Monday, June 4, 2007

Adabi Mai Tafiya: Waiwaye A Kan Fasahar Mai Da Littafi Zuwa Fim

Mun rubuta wannan takarda tare Dr. Malami Buba SOAS, University of London.

An gabatar da Wannan Takarda a Babban Taron Duniya da aka yi a kan Finafinan Hausa, Wanda Cibiyar Nazarin Al'adun Hausawa ta Shirya a Dakin Karatu na Murtala Muhammad, Kano. A Tsakanin Ranakun 4 zuwa 7 ga watan Agusta 2003.


Jama’a sukan ce ‘Noma tsohon ciniki’. To shi ma Fim ko Majigi tsohon tsime ne da Hausawa suka dad’e suna sha. Ya Allah don maganin kewa, ko kuma hanyar samun walwala daga fadi-tashin yau da kullum. Ba fa ‘Jigiri Dos’ da ‘Kabi-Kabi’ da ‘Bigibos’ da ‘Shawalin Temful’ ne kawai majigi ba; hada mini da wasanninmu na gargajiya irin su Tashe da Hawan Salla da sauransu. Abin nufi a nan shi ne duk wata hanyar nishadi da ke da nasaba da canza kama ko murya da anniyar aike sakon ana-buki-ana-salla, ko na fadakarwa, kai ko ma sanarwa ce, to ana iya kiran wannan fasashar majigi. Shin mene ne majigi? Ba wasa ba ce mai fayyace yadda wani dan cikin gida ke hangen wani sashe daga cikin makwabtakar al’ummarsa ba? To ai gaba-dayan abin da muke kira al’ada ya zamo majigi ke nan, wato madubin auna inda muka kwana a rayuwar al’umma ne. Kada a manta kuma da cewa, kafin majigi ya fito turu, sai da ya biyo ta hikimar kwakwalwa, ya samu taciya a rubuce, sannan aka aiwatar da shirin a bainar jama’a. Don haka, hoton da muke gani baje-kolin fasaha ne da aka jima ana sarrafawa.

To da ‘yar wannan matashiya ce muke son mu baje hajarmu ta Adabi Mai Tafiya. Abu biyu muke son mu fifita a nan. Na daya, mun riga mun tabo shi, wato wasannin fim, ko na kwaikwayon Gidan Kashe Ahu, da na Yau da Gobe, ko na Tashe, da Ajo, da na Mabanci, kai ko ma Shelar gari, to fa duk cikin sahun fasahar canza kama ko lafazi suke. Abu na biyu kuwa shi ne cewa Finafinan Hausa, idan aka dubi asalinsu kagaggun labarai ne da aka shirya a takarda, kafin mai da su finafinai. A takaice, majigi Adabi ne mai tafiya (ko in ce mai ‘moshin’ a zamanance). Za mu sake shigowa wannan gonar a yayin da muka zurfafa a cikin wannan bayani.

Don tabbatar da inganci da kuma kafuwar somin-tab’in hujjojin da muka ambata a sama, mun tsamo marubuta hu]u wadanda ko dai su da kansu, ko kuma wasu ma’aikata na daban, suka dauki nauyin mayar da littafinsu zuwa fim. Daga ciki akwai In Da So Da kauna na Malam Ado Ahmad, abokin tafiyata, sai Alhaki Kuikuiyo na Hajiya Balaraba Ramat, ga kuma Naira da Kwabo na Malam Nazir Adam Saleh da Kara Da Kiyashi na Malama Zuwaira Isa Danlami Jos.

In Da So Da Kauna
Sanin kowa ne dai cewa littafin In Da So Da Kauna ya zuwa yanzu ba a sami littafi da ya kai shi tagomashi da karbuwa a zukatan jama’a ba, musamman Samari da ‘yan mata (ba ma dai ‘yan matan ba). A wata hira da na yi da Alhaji Garba Mohammed ‘bookshop’ ya tabbatar mini da irin dubban kwafin In Da Son da ya sayar wa diloliln littattafai a ciki da wajen kasar Najeirya a daidai wannan lokaci. Haka ma Malam Sadisu Musa Mandawari, wato Ririm, wanda shi ma dai dillalin littattattafn ne, ya shaida mini cewa a wancan zamanin ne karatun littattafan soyayya ya zama ruwan daren da har ‘yan mata a Sakandire sukan soka ire-iren littattafan wannan littatin cikin wani littafin larabcin da Malam ya ce a bude don bita. Maimakon bin shedarun da Malam ke ta fafitikar ba da sani a kansu, sai suna bin littafin kalma-kalma! Daga baya kuma sai musayar ra’ayi dangane da adabin. To wannan fa ne ya kai shi juya akalar lebarancin sai da littattafan Arabin da yake yi ya zuwa littattafan soyayya.

Mawallafin kuwa, wato Ado Ahmad Gidan Dabino Sani Mainagge, ya yi suna fiye da yadda ake tsammani. A lalace wasikun yabon da ya samu ya zuwa yanzu sun wuce dubu biyar. Wadannan fa wadanda muka kirga a ‘yan kwanakin nan ke nan. Ba abin mamaki ba ne idan da akwai ninkin wannan adadi da ya salwanta a sabili da rashin tanadi da sauransu.[1] To kafin mu ci gaba, ina son in dada nanata cewa babbar fasahar da marubucin na In Da So ya yi ita ce ba da izinin karanta littafin a shirye-shiryen rediyon Kaduna da kuma sauran jihohin arewacin Nijeriya, kai har da Lagos (Ikko) inda a sanadiyyar hakan ne tarin makaranta suka camfa cewa idan dai ba na Gidan Dabino ba (ko kuma in jam’o, in ce, in ba na Raina Kama ba) to a yi gaba. Alhaji Garba ‘bookshop’ ma ya shaida mana cewa har yanzu idan gogan namu zai dage ya dabaibayo wani labari, to kasuwar littafi za ta yi tashin gwauron zabo! To shi wannan littafin karbuwar da ya yi fa ta wuce ta makaranta. A cikin hirata da marubutan da zan ce sun kai goma sha biyar, wadanda mafi yawancinsu a yanzu haka su ne taurarin marubuta littattafan na soyayya, sun tabbatar mini cewa wannan littafin ne ya fara cusa musu ra’ayin son karatu har ya kai su ga ba da tasu gudummawar littattafan. Ga shi yanzu sunansu yana so ya mamaye na Malam! To amma da sauran tafiya!!! Babban abin da suka tsinta a cikin wannan littafi shi ne yadda kwalekwalen soyayyar ke tafiya da kuma yadda ake tabbatar da ba a nutse ba yayin tafiyar. Ga ‘yar bitar yadda tafiyar takan kasance.

In Da So dai labarin Sumayya da Muhammad ne, wanda ke ba mu bayanin irin tsananin son da wadannan banaayee ke yi wa juna. Sumayya ‘yar Sarki ce idan aka kwatanta rayuwarta da ta masoyinta, kuma abin kaunarta, Muhammad. Ba shakka iyayenta suna da wurii, kuma suna da wayewar kan da har ’ya’ya mata a gidan nasu sukan yi karatun boko (anya ko babanta ba dan boko ba ne; to ko da bai yi karatun ba, yana tafka zamananci a gidansa.) Muhammad kuwa ga dukan alamu talaka ne, kuma ba alamar karatun zamani a harkokinsa (ko da yake an ce wai ya kamala karatun sakandire). Ina ji ma dai za mu ce BaRome ne dan cikin gari.[2] To kamar dai yadda aka saba, son nasu ya kai so, kuma iyayensu na sane da irin zumudin yaran nasu na ganin cewa sun zama Ango da Amarya a gaba. Da alamun amincewarsu, to sai dai a cikin dangi akwai mashaya APC, wato sha yanzu, maganin yanzu. Ji suke yi idan dai babu arzikin sutura a daidai lokacin da ake neman yarinya, to alkalami fa ya bushe na samun wadata gobe. Nan ne Abdul}adir, abokin hamayyar Muhammad, yake da galaba. Ga ku]i, ga isa, ga kuma yin yayyafin naira ga kakannin Sumayya. Ita kuwa ba ta so, ba ta kaunarsa, balantana dukiyarsa. A karshe dai ta gwammace rijiya da aurensa. Addu’ar Sumayya da Muhammad ta kawar da ku]i, da makirci da asiran boka da aka yi ta amfani da su. Ga kuma shigo-shigon da wasu ‘yan matan na daban ke yi wa Muhammad, duk dai don a ga bayan zumuntar tasu. A karshe an nuno Allah ya ba su wadata. Suka je Hajji. Sun kai iyayensu kasar mai tsarki. Sun haifu kuma yanzu haka sai cin duniyarsu suke yi bisa tsinke.[3]

To akwai tarin littattafan soyayya da ke tsokaci a kan irin wannan lamari. Yaro na so, kuma yarinya tana so. Iyaye kuwa sun zura musu ido. Ita ‘yar mai wuri ce, shi kuma dan talaka ne. Wani lokacin tauraruwar ta yi boko, shi kuma gogan sai talla. A yi, ba a yi ba, wani dan zamani mai hali, ko kuma a cewar Sheme da Abdalla, wani ‘nigga’ mai tashe ya le}o ya ce da shi za’a yi.[4] Shi din zai kashi naira inda su gwaggo da kaka. Amma ta Allah da yake ta fi ta mutum, bugu, da zagi, da bokanci, duk a karshe za su kasance banza, yaro yai gaba da yarinya, kuma tafiyarsu ta yi albarka. To ba don a ce na sha ta dubu ba, to da na ce a duk duniya haka lamarin yake. Kuma ba ni ka]ai nake da wannan ra’ayi ba. Wani Shaihi Ba’Amerike ya kira irin zumuntar nan da sunan ‘Unlikely Coupling’, wato gamin- gambiza (Wartenberg, 1999). Jama’a ku dubi tarin finafinan Hollywood da na Bollywood ku yi nazarin yadda iyaye kan yi tir da zab’in yarinya, ko don rashin nuk’ud, ko asali, ko kabilanci, ko kuma don zaman masoyinta bagidaje. A tamu nahiyar kam, asalin soyayyar daga littattafai ne. Shi kuma adabi a ainihin halin zamantakewar Hausawa ya cicciro nau’ukan lobayyar da banaye ke yi, ba wai daga Bollywood ba kawai, kamar yadda wasu masana suka sha nanatawa (Larikin 1999, 2000, 20002).

To fim din na In Da So shi ma ya nuno yadda soyayyar Sumayya da Muhammad ta kasance. An yi bayanin kai-da-kawon abokai, da na ango mai jiran gado, da wahalhalun da suka sha kafin su cimma burinsu. Muhammad ya yi gudun hijira, sabo da bakin cikin kasashin da yake je Abdulkadir ya yi. Sumayya ta zartar da habaicin banaye na ‘in ba kai ba rijiya’, inda ta fada rijiya da anniyar kashe kanta bayan ta aika wa Muhammad da sakon ya zo jana’izarta, tare da fatar ‘Allah ya sada mu gidan aljanna’. A karshe dai ana muzuru ana shaho, auren ya tabbata. Duk kuwa da makirci, da kisisinar wadanda suka lashi takobin atabau ba za’a yi auren ba, wato su kakar Sumaya da dan kazaginta boka, da Abdulkadir da abokansa da kuma ‘yan barandansa da ya tura don su caccakud’a Muhammad. Ga kuma abokan hamayya Naja’atu da Saratu. Kar a manta kuma da cewa a duk lokacin da adabin nan ke tafiyar tasa, rayuwa ma ba ta tsaya cif ba. An nuno haihuwa da auratayya, da mutuwa da zumunta irin ta jini da kuma ta kauna tsakanin abokai da kawaye; wato kamar dai ana bayyana mana yadda Hausawa ke tinkarar manya-manyan lamuran da al’ada ta tanadi yadda za’a yi su. To kuma kowace al’umma a duniyar nan tana da yadda take taka tata rawar a wannan tafiyar ta zama mutum da turawa ke kira ‘Rites of Passage’.

To ina tafiyar ta sha bamban tsakanin littafi da fim, da yake dukansu sun yi bayani dalla-dalla game da makomar soyayya tagari da kuma wadda ba ta da tushe? Haka kuma, daga irin jawaban da marubuta suka furta ta yadda suka koyi d’ab’i, da farautar jari da dillancin littattafan da suka haifar bayan jan aikin nakudar adabin, su ma shugabannin shirya fim haka tafiyar tasu take. A ganawarmu da Malaman ha]e da abokin laccata Ado Ahmad, sun bayyana mana irin halayen da suka shiga kafin su fito da finafinan. Misali, Ado dukufa ya yi wajen koyon aikin shirya fim, kamar yadda ya yi a harkar sana’ar buga littattafai. A cikin fim din In Da So, komi-shi-na (cf.commissioner)[5]. Shi ne marubucin wasar, shi kuma ne aftan aftoci a ciki! Kada kuma a manta da cewa kamfaninsa ne ya dauki nauyin shiryawa da tallata shi da kuma ba da izinin hayarsa da kuma nuna shi a gidajen silima. Ya nuna mini cewa ba in da bai shiga ba a duk fadin arewa ya zuwa Yamai don yin shelar fitowar wannan fim. A cikin fim din kansa ana nuno tallar shagunan bidiyo na manyan biranen arewa wadanda ke dillancin fim din na In Da So Da Kauna.

Alhaki Kuikuiyo
Kamar dai yadda sunan littafin Hajiya ya nuna, Alhaki Kuikuiyo ne, kuma mai shi yake bi. Shi ma dai ya tabo wani nau’i ne na rayuwar Hausawa da marubiciyar ta bayyana shi a matsayin ‘danniya a auratayyar Hausawa... (inda) Malam Bahaushe… zai ajiye mace ta zama mallakarsa kuma abar ikonsa don ya zalunce ta ya musguna mata kuma ya yi amfani da ita ya samu wasu abubuwa na rayuwa’[6] (Watakila da haka abin zai kasance da an yi auren Abdulkadir da Sumayya!) To haka dai labarin ya kasance, inda Alhaji Abdu ya dada wulakanta uwargidansa Rabi, kuma mahaifiyar ‘ya’yansu tara, bayan ya zama wani hamshakin mai kudi. Sau biyu yana sake auren sabon jini, amma da yake Delu ‘yar bariki ce ta shiga aikin raba Alhaji da su Rabi. A daidai lokacin ta soma juya shi kamar yadda take so, har inda yakan kai ta wajen wani kwartonta cikin rashin sani. Ga kuma bala’in gobara da ta tab’arb’arar da arzikinsa. A karshe dai, Allah ya ceto Alhaji daga kilakancin Delu, aka kuma sami daidaituwa tsakaninsa da Rabi. Inda alhakin ya zama kuikiyo shi ne ganin yadda Delu ta dinga wala-wala da Alhaji fiye da mawuyacin halin da ya shigar da uwargidansa ta farko. To ba a nan kawai alhakin ya zama kuikiyo ba.

A hirar da muka yi da Hajiya Balaraba ta nuna rashin jin dadinta game da yadda fim ya fatattaka littafinta, aka tsami na tsama a ciki, aka kuma yi watsi da ainihin sakon fadakarwar da fasaharta ke son idarwa ga jama’a. Wannan sakon shi ne: ‘… mutane su gane yadda yawancin maza Hausawa suke tafiyar da harkar rayuwar gidajensu’, da fatar cusa al’adu nagari a cikin zamantakewar maigida da uwargida. A cewar marubuciyar, maimakon fitowa da wannan sakon tsagaronsa, ta hanyar ba da karfi a kan rayuwar Rabi da ‘ya’yanta masu ‘ladabi da biyayya … da kyakkyawar tarbiyya’ sai su masu shirin fim suka mai da karfi ga ‘…rayuwar Delu ta kwartnaci … Watakila suna ganin shi zai sayar musu da fim din’. Ire-iren canjin da marubuciyar ta bayyana rashin jin dadinta a kansu sun kai goma sha biyar, har ma tana korafin cewa kamfanin Filaps da ya sayi izinin mayar da littafin fim ‘… ba su d’ebi komi ba sunan kawai Alhaki Kuikuiyo suka dauka’. Wadannan canje-canjen sun hada da saka waka da nuna alfasha, kamar ciccib’ar da Alhaji ya yi wa Zulai ya kwantar da ita a kan gado, da nuna shiga mayafi daya tsakanin ma’aurata da dai sauransu. To su ne Hajiya Balaraba take jin suka jawo rashin ‘tafiyar’ fim din a kasuwar finafinai.[7] Ana iya auna damuwarta da taciyar rariyar da take ganin an yi wa littafin nata a bayanin da ta yi na cewa ta dawo daga rakiyar fim da ‘yan kazaginsa:

ba zan sake yi ba, sabo da sana’ar fim ba ta karb’e ni ba … kuma babu tsafta a harkar fim. Na yi iyakacin bakin kokarina a ciki. Na yi kungiyoyi da dama don gyara harkar, amma harkar ta ki gyaruwa. To don haka ni na gudu. ‘Yan fim da suka san ni a harkar da wadanda na yi musu laifi, duk salamu alaikum. Na koma harkar littafi. [8]

Naira Da Kwabo
Littafin Naira da Kwabo na Malam Nazir ya yi suna ainun, kuma yana dauke da darussa ga ‘yan mata da su guji samari masu kokarin yaudararsu. Tauraruwa A’isha ba ta ankara da wannan ba, shi ya sa ta dauki ciki a soyayyarta da Sadik. Yaron da aka haifa, aka kuma jefar ya samu shiga cikin ran Alhajin da ya tsince shi. Shi ma dai yaron ya shiga kogin soyayya da shi da yar’uwar matar gidansu, wadda ba ta sonsa kuma ba ta kaunar wani alheri ya same shi, balantana har a ce za ta bari a yi auren zumunta-zumunta tsakanin wadannan masoyan. Kamar yadda aka saba, bukatar masu makirci ba ta biya ba, domin kaikayi ya koma a kan mashekiya.

Ga dukan alamu dai fim din bai shigi zukatan jama’a sosai ba. A cewar marubuci, wanda kuma yana d’ai daga cikin wadanda suka dauki nauyin fitar da fim din, ko kusan mai da kudin da aka kashe a yinsa ba a yi ba. Shi ya sa ma ya zuwa yanzu ba a yi na biyunsa ba, kuma ya sa Malam Nazira ya ‘zama discourage’ ga yunkurin karasa fim din. Tafiyarsa kuwa ba ta yi armashi ba. Ba kamar littafin ba, wanda marubuci ya yi ikirarin samun ‘daukaka … mutane suka san ni … ga shi littafi har yanzu yana tafiya’. Ya kara da cewa tun daga rubuta tsarin wasar aka fara shan bamban, sannan kuma aka kasa samar da zamanin shekararar 1970.[9]

Kara Da Kiyashi
Dan bayanin littattafan nan da finafinanu guda uku ya sha bamban da na Kara Da Kiyashi littafin Malama Zuwaira Isa. Ta tabbatar mana da karbuwar fim din littafin, wanda take gani an kwatanta adalci ga sakon da tun can cikin littafi ta fara mikawa ga ma’abotanta. Amma a bangaren jigo maganar Gizo ce, wadda ba ta wuce Koki, domin ana nuna auren zumunta tsakanin Khadija da Sa’id cike da soyayyar juna. Kamar yadda aka saba, iyaye sun nace sai lamura na al’ada sun shiga cikin rayuwar wadannnan ‘yan birni. Sun tilasta haihuwar farko ta Khadija a kauyensu. To ganin bango ya tsage shi ne sai Bebi (masoyiyar Sa’id a da) da tallafin makircin Sima ta samu ta kutso kai cikin gida. Ita kuwa Khadija tana can tana famar nakudar ’yarsu ta fari a kauye, kodayake maigidanta ya shaida mata cewa za ta tarar da kishiyarta ta yi kane-kane a cikin gida lokacin da ta dawo daga mahaifi. Zaman dai bai yi ba, kuma surukanta (iyayen Sa’id) su suka ceto ta daga mugun halin kishiyarta da kuma ko-ohon mijinta. An kuma nuno mugun nufin likita Mansur na yi wa Khadija fyade yayin da ba ta cikin hayyacinta saboda duren giya. A karshe dai bukatarsa ba ta biya ba, kuma duk da irin wahalhalun da ta sha, Khadija ta hakure, kuma ta nemi karatu ta samu, sannan kuma ta yafe wa Sai’d suka koma lambunsu na soyayya komi lami lafiya.

Hannunka Mai Sanda
To irin wannan tafiya mai tattare da sakon hannunka-mai-sanda cikin nishadi na daga cikin muhimman dalilan da ya sa finafinan Hausa, ba wadannan kawai ba, suka sami karbuwa sosai a halin da muke ciki. Ba ma abin mamaki ba ne idan aka ce ba wata kafa a tarihin bambadancin turu, ko na gida ko kuma na waje, da ta kai finafinan Hausa shiga sako-sako na al’ummar Hausawa ba.[10] Ba kuma sai mun yi dogon bayani a kan kasancewar fim Hausar baka ce zalla, wadda komai dakikancin mutum zai fahimci inda alkiblar fim din take. Ka ga ai adabin tabarau (wato na karatu) sai ‘yan takarda, masu iya ta da baki kuma masu nacin gane rabe-raben kalmomi a rubutun Hausa, da yake wasu marubutan kansu ba su nakalci ka’idojin rubutun na Hausa sosai ba[11]. Duk da haka, adabon da Hajiya Balaraba ta yi wa Finafinai (a cewarta ba ta tab’a kallon Alhaki Kuikuiyo don ra’ayinta ba) yana tsokaci da dari-darin da wasu marubuta, masana da kuma jama’ar gari suke yi wa wannan salon. A wajensun za mu juya akalar binciken namu a sashe na gaba kafin a karshe mu kai ga yanke shawarar matsayin adabi na tabarau da mai tafiya a zamantakewar yau da kullum ta Hausawa da makwabtansu.

Adabi Mai Tafiyar Lilo
Wasu mawallafa da muka zanta da su, ba wai kawai sun la’aanci finafinai ba, su kansu kuma sun sha aradun cewa ba za su taba amincewa a juya littafinsu ko da kwaya daya zuwa fim ba. Ga shi dai shi Fim din ba hikima; mutum na kallo ido na ruwa sabo da marmadin hoto, ga bakin al’adu masu bakar anniya. Suka ce Fim shi ne ke dada janyo tabarbarewar al’umma ta hanyar nuna batsa, da kwadaita wa ‘yan cikin gari rayuwar GRA, da kaskantar da zumuntar ‘ya’ya da uwaye kamar yadda aka santa a tsakankanin Hausawa. Ba kamar littafi ba, in ji gwanayen namu, wadanda suka jaddada kakkarfan tushensa daga hannun manya magabata irin su Marigayi Abubakar Imam, da Tafawa alewa, da Sarkin Musulmi Abubakar III (Allah ya jikansu) da Kayayen Sardauna, Alhaji Abubakar Tunau Mafara. Suka ce ire-iren wadannan littattafai su suka fara jansu zuwa lambun soyayya kafin su Ado su kawo jiki. Ka san kuwa iyakar asali ke nan! Kar kuma a manta da cewa asalin rubutu labari, shi kuwa labari akan camfa cewa yana cike da kanshin ‘gaskiya’ komai yaye-yayensa. Ba kamar kwaikwayo ba dangin tatsuniya. Ko a sunan kawai wannan salo ya ba da kansa, a ra’ayin marubutan!. To sai dai mu yi waiwaye adon tafiya, mu ga irin ca din da masana suka yo wa marubutan soyayya na farko-farko kafin kanshin nairar fim ya game Sabon Titi da kuma titin Gidan Zoo.

Ba sai na sake nanata irin musayar yawun da aka yi ta tafkawa tsakanin Dr Malumfashi da Furofesa Abdalla Uba Adamu, da kuma tsakanin Malam Ado da Malam Danjuma (Gidan Dabino da kuma mujallolina). A gurguje dai gwabzawar Malumfashi da Abdalla ta dogara ne a kan sahihancin (‘orijinancin’), ko ma a ce kasancewar littattafan na soyayya cikin jerin adabin Hausawa. ‘Yar jituwar da aka samu ita ce har madugun kada ta mike ya aminta da cewa littattafan sun cancanci a kira su adabi (dubi taken ‘Adabin Kasuwar Kano, Malumfashi 2002’). Matsalar ita ce wai marubutansu, da siffar littattafan da gwarancin da ke tattare a ciki, balantana tarin alfashar da suke dauke da ita duk ya rusar da diyaucin sabon salon. Nan fa ne su Abdalla ke matashiya da cewa a yi hattara kar allura ta tono garma, suka ce idan ana maganar ‘ca-buros’ ne na tafka ta’asa to ba littafin Hausar da ya ko kusan jin kanshin irin su Dare Dubu da Daya ba. Kai har ma su Magana Jari Ce da Ruwan Bagaja ba a bar su a baya ba wajen maganganun sake a ciki. Idan muka juya a gwagwarmayar Malam Ado da Malam Danjuma za mu ga cewa ita kam keyar addini aka izo cikin zauren ya zuwa inda kalmar kafirci ta kunno kai . Dubi kuma yadda ake yi wa soyayya kirari irin na Islama, musamman amfani da kalmomi kamar ‘hasken zuciyata… ka fi kusanci a jikina, a kan yadda raina yake kusanci da ni… ya rana mai hasken duniya’.[12] Hujjojin kariyar marubutan da Ado ya bayar su ne, da farko dai hannunka mai sanda suke yi wa jama’a da irin ainihin abububwan assha da ke wakana a kofar gidajensu kulli yaumin (mai yiwuwa ba su lura ba ne). Hujja ta biyu ita ce ‘kowa ya raina tsayuwar wata...’. Iya gudummawar da suke iya bayarwa a lokacin ke nan, to kuma da yake su ba malamai ba ne, kira suke yi ga shaihinnai su gaya musu inda kura-kuran suke domin a yi gyara a gaba. Haka dai tafiyar ta kasance, wadda ina ji har yanzu ba a kai makurinta ba. To yanzu kuma ina kuka dosa?

To a nan fa ne muke da ja. Idan an tuna, mun faro tafiyar ne muna ikirarin cewa tafiyar madugu ce ake yi, yana gaba mukarrbansa na biye, su kuma sauran ayari na take musu sawu. Mun kuma ambato sahu, inda shi ma a gaba da Liman, sannan rabon lada ya faro daga dama zuwa hagu, dama zuwa hagu, har lokacin da Liman ya sallama. A namu hasashen ya zuwa yanzu ban ji ba, kuma ban ga wani muhimmin bambanci tsakanin fim da littafi ba. Ya Allah ko ta siffa ko kuma sakon da ke kunshe a cikinsu. Wato dai ashe dai tafiyar kwambon da Fim ke yi daga Adabi ya kwaikwayota, in fa wadannan zarge-zargen gaskiya ne. Shi kuma adabin daga al’adun Bahaushe ya yanko nasa salon. Ga karin bayani.

A baya can mun tabo zancen soke-soken da ake yi wa Fim da littafi a matsayin magurb’ata al’umma, masu kuma yi mata zagon kasa. Wace al’umma ke nan ake nufi? Ta Hausawa? Ta Musulmi? Ko ta ‘yan Nijeriya. A tuna fa da cewa ko da yake dukanmu da Allah ya nufi had’uwarmu a nan ko dai Hausawa ne ko kuma masu kishin Harshe da al’adun Hausawan ne, a cewar Marigayi Malam Aminu Kano ‘in dare ya yi dare…’. A tamu fahimta, akwai wata manufar wannan kalami da ta danganci rabe-raben akida da rashin cudanyar kut-da-kut kan jawo, ko da kuwa akwai zumuntar uwa da uba tsakanin juna. Alakar wannan hasashe da harkar fim da adabi shi ne cewa ana sukar marubuta da ‘yan fim da kibiyar da ba ta dace da su ba. Ilahirin masu wannan hidima ta nuna So da kauna a cikin littafi ko a faifan fim ‘yan cikin gari ne, wadanda kusan aa iya a ce d’abiunsu sun sha bamban da na ‘yan boko, yan GRA. Shiga fim, da zukar buke, da tafiya disko, da karta ta masha’a da ta kudi, neman mata da dai sauran kaba’irori da Allah da manzonsa suka hana (hada har da bori uwa-uba), ai duk fannoni ne na al’adar banaye Hausawa ‘yan cikin gari Na Kano ne, ko na Katsina, ko na Bauchi, ko na Zaria, ko kuma na Sakkwato. Ba don da Malam Abubakar Gummi (Allah ya jikansa) da sauran magabata suka tashi tsaye da wa’azi ba ai da har yanzu a kowace unguwa za ka tarar ana dara gidan magajiya (gwaggo ga wasu samarin unguwar!).

Mu a namu hange, ba a raba dan cikin gari da nuna tsageranci. Ala kulli halin ba zai rasa samun wata hanyar tsokanar masu gari ba. A tuna fa cewa yawancinsu ba sun kammala karatu, amma ba su sami aiki ba zaman hakurin kawai ake a bakin titi. Kuma ko da suna da aiki zaman dai shi ke sa rayuwa ta dada armashi. To balantana wannan hanya ta rubutu da finafinai mai janyo arzikin miliyan barkatai. To sai dai ba na ji a cikin gari, an dauka cewa wannan ta wuce tsokana. To ita kuwa tsokana a nazarin da mutane suka sha yi dangane da wasu al’ummu na duniya amfaninta jijjigawa ‘destablisation’ in ma ta yi tasiri ba wai juyin juya-hali ba. Wani Ba’ingile, Chiris Humphrey ya yi nazarin wasu al’adun zamanin fir’auna da Turawan ingila ke yi, na nuna bijirewa ga ak’idun masu gari. To sai dai wannan yakan faru ne a kayyadadden lokaci da kowa yake sane da cewa tsokanar za ta fara, kuma za a kammala ta cikin lokaci. Misali matan coci sukan yi shigar maza su tilasta mazan gari ba su kudi a jajiberin wani buki da suke yi. To shi ne masu nazari ke cewa tsokana ce marar ta da hankalin magabata da yake washegari komi yakan koma yadda yake, kura za ta lafa, mata duk su koma d’aura kallabi da yafa gyale. To kwatanta wannan da al’adun ‘yan cikin gari irin su Tashe da Hawan Sallah. Shin kun ko ga irin jerin gwanon da ca-buros kan yi bayan tasowa daga sallah? Saraki na kan dawaki ‘yan bori da ‘yan daudu da bokaye da makada da maroka da ‘yan tauri da ‘yan gari da dai sauran gidadawan daula duk fa za su danno suna dab’a alfasha a washegarin kammala azumin cikin wata Ramalana mai tsarki! To idan bak’o ya shigo gari da kyamara, kai ko ma dan bariki ne (amma mai zai kai ‘yan GRA kanwuri) zai koma masauki ya ba da labarin irin rashin kunyar da talakawa suke yi wa Sarki matsarin al’adu da dabi’un addinin musulunci nagari. To muna fa maganar wanda bai tsaya ya ga jahi ba ke nan. Domin duk wanda ya kwantar da hankali, kuma ya natsu yana ganin abin da ke wanzuwa zai ga cewa dawaki za su dako sukuwa su yi turjiya a gaban sarki, yayin da dagatai ke jinjina wa Sarki suna taya shi murnar zagayowar shekarar mulkin mallaka a kansu. To ka ga ai ke nan hawan, hanya ce da maigari cikin ikonsa da amincewarsa zai ce wa talakawa su fito su wataya, kafin gobe a koma fada wajen karb’ar gaisuwa. A gaskiya wannan ba za ma a ce tsokana ce ba. Wato kamar dai yadda ‘yan fim suka ambata , wa’azi ne cikin nashadi don karkato da alkiblar banaye.

To haka ita ma tafiyar fim da littafi take. Tsokana ce mai kama da hawan sallah, inda marubuta da ma’aikatan fim sukan tsokani al’umma ta hanyar nuna musu kurakuran da suka yi a baya can, wadanda yanzu hakan wasu na kan yinsu, amma a boye. Misali, sukar da aka jima ana yi wa matafiyan namu shi ne cewa wai sun fi ba da fifiko a kan soyyayya fiye da komi a cikin ayyukansu. Sai ana nuni ga irin matsanancin halin da al’umma take ciki na tabarbarewar tattalin arziki da ilimi, na zamba cikin aminci, na tashe-tashen hankula. Maimakon su gina tubalin labaransu a kan wadannan nannauyan lamura, a’a sai soki-burutsun wance ta wane, wane mallakin gajimaren zuciyar wance. Anya ko haka abin yake? Mu koma mu dubi dan tak’aitaccen bayanin da muka bayar a kan fina-finan da muka tsamo. Yaya soyayyar take kasancewa a cikinsu?

Ai babban jigonsu tsokaci ne ga rashi ba wai samun masoyi(ya) ba. Ko a littafi, ko kuma a fim, labaran sukan kwashe yawancin tsawon littafi don ba mu bayanin mummunan halin da masoya da iyalansu kan shiga, ba don kome ba sai don takurawar al’ummar da suka sami kansu a cikinta, wadda wata ko wani tauraro ke wakilta. Misali, Muhammad ya sha dukan kawo-wuka a hannun ‘yan bangar masu hannu da shuni. An kuma nuna zaman zullumin sauran jama’a da suka hada da iyalin Muhammad da abokansa. Kwatanta wannan da irin aljannar duniyar da iyalan Abdulkadir da Sumayya suke cikinta. Shin anya ko ba rashin isasshiyar lura a asibitin gwamnati ta hanzartar da ajalin mahaifin Muhammad ba? Domin mun ga jerin majinyatan reras a dakinsu ba likita. Ba kamar ‘yar gata Sumayya ba, wadda ga dukan alamu cikin ni’imar ‘Clinic’ take, kuma manya irin su Abdulkadir idan suka zo sai su ]ora tasu kyautar a kan ta wasu a wajenta. A tuna fa, baban Muhammad a dukan alamu tsohon ciwo ne da rashin ba da magani akai-akai ya tsanantar. Ita kuwa Sumayya rijiya ta fada ido-rufe, abin da ya yi sanadiyyar gwabgwabjewa a ciki da wajenta har ya kai ta ga somewa. Ita ta farfado da yake ta sha dauren jini da ingantacciyar kulawar likita da nas-nas. To sai dai kar a yi tafi game da watayawar mata kamar su Sumayya a cikin wasannin.

Rijiyar da Sumayya ta fada ba fa wani sabon salon rawar ‘yan mata ba ce. Abin da ya kori bera ne… to kuma wannan shi ya kamata a duba. Wasikar karshe da ta rubuta wa Muhammad ta yi nuni ga dalilin sa kanta cikin yin riddar kashe kanta. Duk isarta, da wani kwambo, da salula, da ilimi da bai wa Muhammad kudin kalaci, a karshe dai an nuno cewa mace Bahaushiya ba za ta fi karfin al’ada (ta maza) ba. Wakiliyar al’adu, kaka mai idon cin naira, ta yi amfani da wannan dama don tilasta wa Alhaji Muttaka ya bayar da Sumayya ga ‘gidan kwarai na yesu-yesu’. Da kuka, da barazanar tsine masa ta ce alanbaran ba za a kai jikanyarta ‘gidan wahala ba. Shi kansa Alhaji Muttaka, ga alama nasu ne, domin sanin kowane Bahaushe ne cewa asali babban tushen auratayya ne a rayuwarmu.

Marigayi Farfesa Smith ya yi bayani dalla-dalla a kan irin rabe-raben al’umma da Hausawa suka zayyana a kan dutse, don tabbatar da cewa Saraki da ‘Yan Fada, Malamai da Attajirai, Manoma da Makera da Masaka, Mahauta da Makada kowa ya san inda dare ke yi masa (Smith 1959). Ai mun jin duk abin da zai sanya wani mahaluki a cikin halin kaka-ni-ka-yin da zai sa ya gwammace aikata ridda, babban zunubi, to wannan abu ba shakka, labudda ya cancanci masu hikima su yi jigo da shi. Abin takaici ganin an nuno cewa sai mata sun kai ga numfashin ajali kafin a ankara da halin kuncin wahalar da suke ciki! Nata halin wato Sumayya yana da muni, amma sauran taurarin fim da kadan ta zarce su.

Rasuwar mahaifin Muhammad, da alamu za ta janyo zaman makoki na har abada ga mahaifiyarsa. Wannan zama ne na rashi, da yake shi kansa Muhammad matsin rayuwa ya kai shi ga yin ‘hijira’. Sauran yayyen nasa kuma mata ne a gidajen mazajensu nesa da mahaifinsu. Hada mini wannan damuwar da kewar rashin abokin hira, tun da sake wani aure gare ta sai dai ikon Allah. (Zawarci ko ai ya zama kamar wata sababbiyar al’ada ce ta Hausawa.) Idan kuma muka juya ga wasu matan a wasannin fim sai mu ga su ma haka zaman yake. Idan miji bai daddare (farfasa) musu baki ba, to wani namijin yana nan yana dabarun kai su ya baro, ko ta hanyar duren giya (Kara Da Kiyashi) ko kuma bone (dubi zagi da wulakancin da Rabi ta sha a Alhaki Kuikuiyo). Ku dubi rashin ta-yin mata, wai har a ce duk da Muhammad, mijin Hajiya, mai karamin sani da talauci, mata ribibinsa suke yi! Ina tuni ne ga ziyarar ba zatan da Sumayya, da Naja’atu da kuma Saratu suka kai wa Muhammad a dan ]akinsa, kowace na hararar ‘yar’uwar da ikirarin da ita za a yi. Amma ina, ga Bafilatana Muhammad zai kula duna. Na ga wasikun da makallata/makarant suka aiko wa Ado Ahmad, inda suke jin takaicin rashin siffanta tauraruwa da za a ce ga ta kyakkyawa baka sidik da ita; hancin ko nananne; sannan lebbanta zala-zala da su kamar ita ta yi wa kanta! Ban sani ba ko a cikin wannan haraba, wasu na sane da fim ko littafi mai bayani irin haka. Ba fa gare mu abin ya faro ba. Shekaran jiya-jiya aka nuno babban shaihi Henry Louis Gates na jami’ar Harvard yana hira da aftoci bakar fata da manyan masu rattaba hannun ga bukatar shirya fim. A cikin hirarsa da tauraruwa Nia Long ta shaida masa cewa da dai za ta turi fatarta da Ambi, to da hayarta sai an dada dala miliyan hu]u daga tarfen da take samu yanzu. Wannan hasashe nata ya sami amincewar Arnon Milchan, wanda ya shirya fim din ‘Pretty Woman’ (Ka fa ji sunan! Karuwa fa ce, amma da yake kirar Sumayya take da ita, ka ga da masu gari take masha’a).

Don haka, kamar dai yadda su kansu ma’aikatan ke ta famar nanatawa, jigon na Soyayya zaurance ne, musamman ga mata, da ke bayyana wa al’ummma halin bacin rai da sukan sami kansu a gidajen mazajensu. Ba kuma yanzu aka fara wannan ba, a’a yanzun dai ne da mata suka taso da hobbasar shiga harkokin fasahar aka fara ji da ganin irin wainar da ake toyawa a kuryar gida. Mai yiwuwa ne abin da ya sa maza ba su dauki wannan bangare da muhimmanci ba, sabo da ai su ne masu laifin! Laifi kuwa aka ce tudu ne, mutum yakan taka nasa ya hangi na wani. Ashe sai mu bar mamakin yadda littattafai da finafinan mata suka fi ‘tafiya’ a kasuwar Sabon Gari da ta Kurmi, da yake su ne ke soso wa mata inda yake musu kaikai, wato zaman zullumi da dar-dar, ko dai a gidan miji ko kuma a gidan iyaye.

Wani jigon kuma da aka sha korafi a kansa, mai kuma alaka da taken soyayya, shi ne cewa ana gurbatar da al’adun Hausawa nagari da wasu baki ko kuma miyagun dabi’un. Akan yi nuni da zamanancin soyayyar da raye-raye da wake-wake da dai sauran ababen da ake ganin sun sab’a wa al’ada. Ba ma ji za mu yi ficen da su kansu ma’aikatan suka yi a mujallu da laccoci wajen kare kansu ga wannan sukar. Abin da za mu dada a nan kawai shi ne cewa kamar dai an jahilci tafiyar adabin ne. Ai wannan take namu ya samo suna ne daga dogon waiwayen rayuwar Hausawa tun ta kaka da kakanni, kafin ‘yan takarda su diro cikinta.

A wannan lokaci, kamar yadda muka sani, kakanni da gwaggonni ke ilmantar da yara cikin nishadin tatsuniya. Baka da baka ake yada wannan ilmi, mai bayyana dabi’u nagari da miyagu. Ana amfani da dabbobi da aljannu da dodanni a siffanto su suna rawa, suna waka, yayin da kowannensu ke da irin kiwon da ya karbe shi. To sai ana karbebeniya da tatsuniyoyin, inda ake canza lafazinsu, ko sunayen wasu wuraren ko na zakarun da ke ciki. Akan bar jigon fadakarwar ya yi ta tafiya daga wannan zuri’a zuwa ta gaban gabacinta. Idan ‘ya’yan Hausawa sun dan girma, sukan shiga harkokin nishadi na Yawon Sallah da Tashe da ire-iren wadannan wasanni, kamar dai yadda muka ambata a sama. Idan kuma suka kai zama banaye sukan je heru (zance, a zamanance), daga nan kuma sai bin juna guhi ko kuma tsarance. A gaba can sai a hange su cikin tawagogin hawan sallah a matsayin saraki, dogarai, yan tauri, ko ‘yan kama, ko makada da maroka da dai sauran rukunai na al’ummar Hausawa.

To fa wannan a ganinmu shi ne tushen adaban da muke magana a kansu. Yawanci akan zubo labarin yadda ya fado a rai, kamar yadda da dama daga cikin ma’aikatan da muka zanta da su suka shaida mana. Idan ma an sami mai taimakawa wajen yi wa aikin gyaran fuska, to shasshafawa ake yi. Akan taso da labarin ne kamar ana tatsuniya. To ban sani ba ko shi ne dalilin da ya sa ‘yan takarda ke jin ba sa kaunar riwayar ta soyayya ko miskala zarratin. Wannan kuwa ai dadaddiyar matsala ce, wadda ta samo tushe daga fifikon da aka fi bai wa zanannen abu fiye da jita-jita. A kashin gaskiya ma dai a iya cewa rubutu hanyar Islama ce, kuma tana daya daga cikin mataslolin da Adabi (rubutacce) ya fuskanta a farko-farkon cuso shi da ‘yan mulkin mallaka suka yi. Zurfin ilmi irin wannan kuwa maza aka sani da yinsa a makarantun allonmu na gargajiya da kuma na book. Shi maza ke yadawa ga al’umma gaba daya, su kuwa mata an kafe su a turken tatsuniya mai fadakar da zuri’ar jinin jikinsu kawai. Dubi irin cece-kucen da aka sha yi wajen bambanta rubutacciyar waka da irin ta su Dan Kwairo da Dan Maraya. To a wani hangen, sai a ce ba karamin tasiri irin duban hadarin kajin da ake yi wa mata da hanyoyinsu na tarbiyyantar da yara na tatsuniya yake da shi ba ga sukar adabin da ake yi. Muna fatar dai ana biye da mu a wannan tafiya ya zuwa finafinai, inda shingen karan ya cim ma ajalinsa, kurunkus. Abin nufi shi ne idan dai tatsuniya (wato magana) da sauran al’adun gargajiya da mata suka fi amfani da su wajen raya al’umma sharholiya ne, to finafinai da aka dora a kan wannan sun zama d’agutu ke nan. Wuce nan, in ji masana, makaranta da makallata da dama.

Babbar sukar da aka sha yi wa marubuta da ma’aikatan fim shi ne cewa suna zaluntar addininmu na Musulunci ta hanyoyi da dama. Aka ce nuno banaye suna yi wa iyayensu ‘tsageranci… maganganu gatse-gatse’, musamman a yayin da su iyayen ke yi musu wa’azin su guji kyalkyalin soyayyar‘… rawa… da yawon shakatawa’ (Dunfawa 2000:14ff). A cikin wannan hali na rashin mutunci su kuma uwaye da kakanni sai a nuno su sun dukufa neman raba zuriyyarsu da abin kaunarsu. Bokaye, masu aiki wai da aljannu da fatale da dai ire-iren siddabarun duban yanayin gobe, ake dora wa alhakin kawar da bakon hauren da ba a maraba da ziyartarsa.[13] A nan ma dai ba za mu yi dogon sharhi a kan hujjojin da ma’aikatan suka kakkawo don kare sauran marubuta da masu finafinai daga wannan mummunar suka ta kafirta su. Sai dai ya kamata mu dan kalato wasu daga cikin hujjojin da su ma’aikatan ke bayarwa.

A hirarmu da su, a koyaushe sukan fara da addu’a da rokon kariya daga sharrin shaidan da shaidanun mutane. Haka ma a farko-farkon littattafansu:

Godiya ta tabbata ga Allah mai ba kowa komai, ba ya bukatar kamai a wajen kowa. Tsira da aminci su tabbata ga Annabin karshe shugaban manzanni (SAW) da alayensa da Sahabbansa da masu bin sunnarsa. Ina dada gode wa Allah da Ya ba ni ikon rubuta wannan littafi mai suna In Da So Da Kauna, Kulle-Kulle Ba Ya Raba Masoya.

Kusan dukan marubuta sukan kafa hujjar rubutun nasu da tsokaci ga kasancewar fasahar baiwa daga Allah, wadda suke yunkurin sarrafawa don amfanar al’umma. A cikin littattafan da finafinai kuma akan yi amfani da ayoyin Alkur’ani da Hadisai masu nuna halacci ko haramcin wani abu da wasu taurarin ke kokarin aiwatarwa. Dubi littafin Allura Cikin Ruwa (shafi na 3, da na 13) da Fim din In Da So (da littafinsa a shafi na 68, 117) don ganin yadda malaman ke amfanin da tsarkakakkun littattafan. A ganawarmu da kuma ta wasu manazartan daban, ma’aikatan Adabin tabarau da mai tafiya sukan sha nanata cewa tabbatar da kafuwar sunna shi ne burinsu, kuma wannan shi ne babban ‘sakon’ da suke son su mika zuwa ga al’umma. Sukan nuna cewa kowa da irin dabarar da Allah ya huwace masa, wadda kuma ake fatar mutum ya yi amfani da ita don janyo ra’ayin na gaba da na baya ga tafarki nagari. Tasu dabarar ita ce bin banaye da halinsu na son nishadi, tare da cuccusa akidojin zama mutum a gaba.

Misali, a cikin littafi da kuma fim din In Da So ba ma ji akwai wani wuri da aka nuna sabo karara, ko kuma wata halayya mai musu da addinin Islama ba tare da tozartar da ita a matsayin ramin karya ba. Ai ka ga sihirce-sihircen boka ba su ci nasara ba. Shi kuma Abdulkadir ai daga baya ya koma kan hanya mikakkiya. Muna kuma son a dubi irin yadda ake suranta aftoci a cikin shirin. Duk da Abdulkadir da Kaka Mai Idon Cin Naira da ake jin su ne mutanen banza a ciki, ai ka ga surarsu ba mishkila a gare ta. Kammalalle aka nuno shi, kuma mai mu’amalar zumunta da abokansa. Ga shi da kamun kai wajen zance da Sumayya, har da zuwa ganinta shi da abokansa, ya kuma kai mata guzuri. To ina laifi! Balantana Sumayya da Muhammad Uwa-Uba. Siffarsu ta ‘yan kwarai ce, kuma ba su gaji iskanci ko azzara a gidajensu ba.[14] Iyayensu sai tak’awa da rungumar kaddara da hakurin halullukan da suka sami kansu, da nuna so da kauna ga iyalansu ko da sun dan nuna fandara. Su wa ye suka rugo zuwa wajen likita don neman a ceto musu Sumayya bayan da ta fada rijiya da anniyar kashe kanta? Ita kuma uwar Muhammad ai hakure masa rabuwarsu ta yi, duk da yake shi kadai ne mai iya rage mata kewar rashin mai halin waliyyai, Malam Gali, wato mahaifin Muhammad. Ka ga ashe sun cancanci a dauke su mutanen kirki, domin halayensu irin na Hausawa ‘yan asali ne, kamar yadda masana irin suka tsaro halayen nagari.

Kada kuma a manta da cewa su da kansu banayen mawallafa da ma’abota fim suka shiga neman hanyoyin kange kansu daga wasu dabi’un da al’umma ke ganin ba su dace ba. A hira da shugaban Raina Kama, kuma babban dan kungiyar ANA ta Kano, ya ba da labarin yadda suka bullo da lambar sahihanci a littattafan da kungiyar ta yi wa taciyar kammala (dubi bangon baya na Duniya Sai Sannu don ganin irin wannan lamba). Haka kuma majalisar nan mai farin jini ta Finafinan Hausa, a koyaushe tana jaddada matsayinta na hakimcin tafiyar harkar, kai har masu sarauta ke akwai a ciki. Wadannan suna da ikon yanke hukunci a kan finafinai da suka ci sunan zama na Hausa.[15] A ganinmu da ci gaba, ko da yake wani malamin cewa ya yi ‘ci gaban’ da ake ji ana samu na taciyar, da samar da aikin yi ga marasa shi, da koyar da magidanta yadda ake zaman aure, to fa irin ci gaban mahakin rijiya ne, wato tana dada zurfi shi kuma yana dada nutsewa a ciki. Wato dai duk da shure-shuren ma’aikatan na bayanin cewa suna nuna yadda ake owambe da naira (ko kari), da kuma tsageranci ga iyaye don yi wa banaye akul din samun kansu cikin halayen, malam ji yake ai tafiyar ce ke ba samari da ‘yan mata sha’awa, ba wai ganin makomar masu karin naira da tsageranci ba, har wayau dai in ji malamin (Argungu, 2002:13).

To idan an tsangwame mu da yanke hukunci, to ji muke yi kusan kowa da kowa da ke tofa albarkacin bakinsa a wannan lamari alkiblarsu daya ce. Wannan ita ce amfani da dabaru, ko na rubutu, ko na fim, ko kuma na sharhi don kawo gyara ga halin ci-bayan al’amuran Hausawa. Kowa daga cikin jerin nan na alfahari da harshe, da al’adu da addinin Hausawan. To shi ya sa muke tambayar shin anya ko ba wata boyayyiyar baraka a kace-nacen da ake kan yi a kan littattafai da finafinai?

A sama, mun tabo bambance-bambancen da ke akwai tsakanin ‘yan cikin gari da ‘yan bariki, musamman dangane da dabi’unsu da yadda suke bayyana su a fagen mu’amalar yau da kullum. Buba da Furniss (1999) sun yi dogon bayani kan zamantakewa da ke bibbiye da juna a cikin Sakkwato. A cikin bayanin nan sun misalta yadda al’adun mazan jiyan Hausawa, kamar goge, da dara, da shiga bokaye, suka caccakudu da addinin Islama a unguwannin da ke zagaye da Kanwuri kai har takan kasance ba a lura ko damuwa da lahanin wannan surkullen. Suka kara da cewa shiga silima da shan sigari da bakuntar gidan mata su ma sai aka rungume su a matsayin al’adun samartaka[16]. Wadannan al’adu sam ba sa bai wa ‘yan bariki (wadanda yawanci baki ne, ko kuma yan cikin gari masu hijira) sha’awa. Hasali ma, sai suna ganin kazantar wadannan halaye. To irin wannan sabani tsakanin ‘yan bariki da ‘yan cikin gari na faruwa a manya-manyan biranen Hausawa tun ba yau ba. To kuma ga alamu mafi yawan masu sukar littattafai da finafinan Hausar ko dai ‘yan barikin ne ko kuma suna yi wa al’adar Adaban Soyayyar hange irin na barikanci. Barikancin kuwa ba a rashin shiga silima da shan sigari kawai ya tsaya ba. Akwai ma bambancin akida a hade.

Har yanzu dai ina son in ci gaba da tsokaci ga wancan bincike da Buba da Furniss suka yi a Sakkwato Mun nuna yadda Bandiri ya samu karbuwar banayen cikin gari da sauran jama’ar gari, sabo da juyar da hankalin samari daga alfashar shiga silima zuwa ga tafarkin Kadiriyya. Wannan kuwa akidar Sakkwatawa ce ta gadin-gadin, tun kafuwar daular Usmaniyya a farkon shekarun 1800.[17] Kwatanta irin karbuwar nan da shafawar ta Bandiri ta samu, duk da rawa da waka da rangwadarsa, da gunagunai da suka biyo bayan fara turarowar Izala a cikin taskiyar gari. To sai muke ji tamkar akwai bambancin akidanci ga hamshakan masu mahawarar duba adabi da finafinan Hausa.

Kano dai ita ce cibiyar harkar rubutu da finafinai, kuma tun ba yau ba ta yi suna a ko’ina kan kasuwanci. Dadin dadawa, a nan ne Sufanci, ya Allah ko na Kadiriyya ko kuma na Tijjaniyya ya fi karfi.[18] Su kuma yawanci ma’abota adabin tabarau da mai tafiya to suna da alaka da daya daga cikin wadannan darik’u. A daya bangaren kuma, sai muka ga kamar jiga-jigan masu sukar zamanancin suna da dadaddiyar zumunta da akidar Izala. Sanin kowa ne cewa ‘yan takarda mazauna bariki, ko unguwannin kewayen birni su ne suka fi yawa a ciki. To kuma a farko-farkon kunno kan Izala (kai ya zuwa yanzu) an tanadi makarantu da masallatai da kasakasai na wa’azi da ke nuna bidi’anci (kafirci ga wasu) na kida da zikiri da bin shaihunai. To ba abin mamaki ba ne cewa mabiya akidar da take alfahari da kwaikwayon Al-kur’ani da Hadisai kawai, za su kawo tsananin suka ga ‘zamananci’. A nan wasu mabiya har suna fassara zamananci da nufin duk wani tsari da bai bayyana a zamanin Annabi Muhammad (SAW) ba. A takaice dai, sukar masu finafinan tamkar suka gamagari ce ake yi.

A tuna fa, ma’aikatan sun sha nanata cewa manufarsu ta nuna halayen banaye a wannan karni shi ne su fadakar da al’umma ta hanyar amfani da fasahar zamani da samari da ‘yan mata suka saba da ita. Wato kamar yadda ‘yan Bandiri suka sha nanatawa a Sakkwato, inda su ma suka fuskanci suka daga bakin malamai, musamman masu adawa da Kadiranci.

Bin Bahasi
Marubuta da masu finafinai ya kamata a aminta da kyakkyawar anniyarsu, ta samar da abin yi, ta ilmantarwa, ta kusanto da adalci a zamantakewar cikin gidajenmu da ta waje, ta habaka harshen Hausa da sauran al’adunmu na gargajiya (masu kyau), da ta musulunci, sannan a karshe sai mu hada da yunkurinsu na dada dankon zumunci tsakanin Hausawa da abokan tafiyarsu a ko’ina suke a duniya. Tammat.

[1] A yanzu haka akwai wani yunkurin shirya wadannan wasikun a cikin littafi dauke da dogon sharhi a kansu don amfanin jama’a.
[2] A cikin bincikenmu a kan Bandiri a Sakkwato, mun siffanta Rumawa da cewa su ne yan unguwannin da ke waje-wajen tsakiyar birni. Takwarorinsu su ne ‘Yan Batikan masu gidaje zagaye da gidan sarki ko a kurkusa da Kanwuri (Buba & Furniss, 1999).
[3] Larkin (1997, 2000) ya yi dogon bayani a kan jigogi da hikimar littafi da kuma Fim na In Da So Da Kauna.
[4] A barayarmu kawai muna da irin wadannan litattafai fiye da guda dari bakwai, kuma muna kan buga littafi a kansu da cikakken bayanin abin da suka kunsa.
[5] Wannan wata fasaha ce da Sarkin Musulmi Abubakar III kan yi amfani da ita don sarrafar da turanci zuwa Hausa kuma mai ma’ana uwar fassarar. Misali, komi-shi-na ‘he is everything’ yana tsokaci ga muhimmanci matsayin a wancan lokaci ya zuwa yanzu. Ga wani kuma: sa-ka-tare ‘put up a barricade’ (Secretary), da kwance-tushe ‘uproot’ (Constitution).
[6] Idan dai ba ambata aka yi ba, to dukan ganawa da ma’aikata mun yi ta ne a Kano da kuma ta wayar Intaneti a cikin watan Mayu da Yuni na 2003.
[7] Wannan kuma wata manufa ce da ma’aikatan ke bai wa tafiya. Wato idan littafi ko fim yana ‘tafiya’, to ya yi albarka a kasuwa ke nan..
[8] To sai dai Furodusan na Alhaki, wato Abdulkarim Mohammed, ya kare kansa da cewa da yake sayen ha}}in fim ya yi wa littafin sukutum yana da iko ya sarrafa shi yadda ya ga dama, ba tare da la’akari da ko ya yi wa marubuci da]i ko bai yi ba.
[9] Wannan zamani ne na yayin wando fantalo, da tayar da gashin ‘Afro’, da motoci masu tukin hannun hagu da dai sauransu. Bai kuma ji dadin rashin samun kayan daki irin na da kamar kumbu da tasa da sauran kayan cikin gida na gargajiya.
[10] A cikin fim dinsu na Lake Chad… Kirscht da Krings (2002) sun nuno yadda ake gwagwarmayar yankan tikitin shiga rumfar kallon wani Fim na Hausa da dare bayan kammala ayyukan lebaranci a kauye.
[11] Dubi sukar da Argungu (2002) ya yi ta gaurayen ‘Ingausa’ da marubutan Hausa ke yi, wanda yake ganin sam bai dace ba, kuma ya nuna rashin ‘salon sarrafa harshe’. To sai dai shi ma fa Malam ya surka ‘salo na iya nufin wata hanya da mutum can zaba wajen … (p. 3).
[12] Hiskett (1975:17) ya bayyana makamancin ra’ayin magabatan malamai ga irin kirarin maroka da mawakan fada.
[13] Manazartan harkokin fim da dama sun gano cewa daukar garawar iskoki na daga cikin manyan siffofin finafinan Nijeriya da na Afirka ta Yamma baki dayanta.
[14] Abin nufi nan shi ne an suranta su da kirar asali da Hausawa suka fi bai wa fifiko, wato siffar Fulani. Misali, an bayyana Sumayya da cewa fara ce, mai }aramin baki da gashi har kafada, kuma ‘yar doguwa siririya mai ilimi (p. 15). Haka shi ma Muhammad da Abdulkadir. An kalubalanci marubuci/mashiryin fim din In Da So bisa yadda yake siffanta kyawawan mata, sai ya ba da amsa da cewa yana kwatanci da matayen ‘yan aljanna ne, don bai taba jin Allah ya ambaci wata siffa akasin wannan a aljanna ba.
[15] Misali, wata kuri’ar jin ra’ayin ‘yan majalisa ta nemi ta san ko an ‘… yarda da wannan doka, ba a yarda a shigar da duk wani fim da nazari da bincike suka nuna yana da nasaba da wani fim ko finafinai daga Indiya, Amirka, Cana, Kudancin Nijeirya, ko kuma wata al}arya in ba Hausawa ba?’ (Finafinan_Hausa@yahoogroups.com (27.07.03)). Kusan kashi 70% suka yi na’am da wannan tambaya. Hausawa, ga masu shakku-shakkun asalinsu, to ‘sun hada har da Hausawan Fulani da kuma Hausawan Tarwatsen Duniya’.

[17] Kadiriyyar Sakkwatawa ta sha bamban da ta Kanawa, da yake ta tsaya ga addu’o’i (lazimi) ne da mutum yakan yi (a kebe) bayan kowace sallar farali. Ba a da’ira, kuma ba a shafa gangar wa’azu. Waje daya ne idan bako ya shigo cikin birnin Sakkwato zai san cewa har yanzu dai tafarkin Kadiriyya ba a manta da shi ba; wannan wajen shi ne na shelar sarki, inda za ka ji ana ‘Kuna jiyawa Kadirawan Shehu. Sarkin Musulmi ya gaishe ku. Bayan gaisuwa kawa, ya ce a sannasshe ku..’ Dubi takardar Buba and Furniss (1999) da ta Larkin (2002). Da kuma littafin Hiskett (1975:73ff), inda ya ke~e babi guda don bayanin tarihin sufanci a kasar Hausa. Dubi jaridar hantsi ta ranar (Litinin, 9 ga Agusta 2003) don karin bayani a kan yadda dariku suke a halin yanzu.
[18] Abin lura a nan shi ne ko a Sakkwato, karshen biranen Hausawa a Nijeriya, gaggan harkar rubutu da finafinai, kamar su Bashir Ahmad Umar da Salihi, a Kano suka yi wayo kafin su dawo gida tare da iyayensu.

No comments: