marubuta da masu wallafa littattafai sun yi abin a zo a gani a cikin jama’arsu, an yi tarukan kara wa juna sani, an fadakar da marubuta dabarun yin rubutu da rabe-raben Hausa, a Kano. An yi taron kasa da kasa a birnin Yamai a cikin shekarar 2006, sai kuma Sokoto an yi a cikin wannan shekara ta 2008, badi kuma in Allah ya kai mu 2009 za a yi a Katsina.
Har ila yau, kungiyoyin marubuta ne a jihar Kano suka fara hana sayar da wani littafi wanda ake ganin yana dauke da batsa, kuma sun sha shawartar marubuta da su cire duk wani abu da ake ganin zai zama barna ga jama’a, Allah ya sani kuma wadanda suka sani sun sani. Kuma kungiyoyin marubuta su suka fara dubawa da tace littattafansu da kansu a cikin shekarar 1997. Kungiyoyin marubutan nan dai su ne suke bayar da littattafansu a karanta a zo a yi musu taron gangami don a fito da kurakuran da mutum ya yi, don gaba ya kiyaye, wasu kuma kafin a buga littafin ake yi musu irin wannan taron gyara kayanka din. Sannan ga tarukan kalubale da ake yi a lokuta mabambanta a zaunar da marubuta, masu karatu su yi musu tambayoyi su fito musu da kura-kuransu a fili, kuma marubutan su amsa kai tsaye.
Bayan haka kuma kungiyar masu bugawa da wallafa littattafai su ne su fito da dokar hana sanya hotunan da ba na Hausawa ba a bangwayen littattafai, kuma an amsa har yanzu da wannan doka ake amfani. Idan Bahuri duk bai san wadannan ba, to ya tambayi na kusa da shi a cikin marubutan Kano, na san ba zai rasa samun abokai wadanda suka san ire-iren wadannan abubuwa ba.
Batun Hukumar A Daidaita Sahu, ai abin a bayyane yake, kungiyoyin marubutan dai da ka dauka jahilai su aka fara gayyatowa suka rubuta wa hukamar littattafai guda goma sha bakwai, kuma ka san sau nawa hukamar ta shirya taron jinjinawa da yabawa da kuma cin abinci ga marubutan wadannan kungiyoyi? In ba ka sani ba ka shiga fagen bincike.
Ga sunayen littattafan da marubutanmu suka rubuta musu:
1. ‘Yar Bahaushe
2. A Dalilin Talla
3. Algus
4. Da Muguwar Rawa…
5. Garin Banza
6. Hadarin Kaka
7. Himma Ba Ta Ga Raggo
8. Kantafi
9. Karkon Dabino
10. Kowa Ya Yi Nagari…
11. Kowag gyara Ya Sani
12. Mugun Ji
13. Tarbiyyar Iyali
14. Tsuntsun Da Ya Ja Ruwa
15. Wanzamin Bono
16. Ceto ko cuta?
17. Jiki Ya Fi Kunne Ji

Game da kona littattafai da hukumar ta yi, a nan ma wata siyasa ce ta gwamnati, wadda in ba ka san ta ba babu yadda za ka yi ka gane ta, sai a yi ta wasa da hankalinka, kai da kake ganin kana da ilmi. A wannan lokaci da abin ya faru ga abin da Farfesa Abdalla Uba Adamu ya bayyana a wata hira da aka yi da shi a jaridar Leadership Hausa, in da yake cewa ‘Amma ko da sun aikata laifi, konawar ba shi ne mafita ba – domin konawar zai jawowa gwamnati wata matsala inda za a funskance ta a kan maras son ci gaban al’uma. Sannan kuma za a iya kwatanta wannan da ire-iren abubuwan da gwamnatin Taliban ta yi a Maris 2001 na dandake gumakan Buddha, wadanda sun fi shekaru dubu a kasar, har ma duniya ta dauke su a matsayin jarin al’adun al’ummatan duniya. Manazarta sun yi kuka da lamarin da nuni da cewa duk da wadannan gumakan na kafirci ne, wanda kuma ya saba wa gwamnatin Taliban ta wancan lokacin, amma adana su na da humimmanci wajen tattara tarihin dan Adam da nuni da yadda rayuwarsa ta gabata, wannan ma kadai zai hana a sake yunkurin bauta musu domin da ganinsu ka ga sakakkun abubuwa wadanda ba su cancanci a bauta musu ba. Af, ji nake ita dai wannan hukumar mai kona littattafai, ita ce ta gayyaci marubutan a 2005, ta ba su kwangilar rubuta irin wanda hukumar ke so? Sai yanzu ne kuma za su ce wadannan mutanen lalatattu ne? Ashe ka ga da sake kenan’.
Kuma wani abu da zai ba ka mamaki har ka fara gane akwai siyasa a cikin kona littattafan shi ne, da muka nemi sanin sunayen littattafan da aka kona sai aka kasa samin wanda zai ba mu su, sai aka shiga kame-kame, ana cewa ba a rubuta sunayensu ba an dai je kasuwa an sayo kamar guda hamsin an karanta an ga goma suna da batsa, karshe dai da aka ba mu sunayen littattafan, cikin sunayen sai aka ba mu har da wadanda ba su fito kasuwa ba, wani littafin ma ana buga shi ne kadan-kadan a cikin wata mujalla, don haka ka ga akwai wata manufa ke nan.
4. Ka ce ‘A yau basirar ka ta isa ta daga ka, ba wai da kwalin difiloma ko digiri ba, an wuce bautar satifiket, don ko a yau wanda ya fi kowa kudi a duniya kirkira mafita ya yi a kwamfutance, a haka madugu Bill gates ya yi tazara…..Shin wane tasiri rubutun marubutan Hausa yake yi?
Amsarka a nan mai sauki ce, domin wannan maganar ta warware ta baya da kake cewa ‘Mutane nawa ne suke da digiri a cikin marubutan? Da kyar in sun kai mutane 30’ ashe takardar digiri ko difiloma ba su ne masu bayar da komai ga marubuci ba, basira ce da Allah yake bai wa wanda ya so a cikin bayinsa ko?
Don haka in har mutum yana da basirar rubutu ashe ba a maganar takardar shaida, tun da babu wata makaranta a duniyar nan da ake cusa basirar rubutu a kwakwalwar da’adam, sai dai a ce ana koyar da dabarun rubutu, don wanda bai da fasahar rubutun kagaggun labarai ko ka koya masa ba zai yi shi ba komai ilminsa, shi rubutu baiwace, kuma marubuci dan baiwa ne, haihuwarsa ake yi ba yin sa ake ba.
Allah Madaukakin sarki Yana cewa:
“Yana ba da hikima ga wanda Ya so, kuma duk wanda Ya ba wa hikima Ya ba shi alheri mai yawa. Kuma ba kowa ke tunawa ba sai ma’abota hankula”. (Suratul Bakara aya ta 269).
Kuma a matsayin ka na mai ilmi ya kamata ka san cewa an yi marubuta a fadin duniyar nan wadanda ba su yi zurfin karatu ba amma daukakar su ta kai kololuwa a duniya, wasu marubutan ma sai sun shahara sannan suke samun damar su yi karatu mai zurfi.
Kuma ko an ki ko an so marubutan Hausa na zamani sun bayar da gudummawa sosai wajen bunkasa adabi, domin daga rubuce-rubucen da suka yi ne wasu suka fara koyon karatu da rubutu, wasu suka gyara halayensu na zamantakewar yau da kullum, a cikin gida ne, wato mata da mazajensu ko kuma a waje maza da abokan mu’amalarsu. Saboda karatun da wasu suka dinga yi ne suke fahimce yadda in sun sami kansu a cikin matsala ga yadda za su bi su warware ta. Kai akwai abubuwa da dama wadanda in za a tsay kawo su suna iya cinye mana shafukan.
Muna sane da cewa duk jama’ar da ta rasa marubta a cikinta, ba za su sami cigaba ba, harshensu ba zai daukaka ba, kuma ba za a san su a ko’ina ba.
Don haka Yana da kyau mu fahimci cewa marubuci na da matukar muhimmaci ga duk al'ummar da yake zaune a ciki domin kuwa kadara ne ga wannan al'umma kuma yana iya jawo wani ci gaba da alkalaminsa. Marubuci yana da matukar muhimmanci da tasiri ga al’umma, saboda haka ya wajaba a kan al'ummar da ta sami marubuci a cikinta ta yi kokarin jawo ra'ayinsa ko yin tasiri a kan tunaninsa don ya yi rubutu na kwarai.
5. Ka ce ‘A cikin marubutan Hausa na wannan zamanin akwai Yahudawa, Dagutai da Fir’auna
6. Ka ce ‘wasu marubutan ba sa rubutu sai sun sha wiwi’
7. Ka ce ‘Hakika akwai Mala’iku a cikin marubuta
Idan muka bibiyi wadannan bayanai naka za mu fahimci lallai ba marubutan littafan zamani ne ke shan wiwi kafin su yi rubutu ba, kai ne kake shan wiwi kafin ka yi rubutu, domin in ba dan wiwi ba yaya za ka daddage ka dinga zagin mutane, ai a fagen ilmi ba a zagi sai dai a bayyanar da hujjoji, amma kai da yake dama ba abin da kake son yi ba kenan, cin zarafi ka yi niyyar yi sai ka rufe idonka ka yi ta zagin ‘yan’uwanka, amma kada ka manta komai ka ce wa ‘yan’uwanka kai ma yana kanka, domin ka yi rubutun nan kuma kana kan yi, sannan ba a canza wa tuwo suna. Idan ma sa ka aka yi ka yi wannan rubutun don a ga wallen ‘yan’uwanka marubuta, to ya kamata ka sani, komai daren dadewa wadanda suka sa ka za su bar kujerar da suke kai, kuma za ku raba hanya ka zo ka ci gaba da zama tare da mu.
Shin don marubuta sun ce ba su yarda da a yi musu rijista a daidaikunsa ba shi ne laifi?
Dokoki nawa suka bi a can baya?
Wadanne masu sana’a ne suka karbi dokokin wannan hukuma hannun biyu-biyu kamar marubutan?
1. Kamfanonin dab’I sun yi rijista da hukumar
2. Kungiyoyi sun yi
3. Sannan marubuta suna kai littattafansu a duba a yi musu gyara
4. Abu na hudu wato rijista daidaiku shi ne ba mu yi na’ama da shi ba.
Sai ka je kai kadai an tace ka an ba ka takardar shaidar kai kana da basirar rubutu sannan za ka yi rubutu a Kano, in ba haka ba a kama ka a kulle, don kawai ana takama da mulki da kuma danniya da zalunci da tauye hakkin Dan’Adam. Shin a duniya a wace kasa ake irin wannan, wai sai an tantance ka an yi maka rijista kai kadai, sannan kake da ikon yin rubutu? Amma kila Buhari zai taimaka ya kawo mana sunayen kasashen da ake yin haka, a matsayinsa na mai ilmi, kuma malamin makaranta.
Mu a saninmu shi ne aikin da ka yi ake so a tantance, kuma mun yarda a duba a gyara in ma ba a yarda da shi ba a hana shi fitowa kasuwa. Don haka duk abin da marubuci ya rubuta a littafinsa ya san da cewa akwai tacewa a gaba tana jiran sa.
Kungiyar ‘yan jaridu ta kasa NUJ, ba sa yin rijista a daidaikunsu, a dunkule kungiyarsu take yin rijista a madadin ‘ya’yanta, haka nan kungiyar lauyoyi (NBA) ko ta likitoci watau (NMA) balle irin su ASUU. Da dai sauran makamantansu.

Mun tabbatar wadannan dokoki da aka dora wa marubuta akwai son zuciya a ciki, kuma akwai takamar ni ina da karfin danne duk wanda na ga dama, amma kada fa a manta kafin wannan zamanin an yi azzalumai da dama sun yi yayinsu sun kare, tarihi kuma yana nan yana tunawa da irin zaluncin da suka tafka wa jama’arsu, kuma tarihi ba zai kyale su ba sai ya rubuta su ya ajiye.
Wani mawaki Sani Yusuf Ayagi ga abin da yake cewa a cikin wakarsa ta Alkalami Ya Fi Takobi:

Al-kalami mai hagun da dama,
Mai haske ga duhu ku duba.

Mai zaki alkalam da daci,
Ko ba ku san me nake nufi ba.

Ai ma’ana gaskiya da karya,
Babu guda wadda bai iya ba.

In ya so yanzu ai zumunci,
Sai ya matsa can ya kulla gaba

In an so, sai a kulla yaki,
Ku hargitse ba da kun sani ba.

Da shi masoya ka daukaka,
Da sun rubuta ba a musa ba.

Da shi akan sa a kassara ka,
Da dai ba ka kara daukaka ba.

Da an rubuta ana yabonka
Ko kai sata ba a sani ba.

Da shi sukan bata dan’ adam kaf,
Akan abin shi dai sani ba.

Ba mu ce marubuta ba sa yin kuskure a rubuce-rubucensu ba, ai mutane ne su, tara suke ba su cika goma ba, amma sun yi na’am da a yi musu gyara a duk wani rubutu da suka yi, sai kuma me?
Saboda haka, ina ba Buhari Daure shawara, in yana afka ‘a-rungumi-zaki’ ya daina, in kuma wani abu na damunsa, to ya roki Allah ya yaye masa. Buhari yaro ne mai hazaka, don Allah kada ka bata rawarka da tsalle. Ka maida hankali wurin yin rubuce-rubucenka na ilmi kada ka shiga baragada.

No comments: