Monday, May 28, 2007

Ta Leko Ta Koma: Jaridu Da Mujallun Hausa - Ina Mafita?

An Gabatar Da Wannan Takarda a Babban Taron Kara wa Juna Ilmi Na Shida Kan Harshe Da Adabi Da Al’adun Hausa Wanda Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayero, Kano ta shirya a Ranakun 12 Zuwa 15 Ga Watan Disamba, 2004.

Gabatarwa:
“Ga alama dai tun da aka fara yin rubuce­-rubuce a kasar Hausa, kafin karni na ashirin, ba a kago sarrafa jarida ko mujalla ba ko don wayar da kai ko kuma don sadar­wa a tsakanin mutanen wurare. Watakila dai wasikun da suka yi ta gilmawa cikin Larabci da Hausa, rubutun Ajami a tsakanin malamai da sarakuna na wurare daban-daban sun wadatar da bukatun sadarwa a wannan lokacin. Sai dai abin ya fi ba da mamaki idan aka fahimci cewa su wadannan kalmomi na jarida da mujalla asalinsu kalmomin Larabci ne wadanda suke nufin labarai da bayanai wadanda ake rubutawa ko ake bugawa cikin warkokin takardu, su fito da wani tsa­yayyen suna da aka ba jaridar ko mujallar a wani kayyadadjen lokaci, amma a jere a jere, misali kullum-kullum, ko mako-mako, ko sau biyu a wata, ko a wata-wata, ko sau hudu a shekara, ko kuma a shekara-shekara. Ko da a cikin rubutun boko ma ba a fara tsara jarida ana bugawa ba sai a cikin wannan karni na ashirin, bayan an bude makarantun ilmin zamani a larduna, an sami isassun masu iya karanta Hausa cikin rubutu sannan ne jaridun Hausa suka fara bullowa, har suka zo suka habaka, wadansu suka bata bayan sun yi dan zamani kadan, labarinsu ma ya shige duhu. Saboda haka za mu ambaci wadanda Allah ya nufe mu da samun labarinsu ne kawai” (Yahaya, 1988).

A wani bayanin kuma an ce “A kasar Hausa akwai rubuce-rubuce wadanda suke kama da jaridu da mujallun zamani, wadanda suke kunshe da labaru da wasiku da hikayoyi da shagube da ra’ayoyi da siyasa da mulki da kimiyyar magunguna da tattalin arziki da kuma zaman iyali. Wadannan rubuce-rubuce an yi su cikin harsuna uku, akwai Hausar Ajami da Fulatanci da Larabci, akwai kuma wadanda ake hada harsuna biyu ko ma ukun gaba daya, sai dai suna zagayawa a tsakanin Malamai da Sarakuna da mabiyansu ne kawai. Wadannan rubuce-rubuce ana kiran su kundaye” (Yakasai, 2004).

Babban burin wannan takarda shi ne ta nuna irin kwan-gaba-kwan-baya da jaridu da mujallun Hausa suka yi ta samu tun daga shekara ta 1932 zuwa yau. An yi kokarin bayyana dalilan da suke jawo ire-iren wadannan matsaloli. Sannan an bayar da shawarwari dangane da hanyoyin da za a bi don kare wannan muhimmin aiki na samar da mujallu da jaridun Hausa daga tabarbarewa.

Ba zai yiwu a bayyana kwan-gaba kwan-baya da mujallu da jaridun Hausa ba dole sai an tuna baya wanda aka ce shi ne roko, sannan a yi waiwaye adon tafiya game da shi kansa aikin jarida da kuma samuwar jaridu a Nijeriya ta Arewa. Wannan zai taimaka a fahimci bayanin gwari-gwari, karatun yankan jaki.

Ta Leko Ta Koma:
Bahaushe na asali ko kuma wanda ya fahimci Hausa sosai idan aka ce masa ta leko ta koma, kai tsaye abin da zai zo zuciyarsa shi ne, wani abin alheri ya doso ka gadan-gadan har ka kusa samun sa sai ya kubuce. Ko kuma ka sami wani abin alheri, ga shi ya zama naka, amma sai wani tsautsayi ya ratso ka rasa shi. Ire-iren wadannan abubuwa kuma su yi ta faruwa lokaci-lokaci. A dunkule ana nufin a dinga samun abubuwa suna kubucewa. Wannan shi ake nufi da ‘Ta Leko Ta Koma’.

Aikin Jarida:
Aikin jarida yana daya daga cikin kafafen sadarwa ga jama’a masu yawa a lokaci guda. Aikin ya samo asali ne tun lokacin da dan’adam yake kokarin sadarwa ga dan’uwansa mutum. Mutane ba za su iya rayuwa ba tare da sun cudanya da juna ta hanyar ilmantarwa da fadakarwa da kuma nishadantar da juna ba. Aikin jarida abu ne da yake tattare da kowacce al’umma, kuma wata hanya ce tsararriya da ake bi domin isar da sako ga daidaikun mutane ko masu yawa ba tare da wani tarnaki ba. Babu shakka aikin jarida ya dade a cikin al’umma amma kuma ba su fahimci cewa aikin jarida ne ba. Tun tuni, mun dade a kasar Hausa muna da tsarin isar da sako ta hanyar yekuwa ko shela da sankira yake yi domin fadakarwa ko sanarwa ko kuma nusarwa ga mutane ko ilmantar da su dangane da wani muhimmin abu da ya shafi rayuwarsu. Akwai kuma sakon kan-ta-kwana, wanda sarkuna suke yi. Irin wannan aike na sarakuna ne wanda suke yi zuwa wurare a kan doki. Irin wannan yekuwar (shela) da sakon kan-ta-kwana da kundaye da kuma kuma takardun da ake likawa a dandalin jama’a suna daga cikin tushen aikin jarida na farko a kasashen Afrika, musamma ma kasar Hausa.

A yau aikin jarida da muka fi sani ko fahimta ita ce tsararriyar hanyar da ake bi domin ilmantar da jama’a ko fadakar da su ko nishadantar da su ta hanyar amfani kafofin yada labarai na dab’i da kuma na lantarki kamar rediyo da talbijin da fim da bidiyo kuma wadanda suke tallafa musu, kamar kamfanonin dillancin labarai da ma’aikatun yada labarai masu zaman kansu da na gwamnatoci da kuma sassan hulda da jama’a.

Samuwar Jarida A Arewacin Nijeriya:
Tun cikin shekarar 1859 aka fara samun jarida a Nijeriya inda wani Rabaran Henry Townseed ya fara buga jarida ta farko mai dauke da harsuna biyu (Turanci da Yarbanci) mai suna Iwe Irohin.

Jaridar Hausa ta farko da aka fara bugawa a Arewa ta samu ne a shekarar 1932, wannan jarida ita ce ‘Jaridar Nijeriya Ta Arewa’ mai yawan shafuka 22, a lokacin ana sayar da ita sisi kuma a madaba’ar Gwamnati da ke Kaduna ake buga ta. Ita ma da harsuna uku ake yin ta: Turanci da Hausa da Larabci, a jere cikin shafuka tare da hotuna a wasu shafukan, kowane ~angare da sunansa, ta Hausa ‘Jaridar Nijeriya Ta Arewa’ ta Turanci ‘Northern Provinces News’ da Larabci kuma ‘Jaridat-Al-Nijeriya Al-Shimaliyya’.

Samuwar wannan jarida ya sanya aikin jarida ya dada fadada a Arewacin Nijeriya, saboda haka a shekarar 1939 aka yanke shawarar kago jarida don a rika yada ta lardi-lardi don a wayar da kan jama’a game da abin da ke faruwa a cikin kasa da kuma kasashen waje, musamman ma da yake a cikin wannan shekara ne yakin duniya na biyu ya ~arke, wannan jarida ita ce ‘Gaskiya Ta Fi Kwabo. A watan Janairu na 1939 aka fara buga ta, Editanta na farko shi ne marigayi Abubakar Imam, mataimakinsa kuwa shi ne Mr. Gilas. Ma’anar sunan jaridar shi ne gaskiyar da ake fada a cikinta, ta fi kwabon da za a saye ta. A shekarar 1941 ne aka bullo da wata jarida mai suna Suda don ta rika bayar da labarun yake-yake, musamman na kasashen waje.

Hukumar talifi ta jihar Arewa wato ‘North Reginal Literature Agency’ NORLA, an kafa ta ne a shekarar 1941, ayyukan hukumar sun hada har da shirya wadansu jaridu cikin Hausa da wasu harsuna domin amfanin larduna, kamar jaridar Zaruma don lardin Sakkwato da Himma a lardin Katsina da Gamzaki a Filato da Zumunta ta Bauchi da Bazazzaga ta Zazzau da Haske (ta farko) ta Neja da Ardo ta Adamawa da Albishir ta Borno da Sodangi ta lardin Kano. Akwai kuma wasu jaridu da ake bugawa don ’yan makaranta da sauran masu sha’awar karanta Hausa, Jaridun su ne Jakadiya da Aboki da Majalisarku, sai kuma mujallar Alfijir wadda take bayanin yadda ake gudanar da sana’a. A tsakanin shekarun 1953 zuwa 1959, lokacin da hukumar Norla take aiwatar da ayyukanta na rubuce-rubuce don wayar da kan jama’a, wadannan jaridu sun yi tashe, sai dai abin ban haushi ana rufe hukumar Norla su ma jaridun da mujallun suka kwanta dama.

Bunkasar Jaridu Da Mujallu A Arewacin Nijeriya
Jihar Arewa ta shiga halin ni-’yasu ta fannin jaridu sakamakon rufe hukumar Norla domin sai da ya zama babu wata jarida a Arewa in ban da Gaskiya Ta Fi Kwabo. Bayan wannan hali na ni-’yasu da aka shiga sai kuma harkar jarida ta dada bunkasa a Arewa, aka yi ta samun sababbin jaridu da mujallun Hausa. An yi jaridar Muryar Kano, ana buga ta da Hausa da Turanci, kamfanin Concord Press da ke Legos ne yake bugawa. A shekarar 1980 jaridar Maganar Kano ta bayyana, kamfanin Sarkimedia ne suke buga ta, kuma ta yi farin jini sosai ga jama’a, amma ba ta yi nisan kwana ba, du-du-du shekararta biyu ta yi ta ce ga garinku nan. A dai wannan shekarar jaridar ’Yancin Dan’adam ta fito da kuma takwararta ta Turanci wato ‘Nigerian Standard’ dukkansu mallakar jihar Filato ce. A shekarar 1984 sai aka daina jin Duriyarta.
Marigayi Cif M.K.O Abiola, mai kamfanin jaridar Concord ya fara buga jaridar Amana a cikin shekarar 1981, ana yin ta ne a Zariya, ita ma sai aka wayi gari babu amo ba labari. A dai cikin wannan shekara ta 1981 gwamnatin jihar Kano ta kafa kamfanin Triump, har suka fara buga jaridar Albishir ta Hausa da kuma ta ajami mai suna Alfijir. A shekarar 1985 wadannan jaridu aka hada su waje daya, bari daya Hausa daya kuma ajami. Jaridar Zuma ta rarrafo a shekarar 1982, wadda kamfanin buga jaridar Telex yake bugawa, kuma ya samar da wata mujallar ta musulunci wadda ake kira Nasiha, mai bayar da bayani a kan harkokin addini da wasu matsaloli na yau da kullum. Mujallar Abokiyar Hira wadda kamfanin Albah suka fara bugawa ta fito sau daya a shekarar 1987 daga nan ba ta sake fitowa ba.

Kamfanin Soyayya Communication, sun fara buga mujallar Ruwan Zuma a shekarar 1991, mujallar tana bayar da labarai cikin hotuna ne, sannan dalilin kafa ta shi ne don a samar da abin karatu da kuma nishadantar ga masu karatu, ganin a lokacin mujallar Ikebe Super ta mamayi Hausawa. Da ta mutu sai editanta ya kafa wata mujallar mai suna Tambari, ta fito a shekarar 1992, ita kuma tana bayar da labarai da suka shafi ban dariya ne cikin zanen hotuna. A shekarar 1992 aka kafa mujallar Gwagwarmaya ta ’yan’uwa wadda kamfanin I.M. Publication da ke Zariya suke bugawa. Mujallar Matambayi ta zo a shekarar 1993, wadda ita ma take bayar da labaru masu dauke da hutuna zanen. Muryar Bebeji ta bayyana a shekarar 1994, wadda sashin Yada Labaru da Al’adu da ke Ma’aikatar Kyautatuwar Zaman Jama’a ta Karamar Hukumar Bebeji suke bugawa. Kamfanin Al-kalam Communication Ltd., Kaduna, sun fito da mujallar Tambari a shekarar 1995. Jaridar Muryar ’Yan kasuwa wadda kungiyar ’yan kasuwar Sabon Gari suke daukar nauyi, an fara buga ta a shekarar 1995, tana bayar da labarun harkokin kasuwanci. Jaridar Haske Maganin Duhu kuwa ta fito ne don ta fadakar da masu amfani da wutar lantarki, a shekarar 1998 aka fara ta, kamfanin Haske Maganin Duhu da hadin gwiwar Sashin Wayar da Kai Da Yada Labarai na Ma’aikatar Nepa da ke Shiyyar Kano suke bugawa. A shekarar 1999 {ungiyar Kula Da Kare Hakkin Dan’adam ta Nijeriya (Human Rights Monitor) wadda ke Jihar Kaduna suka fito da wasu mujallu guda biyar, Muryar Mata da Dimokuradiyya Mata da Lura Da ’Yancin Shari’a da Jinsi Da Addini da kuma Shaida. Akwai Kakakin Noa wadda Hukumar Fadakarwa Ta Kasa reshen Jihar Kano yake bugawa. An yi jaridu da mujallu kamar su Kakaki da Bagaruwa da Lokaci da Jagora da Sha Kallo da Matambayi da kuma Jakadiyar Unesco, wadannan jaridu da mujallu da aka bayyana, wasu an wayi gari babu su babu alamarsu, sun tafi halan-ya-halaku. Akwai kuwa wasu mujallun da jaridu da suke yin barci suna farkawa, amma wani lokacin in sun yi dogon gyangya]i har sai an yi zaton sun zarce lahira ne, sai a ga sun farka firgigit kamar ba su taba gyangyadawa ba. A haka aka yi ta samun kwan-gaba-kwon-baya na mujallu da jaridu musamman daga wannan shekara ta 1980, kawowa yau. Wadansu jaridu da mujallun sukan yi yayinsu su gama ba a san su ba, wasu kuwa sukan shahara a san su a ko’ina amma a karshe sai su mutu, kamar Nasiha da Fitila da A Yau da Amana da suke Kaduna da Alkalami da kuma Al’aharam da suke Kano.

Haka dai abubuwan suke ta tafiya, ana tafiyar hawainiya, yau idan wata sabuwar mujalla ko jarida ta fito sai ka ji wata ta mutu ko kuma ta yi dogon suma, abin dai za a iya cewa ga koshi ga kwanan yunwa ko kuma babu yabo ba fallasa. A yanzu akwai jaridu da mujallu masu bayar da labaran yau da kullum kimanin guda goma sha bakwai wadanda suke fitowa kowanne lokaci, akwai Almizan da At-tajdid da Gamzaki (sabuwa) da Sawaba Albishir (sabuwa) da Alfijir (sabuwa) da At-tatbiq da Bazawara da Gaskiya Ta Fi Kwabo da Manuniya da Magama da Sakon Zamfo da Za~i Sonka da Alfurkan da Alburhan da kuma Hantsi. Sannan akwai guda takwas masu fitowa jefi-jefi, kamar Adala da Ar-Risala da Al-Ihsan da Al’aqeedatus Sahiha da Haske Maganin Duhu da Taskira (sabuwa) da Jakadiya (Sabuwa) da kuma Dillaliya (sabuwa).

Mujallun ’Yan Fim Da Marubuta Littattafai
A bangaren masu shirya finafinai da marubuta littattafai, su ma ba a bar su a baya ba domin an samar da mujallu masu bayani game da masu yin wannan harka. Kamfanin Gidan Dabino Publishers, Kano, su ne suka fara buga mujalla ta farko a jihar Kano mai suna Zamani, wadda take bayar da labaru a kan masu yin wasan kwaikwayo da kuma marubuta, a cikin watan Yuli na shekarar 1994 aka fara buga ta. Wannan mujalla tunanin wasu fitattun marubuta ne masu sha’awar ci gaban harshen Hausa, mutanen da suka gudanar da ita su ne Aliyu Abubakar Aliyu da Bala Anas Babinlata da Dan’azumi Baba Chediyar ’Yangurasa da Balarabe Abdullahi Sani da Yusuf Muhammad Adamu da Sunusi Shehu Daneji da marigayi Aminu Hassan Yakasai (Allah ya jikansa) da Bashir Sanda Gusau da kuma Ado Ahmad Gidan Dabino. Wadannan mutane su ne musabbabin duk wata mujalla da take buga labrun da suka shafi ’yan fim da kuma marubuta, dalili kuwa saboda su suka fara aka gani har ake kwaikwayon su, domin daga cikinsu ne aka sami wadanda suka kafa mujallun Tauraruwa da Fim da kuma Mumtaz. Bayan haka kuma suna daga cikin mutanen da ake shawarta a harkokin kafa mujallu makamantan wadannan.

Kungiyar Wasan kwaikwayo ta Tumbin Giwa, Kano, ba a bar ta a baya ba domin ta yunkuro da tata mujallar mai suna Taskira, ranar daya ga watan Yuli na shekarar 1996. Mujallar Tauraruwa ta fito ne a watan Janairun shekarar 1999. Sai mujallar Fim da ta fito a watan Maris, 1999, dukkaninsu suna bayar da labarun ’yan wasan kwaikwayo. Sannan Garkuwa ta biyo bayansui a watan Janairu, 2000, ita kuma ta hada biyu labarun yau da kullum da kuma na ’yan fim. Ga kuma Nishadi da ta zo a watan Fabrairu, 2000. Mujallar Shirin Fim ta bullo ne a watan Nuwamba, 2000. Ita kuwa Mumtaz a watan Satumbar, 2000 ta fara fitowa. A cikin watan Satumbar 2001, aka kyankyashe mujallar Annuri. Mujallar Bidiyo kuwa ta iso a watan Yuli, 2001. A shekarar 2002 cikin watan Afrilu Duniyar Fim ta kutso kai, sannan mujallar Majigi ta zo kasuwa a watan Yuni. Can kuma sai ga Annashuwa ta danno kai a watan Yuni. Su ma suna magana ne a kan masu shirya finafinai. Marubuciya ta rarrafo a watan Nuwamba, 2001. Sai Wakiliya da ta bayyana a watan Agusta, 2002, su kuma sun fi ba da karfi wajen kawo labarun marubuta. Mujallar Bahaushiya ta iso a cikin shekara ta 2002, tana bayar da labaru a kan adabi da al’adu, amma tun da ta fito sau daya ba ta sake fitowa ba. Mujallar Indiyana mai bayar da labarun da suka shafi masu shirye-shiryen finafinai na kasar Indiya, ita kuma a shekarar 2003 ta iso kasuwa. Mudubi da Gidauniya sun iso kasuwa a cikin wannan shekara 2004, dauke da labarun ’yan fim, kuma ana buga su ne cikin hotuna masu kala gaba daya da kuma takarda mai kyalli.


Tun daga shekarar 1994 da aka fara buga ire-iren wadannan mujallu na wasan kwaikwayo da marubuta har zuwa wannan shekara da muke ciki 2004, wato shekaru goma ke nan, an kafa mujallu kimanin guda goma sha tara, amma guda goma sha biyar sun kwanta dama sai guda hudu ne suke raye. Sai dai kuma wadannan mujallu sun fara samun tagomashi ne a shekarar 1999, lokacin da aka fara buga mujallar Tauraruwa, daga nan ne kuma aka fara gasar buga ire-iren wadannan mujallu, don haka za mu iya cewa daga shekarar 1999 harkar ta karbu, saboda a lokacin ne kasuwar finafinan Hausa ta fara tashe sosai, masu kallo suna da sha’awar su sami labarun ’yan wasan da suke gani a cikin kasakasan bidiyo, kuma babu wata hanya da za su same su in ba ta cikin wadannan mujallu ba. Kuma masu buga ire-iren wadannan mujallu suna buga zafafan labarai masu dadi da marasa dadi wadanda suka danganci ’yan wasa da kuma marubuta littattafai, don haka masu kallo da kuma masu karatu sai suka mayar da mujallun suka zama idanuwansu da kunnuwansu, wadanda kuma suka zamar da su wasu kundayen dogaru ko kafa hajja game da labarun da suka karanta a ciki.

Mujallun Masu Wakokin Yabon Annabi (SAW)
Masu wakokin yabon Annabi (S.A.W.) su ma sun fara buga mujalla mai suna Muhammadawa, a cikin watan Satumba, 2002. Sannan Tsumagiya ta zo a watan Janairu na shekara ta 2003. Sai kuma wata mai suna Bakadiriya, amma ita ba bayanan mawaka take yi ba, tana bayar da labarun da suka shafi mabiya darikar Kadiriyya ne.

Mujallun Harkokin Mata
Mata ma ba a bar su a baya ba domin an samar musu da mujallu wadanda suke bayar da labarun harkokinsu. An yi ire-irensu da yawa, amma wadanda muka samu ga ni su ne kamar, Al’usra wadda ta fito a shekarar 1987. Sai kuma a shekarar 1993 aka sami wata ta bullo mai suna Mujahidah, wadannan mujallu biyu suna bayar da labarun da suka shafi mata ta fuskar harkokin addini. A 1999 an sami mujallu guda biyu Dimokuradiyya Mata da kuma Muryar Mata. Akwai kuma Kallabi wadda ta fito ranar daya ga watan Janairu na shekarar 2003. Sai kuma a cikin watan Fabrairu na wannan shekarar ta 2003, aka sami wata mai suna Dangin Nono ta bayyana. Su kuma sun fi mayar da hankali a kan harkokin yau da kullum da kuma siyasar mata.

Yawancin wadannan jaridu da mujallu da aka lissafa duk sun kwanta dama, wadanda suka yi dogon suma kuwa sai an yi da gaske za su farfado, domin in ba a yi sa’a ba daga wannan dogon suman za su zarce su mutu. Yanzu sai ’yan kadan ne daga ciki suke raye, kuma suke fitowa a kai a kai

A duba makala ta biyu a wannan Turakar, za a ga jerin sunayen wasu mujallu da jaridun Hausa masu fitowa kowane lokaci da wadanda matagugun mutuwa ya kama su suke fitowa jefi-jefi da kuma wadanda suka mutu murus. Jimlar adadin da muka samu a yanzu sun kai guda 120, 90 duk sun mutu, 22 su ne masu fitowa kowane lokaci, sannan guda 8 kuma suna fitowa jefi-jefi.

Rashin Tabbatar Mujallu Da Jaridu A Arewa:
Idan aka dubi dinbin jaridu da mujallun da suke fitowa a Arewa amma cikin dan kankanen lokaci sai a ga sun bace bat ba amo ba labari ko sun kwanta dama ko kuma suna shure-shuren mutuwa, abin dole ya bai wa mutum mamaki da rashin jin dadi da kuma shiga kogin tunanin me ya sa jaridun da ake kafawa a kudancin kasar na suke dadewa, wasu ma har sun kwashe shekaru masu yawa amma suna nan daram-dakau, namu kuwa na Arewa (musamman na Hausa) da sun taso sai su yi tashin gishirin andiris, ko kuma mu ce sammakon bubukuwa? Masu iya magana suna cewa da walakin goro a miya, kuma banza ba ta kai zomo kasuwa. Shin wane dalili ne ya kai fura zane.

Babu shakka kafa mujalla ko jarida aiki ne ja wanda kuma ba a sa ran riba a kurkusa, shi ya sa mutanen Arewa ba sa jure wuyarsa saboda ba su saba da kasuwancin da babu riba a kusa ba, sun fi ganewa da duka-dauka, ga-wuri-ga-waina, shi ya sa ko sun kafa jarida sai su watsar su koma sana’a mai riba kusa. Abin da muka sani ne jaridu da mujallu suna rayuwa ne ta hanyar tallace-tallace da suke samu, amma abin takaici sai ka ga ’yan Arewa sun ki bai wa jaridunsu talla (musamman na Hausa) saboda sun raina su, amma suna bai wa na kudu, wannan yana nuna yadda ’yan Arewa ba sa kishin jaridunsu, kuma suna daga cikin masu taimakawa wajen mutuwar jaridun, don haka in aka ce ’yan Arewa su ne suke kashe jaridu da mujallunsu da kansu ba a yi kuskure ba an yi daidai, amma don rashin kishi sai ga shi suna raya na kudu ta hanyar zuba musu jari wajen kafa su da ba su talla da kuma sayen jaridun kowane lokaci.

A ranar 4 ga watan Satumba, 2001, wani dan majalisar tarayya mai wakiltar Roni da Kazaure da Gwiwa da ’Yankwashi, ya sayi shafi guda a jaridar Thisday yana taya jama’arsa murnar bikin cika shekara goma da kafuwar jihar Jigawa, shin mutane nawa ne suka san da wata jarida Thisday a wadannan yankuna da ya fito? Shin mene ne hikimar yin haka?

Tribune ita ce jaridar da ta fi kowace jarida cin zarafi da ~atanci da kazafi da kage ga ’yan Arewa da kuma ita kanta Arewar, amma wannan jarida tana kan gaba wajen samun talla daga wajen ’yan Arewa masu rike da babban matsayi. A ranar 11 ga watan Satumba, 2001 wani kwamishina a jihar Zamfara ya sayi shafi a jaridar yana taya Gwamna Ahmad Sani Yarima murna. Karamar hukumar Zurmi ma ba a bar ta baya ba, ta sayi shafi mai kala tana tallata aikace-aikacen da take yi wa talakawanta. Wadannan kadan daga cikin misalai ke nan.

Vanguard da Guardian da kuma Punch duk kanwar ja ce kuma taron Kwara da Hama ne, ba su da wani buri da ya zarce su yi batanci da muzantawa da kokarin ganin bayan Arewa amma don rashin kishi na shugabanninmu da ’yan siyasa da masu kamfanoni, ba su da jarida ko mujallar da suke bai wa talla fiye da ire-iren wadannan jaridu.

Matsalolin Da Jaridu Da Mujallun Hausa Suke Fuskanta

Akwai manyan matsaloli kamar guda bakwai wadanda suka zame wa jaridun Arewa musamman na Hausa dabaibayi. Ga su kamar haka:

  1. Masu kudi (masu zuba jari)
  2. Masu bayar da tallace-tallace
  3. Ma’aikatan jaridu da Mujallu
  4. Gwamnati
  5. Jama’ar gari (masu karatu)
  6. Dillalai
  7. Tsarawa da kuma Dab’i

Bari mu dauke su daya bayan daya mu ji yadda aka yi suka zama matsala.
Na farko, masu kudi su ne suke da hali ko karfin zuba jari don a bude kamfanonin buga jaridu da mujallu amma sun ki mayar da hankali wajen daukar sana’ar da muhimmanci don suna ganin ba mai kawo riba da wuri ce ba.

Har ila yau kuma, mafi yawan masu son kafa jaridu da mujallu suna kafa su ne ba da dorarriyar manufa ko akida ba, yawanci manufar siyasa ce ta dan kankanin lokaci, duk lokacin da suka cim ma burinsu ko akasin haka shi ke nan, ko kuma aka rushe harkokin siyasa, to su ma sun rushe ke nan.

Na biyu, talla yana daya daga cikin abubuwan da ke taimaka wa wanzuwa da bunkasar jaridu da mujallu ko kuma mu ce shi ne kashin bayan rike jaridu da mujallu a kowace nahiya ta duniya, amma abin takaici masu kamfanonin da ke Arewa ba sa bai wa jaridu da mujallun Hausa tallace-tallacensu domin ba su dauke su da muhimmanci ba.

Na uku, ma'aikatan jarida, laifukansu suna da yawa, daga ciki akwai rashin hadin kai da hassada da keta da nuna fifiko da danne na kasa da son kai da rashin iya tattali, babu shakka wadannan abubuwa sun yi gida sun tare a harkar aikin. Wannan dabi’a wata annoba ce da ta fada wa kusan ilahirin ma'aikatan jarida na Arewa. Ba na jin tun daga lokacin da aka fara buga jaridu da mujallu a Arewacin Nijeriya, a shekarar 1932 zuwa yau an samu 'yan jaridu kwararru guda biyar da suka hadu suka kafa gidan jarida mai zaman kansa kuma ya ci gaba da dore.

Yawanci sun gwammace kowa ya kafa tasa. Idan kuma har an samu an yi hadin gwiwa ana aiwatar da ire-iren wadannan sana’o’i, to karshe dai a rabu uwa kuturwa kaka mayya.Wannan kuma yana daya daga cikin abubuwan da suke sawa jaridu da mujallu ba sa yin karko da inganci da kuma dauwama. Har ila yau akwai tsagwaron son kai da ra'ayi a gidan jaridar da mutum daya ya kafa. Wani lokaci kuma akan samu wasu kalilan daga cikin masu hannu da shuni su kudiri aniyar kafa gidan jarida domin alkida ko kuma domin wata boyayyiyar manufa, ko da kuwa ta mece ce. Amma abin takaici, bayan komai ya kammala, sai jami’an gudanarwar jaridu da aka danka wa amanar gudanarwa su ba da dama son rai ya dakile kwakwalwar tunaninsu da hangen nesansu, su karkatar da dukiyar da ake gudanar da jaridar ga wata takaitacciyar bukata tasu, wanda dole daga karshe sai hakan ya zamo sanadin durkushewar gidan jaridar. In ba haka ba kuma shi kansa mai gidan jaridar da kansa, idan ya ga bukatar da yake nema ta samu sai ya shiga facaka da kudin har sai ya rusa kamfanin ba mai kwabarsa.

Na hudu, Gwamnatocin jihohin Arewa suna da muhimmiyar rawa da ya kamata su taka wajen ganin tabbatuwar jaridu da mujallun Hausa a Arewa, amma abin haushi ba sa iya yin komai a kai game da tabbatuwar su sai ma taimakawa wajen kashe su da suke yi. A duk fadin jihohin Arewa guda goma sha tara da muke da su, ba za a sami jihohi biyar da suke da jaridu da mujallun Hausa mallakar Gwamnati ba. Ma’aikatun Gwamnatocin Arewa ba sa sayen jaridu da mujallun Hausa domin karantawa ko ajiyewa a ma’ajiyarsu kamar Dakunan karatu da Hukumomin Adana Tarihi da Al’adu da Ma’aikatun Yada Labarai, sun fi sayen na Turanci, don haka ma ba sa sa su a cikin kasafinsu na sayen jaridu da mujallu domin ba su damu da su ba. Bayan haka kuma wadannan jihohi ba kowace ce take bai wa jaridu da mujallun Hausa masu zaman kansu tallace-tallace ba illa hana rantsuwa ’yan kalilan daga cikiinsu. Kai wasu jihohin ma idan ka yi musu tallan ba sa biyan kudin sai dai ka yi musu Allah ya isa. A wasu jihohin kuwa Daraktoci ko sakatarorin yada labarai ne suke yin sama da fadi a kan kudin tallan da jaridun Hausa suka yi musu, idan ka zo ka matsa sai a yago maka wasu ’yan kudi a ba ka kamar wanda ya zo maula, ni ganau ne ba jiyau ba domin ta faru a kaina lokacin ina wallafa mujallar Mumtaz. A cikin watan Fabrairu shekara ta 2001 na yi wa karamar hukumar Tarauni ta Jihar Kano da karamar hukumar Buji da ke Jigawa Da karamar hukumar Ningi da ke Bauchi, har zuwa yau da nake gabatar da wannan takarda ba su gama biyan kudin ba. A cikin dai wannan shekara ta 2001 na yi wa Gwamnatin jihar Zamfara talla amma har kawowa yau ba su ba da ko kwabo ba. A cikin wannan shekara ta 2004 wata mujalla mai suna Manuniya ta fito har kuma ta yi wa Gwamnatin jihar Kano talla na shafi daya amma kudin sun gagara fitowa, sai dai in sun je a ba su kudin talla sai a ~uge da ba su kudin hawa mota su koma Kaduna. Abin dai da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa. Ana yin irin haka a ina jaridu da mujallun Hausa za su sami gindin zama?

Na biyar, jama’ar gari (masu karatun Hausa), mafiya yawa ba sa iya cire kudi su sayi jarida ko mujalla saboda matsin tattalin arziki, maimakon jarida sun gwammace su sayi wani abin. Sannan manyan ’yan bokonmu ba sa son karanta jaridu da mujallun Hausa, a ganinsu wannan koma baya ne a gare su ko kuma kauyanci, wannan ne ya jawo ’ya’yansu ma suke koyi da su. Bayan haka kuma an tabbatar da cewa Hausawa ba su da dabi’ar karance-karance. A kudancin kasar nan abin ba haka yake ba, talakawansu sun yi amanna da karanta jaridu da mujallu, suna iya fasa cin abinci su sayi jarida ko mujalla, saboda suna da dabi’ar karance-karance.
Wani abu kuma da aka gane shi ne rediyo ta fi karbuwa ga mutanen Arewa, kusan kashi casa’in sun fi sauraron rediyo, ga kuma saukin samuwa, shi ya sa suke ganin kyashin sayen jaridu da mujallu, sun manta cewa 'duk abin da aka rubuta yana tabbata, alhali wanda aka haddace, gushewa yake yi', kamar dai yadda ya zo a karin maganar nan na Larabawa. A koyaushe, masu karatu sun fi masu ji wayewa da fahimtar al'amura. Sannan kuma ci gaban kowace al'umma yana dogara ne da du}ufarta ga karance-karance. Idan kuwa haka ne mene ne abin tutiya idan aka kira al'ummarmu da 'al'umma marar dabi'ar karatu?

Na shida, dillalan jaridu da mujallu suna da babbar matsala, wasu lokutan ma cewa za su yi ba za su karbi jaridar ko mujallar ba, in kuma ma sun karba sai su cinye wa masu buga jaridu kudadensu idan sun kai musu talla, sai sun gama sayar da kayansu tsaf amma biyan kudin ya gagara, daga nan kuma idan dama masu buga jaridar ko mujallar ba su da wadatattun kudi sai harkar ta tsaya cak, ba gaba ba baya.

Na bakwai, rashin yin aikin mai kyau da inganci. Masu iya magana suna cewa ‘fuska ita ke sai da riga’. Lokuta da dama jaridu da mujallun Hausa ba sa samun kyakkyawan aiki, tun daga tsara rubutun ciki da jera hotuna da sanya launukan da suka dace a cikin rubutu.

Wadannan dalilai da ma wasu da ba a bayyana ba su ne suka sa duk mujallu da jaridun da suke bullowa in aka cire Gaskiya Ta Fi Kwabo, babu wadda ta kai tsawon shekara goma tana fitowa.

Ina Mafita?
Akwai takaici kwarai da gaske a ce har zuwa yanzu babu wasu isassun jaridu da mujallun Hausa a arewacin kasar nan, alhali duk wata dama da za ta iya samar da mujallu da jaridu masu ma'ana kuma na zamani, suna nan birjik. Misali muna da masu hannu da shuni, muna da masana aikin jarida da masana harshen Hausa da marubuta a fagage daban-daban da kuma abubuwan da za a yi rubutu a kansu wadanda suka shafi ilmi da fadakarwa da nishadantarwa da tattalin arziki da al’adu da wuraren yawon bude ido da shakatawa da sana’o’in hannu da kimiyya da fasaha da hada kai don yin magana da murya daya, sannan akwai neman kare daraja da martabarmu daga kallon hadarin kaji da ake yi mana da samar wa da jama’armu aikin yi. Bayan haka ga maganar tallata kamfanoni da masana’antu da aikace-aikace da sana’o’i, da dai sauransu.

Kamar yadda muka sani aikin jarida yana da mutukar muhimmanci a rayuwar kowane dan’adam a wannan zamani domin da shi za a iya yin juyin-juya hali a kowace kasa. Domin farfagandar jarida tana daya daga cikin hanyoyin da ta sanya Amurka take ganin ta kai matsayin da ta fi kowa karfi a duniya. Farfagandar ce ta sa har yanzu aka kasa kawo karshen zaluntar musulman Palasdinu da Yahudawan Isra'ila ke yi.

Da farfagandar jaridu ne galibin dattijan Arewa suka ga wajibcin dan kabilar Yarbawa ya mulki kasar nan a shekarar 1999, abin da a yau yake ci wa akasarin al'umma tuwo a kwarya. Idan haka ne, wane dalili ne ya hana aikin jarida samun tagomashi a Arewa balle har ya bunkasa ya kare darajarmu da ta jama’armu? Shin ma'aikata ne babu ko kuwa don an rasa masu zuba kudin ne ya sa muke ta yin kwance da kaya? Idan dai muna son mu fita daga wannan matsala ko kuma a dan sami sauki-sauki kadan, lallai sai mun yi jan aiki domin an ce ‘mai hali ba ya fasa halinsa, kuma mahaukaci ba ya warkewa sai dai ya sami sauki’, to lallai sai mun yi karatun baya ha]e da karatun ta-natsu.

Masu iya magana suna cewa ‘naka-naka ne ko ba za ya ba ka komai ba’. Ko mun ki ko mun so ba mu da inda ya fi Arewa, don haka ya wajaba mu tsaya kai da fata don ciyar da Arewa da kuma harshen Hausa gaba, musamman idan aka yi watsi da bambance-bambance aka hada kai aka kafa jaridu da mujallu, ta hanyar zuba jari na hadin gwiwa ba don neman riba ba, sai don kare kai da kuma Arewa da jama’arta baki daya. Kuma in an tashi nada jami’an gudanarwa a sami wadanda suka dace wajen jagorancin kamfanin, ba wadanda za su gurgunta shi ba. Mutanenmu da suke da kamfanoni su tallafa musu da tallace-tallace, da yin rubuce-rubuce masu inganci don ilmatar da jama’armu, ba rubutun bambadanci da fadanci don neman gindin zama ga wasu ’yan tsirarun mutane ba. Idan gaskiya ta zo a fade ta komai dacin ta, ba yin kage ga wasu wadanda aka raina ba. Jaridu da mujallu suna daga cikin hanyoyin bunkasa al’umma, don haka ya zama wajibi ne ga masu kudi da ’yan boko da Gwamnatocin jihohin Arewa su kar~i wannan harka da hannu bibiyu. Bayan haka sai mun sa hakuri da juriya da wahala da kula da hakkin kowa da yarda da kowane mai daraja a ba shi darajarsa sannan da kau da kawa-zuci. Su mujallu da jaridu in dai ana son karbuwarsu da dauwamarsu a Arewa, dole ne 'yan jaridu su rika tantance me masu karatunsu suka fi son karantawa. Wannan kwarai abin dubawa ne domin matsala ce mai zaman kanta a aikin jaridun arewacin Nijeriya. Farin jinin jarida, ya ta'allaka ne da fasali da rubuce-rubucen cikinta. Matukar ana so mutane su gane kullum su fahimta, to, dole ne a yi abin da zai burge su masu karatun ba wanda marubutan ne kawai zai birge su ba. Lallai akwa bukatar jama’armu su farfado daga suman da suka yi don abin ya wuce barci sai dai suma.
Gwamnatocin jihohin Arewa musamman arewacin arewa, su wajabta wa kawunansu buga jaridu da mujallu na Hausa mallakarsu, sannan su tilasta wa ma’aikatun gwamnati bai wa jaridu da majallun Hausa masu zaman kansu tallace-tallace kamar yadda suke bai wa na Turanci. Har ila yau kuma, Dakunan Karatu da Ma’aikatun Yada Labarai da Ma’aikatun Adana Tarihi da Al’adu su ma a wajabta musu sayen kowace jarida da mujalla wadda ake bugawa da harshen Hausa. Babu shakka sai mun tsaya da kafafunmu sannan za mu kai ga gaci.

Idan kuwa mun ki, to, kullum za mu yi ta yin da-na-sani da kuma fargar-jaji. Duk masu niyyar shiga wannan sana’a ta bude kamfanin jaridu da mujallu, su shige ta ba da takaitacciyar manufa ba, domin shiga harkar da takaitacciyar manufa ba karamar illa ce ba ga sana’ar. Kamar yadda mai Ta’alimi yake cewa:

“Duk wanda ka ga ya zama wani abu,
Da kokari ne ba da kaka ba (dangi)”.

Kuma ya kamata ’yan jaridunmu su zama masu kishin addini da al’adu da harshensu. Duk abin da aka san cewa abin ki ne, to wajibi ne a kawar da shi daga cikin rubuce-rubucen da za a sa a jarida ko mujalla domin kada a gurbata tarbiyyar mutane da al’adunsu nagari. Rashin bayyana gaskiya da kage ba shi da fa’ida, misali, idan aka nemi dan jarida ya rubuta wani abu game da fa’idojin mulkin damukaradiyya irin ta Turawa, wajibi ne ya fadi gaskiya, idan kuwa wani dalili ya sa ya kauce wa gaskiya, to ya zama mai batar da jama’a ta hanyar yada gurbataccen ilmi. Babu shakka Allah ya hana boye gaskiya, kamar yadda wannan aya take nunuwa:

“Kuma kada ku lullube gaskiya da karya,
ko kuma ku boye gaskiya, alhali kuwa kuna sane.”
(Suratul Bakara, aya ta 42).

Ya kamata mai rubuta ko mai sharhi ko bayar da rahoto ko kuma bayyana wani al’amari ya yi adalci ya kuma guji bata al’amura da gangan. Sau da yawa mutane suna cusa son rai a wajen rubuta wani bayani game da wadansu mutane domin kiyayya ko gaba.

Manzon Allah (S.A.W.) a wani Hadisi da Dabarani ya rawaito, ya ce:

“ Duk wanda ya fadi wani abu dangane da wani mutum
wanda yake karya ne domin kawai ya bata shi,
Allah zai sanya shi a cikin wuta har sai ta taushe maganganunsa.”

Lallai zai yi matukar kyau idan masu jaridu da mujallun Hausa suka kafa wata kungiya, sannan kuma su dinga yin taro a kai-a kai domin su dinga tattauna ire-iren matsalolin da suke addabar mujallu da jaridun Hausa, ta wannan hanya za a dan magance yawan mutuwar mujallu da jaridun. Sannan a yi wani gangamin wayar da kan jama’ar da suke ganin karanta jaridu da mujallun Hausa rashin wayewa ne ko kuma rashin ilmi ne kawai yake sawa a karanta. Bugu da kari, su kansu mutanenmu a dada wayar musu da kai wajen daurewa suna sayen jaridu da mujallun Hausa. Kamar yadda wasu mawaka na kasar Nijar suke cewa:

“Kai zabo mai kyawun zane,
Ka tuna zanenka na gado ne,
Komai ka yi ba zai goge ba”.

Lallai ’yan matan Matamaye sun fadi gaskiya a cikin wannan waka tasu. Har ila yau mu fadakar da mutanenmu don su kasance masu bincike da yawaita karatu don a dada gano hanyar da za a ciyar da wannan harshe na Hausa da kuma jaridu da mujallunsa gaba. Wani mawaki Muhammad dan Hassan dan Abdullahi ya yi wani baiti inda yake cewa:

“Ka kasance mai yawan nutsawa cikin neman ilmi,
Sai ka wayi gari ka zama kogin fa’ida”

Har ila yau akwai wani baiti da yake cewa:

“Shi ilmi yana daga gidan da ba shi da katanga,
Jahilci kuma yana rushe gidan girma da daukaka”.

Mai Ta’alimi a cikin wani baitin yana cewa:

“Dukkan wani al’amari na daukaka akwai wahalhalu,
Sai dai daukakar mazaje ita ce juriya”.

Don haka ya kamata mu zama masu juriya wajen ciyar da wannan harshe gaba ta hanyar aikin jarida, domin in muka dage wata rana sai labari. Kamar yadda Imamu Ashshairazi yake fada wa Imamu Shafi’i cewa:

“Shi kokari shi yake matso mini da abin da ya yi nesa kusa,
Sannan kuma shi yake bude dukkan wata kofa rufaffiya”.

Duk yadda muka kai ga kin harshenmu shi din ne dai namu kuma shi ne mai girma a gare mu, sannan shi ya cancanta mu girmama. Wani mawaki yana cewa:

“Idan ka girmama mai girma,
Sai ka mallake shi”.

Kammalawa
Kafin a kammala wannan jawabi, zai yi kyau idan aka dada tunasar da kowane Bahaushe a ko’ina yake a duniya cewa, wannan harshe namu abu ne mai girma, girmama shi kuwa shi zai kara masa girma da bunkasa, domin an ce, idan ba ka ganin darajar kanka babu mai ganin ka da daraja. Don haka wannan aiki ya shafi kowa da kowa (Bahaushe da mai son harshen Hausa). Shugabanni da masu kudi da gwamnatocin jihohin Arewa da sauran jama’a, kowa yana da irin tasa gudummawar da zai bayar gwargwadon iko, an dai ce hannu daya ba ya daukar jinka. Idan kuma mun ki sharar masallaci ba makawa sai mun yi ta rumfar kusuwa. Sayyadina Ali, Allah ya yarda da shi yana cewa:

“Idan kana cikin wani al’amari,
To ka kasance a cikinsa”.

Hakika akwai jan aiki a gaban duk wani Bahaushe ko mai son harshe Hausa, amma abu ne mai sauki in za mu zama masu adalci ba masu zalunci ba, sannan mu zama masu kwazo ba ragwanci ba. Har ila yau mu zama masu tattali ba almubazzaranci ba, a kan shi kansa harshen na Hausa. Kowa ya sha inuwar gemu bai yi kamar makogwaro ba. Sannan kowa rai ya yi wa da]i bai yi ya mai shi ba.

Akwai wani baitin waka da Ibn Ruumiy yake yi wa dansa da ya rasu, yayin da idanunsa suke zubar da hawaye. Ga abin da yake cewa:

“Kukanku yana warkarwa, Ko da ba zai dawo da shi ba,
Ku zubar da hawaye don an dauke muku dan’uwanku.

Duk wani mai kishin harshen Hausa yana kuka da hawaye a kan irin halin tasku da ni ’yasu da jaridu da mujallun Hausa suka samu kansu a ciki saboda sakaci da rashin kulawa daga masu harshen musamman ma wadanda suka yi zufin ilmi a kan wannan harshe. Amma duk da haka dole ne a ce da mijin iya baba. Gaba dai gaba dai harshen Hausa! Allah ya taimaki harshen Hausa da jaridu da mujallun Hausa da masu taimaka musa. Amin.

Manazarta
Tarjamar Ma’anonin Al’kur’ani Mai Tsarki. Fassarar Malam Abubakar Mahmud Gumi
Ta’alimul Muta’allimi. Al’imamu Burhanu Al’islami Al’zarnuji, Madaba’ar Mashhadu-Al-Husaini, Alkahira
Rasheed, Abubakar (2002) Jaridu Da Mujallun Hausa: Samuwarsu, Kafuwarsu da Rashin Tabbatarsu,
Mukalar da Aka Gabatar a Taron Bikin Cika Shekara Biyu Na Mujallar Garkuwa, Arewa House,
Kaduna.
Adamu, Yusuf. M. (2002) Print And Broadcast Media In Northern Nigeria. http://www.kanoonline.com/
Gusau, S.M (2002) Jawabin Bude Taro, an Gabatar a Taron Kolin Hausa Na Shekara-shekara Na Farko, Mai Taken: Matsayin Nazarin Hausa a Yau, Jami’ar Bayero, Kano.
Gidan Dabino, A.A, (1993) Gudummawar Adabin Hausa Ga Addinin Musulunci, Takardar da aka gabatar a taron kara wa juna sani na Dalibai Musulmi na Babbar Makarantar Sakandaren
Dawakin Tofa.
Sharifai, Hamisu Isa, (1997) Gwagwarmayar Da Ke Gaban Hausawa A Karni Na 21, Takardar Da Gabatar Da a Bikin Makon Hausa Na {ungiyar Habaka Hausa Ta Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya Da Afrika, Jami’ar Ahmadu Bello Ta Zariya.
Sulaiman, Sa’idu, (2002) Musuluntar Da Fannonin Ilimi: Sako Ga Murubuta, ’Yan jaridu Da ’Yan Wasan Kwaikwayo, Takardar Da Aka Gabatar a Taron Fadakar da Masu Irin Wadannan
Sana’o’i, a Jami’ar Byero, Kano.
Muhammad Dawaki Alhassan, (1983) Tsarin Addinin Gargajiya Kan Hausawa, An gabatar Tsakanin Dalibai Da Malamai Na Jami’ar Bayero, Kano.
Kafin Hausa, Abubakar Adamu, (1987) Ma’ana, Manufa da Makomar Wasu Al’adun Hausawa a Yau, Takardar aka Gabatar a Taron Kara wa Juna Ilmi na Duniya Kan Harshen Hausa da Adabi da Al’adu na Hudu, Jami’ar Bayero, Kano.
Gidan Dabino, A.A, (1995) Muhimmancin Marubuta a Cikin Al’umma, Takardar da Aka Gabatar a Bikin Kaddamar da Littafin Karshen Mai Zalunci, Koko, Jihar Kebbi.

Hira Da Mutane
Hira da Bashir Mudi Yakasai, Kano. Tsohon Dan jarida. Ranar 25 ga Watan Disamba, 2002.
Hira da Alhaji Magaji Dambatta, a filin Gyara Kayanka, na Rediyo Kano, Ranar 6 ga watan Janairu, 2003.
Hira da Muhammad Mu’awiyya, Editan Mujallar Manuniya, ranar 15/10/2004.
Hira da Yakubu Liman, Editan Mujallar Ruwan Zuma kuma Mawallafin Mujallar Tambari, ranar 12/11/2004.
Hira da Muhammad Usman (Sunusi Shehu), Mawallafin Mujallar Tauraruwa, ranar 5/10/2004. Hira da Badamasi Sha’aibu Burji, Editan Mujallar Matambayi, Mawallafin Jaridar Adala da Mujallar Concern, ranar 17/10/2004.
Hira da Sa’idu Muhammad Sunusi, Mawallafin Jaridar Zabi Sonka, ranar 9/11/2004.
Hira da Dr. Yusuf Muhammad Adamu, Malamin Jami’a, ranar 5/10/2004
Hira da Lawan Adamu Giginyu, Editan Mujallar Kallabi, ranar 5/10/2004.
Hira da Adamu Muhammad, Editan Mujallar Taskira (ta farko), ranar 24/11/2004.
Hira da Dr. Umar Faruk Jibrin, Malamin Jami’a, B.U.K, ranar 6/12/2004
Hira da Muhammad Danjuma Katsina Dan jarida, ranar 8/12/20004
Hira da Ibrahim Musa, Mawallafin jaridar Dillaliya kuma Editan Jaridar Almizan, ranar 8/12/2004
Hira da Kabiru Muhammad Asada, Mataimakin Edita na Jaridar Hantis, ranar 8/12/2004
Hira da Muhammad Lawal Maikudi, Mawallafin Jaridar Gamzaki, ranar 8/12/2004
Hira da Mansur Bawa Funtuwa, Editan Mujallar Ar-Risala, ranar 9/12/2004

1 comment:

Muhd Mutawakkil jumar galadima said...

Jazakallahu khair malam Allah ya Kara basira Da fahimta ameeen