Monday, May 28, 2007

Dabarun Rubuta Waka

Na Gabatar da Wannan Takarda a Taron Sanin Makamar Aiki Wanda Kungiyar Marubuta Ta Nijeriya Reshen Jihar Kano Tare da Hadin Gwiwar Hukumar Dakunan Karatu Ta Jihar Kano Suka Shirya a Dakin Karatu na Murtala Muhammamd, Kano. A Tsakanin Ranakun 1 Zuwa 2 ga Watan Yuli 2004.


“Malaminsu mawaki, sarkinsu mawaki, bayinsu mawaka, tsofaffinsu mawaka, samarinsu mawaka, mata mawaka, maza mawaka, sadaukai mawaka, matsorata mawaka, masu wayo mawaka, wawaye mawaka. Don haka a bayyane yake tasirin waka ba zai boyu ba a zukatan mutane, musamman ma wakokin da abubuwan da ke cikinsu mabayyana ne, kuma aka fahimci matsayinsu, musamman Larabawa wadanda su ne ahalin waka kuma danginta” Walidul A’azamiyyun.

Wani lokaci mutum yakan tsinci kansa cikin waka, ko dai ta wani mawakin daban, mai amfani da kayan kida ko mara kida ko kuma wadda ya kirkira da kansa. A bisa dabi’a ta dan ‘adam, wani hali ko yanayi ne yake sa shi ya dinga yin waka, (yana sane ko ba ya sane), shi ya sa wasu masana suke ganin kowane dan’adam mawaki ne.

A kasar Hausa mawaki yana da matsayi babba kamar yadda yake da matsayi a sauran al’umma, yana zama garkuwa ga jama’arsa da kare mutuncin jama’ar ko zuga su, su tashi su yi aiki nagari, kamar yadda mawaki yake kokarin kare wani shugaba idan wannan shugaban mai adalci ne ga jama’arsa. Misali Sarkin Zazzau Aliyu dan Sidi yana son ya bayyana irin kokarin tabbatar da mutuncin zaman jama’a da gujewa laifuka da Sarkin Musulmi Bello yake yi sai ya ce a cikin wata wakarsa:

“Wajen munkari in ya wuce sai sayin jiki wajen munkari,
Ka ce yana da fukafuki wajen zikiri ka gan shi ko da jan ciki.

A nan mawakin yana nuna matsayin Bello da mutuncinsa yadda har ya nuna shi Bellon yana da fukafuki na tashi in ya ga abin da Allah ba ya so don gujewa wannan abu. Amma wajen alheri ko jan ciki yake sai ya je don kwadayin aikata abin kirki. Abin lura a nan shi mawakin ba wai mutuncin Bello kawai yake karewa a nan ba, a’a har da jama’arsa baki daya, domin bisa ga al’ada idan shugaba nagari ne to, jama’arsa ma sai su zama nagari.

Manufar wannan takarda ita ce ta bayyana wasu dabaru da za su iya taimaka wa mai sha’awar rubuta waka da harshen Hausa, sannan kuma ta bayyana wasu daga cikin ka’idoji da ma’aunan rubutacciyar wakar Hausa wadda take da ma’aunin Larabci.

Gabatarwa:
Waka tsararriyar magana ce cikin hikima da basira, kuma ta bambanta da zance na yau da kullum. Aba ce wadda take kunshe da sako cikin zababbun kalmomi masu dauke da maganganu daki-daki cikin azanci da nuna kwarewar harshe. Waka tsararren zance ne mai tattare da kafiya wanda zuciya kan raya shi baki ya siffanta shi cikin zance mai balaga. Ibranawa da Yunanawa da Faranjawa sun bayyana cewa ”Waka wata aba ce da ke cikin kirazanmu sannan harshenmu ya fito da ita”. Harshen waka a bisa kansa cikakke ne duk da yakan kauce wa wasu ka’idoji na nahawu. Waka takan hau wani tsari nagartacce, mai daga hanlali a cikin wasu dunkulallun manufofi. Domin haka ana tsara ta ne a cikin layuka, ana yi ana daidaita tsayinsu ta amfani da kwayar sautin gabar karshen kalmar karshen layi. Haka kuma tana bukatar a dinga daidaita muryoyin layuka su dinga hawa da sauka ko faduwa daidai tsayin layukan da ake shiryawa. Dole ne waka rubutacciya ta dauki tsari na daidaito, ba ruwanta da tsari na bambanto.

Rubutacciyar waka ta samu ne a kasar Hausa bayan da aka kirkiro rubutun ajami daga harufan Larabci. Tarihin samuwar waka rubutacciya yana da alaka ta kut-da-kut da zuwan addinin musulunci kasar Hausa, sannan da iya rubutu da karatu cikin harshen Larabci. Duniyar fasahar Bahaushe da basirarsa kafin ya hadu da bakin al’ummomi ta amfani da hadda da kiyayewa ce da ka. Ashe ke nan, tsarin rubuta waka bakon abu ne a wajen Bahaushe. Rubutun ajami na Hausa da ake yi da bakaken Larabci da shi ne aka fara rubuta waka, musamman a lokacin, malamai da almajiran makarantun ilmin addinin musulunci ne suka fara wannan aiki. Bayan zuwan Turawa kuma da iya karatu da rubutun boko aka fara samun wata hanya ta rubuta wakokin Hausa cikin yanayin bakaken Romawa.

Abu ne mawuyaci ainun a ce ga lokacin da aka fara rubuta waka da Hausa, amma an samu wasu wakokin na Hausa da aka rubuta tun kafin jihadin Shehu Usman, irin ‘Jiddul-ajizi’ ta Malam Shi’itu game da Fikihu, da ta Wali Danmasani game da ‘Yakin Badar’ don haka masana sun yi ta karakainar tunani, kowane yana bayyana ra’ayinsa dangane da wakokin da aka fara rubutawa da kuma lokacin da aka yi su. Wasu manazartan suna ganin daga karni na 15 zuwa karni na 18 ne aka sami kanshi da alamu da burbushin rubutattun wakokin Hausa.

Ilmin Ma’aunin Waka:
Bincike ya nuna cewa mutum na farko wanda ya fara rubuta littafi a kan ilimin ma’aunin waka wanda da Larabci ake kira Arudhi shi ne Khalil Ibn Ahmad Alfarahidi Albasari, a karni na biyu. Marubucin ya rasu a shekara ta 174 bayan hijira daidai da 791 miladiyya. Amma tun kafin ya rubuta wannan littafi akwai mawaka da suke rubuta wakoki, ko da ya zo ya rubuta wannan littafi sai ya dace da ma’aunin ire-iren wakokin da suke yi tun dauri.

Dalilin da ya sa ya rubuta wannan littafi shi ne, Khalil ya yi kwadayin ilmi irin na Sibawaihi malamin Nahawu ko kuma marubucin Nahawu, sai ya fita yana kewaya Ka’aba yana rokon Allah ya ba shi baiwa ta ilmi, sai Allah ya yi masa baiwa ta wallafa littafin ilmin ma’aunin waka, Arudhi. A cikin littafin ne ya takaita waka a kan ma’auni goma sha shida.

Arudhi, wani waje ne da ke tsakanin Makka da Da’ifa a nan ne Khalil ya rubuta littafin shi ya sa ake kiran littafin da sunan wajen.

Fa’idar Ilmim Ma’aunin Waka:
Fa’idar ma’aunin waka shi ne, yana hana shigar wani ma’aunin waka cikin wani ma’auni, sannan yana hana waka karyewa da shigar wasu canje-canje da ba su cancanta ba, kuma yana bambancewa tsakanin waka da maganar baka.

Mene Ne Arudhi?
Arudhi wata sana’a ce wadda da ita ake sanin ingancin ma’aunin wakar Larabawa da rauninsa.

Tsarin Waka:
Rubutacciyar waka tana da tsari wanda ake son mai rubuta ta ya bi su. Tsarin shi ne, dole ne duk mawakin da ya tashi yin waka rubutacciya ce ko ta baka, tilas ne ya tabbata ya sami wani kari na musamman wanda ya gamsu da shi, yake kuma ganin wakar ta dace da ta hau shi, ta kuma ci gaba da shi ba canzawa har karshenta. Idan kuwa ya yi ta kara-zube, to ba ta da bambanci da zancen baka na yau da kullum ko kuma a kira ta ‘zube’. Haka kuma tilas ne wannan wakar ta zamanto tana da manufa, wato wani sako na musamman da take isarwa ga mai sauraron ta.

Ma’aunin Waka:
Ma’auni shi ne wasu kayyadaddun lafuza ko kalmomi da za a iya kira tubalai wadanda da su ne za a hada a tayar da ginin baiti na waka, ya zamana kuma ba a samu wani kari ko ragi ba a wadannan tubalan har zuwa karshen wakar. Wadannan tubala iri 16 ne; amma an samu yin amfani da 13 zuwa 15; kuma duk wakar Hausa mai ma’auni irin na Larabci da irinsu ake gina ta. Ga jerunsu kamar haka:

1.Dawil
2.Madid
3.Basid
4.Wafir
5.Kamil
6.Hazaj
7.Rajaz
8.Ramal
9.Sari
10.Munsarih
11.Hafif
12.Mukutalib
13.Mujtas
14.Mutakarab
15.Mutadarak
16.Mudari, shi ne wanda har yanzu ba a samu misalinsa ba.

Wasu Jigogi Da Ake Yin Waka A Kan su:
Akwai jigogi da dama wadanda ake shirya waka a kan su, a nan mun bayyana wasu daga cikinsu ne kamar haka:

Yabo: Mawaki yana yin sa ne ga wani muhimmin mutum mai
daukaka da daraja ko basarake ko mai dukiya don ya sami wani
lada.

Jihadi: Mawaki yana yin sa ne don kwadaitarwa ko kira ko zaburarwa
izuwa ga fagen fama don daukaka kalmar Allah.

Soyayya: Mawaki yana yin sa ne domin ya nuna abin da yake zuciyarsa
game da wata ko wani abu wanda yake so ko kauna.

Jarumta: Mawaki yana yin sa ne don ya nuna yadda wasu mutane suke
kasancewa musu dauriya da dagewa da gwagwarmawa da kuma
tarar aradu da ka a kan al’amuran su na rayuwa

Alfahari: Mawaki yana yin sa ne don ya nuna isarsa ko kwarewarsa
ko ta kabilarsa a kan wasu al’amura na rayuwa

Zambo: Mawaki yana yin sa ne don cin zarafi ko tozartawa ko
kaskantarwa ga wani mutum ko kabila.

Neman Uzuri: Mawaki yana yin sa ne don neman a yi masa uzuri a kan
wani abu da ya yi na kuskure.

Batsa (Gazalu): Mawaki yana yin sa ne don ya suffanta wasu sassa na jikin
mace, wanda a wasu lokutan sai ka dinga ganin mace
kamar tsirara take saboda yadda ake bayyana surorinta.

Ta’aziyya: Mawaki yana yin sa ne bayan wani mutum ya rasu, a
cikin wakar zai dinga bayyana kyawawan halaye da
dabi’u da irin kyakkyawan zaton da ake yi wa
mamacin.

Siyasa: Wakar siyasa ta kasu uku, akwai ta addini akwai ta kabila
da kuma ta jam’iyya. Mawaki yana yin ta ne don ya
bayyana ire-iren bambance-bambancen da ke tsakaninsa da
wanda ba siyasar su daya ba, da kuma irin gazawar da
wancan bangaren ya yi a wani fage wanda yake ganin in
da su ne ba haka za su yi abin ba.

Mene Ne Baiti a Waka?
Baiti shi ne cikakken zance wanda yake da nau’i-nau’i kuma yake karewa da kafiya. Ana kiran baiti daya mufradan wato (mara) ko yatiman wato (maraya). Baituka biyu ana ce musu Natfatan. Ana kiran baiti uku zuwa shida kid’atan wato wani yanki. Shi kuwa baiti bakwai zuwa sama ana kiransa kasidatan wato waka cikakkiya. Shi baitin waka yana da makoma guda biyu, layi na farko ana kiran sa sadaran na biyu kuma ana kiran sa ajuzan.

Ire-iren Waka:
Akwai ire-iren waka guda bakwai wadanda mawakan Hausa suka aro daga tsarin wakokin Larabci ta fuskar adadin dango a kowane baiti na waka. Ga su kamar haka:

-Gwauruwa
-’Yar Tagwai
-Kwar Uku
-’Yar Hudu
-’Yar Biyar
-Tarbi’i
-Tahamisi

Ga bayanin kowane daga ciki:

Gwauruwa:

Gwauruwar waka ita ce mai baiti dango dai-dai da babbar kafiya, wato amsa-amo guda daya. Misali:

Alhamdu lillahi mun samo fita hadari,
Wancena jan zamani da ka sa maza wadari,
Jama’a Musulmi ku ce amin mu zam shukuri,
Mun samu Sarkin Musulmi wanda yay yi fari,
Kun san ga dauri kirin muke babu mai fikiri,
Balle shi yaye duhu jama’a su sam sarari,

’Yar Tagwai:
Ita ce waka mai baiti dango bibbiyu da babbar kafiya (wato amsa-amo) guda daya. Misali:

Ni na zamo sarki a harkar so ku san,
Amma a yau na zam mariri gun ta.

Kwar Uku:
Waka kwar uku ita ce mai baiti uku-uku da karamar kafiya da babba daya. Misali:

Farkon wakata Ubangiji naka sawa,
Sarki mahallicci Ilahu ba shi gazawa,
Alkawarin Allah mai haka bai tabewa.

’Yar Hudu:
Waka ’yar hudu ita ce mai baiti hudu-hudu, da karamar kafiya uku da babba daya. Misali:
Duk masu zargi sui ta yi na dauka,
Ko za ta kai a tule ni ai mani duka,
A rididdige da wuka a kai ni a girka,
Ba za na saurara da son ki ba Dije.

’Yar Biyar:
Waka ’yar biyar ita ce mai baiti biyar-biyar, da karamar kafiya hudu da babba guda. Misali:

Ba ruwan mutuwa da milki,
Ko na mai damara da kaki,
Ko na mai rawanin ga Sarki,
In ta zo tilas ta dauki,
Ransu mulkin bai hana ba.

Tarbi’i:
Tarbi’i shi ne wakar da mutum biyu suka tsara mai baiti dango hudu-hudu. Ta yiwu mawakin farko ya yi wakar gwauruwa ko ’yar tagwai ko kwar uku, sai mawakin na biyu ya zo ya kara dango uku-uku a gwauruwa ko bibbiyu a ’yar tagwai ko daidaya a mai kwar uku. Amma misalin da aka fi samu shi ne na waka ’yar tagwai. Misali:

’Yan Musulmi kui mana hanzari,
A mu zam ka yabo gun Gafiri,
A mu gode badini zahiri,
Jama’ag ga Karimi Kadiri.

Tahamisi:
Tahamisi shi ne wakar da mutum biyu suka tsara mai baiti dango biyar-biyar. Ita ma ta yiwu mawakin farko ya yi tasa wakar gwauruwa ko ’yar tagwai ko kwar uku ko ’yar hudu, sai mawakin na biyu ya zo ya kara dango hudu-hudu a gwauruwa, ko uku-uku a ’yar tagwai, ko bibbiyu a mai kwar uku, ko kuma daya-daya a mai kwar hudu. Ga misalin da aka yi a kan ’yar tagwai:

Jan aiki ne a gabanmu duk,
Jawur yake ko mun san shi duk,
Jama’a sai ga mu a rabke duk,
Jahilci ya ci lakarmu duk,
Ya sa mana ankwa har wuya.

Salon Sarrafa Harshe A Cikin Waka:
Irin wannan salo shi ne ake kira Balaga da Larabci, wato nuna gwaninta da bayyana hikima, ta yadda mawakin zai tsuma mai karatu ko saurare. Kadan daga cikin wadannan hikimomi su ne kamantawa da sifantawa da jirwaye da kuma karangiya.

Kamantawa:
Kamantawa shi ne gwada wani abu da wani dangane da kyau ko daraja ko karfi. Misali:

Wa za ya jure idon da za ta kura masa,
Ko waiwayenki, karan kamar lantarki.

Sifantawa:
Shi ma wani nau’i ne na kamantawa, amma ya fi kamantawa karfi, domin kuwa abubuwan da za a gwada ba za a nuna wani fifiko ne a tsakaninsu ba, sai dai a nuna cewa ai dayan ne dayan kai-tsaye. Misali:

Fitila abin yaye duhu da bakin ciki,
Aljanna ce ke Jalla ya zabe ki.

Jerwaye:
Jerwaye kuma shi ne aro wata kalma a yi amfani da ita a wata ma’ana wadda ba ta asali ba domin kambama ma’anarta a mahallin da aka kawo ta. Misali:

Na bude shafin nan na babin zuciya,
Na bubbuga mai tambarin sunanki.

Na jefa gugata cikin guga dubu,
In samu dan kurbi cikin kaunarki.

Karangiya:
Wasa da kalmomi masu sauti iri daya a ji suna dukan juna, shi ne karangiya. Misali:

Saurin musaya Hausa mai ban haushi,
Sassake sauyi an sakar wa Hausa.

Rago rago rogo ragowa raga,
Rugugi rugurguza rungumar gasasa.

Wasu baitukan kuma cewa suke yi:

Kyakkyawa ce abar kauna,
Da Haliku yai halittarta,
Sidik sumul sosal sanbal,
Cicib cacas libis gwandas,
Inai maka dan bayaninta.

Gwadas gwadadas inmus tantsam,
Santal ga zara-zara dasdas,
Falau kicib damas dambas,
Sambaleliya abar sha’awa,
Kyan kyakkyawa abar kauna.

Hanyoyin Da Ake Samun Dabarun Rubuta Waka:
Dabara wata aba ce da Allah yake hore wa bayinsa wadda da ita ne suke amfani wajen gano wani abu sabo ko tabbatar da shi ko kirkirowa. Da ita suke amfani wajen sarrafa abubuwa na rayuwar yau da kullum. Dabara wata aba ce wadda halittu suke amfani da ita wajen warware matsaloli ko bukatunsu na rayuwa. Dan’adam yana amfani da dabararsa ya yi wani abu wanda zai bai wa mutane sha’awa da al’ajabi har su rika girmama shi. Bayan haka, ana iya fassara wannan kalma da cewa hikima.

Yadda mutane suka bambanta haka ma yadda dabararsu ta rubuta waka take zuwar musu a mabambanta lokuta da yanayi da kuma hanyoyi, don haka za a iya ayyana wasu hanyoyi wadanda da wuya marubucin waka ya kasa fadawa a dayansu kafin ya samu dabarar rubuta waka. Su ne kuwa:

i) Jibiliyya, hanya ce ta dabi’a wadda ake haihuwar mutum da ita. Mutum zai tashi da hikima da basirar tsarawa da rubuta waka, shi kansa ma zai ji waka tana zo masa ne kawai kamar wahayi. A irin wannan hanya mutum zai ji waka tana zo masa ne lokaci- lokaci, musamman a yayin aukuwar abubuwa.
ii) Koyo, hanya ce ta zama da wani wanda ya iya waka, musamman yi masa hidima wadda ta shafi waka kai tsaye. Shi ma irin wannan mutum sannu a hankali yakan kasance mawaki. Ko kuma mutum wanda aikinsa shi ne nazari da tsokaci a kan wakoki da dai makamantan wadannan misalai.
iii) Lalurar rayuwa ko tsananin wata bukata, wannan ma wata hanya ce da takan sa mutun ya tsara waka a rubuce. Bege ko ciwon soyayyar wani abu ko tsoron wani abu kamar talauci ko tsananin wata bukata kamar bukatar kudi da sauran abubuwa na juye-juyen zamani za su iya haifar da rubuta waka.
iv) Yawaita tunanin kusa da hangen nesa, da zabar kalmomi wajen shirya matanin waka mai nauyi. Inganta manufa ko sako a waka don su dace da hali da yanayin da ake magana. Har ila yau akwai kula da inda wakar za ta dosa dangane da muhalli da lokaci da mabambantan jama’a da shekarunsu.
v) Raba-danni, mutum mai son zama da wasu jinsin mutane kamar manazarta da mawaka ko kuma wanda yake son duniya ta yi da shi, ma’ana a san shi (mai neman suna)


Mai Rubuta Waka:
Mai rubuta waka yana a lullube da wata baiwa da take bubbuga daga hikima da kwarewa ko dandano ko ta larura ko ta koyo da kan cusa basirar tsara gunduwoyin zantuka su ta da waka.

Ya kamata marubucin waka ya siffantu da wasu halaye wadanda suka hada da ya zama ya koshi a fagen ilmi da kuma fahimta da kwarewa a cikin yaren da yake waka sannan ya zama mai tambaya, ko mai bincike, ko mai lura a sha’anin rayuwa. Ilmi yana daga cikin ginshikan rubuta wakoki, sannan a sami hikima da basirar zayyana abubuwa. Idan mutum ya mallaki wadannan siffofi ba dole ne sai ya rubuta waka da hannunsa ba, mutum yana iya ba da shifta wani yana rubutawa a madadinsa.

Abubuwan Da Suke Inganta Waka:
Akwai wasu abubuwa guda tara wadanda ake sa ran a ga sun tabbata kafin a hukunta cewa rubutacciyar wakar Hausa (mai ma’aunin Larabci) ta yi yadda ake son ta, ko da yake abu na karshe daga cikinsu bai zama tilas ba, sai dai samunsa cikin waka yana dada mata kwarjini da armashi. Su ma wadannan abubuwan son, ta yiwu ba su wani yake ganin abin da za a yi la’akari da shi ba, abin ya dogara ga irin ra’ayin kowane mai nazarin waka, (akwai bambancin ra’ayi)

1. Waka ta kasance tana da mabudi da marufi, wato a fara da yabon Ubangiji da Salatin Annabi, a kuma rufe ta da su.
2. Lallai ne a sami waka tana da ma’auni, ya kuma kasance yana daya daga cikin
ma’aunan wakokin Larabci guda goma sha uku, (wadanda muka bayyana a baya), wadanda aka tabbata an yi amfani da su a wakokin Hausa.
3. Waka ta kasance tana da amsa-amo wato abin da ake kira ‘kafiya’ da Larabci, wato a samu harafi iri daya wanda kowane baiti zai kare da shi. Ita wannan kafiyar ta kasu kashi biyu, akwai babba akwai karama. Babbar kafiya ita ce ta karshen baitin waka, karama kuma ita ce ta tsakiyar baiti, musamman ga waka mai dango biyar ko hudu.
4. Shirin baitocin kowace waka lallai ne ya kasance yana daga cikin dangogin waka bakwai, (wadanda aka bayyana a baya).
5. Ambaton jigon waka tun daga farkonta, wato mawaki ya bayyana abin da wakarsa za ta yi magana a kai a dunkule, bayan ya gama yabon Ubangiji da salati.
6. Warware jigon waka, wato ya ci gaba da tattauna abin da wakar ke magana a kai filla-filla har karshenta.
7. Ambaton sunan mawaki da lokacin da aka yi wakar, a layukan karshe na zubinta.
8. Salon mawaki ya kasance yana da karfi , wato bayaninsa ya zamana mai kama jiki da gamsarwa, babu kakale, yadda ba sai ya wahalar da jama’a wajen gano abin da yake nufi ba.
9. Gwaninta da harshe.

Abubuwan Da Suke Bata Waka:
Akwai wasu abubuwan guda biyar wadanda suke bata kyawun waka. Wadannan abubuwa kuwa su ne:

i) Yawaita aron kalmomi daga wani harshe daban kamar na Larabci a cikin waka, musamman idan ya zamana harshen Hausa bai hadiye ararrun kalmomin suka zama Hausa ba.
ii) Maimaita kalma iri daya da ma’anarta a kafiyar waka cikin baitoci da ba su shige goma ba, sai fa idan an yi da niyya, wannan kuma sai a dauke shi wani sabon salo ne.
iii) Karyewar ma’aunin baiti ko karuwarsa.
iv) Rashin daidaituwar kafiya a cikin waka guda.
v) Amfani da kalma wurin da bai dace ba, domin neman kafiyar da ta dace ko gudun karyewa ma’aunin waka.

A wannan matsayi , duk da kasancewar mawaki yana da ’yancin karya wata kalma ko ka’idar nahawu ko ya shirbata tsarin kalmomi, don neman mikakken baiti ko kafiyar da ta dace, to wannan ’yanci yana da iyaka. Idan ya dibi mawaki ya yi wani abin da ya bata wakarsa har aka kasa gane abin da yake nufi, to ya ketare haddi.

Wadannan su ne abubuwan da ya kamata kowane mawaki ko mai son rubuta waka ya yi la’akari da su a wakarsa.

Kammalawa
Wannan takarda da aka gabatar a kan dabarun rubuta waka ta takaita ne a bangare daya wato na ma’aunin wakar Larabci wanda wasu suke ganin ba su yi na’am da wannan ba, kamata ya yi a sami ma’aunin wakar Hausa, kamar yadda Alhaji Mudi Sipikin yake nuna me zai hana mu samo wa wakokin Hausa ma’aunan da za su dace da dabi’arsu, maimakon makalkalewa a ma’aunai na Kamil da Basid ko Mutakarab. Don haka muna ganin duk wanda mutum ya fahimta ya kuma iya ko ya bi in dai an samar da abin da ake bukata, to kwalliya ta biya kudin sabulunta. Kuma fagen ilmi abu ne mai fadin gaske wanda ba za a ce an kure shi ba sai dai a yi ta fafutuka a cikinsa har a koma ga Mahalicci. Don haka lallai akwai bukatar a zurfafa bincike ko da na hadin gwiwa ne wanda zai sa a samar da wani ma’aunin waka na Hausa wanda za a dinga amfani da shi a wajen rubuce-rubucen wakokin Hausa maimakon na Larabci wanda aka fi amfani da shi yanzu. Masu iya magana sun ce “Naka naka ne ko ba zai ba ka komai ba”.

Manazarta
Ahmad Hassan Azzaiti; Tarihul Adabil Arabi. Misira: Nahdhatun

Al’abiduna; Abdussalam Abdulhamidi Abdrrahamani. 1999: Muzakkiratu Fil’adabil Arabi. Kano: Ilori Descendants Progressive Union.

Assayyidu Ahmadu Alhashimiyu. Mizanuzzahabi Fisana’ati Shi’iril Arabi

Adamu; Abdalla Uba; Adamu; Yusuf M; Faruk; Umar: Hausa Home Videos: Technology, Economy And Sosiety. Kano: Center For HausaCultural Studies in conjuction with Admu Joji Publishers.

Bayero; Abdullahi, 2004. Siffantawa Bazar Mawaka: Wani Sako Cikin Nazarin Waka: A Cikin Nazari Kan Harshe Da Adabi Da Al’adun Hausa V. Kano: CNHN, Jami’ar
Bayero.

Gusau; S.M., 2004. Wasu Sanabe-sanaben Rubutu Da Nazarin Rubutattun Wakoki Na Hausa: A Cikin Algaita: Journal Of Current Research In Hausa Studies Vol. 2 No 1, Kano: DNL III, Jami’ar Bayero.

Gusau; S.M., 1985. Salo Da Sarrafa Harshe A Wakokin Baka Na Hausa: A Cikin Nazari Kan Harshe Da Adabi Da Al’adun Hausa III. Kano: CNHN, Jami’ar Bayero.

Gusau; S.M., 1995. Dabarun Nazarin Adabin Hausa: Kaduna: Fisbas Media Services.

Ibrahim; S. M., 1982. Rubutattun Wakokin Hausa Kafin Zamanin Shehu Usman Danfodiyo: A Cikin Harsunan Nijeriya XII. Kano: CNHN, Jami’ar Bayero.

Muhammad; Dalhatu, 1978. Waka Bahaushiya: A Cikin Nazari Kan Harshe Da Adabi Da Al’adun Hausa I. Kano: CNHN, Jami’ar Bayero.

Sa’id; Bello, 2004. Tasirin Larabci A Kan Rubutattun Wakokin Hausa: A Cikin Nazari Kan Harshe Da Adabi Da Al’adun Hausa V. Kano: CNHN, Jami’ar Bayero.

Sipikin; Mudi, 1978. Ma’aunin Wakar Hausa: A Cikin Nazari Kan Harshe Da Adabi Da Al’adun Hausa I. Kano: CNHN, Jami’ar Bayero.

Sa’id; Bello, 1978. Salo Da Tsarin Rubutacciyar Wakar Hausa: A Cikin Nazari Kan Harshe Da Adabi Da Al’adun Hausa I. Kano: CNHN, Jami’ar Bayero.

Sa’id; Bello, 1982. Dausayin Soyayya: Lagos: Nigeria Magazine.

Tukur; Tijjani, 1978. Mawaki Da Matsayinsa a Al’umma: A Cikin Nazari Kan Harshe Da Adabi Da Al’adun Hausa I. Kano: CNHN, Jami’ar Bayero.

A’azamiyun; Walidul. 1962.: Sha’iru Islami: Hassanu Bin Sabit Al’ansari. Alkahira. Madaniyun

Yahya; Abdullahi Bayero. 2001. Dangantakar Waka Da Tarbiyyar ’Ya’yan Hausawa: A cikin Harsunan Nijeriya XIX. Kano: CNHN, Jami’ar Bayero.

’Yar’aduwa; Tanimu Musa. 2001. Tarihin Rubutattun Wakokin Hausa a Kasar Hausa: Algaita: Journal Of Current Research In Hausa Studies Vol. 1 No. 1, Kano: DNL III,
Jami’ar Bayero.

Zariya; Mu’azu Sani. 1978. Karin ‘Mujtath’ a Waken Hausa: A Cikin Harsunan Nijeriya VIII Kano: CNHN, Jami’ar Bayero.

1 comment:

yusuf said...

Assalamu alaikum
A gaskiya nayi matukar jin dadi fara kasancewa tare da ku, kuma insha Allah zamu cigaba da kasancewa tare da ku.
suna na yusuf sule adamu. daga cairo.