Monday, May 28, 2007

Matsaloli da Nasarorin Shiya Fim a Kano

Mun rubuta wannan makalar ne tare da Bashir Mudi Yakasai,
Mun Gabatar Da Makalara a Taron Duniya na Karawa Juna Sani a Kan Finafinan Hausa, Wanda Cibiyar Nazarin Al'adun Hausawa (Center for Hausa Cultural Studies) Kano, Ta Dauki Nauyin Shiryawa Da Gabatarwa a Watan Agusta 2003.
An Buga Makalar a Cikin Kundin Sakamakon Wannan Taron Mai Suna, Hausa Home Videos: Techology, Economy and Society, Wanda Abdalla Uba Adamu, Yusuf Muhammad Adamu da Umar Faruk Jibril Suka Dauki Nauyin Zama Editocin sa. An Buga Littafin a Kano a 2005, a Center for Hausa Cultural Studies.

Gabatarwa
Matsala da nasara dukkaninsu dabi’a ce ta dan’adam, suna faruwa ne saboda wasu dalilai. Dalilan nan za su iya kasancewa na mutum ne ko kuma halittattu ne, ana tabo su sai a samu nasara ko kuma kishiyarta. Wannan fagen ba sabo ba ne ga masu ilmin falsafa, inda suke bayyana cewa, komai na duniya yana da kishiya kamar yadda suke bayar da misalai da sama da kishiyarta kasa ko dare da rana ko baki da fari ko tudu da kwari ko rayuwa da mutuwa ko kuma dogo da gajere, haka dai abin yake a fannoni na rayuwa. Sannan wani mawaki yana cewa akwai abubuwa guda takwas wadanda dukkanin dan’adam yake rayuwa a karkashinsu wato farin ciki da bakin ciki, haduwa da rabuwa, yalwata da kuntata da kuma lafiya da rashin lafiya. Malam Bahaushe ma yana cewa duk hannun da ya saba kirga riba wata rana dole ne ya kirga faduwa.
Don haka babu wani abu a rayuwa da dan’ Adam zai shiga ko ya fara shi ba tare da samu ko cin karo da nasara ko matsala ba, nasara da matsalar nan ana sane ne ko ba a sane, ana so ko ba a so, dole ne su faru ko ma ta wane hali. Sai dai kuma wasu nasarorin ko matsalolin mutum shi yake jawo wa kansa, wani lokacin kuwa suna zama ciwon ido ne sai dai hakuri, wato babu yadda za a yi a hana faruwarsu. Domin haka dukkan dan’adam yana rayuwa ne a karkashin nasara da matsala, wadannan abubuwa guda biyu suna zama madubi a rayuwar dan’adam wanda zai kalli kansa da shi don ya gyara al’amuransa na rayuwa, domin yau ita ce madubin gobe.

Duk wanda ya ji an ce ‘Nasarori da Matsalolin Masu Shirya Finafinan Hausa’ dole ya samu abin da zai ce game da wannan batu sai dai kawai a ce kowa da irin ta bangaren da zai kalli abin, domin ba zai rasa abin da zai fada ba, ba kuma zai rasa irin abubuwan da zai hanga da madubin hangen nesansa ba. Bangarorin nan sun kasu kashi daban-daban.
Wannan takarda ta dubi wasu bangarori da dama wadanda ta tabo, game da nasarori da matsaloli a harkar fim musamman na Hausa, wata kila hangen da wannan takarda ta yi za a samu mutane da dama wadanda suke da irin wannan hange ko akasinsa. Ya kamata a fahimci manufar wannan takarda, wato manufarta shi ne taya ni mu gyara, ko kuma gyara kayanka wanda ba ya zama sauke mu raba. Masu iya magana suna cewa idan ka ga kaza tana taka ’ya’yanta ba don ba ta son su ba ne, a’a, sai don ta koya musu hankali ne ko jan kunne, kuma idan ka ga jariri a kan gado lallai ka san dora shi aka yi, don haka duk wanda ya ji an fadi laifinsa, to sai ya yi karatun baya, wato ya yi karatun ta-natsu ya ga haka ne? Don ya gyara. Masu iya magana suna cewa gwano ba ya jin warin jikinsa, kuma shi ido gululu ne ba lallai ne mai shi ya hango wasu matsalolin da ke tattare da shi ba, amma na kusa da shi sai ya iya hango masa. Muna fata manufar wannan takarda ta kai ga cim ma gaci, ma’ana kwalliya ta biya kudin sabulunta.

Mene Ne Fim?
Fim wani bangare ne daga kafar sadarwa ta lantarki wadda take samar da gani da ji da motsi, domin amfanin mutane masu yawa, kuma yare ne da kowane mutum yake iya fahimtarsa a duniya.

Abin Da Fim Yake Aiwatarwa:
Fim tantagaryar kimiyya da fasaha ce, kuma rayuwar dan’adam ce ake nunawa. Fim yana dauke da tarihi da dabi’un jama’a da muhallinsu da abincinsu da kuma suturarsu, musamman bisa harshensa da tsarinsa na rayuwa da hanyoyin tunaninsa da kuma falsafar rayuwar mutanen da ake yin fim din don su. Har ila yau, fim hanya ce ta sanarwa da ilmantarwa da jan hankali da nishadantarwa da fadakarwa da yada manufa da tallatawa. A dunkule kafa ce daga cikin kafafen yada labarai, sannan kuma hanya ce ta kasuwanci da samar da aikin yi ga al’umma.

Don Me Ake Yin Fim?

§ Sanarwa
§ Ilmantarwa
§ Nishadantarwa
§ Karkatarwa
§ Tallatawa
§ Sayarwa
§ Yada Manufa
§ Tsoratarwa
§ Samar da Aikin yi

Tubalan Da Ake Gina Fim:
§ Basira
§ Sako
§ Kyamara da mahadanta da kuma yadawa
§ Masu kallo
§ Aiki da sakon da aka isar

Matakan Shirya Fim

Shiri Kafin Shiri:
§ Basira
§ Labari da tsara shi
§ Kasafin kudi da lokaci
§ Yadda za a samar da kayan aiki da ma’aikata
§ Samammun kudin yin aiki
§ Shiga yarjejeniya da ma’aikata da masu samar da kudi
§ Samar da wuraren da za a yi aikin a cikin gida ko kasashen waje da kulla yarjejeniya da masu wuraren
§ A yayin samar da wadannan abubuwa, lallai ya zama an ba da cikakkiyar kulawa wadda akalla ba akasara ba a dauki kashi saba’in da biyar na lokacin da aka ware wa wannan shiri

Shiri
§ Tsari daya bayan daya
§ Horar da ’yan wasa da ma’aikata
§ Gwada kayan aiki
§ Gwada ’yan wasa a da kayan aiki a wurin da za a yi aikin
§ Akalla a bayar da kashi goma cikin dari na iya kwanakin da aka ware don yin aikin

Aiwatar da Aiki Kai Tsaye
· A aiwatar da aikin cikin hotuna da sauti
· Samar da kade-kade da bushe-bushe da sautuka masu nuna almomin faruwar wasu abubuwa
· Akalla a ba shi kashi biyar cikin dari na lokacin da aka ware don aiwatar da shirin

Shiri Bayan Shiri
· Tsara hotuna da sauti
· Dubawa don tabbatar da abin da aka dauka ya yi daidai

Tun da mun ji wadannan bayanai ya kuma kamata mu gangara ga tarihin samuwar fim ko majigi a duniya baki daya.

Samuwar Fim Ko Majigi A Duniya:
An fara tunanin yin fim ko majigi a duniya tun cikin karni na goma sha tara (19) wato a shekarar 1824, wani likita mai bincike a fannin ido, dan kasar Birtaniya mai suna Peter Mark Roget, shi ne ya fara bincike don samar da wata na’ura mai amfani kamar idon mutum. Daga shi ne aka samu ci gaba aka kirkiro wani abin wasan yara mai suna Zoetrope wato kallo-kallo na yaro.
Shi kuma wani dan kasar Faransa mai suna Charles Emile Renoad, a shekarar 1844 zuwa 1918, ya fito da wata na’ura mai suna Proxiono Scope, wadda ya lillika hotuna a jikin wani kwarkwaro kamar kallo-kallo da ake yi na akwati.

A shekarar 1861 wani Ba’amirki masanin kirkire-kirkire mai suna Coleman Sellers, wanda ya yi zama tsakanin 1827 zuwa 1907 ya fito da wata na’ura mai suna cinema-toscope. A shekarar 1872 wasu Turawan Amurka da Ingila suka yi hadin gwiwar bincike a kan aikin da wani Eadward Muybridge ya yi, suka yi amfani da kyamarar daukar hoton kati guda 24, suka dauki sukuwar dawaki, suka jera hotunan da suka dauka guda 24 din, ya samar da musu da cikakkiyar tafiyar dawaki da motsawarsu bi-da-bi, daki-daki.

Daga nan aka samu wani dan kasar Faransa mai suna Etiene Jues Marey (1830-1904). Wannan Bafaranshe ya bi aikace-aikacen wadancan mutanen ya fito da kyamara guda daya mai motsi, ya sa mata suna Chronophotographe amma duk da haka a kan takarda kawai ake iya daukar hoton. Sai kuma wani Ba’amirike mai suna Hannibal Williston Goodwin (1822-1900) da kuma George Eastman, suka samar da zaren kallo na majigi, kuma ana iya wankewa a kan zaren kuma a gan shi, amma ba ya motsi.

Wani Thomas Alra Edison ya samar da wata kyamara mai suna Kenetographe da kuma na’ura mai suna Kinetoscope, mai kamar talbijin. Ya kuma tara jama’a a New York ya nuna musu.
A shekarar sai ya gina shago a London da Faris, ya mayar da shi gidan kallo, daga nan ne mutane suka fara cewa ashe lallai za a samu kudi a harkar. Daga wannan lokaci ne aka fara tunanin kirkiro projector, don a samu damar tara mutane da yawa. Sai fasahar ta fara zama ta hadin gwiwa, inda wani Bafaranshe mai suna Louas Jean Lumi’ere, (1864-1948) da wani Robert W. Palt dan kasar Birtaniya (1869-1943), da wani dan kasar Amurka Charles Francis Jenkins (1867-1934), wadannan mutane su ne suka kirkiro projector.

Fim ya kankama:
Fim na farko da aka fara nuna wa jama’a a duniya, an yi shi ne a shekarar 1895 zuwa 1910, a duk tsawon wadannan shekaru goma sha biyar fim daya rak aka yi, kuma du-du-du tsayinsa na minti daya ne tak. Har ila yau kuma a lokacin ne aka fara mayar da rubuce-rubucen littattafai zuwa fim, daga nan marubuta suka raja’a a harkar fim. A 1893 aka fara gina dakin shirya finafinai (studio) ta farko a duniya, a cikin wajen ana samun sansanin karuwai da masu wasa da dabbobi da ’yan wasan kwaikwayo, daga nan aka soma daukar su a majigi ana nunawa a silima. Abu dai ya dada bunkasa, aka samar da wuraren yin atisayen harbe-harbe da kuma wajen kallo na kan hanya wanda ake jefa kwandala a yi kallon fasadi, da wajen ajiye tufafin da aka yi wasa da su, aka kuma bude gidajen magajiya inda ake kade-kade da raye-rayen molo da garaya da kuntigi da kuma goge. A shekarar 1896 aka samar da ’yan wala-wala da dabo da rufa ido, mutumin da ya yi suna a wannan harka a lokacin shi ne George Melies (1861-1930). Shi ne yake yin wasa da rana a dauka, idan dare ya yi sai a nuna a silima. A wannan lokaci ne ’yan mishan suka yi Allah wadai da ’yan fim saboda sharholiya da fasadi da ake aikatawa a gidan shirya fim. Kuma su ’yan mishan suna ganin sabo ne domin kamar suna kwaikwayon Allah ne, saboda wannan dalili sai da ’yan mishan suka kashe wasu daga cikin ’yan fim din. Da ’yan fim suka ga an fara kashe su kuma suka ga ba mafita illa su kai da takonsu, sai kawai suka ari takalmin kare suka yi gudun hijira suka bar wajen suka nufi wani jeji inda aka taba yin girgizar kasa ( a shekarara 1853), suka tare a nan, saboda wajen akwai tuddai da suka yi masa ganuwa yadda ba mai ganin abin da ake yi a wajen in ba shiga da’irar ya yi ba. Yanzu wajen shi ake kira Hollywood.

A wannan lokaci idan ana daukar majigi ba a katsewa domin idan aka katse hoton zai yi tsalle wato jumkat (Jump cut), saboda haka sai aka samar da na’ura mai sarrafa hoto tana iya narkar da shi wato (dissolve) ko hoto ya shiga cikin hoto (super imposed) da yi wa hoto wata-gangano (special effects), da dai sauransu. Harkar kirkira ta ci gaba har aka fara yin finafinan cafta-cafta kamar tsarin littafi. Fim din da ya yi suna a lokacin shi ne A trop To The Moon (1902) da Fantasies da Cinderella. A 1903 aka fara shirya fim din Kaboyi, a lokacin ne aka yi shahararren fim din nan mai suna The Great Train Robbery, wanda ya ba da umarni wani mai kirkira ne dan kasar Amurka, sunansa Edwin S. Porter, tsawon fim din minti takwas ne kacal amma fim din ya burge ’yan kallo saboda an tsara shi sosai. Har ila yau shi ne ya fito da wani gidan wasa mai suna Nickelodeons, mai kama da Marhaba ko Plaza silima. Ire-iren wadannan wurare babu mata ko ’yan wala-wala a ciki, don haka samari ba sa kwana a wajen in an tashi daga kallo.

A 1912 aka fara wasan barkwanci da na jarumta, a lokacin ne marigayiya sarauniyar Ingila Queen Elizabeth ta shiga harkar fim, har ta yi suna ta shahara. Tana harkar wasan ne aka ba ta sarautar Ingila, fim din da take yi ya taimaka mata a lokacin da aka zo zaben wadda za ta zama sarauniyar Ingila, inda ta zama ita ce a kan gaba duk cikin ’ya’yan sarautar Ingila. A 1908 aka gina gidan fim na Biography Studio, suka fara yin fim din gwaji na fadace-fadace, fim din da suka fara yi shi ne Griffith, a lokacin aka fara yin daukar kurkusa da nesa, sama da kasa da kuma daukar kyamara a canza mata waje, kuma shi ya fara amfani da kyamara sama da daya.
1912–1913 Shi ne suka yi cikakken fim mai suna Judith of Behulia. Daga nan aka soma fim din yaki, mai suna The Birth of Nation, a 1915 sanadiyyar sune aka samu wayewar kan Amerikawa, har suka yi bore aka yi juyin juya hali a shekarar 1917. Bayan shekara biyu da yin wannan fim. A lokacin juyin-juya-hali masu shirin fim sun dira fagen fama da kyamarorinsu don sudauki yakin na gaske.

A 1914 aka gina katafaren dakin kallo na zamani a kan titin Broad Way da ke birnin New York, har yau babu kamarsa duk duniya. Daga nan aka fara finafinan soyayya inda Willioms Hart ya yi shuhara, kuma ya yi zamani a tsakanin 1872-1946, daga nan sai kasuwar fim ta yadu a kasuwar Turai. A Jamus an fara fim ne a wajen 1924. Amma a kasar Rasha an fara yin finafinan farfaganda da na ilimi a wajajen 1919. Su mutanen Rasha ba su yarda da aiwatar da kowanne irin fim ba in ba na akida da al’ada ba. Wannan dalili ne ya sa kasashen Turai suka fara yin finafinan tarihi wanda ba na kirkira ba a wajajen 1922.

Samuwar Fim A Nijeriya
Turawan mulkin mallaka sun shigo Nijeriya ta bangarori biyu, da farko sun shigo ta Arewa da fuskar Larabawa, amma ba Larabawa ba ne Turawa ne da Yahudawa kuma ’yan yawon dandi. Sun je Katsina da Sokoto da Kano da Daura da kuma Hadeja, amma da suka ga muna da addini sai suka koma suka sake shiri suka shigo ta kudanci, a matsayin ’yan kasuwa. Bayan sun cinye kudu da Arewacin Nijeriya, suka kafa gwamnatinsu suka ce suna so a daina cinikin bayi. Daga nan sai suka fara tsara yadda za su tafiyar da mu da kuma irin tsare-tsaren da za su kawo mana nasu, sai suka ga lallai sai sun yi amfani da ilimi wajen bautar da mu.

A 1903 aka fara yin fim a Ikko ta Nijeriya. Fim na farko da aka fara kawowa Nijeriya aka kalla ce shi a gidan kallo na Gloria Memorial Hall da ke Ikko shi ne Moral Re-Almament, an nuna shi ne a shekarar 1903 fim din Decomentry ne da yake koyar da da mutane a yi biyayya ga nasara a guji Yahudawa, shi ya sa ma suka sa masa suna Farfado Da da’a.

Tun daga wannan shekara 1903 ’yan Nijeriya ba su samu gatanci da kulawa ta musamman a harkar fim ba, yadda jama’a za su rungume shi a matsayin sana’a, duk da kasancewar Nijeriya tana da yanayi da wurare da suka cancanta da kuma dacewa da shirya fim, ga kuma yawan jama’a da rashin aikin yi da zaman kashe wando ga kuma kwararowar mutane daga kauyuka zuwa birane, har ila yau ga katutun jahilci da talauci da ya yi kaka gida ga jama’a. Duk da wannan bukata da ’yan Nijeriya suke da ita amma sai ya zama shigo musu da fim ake yi daga kasashen waje, daga hukumar ’yan mulkin mallaka da kuma kungiyoyin ’yan mishan. Finafinan sun kasu kashi uku, akwai tarihi a kan sarakunan Ingila da yadda ake tafiyar da mulki da kuma labaru a kan abin da yake faruwa a yammacin Turai, har zuwa 1945 bayan yakin duniya na biyu. A wannan shekara ne abubuwan da ake nunawa a fim suka fara sauya fuska, saboda guguwar sauyi ta ratsa duniya, don haka sai finafinai suka sake salon bayar da labarai kan irin bore da zanga-zangar da ake yi don neman ’yanci.

Da aka samu ’yancin kai a shekarar 1960 sai Nijeriya ta kasu kashi uku, haka shi ma tsarin finafinai suka canza, kuma suka tabarbare saboda an mayar da harkar fim a karkashin yanki-yanki. A Arewa sai aka bai wa ma’aikatar yada labarai kula da fim, aka yi masa wata ’yar tsangaya ta shirya fim, daga nan sai ya samu koma baya saboda karancin tallafi da yake samu daga hukumar, sannan babu kwararrun ma’aikatan shirya fim da nagartattun kayan aiki. Bugu da kari babu wata ma’aikata da take da kayan tace fim a duk fadin Nijeriya da Afrika in ban da kasar Afrika ta Kudu da Masar, saboda haka ko an dauki fim ba wai an gama ba ke nan akwai sauran rina a kaba, domin sai an yi tattaki zuwa daya daga cikin kasashen nan biyu na Afrika ko kuma a yammacin Turai, sannan za a tace shi. Kuma ko da ka yi fim din sai ka ci karo da matsalar ’yan babakere da banga-banga a wajen tallata shi. Mutanen da suke yin wannan kafar ungulu su ne mutanen Siriya da Labanon da Yahudawa, domin su ne suke da gidajen nuna finafinai da rarraba su a ko’ina a Nijeriya. Wata babbar matsala da ta sa fim ya dada samun tawaya ita ce, ra’ayin rikau na shugabanninmu, domin ba sa bari a shirya wani fim na musamman sai dai a yi ta nuna wa jama’a ziyarce-ziyarcensu zuwa kasashen waje ko kuma idan ana so a cusa wa mutane wata akida ko manufa, sai a shirya fim a kansa a nuna wa jama’a, shi ma ba irin finafinan da ake yi na wasan kwaikwayo ba ne, a’a na fadakarwa a kan wani abu da gwamnati take da sha’awa.

Bayan an yi juyin mulki na farko a Nijeriya cikin shekarar 1960, sai fim ya sake canza salo, ya koma hannun jihohi, aka yi rabon gado na ma’aikata da kayan aiki, sai wasu jihohin ma suka rasa komai, ba ma’aikatan ba kayan aikin, wasu kuwa suka samu kalilan na ma’aikatan da kayan aiki musamman ma da yake mutanen sun fito daga larduna daban-daban, don haka wata jihar sai ta samu mai daukar hoto, wata ta samu mai hada hotuna, wata ta samu mai kula da sauti, wata ta samu mai shiryawa, kai wata ma in ban da direba ko mai shara da daukar kaya ba abin da ta samu. Haka ma kayan aikin aka yi musu rabon guntu-guntu, domin wani kayan aikin an bayar da shi ga jihar Kano amma mahadinsa yana jihar Arewa ta tsakiya wato Kaduna, ko kuma Biniwai Filato da ke Jos, ko Arewa maso gabas da ke Maiduguri. Ashe kun ga babu aiki ke nan.
Nakasa ta gaba kuma da fim ya samu ita ce fitowar kyamarar daukar hoto ta bidiyo U-matic, tana shigowa kasuwa a shekarar 1973, sai gwamnatocin jihohi suka watsar da harkar fim na kwarkwaro ko majigi, daga nan suka kirkiro sashin bidiyo wato U-matic saboda saukin sarrafawa da araha da yake da shi, amma duk da haka jama’ar gari su dai ya yi musu tsada don haka ba sa iya sayen sa balle har su sarrafa shi, domin babu wata makaranta da ake koyar da aikinsu.

Fim ya fara samun gata ne a shekarar 1981, lokacin da kyamarar bidiyo ta VHS ta zo Nijeriya, sai ya kasance akwai ’yan kalilan din mutane da suka fara mallakarta. Mutane ba su fahimci za a iya daukar fim da ita ba har a yi wani cikakken fim a tace shi a kuma kai shi kasuwa a sayar. Wata babbar illa da ya kamata a fahimta ita ce tun daga shekarar 1960 zuwa 1970, kashi casa’in da tara na finafinan da ake nunawa a Nijeriya duk na kasashen waje ne, kamar Cana da Indiya da yammacin Turai da kuma Amurka. Sannan masu kula da gidajen nunawar kashi tamanin cikin dari baki ne ’yan kasashen waje mazauna Nijeriya, sannan kashi ashirin din da suka rage in aka tace su, kashi tamanin daga ciki ’yan yammacin Nijeriya ne, kamar Yarbawa da ’yan jihar Bendal. Kashi ashirin su ne asalin ’yan arewacin Nijeriya. Duk cikin wannan adadi babu wani manaja guda daya da ya fito daga jihar Kano (a wancan lokacin), in kuwa ka ga dan Kano a aikin silima, to maigadi ne ko mai shara, shi ma saboda mayen kallo da kuma zuwa bakin silimar ne, shi ya sa aka yaba da kokarinsa har aka yarda yake ’yan wadannan aikace-aikace, amma fa kyauta yake yi, in ma da akwai wani abu da ake ba shi bai wuce kyautar katin shiga (free pass) ba, shi ma wata rana ana haramta musu shigar domin za a rubuta da manyan baki a takarda a manne a bakin kofa, a ce (no free pass).

Daga 1960 zuwa 1980 an yi cikakkun finafinai guda dari da talatin 130 a Nijeriya, wani abin takaici shi ne wadannan finafinai guda dari da hudu 104 duk an yi su ne da harshen Yarbanci, guda tara kuwa an yi su da Turanci, guda uku kuma an yi su da harshen Ibo, sauran guda biyun su ne kawai aka yi su da harshen Hausa.

A iya wadannan shekaru ashirin (1960-1980) akwai silimomi fiye da dari uka da hamsin a Nijeriya kuma dukkansu mallakar baki ’yan kasashen waje ne.

Gwamnatin Nijeriya ta yi fim din majigi na karshe wanda har yanzu ba ta sake yin wani ba, haka kuma babu wani dan kusuwa da ya sake yi. Fim din Kulba Na Barna shi ne wanda aka yi a shekarar 1993, ranar 25 ga watan Yuni, daga shi kuma har yanzu shuru kake ji Malam ya ci shurwa. A dai tsawon wadannan shekaru ne aka samu fitattun mutane da suka shirya finafinai kamar Mr. Eddie Ugbomah, shi ne wanda ya shirya fim a kan yadda aka kashe Janar Murtala wato The Death of Black Presdent. Sai kuma Hubert Agunde ya yi The Mask da Jaiyesimi da kuma Aiye da sauransu. Marigayi Adamu Halilu shi ya shirya Shehu Umar. Ola Balugun ya yi Amadi. Akwai Francis Oladele ya yi Ikebe, sai Sule Umar ya yi Maitatsine, ga kuma Brendon Shehu ya shirya Kulba Na Barna. Akwai Sadik Balewa da ya shirya Kasarmu Ce. Akwai masu shiryawa da bayar da uamarni kamar su Dosunmu da Adu.

Samuwar Hukumar Shirya Finafinai Ta Kasa:
A shekarar 1985 zuwa 1993 da gwamnati ta ga mutane sun fara daukar wasan kwaikwayo da muhimmanci sai ta yi wa doka ta 1963 kwaskwarima da gyaran fuska, wato dikiri na 61, sai ya bai wa kowa damar ya dauki fim. Daga nan aka kirkiro hukumar shirya finafinai ta kasa, aka ba ta damar ta shirya fim ta rarraba shi sannan ta hada da kuma samar da kungiyoyi da za su iya shirya fim su nuna su kuma sayar da shi, a matsayin masana’anta. Har ila yau kuma an dora mata alhakin horar da masu sana’ar fim, tun daga rubutawa zuwa lokacin ganinsa a allon kallo na gida da silima. Bugu da kari kuma ana so ta samar da hadaddun kungiyoyin masu sana’ar fim, sannan ta samar da kayan shirya finafinai da tace su. Kuma su samar da dandamalolin shirya fim. Za kuma ta samar da masu zuba jari da tallafi daga hukumomin kasa da jiha da kananan hukumomi da gidajen samar da kudi. An yi mata ofishi na dindindin a Jos. An kuma kafa hukumar daraktocin gudanarwa a shekarar 1982. Daga nan aka kafa dakin tacewa da wanke fefen majigi da kuma bidiyo. A 1990 ta bude dakin juyar majigi mai fadin 16mm da 35mm. A shekarar 1992 kuma ta samar da makarantar koyon aikin shirya fim, sannan ta samar da kadada 161, wato ta samar da fili mai fadin falayen bal guda 161 domin shirya fim a wajen, ba ka bukatar zuwa ko’ina, suna da dakunan saukar baki da koramu da tuddai da kwazazzabai da duwatsu masu fito da ruwan marmaro.

Jinsin farko da aka yi na finafinai a Nijeriya yawancinsu daga rubutattun wasannin kwaikwayo da na zube wadanda aka buga a littattafai ne.

Jinsi na biyu kuwa ya shafi abubuwan da suke addabar mutane a rayuwa.
Jinsi na uku kuwa sun fi mayar da hankali wajen tsafe-tsafe na gargajiyar Yarbawa da Ibo.
Jinsi na hudu sai suka fada bangaren aikata laifuka da rashin da’a da zama cikin gaskiya da adalci.

Ita kuwa gwamnati sai ta fi mayar da hankali a bangarorin kiwon lafiya, har ma shan kwayoyi masu sa maye da kiyaye hadura da noma da samar da ruwan sha da ilimi da yada farfaganda da kawo zaman lafiya tsakanin al’umma ta bayyana ire-iren nasarorin da gwamnati ta samar da kuma yayata ire-iren aikace-aikacen gwamnati, kamar fim din Baban Larai wanda gwamnatin Arewa ta shirya.

Wasu Daga Cikin Nasarorin Masu Shirya Finafinan Hausa

Samuwar Finafinan Hausa A Kano:
Mace ta farko da aka fara dauka a garin Kano ta kuma fito a cikin fim din kwarkwaro na silima wato celluloid ita ce Hajiya Umma ’Yarcinda, tun kafin a samu ’yancin Nijeriya, ta fito ne a cikin wani tallan keken Rali da aka yi a Kano, wannan mata har yanzu tana nan da rai a unguwarsu ta Fagge, Kano. Asalin iyayenta kuma mutanen kasar Nijar ne.

Finafinan Hausa na bidiyo kuwa an fara samun su ne tun daga shekarar 1980 zuwa 1984, sakamakon irin hobbasar da kungiyoyin marubuta littattafai da na wasan kwaikwayo na dabe da na al’adun gargajiya da kuma na wasan motsa jiki da gwada kwanji (kareti) suka fara jarraba shirya fim ba tare da wasu ma’aikata kwararru ba, kuma ba don neman kudi ba. Wadannan kungiyoyi sun hada da kungiyar wasan kwaikwayo ta Gyaranya da Black Eagle da Dynamic Fighters da Tumbin Giwa da makamantansu.

A tsakanin wadannan shekaru an gabatar da finafinai kimanin guda tara, ga sunayensu kamar haka:

  1. Hukuma Maganin ’Yan banza wanda aka fi sani da Kasko, wanda aka yi shi da sigar fim din Cana wato ta fasalin fadace-fadace
  2. Karshen Alewa… wanda aka fi sani da Bakar Indiya, wanda aka yi shi kamar na Indiya wato yadda suke rawa da waka,
  3. Auren Dole
  4. Sabo Da Kaza
  5. Sanda Jan Namiji
  6. Komai Nisan Dare
  7. Sirri Bakwai
  8. Salihi Da Saliha

Yan daukar Amarya

Daga cikin wadannan finafinai guda tara da aka zayyana guda bakwai ba su fito kasuwa ba, ga su kamar haka:

1. Auren Dole
2. ’Yan daukar Amarya
3. Sabo Da Kaza
4. Sanda Jan Namiji
5. Komai Nisan Dare.
6. Salihi Da Saliha
7. Sirri Bakwai

Alhaji Hamisu Mudi Gurgu da Sani Lamma su ne mutane na farko da suka fara daukar hoton fim din Hausa a bidiyo, lokacin ana yayin Bitamaks, domin yawancin wadannan finafinai da aka yi su ne suka dauke su. Da kyamarar VHS ta samu sai ’yan kungiyoyi suka fara tattara kudi a junansu suna daukar hayar kyamara ana daukar musu wasanninsu a ciki idan kuma sun je wasa wani gari sai a bayar da sanarwa cewa bayan wasan dabe da za a yi kuma za a nuna wani wasa da ’yan kungiyar suka yi a kaset na bidiyo, a lokacin ko tace fim din ma ba a yi haka ake nuna shi. Daga nan sai Alhaji Musa Nasale ya fara daukar makada da mawaka a cikin kaset na bidiyo yana sayarwa. Su kuma su Alhaji Hamisu Gurgu sai suka mayar da abin sana’a ana daukar su zuwa wani wajen a biya su wani kuma ba a biyan su, don daukar ire-iren wadannan finafinai, kai har gidan talbijin yake zuwa ya taya su irin wannan aiki kyauta, sai dai su dan saka shi a cikin wasan da suke yi, saboda sha’awarsa da son ci gaban wasannin. Wani abin sha’awa da ban al’ajabi kuma Hamisu Gurgu ne dan wasan kwaikwayo na farko da ya fara auren ’yar wasa a Kano mai suna Hauwa, ’yar unguwar Daurawa ta cikin binin Kano, an yi auren a shekarar 1983. Ta taba fitowa a matsayin jaruma a wani fim, sannan ta yi fitowa ta musamman a cikin fim din Sabo Da Kaza, har ila yau ta sha fitowa a shirin talbijin na CTV 67 Kano, wato Zaman Duniya da kuma Bakin Ganga. Hamisu Gurgu, sana’o’in da yake yi a cikin fim suna da yawa, ya iya kyamara, yana rubuta wasa ya shirya ya bayar da umarni, yana horar da ’yan wasa, yana samar da ’yan wasa da bayar da hayar kayan aiki, yana rubuta waka, ita kanta matar da ya aura kafin a yi auren sai da ya rera mata waka, ga abin da ya ce a cikin wasu baitukan wakar:

Bari bari, ke bari ke Hauwa,
Share hawayenki, ki daina kuka,
Ki daina kuka.
Me ya same ki? Ki yi magana man,
Domin ni na matsu don ke,
Amma in na yi laifi ne, sai fa ki yafe ni,
Ba zan kuma ba, ba zan kuma ba.

Karin wannan waka ya samu shi daga cikin wani fim din Indiya mai suna Giyitiga- cacal, ma’anarta da Indiyanci shi ne waka matafiya.
Hamisu ne ya fara nuna wa wasu daga cikin ma’aikatan C.T.V 67 dabarar yadda za su yi magana da abokan aikinsu ta hanyar wayalis da kuma magana da ’yan wasa ta hanyar amsa kuuwa (in suna da yawa ko nisa tsakaninsu). Shi ne ya fito da dabarar hada baturin kyamara idan na asali ya mutu, ko ya lalace.

Saboda sha’awar Alhaji Hamisu a kan harkar fim, a shekarar 1980 lokacin da suke daukar shirin Karshen Alewa… (Bakar Indiya), motar da ake amfani da ita a fim fijo ce sai ta lalace, bai yi wata-wata ba ya cire kudi wuri na gugar wuri har sama da N4,000 ya sayo wata motar aka zo aka ci gaba da daukar shirin.

A Kano Sidi Musa shi ne mawakin da ya fara wakar finafinai da karin Indiyawa, kuma yakan yi muryar mace da namiji shi kadai, (kamar yadda Sadi Sidi Sharifai yake yi a halin yanzu). Ga wasu daga cikin baitucin wakokin Sidi Musa:

Muryar namiji
Hasken idanunki,
Ya haske min raina,

Muryar mace
Hasken idanunka,
Ya haske min raina.

Karin wakar fim din Darmatima ne ya yi amfani da shi wajen rera wakar. Akwai kuma wata wakar da ya dauki salon wakar fin din Roti inda yake cewa:

Ku taho za mu je wurin fim,
Ba yadda za a yi.

Wakar fim din Karshen Alewa (Bakar Indiya) kuwa daga fim din Fil-waherat ya samu karin, ga abin da yake cewa:

Muryar namiji
Ina son ki Jamila kwarai da gaske.

Muryar mace
Ina son ka Jamilu kwarai da gaske.

Muryar namiji
Idan kin yi tunani Jamila,
Ni ne masoyinki,
Hoooooo!.

Muryar mace
Idan ka yi tunani Jamilu,
Ni ce masoyiyarki,
Hoooooo!.
Ba mu da kowa a yau fa sai junanmu.

Su Sidi Musa ma sun yi fim a wancan lokaci, sunan fim din Bako Daga Sanka.


Akwai wani mawakin da suka yi zamani tare da su Sidi Musa, sunansa Sani Hamza (dan kungiyar Gyaranya ne a lokacin), sai dai shi rubutawa kawai yake ya ba ya rerawa.


Wadannan wakoki da su Sidi Musa da Sani Hamza suka yi su ne wakoki na farko a cikin finafinan Hausa, daga nan kuma aka yi shirin Dausayin Soyayya wanda aka fi sani da Jamila Da Jamilu wanda gidan talbijin na N.T.A Kano ya dauki nauyin shiryawa, a nan ma jarumin cikin fim din Ibrahim Mandawari ya rera wa jarumar (Jamila) waka yana kan bishiya. Daga nan sai fim din Munkar mallakar Kungiyar Jigon Hausa, Bala Anas Babinlata shi ne jarumin fim din, shi ma ya rera wa jarumar waka, wato Jamila, kuma shi ne jarumi na farko a Kano da ya rera wa jaruma waka a gabanta ba tare da kida ba. Fim din In Da So Da Kauna mallakar kamfanin Gidan Dabino Video Production, shi ne fim na farko a Kano wanda aka sanya waka hade da kidan fiyano a cikin fim din Hausa, irin wakar da ake jin muryar mai rerawa amma ba a ganin mai rerawar, wadanda suka yi kidan wakar su ne marigayi Nasiru U. Ishak da Muktar Musa Kwanzuma da kuma Musa Ahmad, dukkansu ma’aikata ne a Hukumar Adana Tarihi da Al’adu ta jihar Kano. Kamfanin Iyan-Tama Multy Media su ne kamfani na farko a jihar Kano wadanda suka fara sanya waka da kidan fiyano ana kuma rera waka tsakanin saurayi da budurwa baki da baki (miming) hakan ta faru ne a cikin fim dinsu mai suna Badakala. Marigayi Nasiru U. Ishak na ya yi kidan wakar fim din.

Baya ga finafinai da ire-iren su Hamisu da makamantansu ’yan kungiyoyi suke shiryawa akwai finafinai da ake shiryawa a gidajen talbijin kamar N.T.A na wasu jihohi da C.T.V 67, Kano, sai dai su ba ana yin su don sayarwa a kasuwanni ba ne, ana nuna su ne a tashoshin talbijin, sai dai ’yan kalilan da ake samu suna fitowa kasuwa ta barauniyar hanya jama’a suna saya, wadannan finafinai sun hada da: Golobo daga Sakkwato da Karkuzu na Bodara daga Jos da Gaskiya Dokin Karfe daga Maiduguri da Jamila Da Jamilu (Dausayin Soyayya) daga Kano, wadannan duk shirye-shirye ne na NTA da ke wadannan jihohi. Sai kuma Bakan Gizo da Hadarin Kasa da Hankaka na gidan C.T.V 67, Kano.

A da can gidajen talbijin ba sa fita waje daukar fim sai dai a dakin shirye-shirye suke yi (studio). A 1980, CTV 67 suka fara fita waje suna daukar finafinansu na talbijin, duk da yake a lokacin ba a bude tashar C.T.V 67 ba, amma suna fita daukar wadannan finafinai ne saboda tanadin gaba yadda da an bude tashar suna da wasannin da za su dinga nuna wa mutanen gari. Sakamakon haka ne har mutane suka fara fahimtar yadda ake daukar fim. A shekarar 1990, Kungiyar Tumbin Giwa ta shirya fim mai suna Turmin Danya, sannan a shekarar 1994 suka shirya Gimbiya Fatima. Tumsy Video Club sun shirya wani fim mai suna Rana Ba Ta Karya. Kamfanin Gidan Dabino Video Production sun shirya fim, In Da So Da Kauna a shekarar 1994. Kamfanin Kwabon Masoyi ya shirya fim ‘Kwabon Masoyi’ a shekara 1993. Haka kuma akwai wata kungiya a garin Birnin Kudu wadda ta shirya wani fim mai suna Wata Rana… Kungiyar Jigon Hausa ita kuma ta shirya fim, Munkar, duk a shekarar 1993 zuwa 1994. R.K. Studio sun shirya fim dinsu mai suna Bakandamiyar Rikicin Duniya, a shekarar 1994 zuwa 1995. Yakasai Drama Association ta shirya fim din Kuturun Danja a 1995. Yakasai Welfare Association sun shirya fin din danduniya a 1994,. Kungiyar Ruwan Dare sun shirya fim mai suna Sarauta Gado a 1996, amma wadannan finafina guda biyu ba su shiga kasuwa ba. (Sarauta Gado da danduniya) Samar da wadannan finafinan da wasunsu shi ne ginshikin da ya samar wa kamfanoni da kungiyoyin kasar nan yin finafinan Hausa, domin yin wadannan finafinai ya jawo sha’awa da kaunar finafinan Hausa ga jama’a masu kallo. Da tafiya ta yi tafiya sai abin ya zama ruwan dare.

Samuwar Kamfanonin Shirya Finafinai a Kano:
A shekarar 1986 an samu wasu mutane masu zaman kansa wadanda suke shirya wani wasa na Turanci mai suna ‘Magaji Family’ wato Iyalin Magaji, wanda ake nunawa a gidan talbijin na kasa. Jarumin fim din shi ne Dakta Umar Faruk Jibrin wanda a yanzu malami ne a Sashin Koyar da Aikin Jarida na Jami’ar Bayero ta Kano. Sunan kamfanin Sahel Motion Pictures, mallakar wasu ’yan kasuwa da ke Kano, Alhaji Tijjani Sani da Alhaji Umar Usman Tofa da Kabiru Ibrahim Gaya, tsohon gwamnan Kano, dukkaninsu masana ne a fannin zana taswurar gidaje suka yi hadin gwiwa suka kafa wannan kamfani. Yayin aiwatar da wannan shiri an dauko mutane kwararru kuma gogaggu a harkar, wasu an dauko su daga NTA Kano da C.T.V 67 Kano da Hukumar Adana Tarihi da Al’adu da Ma’aikatar Yada Labarai ta Kano da Hukumar Bunkasa Aikin Noma ta Kano wato KNARDA, don su dinga gudanar da daukar wannan shiri, wasu daga cikin mutanen su ne, Sule Umar da Ishak Hadeja da marigayi Malam Bashir da marigayi Tijjani Ibrahim da Salisu Galadanci da Nuhu Aminu da Wada Kacako da Salisu Makama da Umar Ya’u (Malam Nagona) da Aminu Mahmud da Amina Habib da Ali Bature da Baba Ali da Abdulkareem Mouhammed da Bala Sabo Usman da Aminu Sarki da Aminu Dakta. Haduwar wadannan mutanen da ma wasu sai ya zama babbar nasara, suka dinga gudanar da aiki cikin jin dadi, kuma kowannensu yana yin aikinsa na gwamnati sai in ya dawo ne zai zo wannan kamfani ko kuma ranakun hutu. Sun shekara biyu suna yin wannan wasa. A nan ma ’yan kungiyoyi sun samu damar ganin yadda ake daukar wasan kwaikwayo a bidiyo, har suka yi ido suka kuma san yaya ma ake yi. Hatta su kansu ma’aikatan a lokacin ba su da kamfanoni nasu na kansu, amma daga baya sai suka fara kafa kamfanoni na wucin gadi ko kuma a ce tafi-da-gidanka wadanda ba su da ofis.

Kafin a gama kwangilar wannan wasa sai aka dinga samun jita-jita cewa masu kamfanin suna karbar makudan kudi suna sokewa a ramin telansu suna dan yafitowa ’yan wasa da ma’aikata, don haka wasu daga cikinsu suka fara tunanin kafa nasu kamfanin don sun ga akwai riba, kamfani na farko da ya fara tashe shi ne Leader Communication wanda aka kafa shi tare da marigayi Bashir Zakari, ya zama manaja mai shiryawa da ba da umarni, sai kuma Moving Image ya bullo da M.T.S Television da Fine Tune da Drum Beat da Sahara Motion Pictures da Mu’azat Enterprises. Bayan samuwar wadannan kamfanoni sai harkar fim ta sake sabon salo, domin wadannan kamfanoni ba suna yin fim don sayarwa ga jama’ar gari ba ne, a’a don yiwa manyan kamfanoni su dinga nunawa a gidajen talbijin ana tallata musu hajarsu, daga nan sai aka samu gasa tsakanin wadannan kamfanoni da gidajen talbijin na jiha da kuma su kansu ’yan wasan, sai aka fara rarraba kawunansu cewa idan kana yin wasa a can, wadancan sai su ce ba za su sa ka nasu ba.

Tun daga shekarar 1990 kungiyoyin wasannin kwaikwayo da na marubuta suka fara shirya finafinai na kansu don sayarwa a kasuwa, da tafiya ta yi tafiya sai aka fara yin hannun riga saboda shigowar kudi da daukaka a cikin lamarin. Sai kishi da kyashi da hassada suka yi katutu ga masu wannan sana’a, saboda haka sai aka fara raba gari tsakanin ’ya’yan kungiyoyin da ita kanta kungiyar. Misali na farko shi ne rabuwar Ibrahim Muhammad Mandawari da kungiyar Tumbin Giwa, in da suka kafa kamfani su biyu tare da Adamu Isah, mai suna Auladi Ventures. Shi kuma Adamu Mohd, Yarima ya kafa Kwabon Masoyi Production tare da Alhaji Hamza Darma. Daga nan sai daraktan wasannin kungiyar marigayi Aminu Hassan Yakasai ya kafa Nagarta Motion Pictures. Shi kuwa Bala Anas Babinlata sun sanya zare tsakanin kungiyarsu ta Jigon Hausa, bayan gudanar da shirinsu na Munkar, sai ya je ya kafa kamfanin Mazari Film Mirage. Haka kuma kungiyar Tauraruwa Drama and Mordern Films Production suka yi baram-baran da Ado Ahmad Gidan Dabino bayan an gama shirya In Da So Da Kauna, daga nan ya kafa Gidan Dabino Video Production. dan Azumi Baba Chediyar ’Yangurasa sun raba tafiya da Garin Malam Video Club, bayan an gama Bakandamiyar Rikicin Duniya.

Yadda Salsalar Haihuwar Kamfanonin FinafinanKano Take:
Kungiyar Tumbin Giwa Drama Club ta haifi kamfanin Tumbin Giwa Drama and Film da Auladi Venture da Kwabon Masoyi da Bright Star. Gyaranya Drama ta haifi Tauraruwa da Jan zaki da Kismatic Group. Gyranya da Organisition for Moral Consensus (OMC) su ne suka haifi Jigon Hausa. Jigon Hausa ta haifi Mazari Film Mirage da Zinariya Film Production. Kismatic ta haifi Dabo Films, ita kuma Dabo ta haifi Lezi Production da Mashhamatic, Dabo da Iyan-Tama su ne suka haifi Dambazau Entertainment. Kungiyar Tauraruwa ta haifi Gidan Dabino Vedio Production da Zik Entertainment da Umaruru Production da Mararraba and Sons da Mai Culculator Production da Fagge Unity da kuma Raja Production. Fagge Unity ta haifi Five Stars. Soyayya Communication ta haifi Kwality Audio Visual. Kwality Audio Visual ta haifi Fasaha Films. Fasaha ta haifi H.B. da F.K.D da Gidigo Production da Rumbun Kaya Production. Kungiyar Raina Kama ta haifi R.K. Studio da Ramat Enterprises, daga nan sai R.K Studio da Gidan Dabino suka haifi Iyan-Tama Multy Media. Iyan-Tama ta haifi Klassic Films da Sadi Sidi Sharifai Production da Aleebaba Video Club. Jan zaki ta haifi dansuleka da Kanawa da Diamond Arrow Film Production. Auladi ta haifi Mandawari Enterpises da Yawawu Production.


Kungiyar Sarauniya ta haifi Sarauniya Films Gwammaja ta haifi Fatima Production da Usmaniyya Production 1da Zainab Production, har ila yau kuma Sarauniya Films ta barke gida biyu aka sake samun Sarauniya Films Sabon Titi dandago. Amge Video Treasury ta haifi Tumsy Video Club. Tumsy ta haifi Godiya and danhassan da Dukku Production. Godiya and danhassan ta haifi Kano West Link. Shi kuma Dukku Production ya haifi Ibrahimawa Production da H.R.B. da dan Fodiyo da S.K. Entertainment da Kwalle Production da Yoko Production da Surayya Production da Kajal Production da kuma Y.K. Soro Production. Dukku da Gidan Dabino su ne suka haifi Kainuwa Motion Pictures. Kajal ta barke gida biyu ta haifar da I.S.I da Jalingo Production. Su kuma Ibrahimawa sun haifi Movie World da Mai Shinku Communications. Garun Malam sun haifi 2 Effect. Nurul- Zaman Self Helf Group ta haifi Nurul- Zaman Association, Nurul-Zaman Association ita kuma ta haifi Martaba Dramatic Association da Al-halal Films Production Dramatic. Threater International (British Council) ta haifi Arewa Films Production. Soult To Soult su ne suka haifi Home Alone, Home Alone sun haifi Hazzy da Arewa Rod & Still Movie da kuma U & A. Yakasai Production Centre Ltd. ta haifi Bamuya Cinerama. Bamuya ta haifi Video Web da Almubarak da Yakaneesa. Kabko Vedio Texjel ta haifi Smart Star.


Daga shekara 1995 zuwa ta 2000 sai da kamfanonin shirya finafinai suka haura 120, wadanda suke da rijistar kungiyar masu shirya finafinai ta jihar Kano, baya ga wadanda ba su da rijista. Yawan kamfanonin ya dada taimakawa wajen jawo rikicc-rikicc tsakanin su kamfanonin, inda ya haifar da kungiyoyin masu irc-ircn wadannan sana'o'i don ko a samu mafita daga ire-iren wadannan matsaloli. Haka kuma an samu kamfanonin da suke hada hoto da tace finafinai da kade-kade da bushc-bushc da bayar da hayar kayan aiki da kuma fasahar aikin.


Bincike ya tabbatar da cewa kamfanin Dukku Production ne ya fara kafawa da yin fim din camama a Kano, har ya shigo da su Ciroki da dandugaji da Katakore da Yautai a cikin finafinansa. Har ila yau shi ne mutum na farko da ya shigo da Ibro cikin birna ya sanya shi a fim dinsa mai suna An Ki Cin Biri.

Bayan haka kuma, kamfanin Dukku Production ne ya haifi ’ya’ya da yawa, wato daga jikinsa aka fi samun kamfanoni masu yawa, masu rijista da kuma marasa rijista wadanda suka yi suna a ma’aikatar shirya finafinai ta Kano da Katsina da Kaduna da kuma Yobe.

Wasu kamfanoni kamar Iyan-Tama da Ibrahimawa da H.B. da Dambazau da Godiya and danhassan da Zik da I.S.I da Mazari Film Mirage da Yoko Production da Sarauniya Films Gwammaja, sun so kafa wani babban kamfani mai suna Film Pick amma sai ya ci karo da shatale da cin dunduniya daga wasu bangarori na 'yan fim wadanda ba a saka su a cikin tsarin kafa wannan kamfani na Film Pick ba, sannan su kan su sun samu matsalar cikin gida wadda ta dabaibaye su har sai da kamfanin ya kwanta dama (mutu).

Bunkasar Finafinan Hausa:
A tsakanin shekarar 1998-2001 a nan ne shirin fim ya yi tashin gwauron zabi ko kuma tashin gishirin Andiris, domin an yi kiyasin cewa a kullum akwai mutane masu hada-hadar fim din Hausa sama da 2000, saboda haka finafinan suka yi ta fita kamar saukar ruwan sama, a duk sati sai fim kamar goma ya fita kasuwa. Hukumar tace finafinai ta kasa ta bayar da kiyasi a shekarar 1995 an shirya finafinai guda 200 kacal a duk fadin Nijeriya. A shekarar 1999 kuwa an shirya finafinai 490. A shekara ta 2000 kuma an yi guda 650, daga cikinsu 192 na Hausa ne. A shekarar 2001 an yi finafinai 1030, sannan a 2002 zuwa watan Agusta an yi finafinai 510, guda 193 daga ciki na Hausa ne. Har ila yau kuma hukumar ta bayar da kididdigar cinikin finafinan da aka yi na Naira Miliyan dubu shida da Miliyan arba'in da biyar (6,450,000.000). A wannan lokaci ne masu shirya fim din Hausa suka dinga gasar sayen motoci kamar gyada, wasu suna sayen filaye suna gina gidaje sababbi, wasu suna yi wa nasu na da kwaskwarima, wasu suna tafiya Makka don sauke farali. Wasu kuma suna zuba jari a wata sana’ar daban. Mata ma suka shiga sayen filaye da gidaje da gwala-gwalai da kayan adon jiki da na daki, wasunsu suka kauracewa cin abincin gida sai na otal-otal, da ci da shan kayan kwalam da makulashe na gwan-gwani da kayan shafe-shafen jiki, wasu kuma suka durfafi yin aure ka-in-da-na-in. Daga nan fa sai aka yi ta samun ka-ce-na-ce da sa-toka sa-katsi a tsakanin masu shirin fim da al'ummar gari da malamai da hukumomi da masu kula da al'amuran yau da kullum da kuma masu katsalandan (’yan gaje-gani), duk aka taru aka yi wa ’yan fim caa, wannan har ya sa hukuma (gwamnati) ta dakatar da yin fim a Kano ranar laraba 13/12/2000, zuwa wasu ’yan watanni, har sai da aka kafa hukumar tace finafinai ta jihar Kano, sannan aka daga musu kafa, tare da dokoki masu tsauri, na hana rawar kada nono da kwankwaso da dai makamantansu. Wani abu kuma game da nasarori shi ne yadda ‘yan wasa mata sama da arba’in suka yi aure.

Ko su kansu majallu masu bayar da labarin ’yan fim sun bayar da tasu gudummawar gwargwado wajen yayatawa da kururutawa da yadawa da tallatawa da kuma sanar da duniya cewa Hausawa sun tsunduma cikin sana’ar fim ka-in-da-na-in, wanda haka ya sa har wasu sassa na duniya wadanda ba su san ma Hausawa suna yin wannan sana’a ta fim ba suka sani. Sannan ’yan fim suka samu damar tallata hajarsu ta hanyoyin wadannan mujallu.
Duk dai a tsakanin shekarar 1998-2001 baki daga sassa daban-daban na Nijeriya da Afirka da ma kasashen jajayen fata kamar Indiya da yammacin Turai suka shigo harkar fim din Hausa. Kadan daga cikin finafinan da baki suka dauki nauyin shiryawa su ne:

Wasiyya da Bi-manic, na Ba’indiye wanda kamfanin Ace-J Ventures suka shirya. dan' Adam Butula da Macijiya da kuma Jamila, na Ibo (Inyamiri) wanda kamfanin Iyke more Investement Ltd. Suka shirya.

Jan Kunne, na Hukumar Kiwon Lafiya mai zaman kanta ta kasar Amurka USAID, wanda kamfanin 2 Effect suka shirya, a karkashin jagorancin Dr. Olofemi, na hukumar ‘Family Health International of Nigeria’.

Uwargida da Albarka da kuma Mai Arziki, na Bayarabe wanda kamfanin Y Films In-corporated suka shirya.

Marainiya ’Yar gurguwa na Bahaushen Ghana mazaunin Zango, wanda Zango Production suka shirya.

Kukan Kurciyana na Bahaushen Ghana daga birnin Accara, wanda kamfanin Silver Line Films In conjunction With Badamasi In-corporated suka shirya.

Masoyiyata (Titanic) na mutumin kasar Kamaru, wanda kamfanin Ashu Media suka shirya.
Wasu ’yan kalilan daga cikin kungiyoyin addinai ma ba a bar su a baya ba, domin kungiyar ’yan’uwa musulmi da ta Tajdid da kuma cocin Ecow duk sun shirya finafinai kamar guda goma sha uku, ga su kamar haka:

§ Kungiyar ’yan’uwa sun shirya
§ Abin Mamaki
§ Mace Saliha
§ Rayuwar Aure
§ Tarbiyya
§ Karbala

Duk a Kano aka yi su. Sai

§ Mary Ko Maryam?, wanda aka yi a Funtuwa
§ Abokan Tsira, wanda aka yi a Tudun Iya
§ Hallayya, wanda aka yi a jihar Bauchi
§ Islahi, wanda aka yi a jihar Katsina
§ Mafita, wanda aka yi a Kankiya
§ Hasken Rayuwa, wanda aka yi a jihar Nasarawa
§ Ma’auni, wanda aka yi a jihar Kaduna.
§ Su kuma ’yan kungiyar Tajdid reshen jihar Kano sun shirya wani fim mai suna Tafarki.
§ Su ma cocin ECOWAS sashin Hausa reshen Kano sun shirya wani fim dinsu mai suna Miji Nagari.

Tun tuni gwamnati take kokarin ta hana shigo da finafinan kasashen waje amma ba ta cim ma nasara ba, sai a ruwan sanyi masu finafinan Hausa suka yi maganin wannan matsala, babu kuma wanda ya sa su. Sannan masu sana’ar fim sun samar wa da matasa maza da mata aikin yi, wannan ba karamin nauyi ne masu sana’ar fim suka dauke wa gwamnati ba, domin hakkin duk wata gwamnatin kirki ce ta samar wa jama’ar kasa aikin yi. Kasuwar masu harkar dab’i ta bude wajen buga kwalaye da fastoci da kum sitika. Masu kwamfutoci sun dada samun aiki na buga labarai da tsara fastoci. Su kuwa masu kamfanonin kade-kade da tace finafinai aiki ya yi musu katutu ana gosulo har sai an bi layi na tsawon wasu kwanaki. Masu sayar da kasakasai sun dada bunkasa, suna ta bude rassan shagunansu a wurare daban-daban, sannan sun mallaki gidaje da motacin hawa da karin aure. Masu mujallu sun samu sana’ar yi inda suke samun abin sawa a bakin salati su da ma’aikatansu da kuma iyalensu. Ita kanta gwamnati ta dada samun hanyar kudin shiga, domin duk fim din da zai fita kasuwa sai an biya kudi an duba shi a Abuja, sannan a zo Kano a biya a duba, ga kuma harajin da ake karba daga masu shiryawa da bayar da umarnin fim da ’yan wasa da masu sayar da kasakasai da masu bayar da haya da masu gidajen kallo na bidiyo da silima.

Wasu Daga Cikin Matsalolin Masu Shirya Finafinan Hausa
Matsalolin da masu shirya finafinan Hausa suke fuskanta tun daga lokacin da suka fara yin sana’ar har zuwa wannan shekara ta 2003:

§ Jahiltar Mene ne Fim
§ Rashin Ingantattun Kayan Aiki
§ Rashin Dandamalolin Shirya Fim
§ Rashin Wadatattun Kudi a Harkar
§ Babu Masu Zuba Jari
§ Rashin Kwararrun Ma'aikata
§ Rashin Bambanccwa Tsakanin Wasan Dandamali da Wanda Ake dauka a Kyamara
§ Rashin Fahimtar Kasuwa
§ Rashin Fahimtar Hanyoyin Nuna Finifinai a Gidajen Kallo
§ Rashin Sanin Dokar Kasa
§ Cin Dunduniya Daga Hukumomin Gwamnati
§ Aringizon kudi a Harkar Fim (kan tawaye)
§ Rashin Adalcin Hukumomin Tace Finafinai
§ Soke-soke daga Malaman Addini da ’Yan Katsalandan
§ Barazanar Karya Tattalin Arziki Daga Dillalan Kasakasai
§ Masu ci da Gumin Wasu (barayin zaune)
§ Kwaikwayon Finafinan Kasashen Waje (Satar salo)
§ Masu Kallo
§ Kwararowar Kananan ’Yan mata Da Matane Aure Cikin Harkar Fim
§ Mujallu Masu Bayar da Labaran ’Yan fim
§ Kungiyoyin Addinin Musulunci
§ Kamfanoni Masu Zaman Kansu
§ Masu Hannu Da Shuni
§ Hadin Gwiwa
§ Rashin Kame Kai

Jahiltar Mene Ne Fim:
Mutanenmu sun jahilci mene ne fim, abin da kawai suka dauka wasa ne kamar yadda ake kiransa, ko kuma don a samar da abin nishadi, alhali ba haka abin yake ba, shi ya sa ma aka yi ta samun matsaloli tsakanin marubuta littattafai da masu mayar da shi fim, kamar yadda aka yi a cikin shirin Alhaki Kuikuiyo wanda kamfanin Filaps suka shirya, marubuciyar (Balaraba Ramat) ta ce ba a yi mata daidai ba. Haka ita ma Bilkisu Salisu Ahmad Funtuwa ta yi kuka da kamfanin Mandawari Enterprises cewa littafinta na Sa'adatu Sa'ar Mata ba a yi shi daidai ba. A cikin Bakandamiyar Rikicin Duniya da In Da So Da Kauna ma an yi ta ire-iren wadannan takaddama tsakanin daraktan fim din marigayi Aminu Hassan Yakasai da marubutan littattafan wato Ado Ahmad Gidan Dabini da dan’azumi Baba Chediyar ’Yangurasa. Saboda irin wannan rashin fahimta ne ya sa matan aure suna cikin gidajensu sai su rubuta wani labari da ya faru a zahiri tsakaninsu da mazajensu ko kishiya ko uwar miji ko danginsa, ta ce sai an mayar da shi fim, kwabo da kwabo, ba sauyi, irin wannan matsala ita ce ta sa ake yin finafinan ba tare da an yi hasashen wadanda ake son su kalle shi ba, da an yi shi sai ya tsaya a wani dan zagaye bai je ko'ina ba. Saboda rashin fahimtar fim sai aka shigo da raba fim kashi-kashi, wanda kuma ba haka ake raba fim din ba, domin ba lallai ne mai kallo ya samu dukkansu ba.

Rashin Ingantattun Kayan Aiki:
Saboda rashin ingantattun kayan aiki ne ya sa kashi casa'in da takwas 98% na finafinan da aka yi na Hausa suka kasance ba su da ingantattun hotuna da sauti, in kana kallo fim din yana rawa ko kuma kalar ta dinga daukewa, har ka kasa bambance launin mutumin na asali. Can kuma ga wani sauti na babu gaira babu dalili kana ji a gefi yana shigowa, saboda haka ne ma hukumar tace finafinai ta kasa ta gano kurakurai har guda saba’in da biyar a cikin finafinan da aka yi.

Babu Dandamalolin Shirya Fim:
Saboda rashin dandamalolin shirya fim sai ka ga finafinan Hausa guda goma duk a daki daya aka dauke su, kujeru daya gado daya labule daya da kwanukan cin abinci da tangaraye duk iri daye. sannan kuma irin daukar hotunan da ake yi a wannan fim din shi za ka gani a wancen, sai ka kasa gane wane fim kake gani, saboda abubuwan sun zo daya, kan-kan-kan.

Rashin Wadatattun Kudi A Harkar:
Shirin fim abu ne da yake bukatar makudan kudi da kuma masu aiwatar da aikin masu yawa, domin yawancin finafinan Hausa ba a ba su hakkinsu don haka idan aka zo maganar gidan mawadaci ba lallai ne ka ga wadatar ba, haka kuma idan aka zo daurin aure, sai ka ga ’yan mutanen ba su fi a kirga su ba, ko kuma a ce taron siyasa ko fadar sarki, kai ga dai abubuwa nan sunan barkatai. Ire-iren wadannan abubuwa suna taimakawa wajen hana fim din Hausa ya yi inganci.

Babu Masu Zuba Jari:
Zuba jari a harkar fim ya kasu kashi uku, akwai zuba jari da daukar nauyi da kuma hadin gwiwa. Zuba jari shi ne ka zuba kudi ko basira ko dukiya ko kuma kayan aiki, ire-iren masu zuba wannan jari suna sa ran cin ribar kudi. Masu daukar nauyi kuwa su ma suna zuba duk wadannan abubuwa da muka ambata amma ba don su ci ribar kudi ba suna da wata manufa ta yada shi wannan fim da kuma tsawon lokacin da zai dauka ana yayinsa, wata kila sun kera wata na’ura ko tallata wata akida wace suke son nan da wasu lokuta ta yi tasari ga masu kallon.

Hadin Gwiwa:
Hadin gwiwa shi ma ana iya samun riba ta kudi ga duk bangarorin biyu ko mai fim din ya samu riba ta kudI, daya abokin hadin gwiwar kuma zai samu ribar sa ne ta hanyar tallata hajarsa ko akidarsa ko kuma su duka biyun su yi shi don samun ribar tallata haja ko akida. Akwai kuma wani hadin gwiwar, misali jarumi ya sanya riga ko hula na wani kamfani, kamfanin ya biya shi ladan tallata masu rigar da za a yi, don haka shi mai fim din zai iya cewa sai jarumin ya biya shi ladan nuna rigar da za a yi a fim din nasa don haka sai su yi wata sabuwar yarjejeniya tsakaninsu babu ruwansa da abin da kamfanin rigar ya biya shi. Don haka ma ake samar da ’yan tsakani wato masu daidaita 'yan wasa da kamfanoni masu son su tallata wata hajarsu, su kuma su dan samu nasu kamashon. Akwai kuma manajojin 'yan wasa, wato masu yi musu kimar abin da za a biya su. Sannan kuma akwai masu tallatawa da kururuta 'yan wasa da ma'aikata da kayan aiki don masu shirya fim su neme su. Amma babu ire-iren wadannan mutane a hakar fim din Hausa kwatakwata.

Babu Kwararrun Ma'aikata:
Ba mu da kwararrun ma'aikata tun daga kan marubuta da 'yan wasa da masu ba da umarni da masu shiryawa da masu sayarwa da masu nunawa a gidajen kallo, sai hana rantsuwa 'yan kalilan masu ’yan kwasakwasai na wata uku, shi ma a wani bangare na shirin fim, kamar daukar hoto ko kwalliya da tsara hotuna da dai sauransu. Lallai kuwa dole ne a samu rudani da matsaloli bila haddin, domin za ka ga mutanen da suka zo hakar fim yau sai ka tsince su sun zama masu ba da umarni, har wani tunkaho da kobobo za ka ji suna yi da cewa, ‘ba kat da akshin ba ne sun iya’.

Rashin Bambancewa Tsakanin Wasan Dandamali da Wanda ake yi a Kyamara:
Wannan rashin bambancewa tsakanin dandamali da kyamara ba karamar matsala ce ba domin a kullum in kai MANTAU ne babu sauyi, kullum kuma a cikin kowane fim sai ka nuna kai Mantau ne, ta wajen magana ko sa kaya ko dariya ko magana ce da ka saba yi wai sai dan wasa ya ce dole sai ya sake yin ta ba zai tafi sak ba sai ya yi kwalan kwanci, alhalin wajen ba na wannan abin ba ne. Yawancin 'yan wasan Hausa ba sa iya canja kansu da gaggawa sai ka ga kamanceceniya cikinsu, ta bangaren sa kaya ko wani abu daban. To wani lokaci kuma idan aka zo daukar fim idan abokin wasanka ba ya nan sai wasan ya tsaya cak alhali za a iya daukar kowanne shi kadai ba tare da dan’ uwansa ba.

Rashin Fahimtar Kasuwa:
Kasuwar fim tana da fadi a duniya amma saboda rashin fahimtarta sai suka taru suka yi dandazo a wuri daya wato bakin Bata wajen da ake sayar da kwali wanda wannan sayar da kwali babu shi a jerin kasuwancin fim na duniya, wadanda aka sani su ne:

§ hakkin mallaka na wani lokaci mai tsayi ko kuma kadan a dinga juya ana sayarwa zuwa iya lokacin da aka yi ka’ida.
§ bayar da dama a yi amfani da fim din don a tara mutane a tallata wata haja ko akida.
§ bayar da haya ga masu son nunawa a kafafan kallo
§ ba da haya ga kamfanonin kasashen waje masu son nuna finafinan kasashen waje don samun kudan shiga.
§ yin yarjejeniya da gidajen bayar da hayar kasakasai don a bai wa jama'ar gari su kalla bisa wani kayyadajjen lokaci.
§ sayar da hakkin mallaka na dindindin.
§ sabunta fim bayan wasu 'yan shekaru a sake sabon daukar wasu wuraren da canja tsarin hotunan don ya zama daidai da wannan zamani.

Rashin Fahimtar Hanyoyin Nuna Finafinai A Gidajen Kallo:
Da yawa daga cikin masu shirya finafinan Hausa ba su san yadda ake bi a yi nunin fim a silimomi ba, alhali kuwa akwai hanyoyi da yawa da dabarun da za su iya kawo kudi masu yawa, musamman ma ta hanyar na da ake kira primer show, wato nunawa ga hamshakan ’yan kasuwar finafinai da masu zuba jari da bankuna da kamfanoni masu kera na’urorin aikin fim da ’yan wasa da masu shiryawa, a bisa wani farashi mai tsada.

Akwai kuma nuni na bai daya a rana daya a lokaci guda a duk silimomin kasa ko jiha ko kuma gari, a farashi daya. Irin wannan nuni na primer daga shi ne ake shiga wannan kasuwa ta nuni bai daya. Babu shakka saboda rashin fahimta da kuma wayewa da yin haka shi ne yake hana masu finafinan Hausa bin wadannan hanyoyi.

Rashin Sanin Dokar Kasa:
Akwai doka da ta tanadar wa masu shirya finafinai wani dan kwaryakwaryan gatanci ta bangaren taimakawa yayin da duk za su shirya wani fim a karamar hukumarsu ko jiha ko kuma kasa baki daya. Akwai kudade da ake warewa don tallafa wa masu shirya finafinai na gida. Bayan kudin kuma kana iya neman duk wani abu da ya shafi kayan gwamnati wanda kake son ka yi amfani da shi yayin aiwatar da wani fim, amma masu shirya finafinan Hausa ba sa neman wannan hakki nasu, ko da yake kashi casa’in cikin dari na masu shirya finafinan Hausa ba su san ma da wannan tsari ba, su kuma kashi goman da suka san da irin wannan tsarin ba sa neman wannan tallafi daga gwamnatin.

Cin Dunduniya Daga Hukumomin Gwamnati:
Lokuta da dama wasu tawaye-tawaye da cin dunduniya daga hukumomin gwamnati ake samun su, misali, ka je neman wani abu da ya shafi kayan gwamnati wanda kake son yin amfani da shi a fim, sai ka ga kemadagas an hana ka bayan kuma dokar kasa ta ba ka hurumin samunsa. Ko kuma wanda zai sanya hannu a ba ka abin ya yi ta ja maka rai har sai lokacin amfani da abin ya zo ya wuce, daga karshe kuma a sanya hannu ko kuma a hana ka ma gaba daya (ihu bayan hari ke nan) ko kuma haka kawai ba gaira babu dalili a kirkiro wata doka a sanya muku don kawai an ga kuna samun riba ko wani abin daban makamancin wannan.

Aringizon Kudi A Harkar Fim (Kan-Tawaye):
Sau da yawa wasu masu shirya finafinai suna yi masu daukar nauyin shirya fim aringizon kudi yadda daga karshe ko fim din ya fito kasuwa da wuya a ci riba sai dai faduwa wanwar, shi ne ake cewa an yi wa mai daukar nauyin fim kan-ta-waye, misali idan za a kashe kudi N250,000 sai a ce N400,000 ko N500,000 za a kashe.

Rashin Adalcin Hukumomin Tace Finafinai:
Hukumomin tace finafinai na kasa da na jiha lokuta da dama suna nuna bambanci da son kai da rashin adalci a tsakanin masu shirya finafinai, misali fim din ka yana dauke da wani abu wanda dokar kasa ta ce bai kamata a sanya a kowane fim ba don gudun batanci ga wani bangare na kasar nan, sai a tilasta maka ka cire (musamman masu fin din Hausa), amma idan dan kudancin kasar nan (Nijeriya) ya zo da abu makamancin haka sai a bar shi ya fita kasuwa ba tare da an matsa masa cewa sai ya cire ba. Kai ko a hukumar tace finafinai ta jiha ma ana samu, wasu lokutan sukan rufe idonsu a kan wani fim din amma idon wani ya gitta sai su yi masa ca sai an cire irin wannan abin da aka kyale wani da shi.

Soke-Soke Daga Malaman Addini Da ’Yan Katsalandan:
Lokuta da dama malaman addini, suna yin mummunan fata ko addu’a ga masu shirya finafinan Hausa. An yi haka a Kano ba sau daya ba, ba sau biyu ba, a tarukan Mauludai da karatun tafsirai na watan azumi da kuma dandalin fatawa daga malamai. Haka su ma ’yan katsalandan suke yin ire-iren wadannan soke-soke. Masu kula da al’amuran yau da kullum suna ganin wannan ba ita ce hanyar gyara mai kyau ba. Idan an ga kura-kurai, to sai a nemi wanda ya yi abin a ba shi shawara da baki ko a rubuce da lallausan harshe ba mai zafi ba. Addinin Musulunci, addini ne na nasiha da wa’azi, Allah madaukaki ya yi umarni ga Annabi Muhammadu (S.A.W.) cewa “Ka yi kira zuwa ga hanyar Ubangijinka da hikima da wa’azi mai kyau”. Allah ya yi gaskiya.

Kwaikwayon Finafinan Kasashen Waje (Satar Salo/Fasaha):
Wata babbar annoba da ta fada wa masu shirya finafinan Hausa ita ce ta satar salon finafinan Indiyawa da Amerikawa da Turawan yamma da kuma ’yan kudancin Nijeriya. Kai hatta wakoki ma an shiga sato salon Indiyawa, abin dai ya zama babu basirar kirkira sai sata ta karara (fashi) ba boyayyiya ba (sane). Wai shin abin tambaya ma ga su masu irin wannan satar salo, ba sa tunanin cewa ba sai sun bar al’adunsu na gado ba sannan za su ci gaba? Idan kuwa suka ce sai sun bari za su ci gaba, to lallai akwai jan aiki da gwagwarmaya babba a gabansu a cikin wannan gomiyar karni da muka shigo.

Barazanar Karya Tattalin Arziki Daga Dillalan Kasakasai:
Akwai babbar barazanar karya tattalin arziki daga dillalan kasakasai wadda suke yi wa masu shirya finafinai. Wasu daga cikin ’yan kasuwar koda sun sayar da kwalinka ba za su biya ka kudin a jimlace ba sai su dinga ba ka su a tsintsinke kamar kudin sadaka, amma akwai dattijai a cikinsu wadanda da sun sayar da kwalinka za su biya ka kudinka yadda za su yi maka amfani, ko ma ka sake shirya wani fim din da su. Kai wani lokacin ma idan ba kwa shiri da su ko ka kawo kwalin naka ba za su buga kaset din su dinga sayar wa da masu bukata ba sai su boye shi, wai a dole sai sun karya maka tattalin arziki. Idan kuwa ka ga suna bin ka har ofis suna kawo maka kudi to fim din ka ya yi farin jini sosai, kamar dai yadda ake yi wa furodusan da tauraronsu yake tsaye a yanzu (Rabi’u Ibrahim, H.R.B.).

Masu Ci Da Gumin Wasu (Barayin Zaune):
Masu gidajen kallo na silima da bidiyo da masu bayar da hayar kaset ga masu kallo na gida sun jawo babbar asara ga masu shirya finafinan Hausa, domin ta wannan hanyar bayar da hayar kasakasai ko nuna wa a gidan silimomi ko bidiyo, ba karamin gibi ko kuma asarar miliyoyin Nairori yake jawowa ba, maimakon su bi tsarin da dokar kasa ta tanada ga mai son yin irin wannan sana’a ta nunawa ko bayar da haya, amma ina sai suka yi shakwalatin bangaro da abin, suna cin karensu ba babbaka. Kai yanzu ma abin har da matan aure sun shiga sana’a masu ci da gumin wasu ko kuma a ce barayin zaune. Da wuya ka je unguwa a cikin birni kai wani wajen ma har kauye sai ka iske matan aure suna bayar da hayar kasaikasai a kan kudi N10 zuwa N20.

Masu Kallo:
’Yan kallo suna da babbar matsala wajen sayen kasakasai domin ba duk dan kallo ne ya san fim din da ya dace da shi wajen kallo ba, a’a sau da yawa su dai su kalli fim ba sa kuma rarrabewa da barcin makaho, ma’ana shin abin da suke kallo mai kyau ne ko ko ba shi da kyau, mai ma’ana ne ko kuwa marar ma’ana ne. Lallai wannan ma babbar matsala ce ga masu kallon fim da kuma su kansu masu shiryawar.

Kwararowar Kananan ‘Yan Mata Da Matan Aure Cikin Harkar Fim:
Lokuta da dama kananan ’yan mata suna baro gidajen iyayensu ba tare da izinin iyaye nasu ba don kawai su zo su shiga harkar fim. Haka su ma matan aure masu sha’awar fim da ’yan fim, takasa-ta-Kano suke baro gidajen mazajensu su zo ganin masu fim daga nan kuma sai ka ji su a cikin fim, wasu ma daga nan auren nasu yake mutuwa gaba daya, su kuma tsumduma cikin harkar fim.

Wata babbar barazana da take fuskanto masu fim ita ce yadda wadannan ’yan mata suke bugewa da yawon bariki kuma da an kama su sai su ce su ’yan fim ne, alhali ma ko kyamara ba a taba hasko ta a ciki ba.

Rashin Kame Kai:
Sau da yawa idan ka ga ’yan wasa a wani yanayi, musamman ma mata, abin sai ya ba ka kunya idan kai mai sana’ar fim ne ko kuma mai son ganinsu da son sana’ar tasu ta ci gaba, sai ka ji ba ka so a alakanta ka da su ’yan fim din saboda ire-iren wadannan dabi’u da yanayi da suka samu kansu ko kuma suka sa kansu a ciki babu gaira babu dalili, sai don son zuciya wanda aka ce bacin zuciya. Abu na farko shi ne sanya sutura marar tsari irin wadda take zubar wa da mutum mutunci da yin maganganu barkatai marasa tsari da dacewa da bayyanar da rashin kunya ko da’a a gaban kowadanne irin jinsin mutune. Tafiya a kan hanya ana ciye-ciye da shaye-shaye a kan acaba ko kuma a kasa. Halarta da zama a wurare da ake aikata fasadi a bayyane, ko kuma tarewa kacokan a wata mattarar ’yan duniya. Duka wadannan abubuwa ba su dace da mutum mai daraja da kima a idon ’yan kallo ba, domin yin haka zai sa darajar da yake ko take da ita su zube wanwar. Masu iya magana dai suna cewa mutunci madara ne…

Mujallu Masu Bayar Da Labaran ’Yan Fim:
Mujallu masu bayar da labaran masu shirya finafinai, suna daga cikin wadanda suka taimaka wajen zubewar mutuncin sana’ar fim a idanun mutanen kirki masu mutunci sakamakon ire-iren labaran da suke bayarwa wadanda bai kamata a ce an bayar da su ga jama’ar gari ba, domin har yanzu ci gabanmu da wayewarmu a harkar fim ba su kai lokacin da duk wani abu na matsalolin da rigingimun masu shirya fim za a fade su ga jama’ar gari ba. Kuma su kansu mujallun ba irin su ya kamata a dinga yi a halin yanzu ba, idan muka lura dukkan mujallun na labari da kuma nishadantarwa ne, babu na kasuwancin fim din wato (Trade magazines), saboda haka karanta ire-iren wadannan labarai da mujallu suke bugawa sai wasu jama’ar gari suke dauka cewa fim ba shi da tsafta wasu ma sai suke ganin haramun ne ko kuma kafirci. Sannan su kansu masu mujallun suna sa son zuciya da rashin adalci da kuma bambance-bambance wajen bayar da labaransu, domin suna yin amfani da mujallun wajen cin zarafin wasu mutane (mace ko namiji) wadanda wata takun-saka ta shiga tsakaninsu. Masu iya magana dai sun ce mai zuwa yana kaba wata rana gun sa za a je a karba, kuma mai gado da katifa wata rana a karkashin gado zai kwana ko kuma a dandagaryar kasa.

Kungiyoyin Addinin Musulunci:
Wani babban koma baya da ake fama da shi game da kungiyoyin addinin musulunci na Nijeriya da kuma su kansu malamai da suke tafiya kasashen waje suna yiwo maular kudi da sunan za a taimaka wa addinin musulunci amma da sun karbo kudin sai ka ji bulunbukwi, ko kuma mu ce shiru malam ya ci shirwa, wato sun watsa kudin a ramin tellansu suna yi musu cin mummuke, sai ka ga suna gina tabka-tabkan gidaje a yi shuke-shuken furanin kallo, idan ka shiga gidan kai ka ci wata ’yar karamar aljannar duniya ka shiga, ka ga suna hawa motoci na alfarma, na gani na fada, sannan su dinga auro kyawawan mata jajazur kamar tsada, amma ba za su iya ware wani abu daga cikin kudin su bayar don a aiwatar da wasu finafinai da za su zama sun taimaka wa addinin musulunci ba. Sai dai su dinga tara almajirai suna ba su sadakar ‘yan kudade ko abinci, wato irin shinkafar nan da ake kira tatsotse kokuma wara, a wasu lokutan kuma gangami suke yi su tafi kauyuka su tara mutane a masallatai su dauke a kaset din bidiyo suna kai wa kungiyoyin addinin musulunci masu bayar da taimako a kasashen waje da sunan wai kudaden da ake ba su a nan suke kashewa. Daga nan kuma sai a dada karbo babban kulli (makudan kudi)
Tun tuni wasu kungiyoyi da ba na addinin Musulunci ba a kasar nan (Nijeriya) da kuma duniya baki daya sun ware dubban miliyoyin Nairori saboda masu shirya finafinansu su tallata addininsu. Mu kuwa namu sai dai su tafi kasashen duniya su ce a ba su taimakon tallafa wa addinin musulunci, alhali kuwa ba haka ba ne, ci da ceto suke da kuma gina kawunansu da ’ya’yansu, to, shin me ya sa namu kungiyoyin da malaman ba sa taimaka wa masu shirya finafinai, sai dai in an yi fim su fito a kafafen yada labarai su yi ta sukar su?

Masu Hannu Da Shuni:
Masu hannu da shuni ba sa kulawa da lamarin masu shirya finafinan Hausa, musamman idan an je neman wani abu da ya shafi harkar fim, amma su ne a kan gaba wajen saya wa matansu da ’ya’yansu domin su samu abin gani a gidajensu, amma a hadu da su a babaka sana’ar abin ya gagara.

Kamfanoni Masu Zaman Kansu:
Kamfanoninmu ba sa son bai wa masu shirya finafinan Hausa tallace-tallace, ko kuma su karbi hayar fim din don su nuna a gidajen talbijin, su ba su kamasho, inda yin haka daidai yake da yadda suke ware mukudan kudade su yi talla ta wata hanya.
Bugu da kari kuma, akwai wasu hukumomi da dama wadanda suke taimakawa wajen samun matsaloli a harkar fim din Hausa amma saboda karancin lokaci ba za a zurfafa bayani a kansu ba, ga jerin sunayensu kamar haka:

§ Hukumomin bincike na Nijeriya
§ Hukumomin adana tarihi da al’adu
§ Hukumomin ilmi
§ Hukumomin ’yan yawon shakatawa
§ Tsarin tafiyar da harkokin finafinai da al’adu na Nijeriya

Wadannan hukumomi ba sa iya taimakawa harkar fim alhali suna da mahimmiyar rawar da za su taka amma sun yi shiru, kuma sun soke ’yan kudadensu a lalitarsu, suna yi wa mutane muzurai a dole ga hukumomi masu yin aiki, bayan ga wani wawakeken gibi sun bari a aikin nasu wanda ya kamata su cike shi.

§ Masu shirya Fim
§ Marubuta
§ ’Yan wasa
§ Rashin Bincike Kafin Aiwatar da Shiri

Har ila yau kuma wasu daga cikin masu shiryawa da rubutawa da ’yan wasa ba su da wata alkibla ta kirki a cikin wannan sana’a, wato komai suka yi su a wajensu daidai ne matukar za su samu kudi su bukatarsu ta biya, ba sa tunanin gaba da kuma baya, wato wane sakamako zai biyo baya na alheri ne ko na sharri, zai bata tarbiyya ko zai gyara, duk ba sa la’akari da wannan. Sannan ba sa yin kyakkyawan bincike a kan wata matsala da suka dauka za su yi fim a kanta

§ Gidajen talbijin masu zaman kansu na gida da na makwabta
§ Baki ’yan kasashen waje
§ Jami’an kula da shige da fice na kasa

Wani abin takaici shi ne yadda jami’an kula da shige da fice na Nijeriya ba su damu da tsare wa masu fim hakkinsu ba, za a iske ana ta fasa kwaurin finafinan Hausa zuwa wasu kasashen waje amma babu mai cewa kanzil. Su kuma masu tashoshin talbijin masu zaman kansu na gida da makwabtanmu suna ta nuna finafinan Hausa a bagas ba tare da sun biya mai mallakar fim din hakkin nunawa da suke yi ba. Su kuwa baki ’yan kasashen waje sun zo garinmu sun fi mu rawa, domin su ne kanwa uwar gami wajen cin dunduniyar masu shirya finafinai na gida saboda irin shigo da bakin finafinai barkatai da suke yi wadanda suke taimakawa wajen kawo koma-bayan na gida.

Kammalawa:
Ko ma dai yaya lamarin fim yake akwai nasarori da matsaloli masu yawan gaske wadanda idan an tashi fadar su sai dai a takaita don ba za a iya bayyana su gaba daya ba, amma ga bisa dukkanin alamu matsalolin sun fi nasarorin masa shirya finafinan Hausa yawa matuka da gaske sai dai in ba a zurfafa bincike ba. Kuma sana’ar fim sana’a ce da take dauke da mutane masu yawan gaske wadanda suke cin abinci ta hanyarta, wadda inda za a tsaya a inganta ta a kyautata ta a tsabtace ta a tarbiyyantar da ita a kuma musuluntar da ita, mun tabbata za a ji dadinta, jama’ar gari da malamai da gwannati da masu kudi da masu kallo za su rike ta da hannu biyu, har su shige ta ba tare da fargaba ko tsoron bacin suna ko tarbiyya ba. Wani abu muhimmi a cikin wannan sana’a wadda masu ita ba su damu da shi ba shi ne hadin kai da taimakekeniya a junansu, gaskiya wadannan abubuwa sun yi karanci a wajen masu sana’ar fim, haka kuma kame kai shi ma suna da karancin sa musamman mataye ’yan fim, domin idan aka lura da ire-iren suturu da suke kwalliya da su za a ga akwai sauran rina a kaba, mutumin da yake da’awar koya tarbiyya amma ya kasa yin shigar sutura ta masu tarbiyya, ko kuma a aikace-aikacensa na rayuwarsa ta zahiri wato na yau da kullum ba a ganin ire-iren tarbiyyar da yake nunawa a cikin finafinansa sai dai akasin haka, aikata ire-iren wadannan abubuwa suna taimakawa wajen rage musu daraja ta kowane fanni. Su kuma shugabanninsu ya zama wajibi gare su su dinga sanya ido don tsawatarwa ga mabiyansu wajen aikata duk wani abu marar kyau domin kare martabar sana’ar tasu. Su kuma manya a harkar su dinga yin abu na dattako da kamala da kuma kame kai, domin an ce inda saniyar gaba ta sha ruwa a nan ta baya za ta sha. Sayyadina Ali, Allah ya yarda da shi yana cewa:

“Idan kana cikin wani al’amari,
To ka kasance a cikinsa”.

Shi kuma mai Ta’alimi cewa ya yi:

“Dukkan wani al’amari na daukaka akwai wahalhalu,
Sai dai daukakar mazaje ita ce juriya”.

Wani mawaki mai suna dahiru Musa Jahun Bauchi, cewa ya yi:

Mai son a ce da shi wane,
Sai yai hali irin wane,
A yi koyi da shi da tarbiyya.
Ko an ki dole a yarda,
In shari’a akwai shaida,
An kare a daina jayayya.
Yaro kamar makaho ne,
Shi babba ai majayi ne,
Na amana da nuna tarbiyya.

Kamar yadda masu sana’ar fim suka sani ne, wannan sana’a tana cikin tsaka mai wuya babu kuma mai tsamo ta daga wannan hali da ta shiga sai su masu sana’ar wadanda suke samun abin sa wa a binkin salatinsu, idan kuma ba su yi mata gata ba to babu makawa za su wayi gari su ga wannan sana’a ta durkushe saboda sun yi mata kisan mummuke da kansu, Allah ya kyauta.
Kafin mu kammala wannan takarda ya kamata mu dubi wani abu wanda muke ganin kamar ba a damu da shi ba, wato tunawa da marigaya ’yan fim da masu taimaka wa harkar fim wadanda suka riga mu gidan gaskiya, wannan abu ne mai kyau da ya kamata a ce masu sana’ar fim suna yin sa a lokuta mabambanta domin ta haka ne za a dinga nuna wa na baya cewa wane fa ya yi wani abu muhimmi wanda ya kamata a dinga tunawa da shi ana yi masa addu’a, wannan zai sa ’yan baya su dinga koyi da ire-iren kyawawan ayyukan wadancan marigayan ko su ma wata rana bayan ransu za a iya tunawa da su. Muna rokon Allah ya gafarta wa dukkanin ’yan’uwanmu musulmi, mazansu da matansu wadanda suka riga mu gidan gaskiya, ya sa Aljanna ce makomarmu baki daya, amin.

Manazarta:
Tarjamar Ma’anonin Al’qur’ani Mai Tsarki. Fassarar Malam Abubakar Mahmud Gumi Ta’alimul Muta’allimi. Al’imamu Burhanu Al’islami Al’zarnuji, Maxaba’ar Mashhadu-Al-Husaini, Alqahira.


Mast, Gerald; 1971. A Short History of The Movies: New York: Pegasus a Division of The Bobbs Merrill Company, Inc., Publishers Indianapolis.


Robb, Scott H.; 1979. Television/Radio Age Communications Coursebook: New York: Communications Research Institute.

Uyo, O. Adidi; 1987. Mass Communication Media: Classifications and Characteristics: New York: Civiletis International.

Sound Basic Science Series-Book II: Singapore: SEP International Privet Limietd. 1988.

Achievements of The Federal Ministry of Information and Culture, 1985-992: Lagos: Federal Ministry of Information and Culture. 1992.

Hedgecoe’s, John; 1992. Complete Guide To Video: London: Collins & Brown Limited. 1993.

National Film and Video Censorship Board Decree. 1995. Film & Video, Nigeria’s Authoritative Film & Video Journal Vol 3 no 1: Jos: Nigerian Film Corpration.

James. C. Ademola; 1996. The Challenges of Film and Video Censorship in Nigeria: Lagos: National Film and Video Censorship Board. 1997.

The Need For a New Direction in Nigerian Film And Video Industry: Abuja: National Film and Video Censorship Board.

Haynes, Jonathan; 1997. Nigerian Video Films: Ibadan: Kraft Books Limited. 1998. The Impact of Video Films on Children and Adolescents in Lagos State. Abuja: National Film and Video Censorship Board. Jos.

Abdul-Mumini Yusuf Dashar; 1998. Harkar Kasuwanci a Musulunci: Jos: Launi Press Ltd.

Abubakar, Ayuba T.; 2001. Maitama Sule danmasanin Kano: Zaria: Ahmadu Bello University Press Limited.

NCAC, Tapping Nigeria’s Limitless Cultural Treasures: Lages: National Council For Arts & Culture.

Gidan Dabino, A.A.; 2001. Gudummawar Finafinan Hausa Game da Addini da l’ada: An gabatar da Wannan takarda a Bikin Makon Hausa na 23 Wanda Kungiyar Hausa ta Jami’ar Bayero ta shirya, a Tsakanin 5 zuwa 8/1/2001.

Mujallar Finafinai; Mumtaz ta 2, Fitowa ta Musamman: 2000. Kano: Gidan Dabino Publishres.
Mujallar Finafinai; Mumtaz ta 3: 2001. Kano: Gidan Dabino Publishres.

2002. Film & Video Diractory in Nigeria: Abuja: National Film and Video Censorship Board.

Sabo, Auwalu Muhammad; 2003. Furodusa da Ayyukansa: An gabatar da Wannan Takarda a Taron Gwaji na Kara wa Juna Sani na Duniya: An Gabatar da ita a dakin Taro na SEP, Kano, Ranar 14/6/2003.

Hambolu, M.O; 2003. Perspectives on Kano-British Relations: Kano: Gidan Makama Museum Publication.

Hirarraki da Mutane Masana
Hira da Umar Sheik Muhammad, ranar 10/5/2003.
Hira da Shehu Inuwa Iliyasu, ranar 24/5/2003.
Hira da Masta Idi (Cana), ranar 24/5/2003.
Hira da Kabiru Maiwalda, ranar 24/5/2003.
Hira da A.A. Kurawa, ranar 5/6/2003
Hira da Murtala Sabi’u Muhammad, ranar 10/5/2003.
Hira da Auwalu Muhammad Sabo, ranar 11/5/2003.
Hira da Hamisu Lamido Iyan Tama, ranar 11/5/2003
Hira da Khalid Musa, ranar 5/6/2003
Hira da Dr. Umar Faruk, ranar 15/6/2003.
Hira da Shehu Masa, ranar 2/7/2003.
Hira da Muhammad Balarabe Sango II, ranar 15/6/2003.
Hira da Mu’azzamu Boss, ranar 15/5/2003.
Hira da Abdullahi Zakari, ranar 2/7/2003
Hira da Umar Sabo Katakore, ranar 2/7/2003.
Hira da Tijjani Abdu (Asase), ranar 8/7/2003.
Hira da Idris danzariya, ranar 10/6/2003.
Hira da Adamu Isa, ranar 10/6/2003.
Hira da Abdulmunafi Sani, ranar 2/7/2003
Hira da Alhaji Garba Muhammad Shayabo (dansanda), ranar 8/7/2003.
Hira da Adamu Sani, ranar 8/7/2003.
Hira da Adamu Yusuf Balantiya, ranar 10/7/2003.
Hira da Umar Bawa Dukku, ranar 30/7/2003.

No comments: