Tuesday, June 26, 2007

Nishadin Matan Kulle: Tsokaci a Kan Wasannin Cikin Gidan Sarkin Kano

Nasiru Wada Khalil da Sadiya Ado Bayero


An Gabatar Da Wannan Takarda a Babban Taron Kara wa Juna Ilmi Na Shida Kan Harshe Da Adabi Da Al’adun Hausa Wanda Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayero, Kano ta shirya a Ranakun 12 Zuwa 15 Ga Watan Disamba, 2004.


Gabatarwa:
Kowace Al'umma tana da tsarinta na zamantakewar rayuwa, wanda wannan tsari shi za a kira al'dar wannan al'umma. Misali al'adar Turawa, al'adar Fulani, al'adar Larabawa, ko Hausa Fulani a wannna zamani da muke ciki. Shima Bahaushe yana da al'adu da dama kamar na abinci da sutura da aure da farauta da nishadi da sauransu, yawancin wadanda suke aro su ya y daga al'adar makwafta da wadanda addinin musulunci ya kawo masa. Duk da haka al'adun sun dan banbanta a tsakanin Hausawa mazauna wurare daban daban, misali Bahaushen Sokoto al'adarsa ta bambanta da ta Bahaushen Katsina ko Daura, suma al'adun sun banbanta da al'adar Hadejawa ko Kanawa (mutanen Hadeja ko Kano).

A nan za mu dauki Bahaushen Kano a tsakanin sauran Hausawa sudanin Shehu Danfodiyo, za mu dauki nishadantarwa daga ciki sauran al'adunsa mu haska da madubi mu kalli yadda mata (daga ciki jinsin mutane) na kulle na gidan sarauta (daga cikin dangogin ayyuka) don yin tsokaci akan hikimomi da dabaru da Salo, da yanayin yadda harkar nishadantarwa take a wanna gida Zamanin da da na yanzu mu kuma yi nazari akan banbancin Nishadin da da na yanzu; ci gaba ko sauyi aka samu tsakanin nishadin da ake yi da a gidan Sarki da na yanzu?

Wannan mukala an yi ta ne domin a samu a mayar da wannan adabi na baka zuwa cikin rubutu, don amfanin 'yan baya da manazarta al'ada, musamman a wannan lokaci da tsohuwar al'adar Bahaushe take bata yau da gobe. Har ila yau an yi wanna mukala ne domin a bayyan hikimomi da fasaha da sigogin da matan kulle suke da su don jin dadin rayuwar su ta yau da kullum kamar sauran mata da suke a wajen kulle.

Ma'anar Muhimman Kalmomi
Nishadi: Yana nufin duk wani abu da aka yi don dadadawa rai.

Matan Kulle: A nan muna nufin bayi mata da musulunci ya yardarwa ubangijinsu ya take su, su haihu wadanda aka killacesu a gida basa fita ko'ina. A cewar Nast (2003) matan kulle "matan da ba auren mutum suke ba amma zai iya amfani da su don harkokin gida da samun haihuwa."

Gidan Sarautar Kano:
Gidan Sarautar Kano za a kira shi gda saboda akwai mai shi da iyalinsa zaune, kuma a iya kiran sa Unguwa, saboda yawan gidajen da suke ciki da jama'u sannan a iya kiran sa gari saboda ya tara abubuwan da gari yake tarawa kamar; unguwanni da Asibiti da Makaranta da Mahukunta da Doka, kai har ma da yare (salon magana) dalilin haka wasu ma sukan ce duniyar gidan sarki saboda kabilu na mutane daban-daban da suka hadu a ciki.

Nishadin Matan Bahaushe
Matan Bahaushe manyansu da yaransu masu aure ko 'yan mata suna da son nishadi kusan a komai na ayyukan rayuwarsu ko sana'a, domin su sami annashuwa a cikin wannan abin da suke yi, misali idan matar Bahaushe tana nika za ta rinka bin nikan nan da waka domin ta debewa kanta kewar wahalar wannan nikan, wakar nan za ta iya zama ta gargadi ko wa'azi ko kuma raha, kowacce dai ta yi za ta sami jin dadi da nishadi yadda saukin wannan nikan zai rayu a gare ta.

Haka nan a lokacin saka ta 'akwasa' nan na suna jefa akwasar suna waka, a haka sai su yi saka mai tarin yawa ba tare da sun ji wahalar komai ba.

Har ila yau, matan Hausawa suna kadi (mayar da auduga zuwa zaren saka ko dinki) a nan mata za ka ga suna kadin suna waka a gidajensu, haka zalika yaran mata "'yan mata" akan tara musu kada mai yawa su yi wada "didi".

Lokacin rarrashin yaro nan ma za ka ga mata na yi wa yaro rawa sun yin kida da hannunsu a bayansa, suna yi masa wasa suna rarrashin sa tare da nishadantar da shi, da su kansu, shi ne za ka ga yaro yana kuka ya dawo yana dariya bayan ya yi shiru daga barin kukan.

Gada, kamar yadda kowa ya sani; "rawa da waka ce da 'yan mata ke yi ta da yamma ko da daddare" ya danganta da gari-gari. Baya ga haka kawaye suna yin ta lokacin bikin "yan matancin Amarya", ma'ana idan ana auren kawarsu.

Ana daka ana waka ne dai ba a san Bahaushe da haka ba sai Fulani, su Hausawa Lugude aka sansu da shi, da sauran ire-iren ayyuka na Bahaushe babu inda ba ya nishadi sai a inda ya san idan yayi zai iya gamuwa da wahala ko laifi kamar tu}in tuwo ko sallah da sauransu.

Nishadin Matan Kulle Na Gidan Sarki
Baya ga wadannan nau'i na nishadi da ake samun su a ko'ina har a gidan sarauta, akwai kuma wadanda kwara-warai ne kawai suke yi a gidan sarki, wadannan sun hada da wasan gauta, kidan ruwa da warar guje, kidan sakaina da kuma tashe.

Wasan Gauta
Wannan wasa ne da sai kwara-warai ne kawai suke yin sa a gidan Sarki wanda aka fara shi tun kafin Musulunci ya kafu a kasar Hausa, kamar yadda Suwaid Muhammad ya fada ko da yake Alkali Usaini Sufi ya musanta hakan inda yake cewa "An ce an fara wannan wasa ne tun cikin yakin duniya na biyu, yakin da aka fi sani da yakin Hitila. Bayan an yi ne sau daya, sai aka dakata ba sake yi ba sai da aka gama yakin sannan aka ci gaba da shi......."

Shi dai wasan Gauta yadda ake yin sa shi ne kamar yadda Sufi (1993( ya kawo:

Shi wannan wasa ana yin sa ne a cikin wata Sallah Babba a lokacin kaka, lokacin da ake cin moriyar amfanin gona da aka samu a wannan shekarar, irin su gujjiya da gyada da rake da takanda da gauta ko data da yalo da dai sauransu. Wannnan wasa na kwaikwayo ne, wanda yake nuna yadda ake tafiyar da mulki irin na gargajiya da kuma yadda ake tafiyar da aikin hukuma na yau da kullum. Ta wani bangare kuma yana nuna cewa ata ma idan da za a ba su dama za su iya yin abubuwan da maza suke yi, domin a tsari nan na wasan Gauta akwai Sarakunan Yanka da Hakimai da Alkalai da "Yan doka da Wakilin doka, har ma da Yari mai kurkukunn tsarewa. Waje daya kuma ga asibiti har da Sitta mai bayar da magani tare da ma'aikatanta wadanda ake cewa da su 'yan diresin."

Daga wannan wasafcin na yadda ake wasan gauta da Alkali Usman Sufi ya yi, za mu ga cewar wasan ana yinsa ne lokacin Turawan mulkin mallaka, amma wasan Gauta ya sami canjin suna ya koma Wasan Gwamna. Saboda Turawan mulkin mallaka sun ga cewar wasan Gauta hanya ce ta fadakar da Jama'a.

Haka ya nuna cewar tun kafin zuwan Turawa aka fara wasan gauta. To amma kuma wane lokaci aka fara wannan wasa shi ne babu tabbas a kai, an daina shi ne a shekarar 1953 lokacin da Sarkin Kano Muhammadu Sunusi ya hau gadon karagar mulkin Kano, a cewar "Matar Daga."

An daina wannan wasa ne, saboda a wannan lokacin NEPU ta fara karfi, saboda haka akwai yiwuwar 'yan NEPU su yiwo shiga a matsayin matan maroka ko matan bayin sarki da suke waje su shigo gidan sarki. A wani bangaren kuma Matar Fada Fagi cewa tayi "An daina ne saboda kwarkwaran Sarki Sunusi ba su da yawa, ba za su isa yin wasan gauta ba kamar yadda aka saba.

Alkali Usaini Sufi (203-205) ya kawo sunayen wasu daga cikin masu wasan gauta da mukaminsu kamar haka:
SUNA LAKABI MUKAMI
Binta Yartsakuwa Sarkin Musulmi
Hasiya Asabe Sarkin Kano
Kayi Kayi Sarkin Katsina
Gaji Malama Sarkin Gobir
Dije Haji Galadiman Kano
Binta Rano Ciroman Kano
Hassana 'Yan Biyu Ciroman Kano
Gadan Gadan Makaman Kano
Jabu Jabu Wazirin Kano
Bilki Maigashi Dan Iyan Kano
Aishatu Iyantumi Tafidan Kano
Rabi Hajiya Ma'aji Walin Kano
Hamamatu Hauwa Magajin Malam/S/Shanu
Daso Tababa Makaman Kano
Rabi Jahun Sarkin Rano
Kubura Malama Alkalin Kano
Rabi 'Yarwawu Marusan Katsina
Aishatu Mai sunan Umma Wakilin Doka
Hauwa Dan Kulu Sitta
Kankani Kankani Yarin Kano
Fagi Yatafada Magajiyar Karuwai

Hikimar Yin Wasan Gauta
Babbar Hikimar yin wasan Gauta bayan nishadi shi ne, a janyo hankalin sarki a kan abubuwan kasarsa, halayya da dabi'un 'yan majalisarsa irin su Waziri da Madaki da Galadima da sai sauransu, wasu suna ganin gauta a matsayin wata dama da ake nusar da Sarki shi kansa irin matsalolinsa ko rauni don yi gyara.

Kidan Ruwa Da Rawar Guje
Shi kidan ruwa yadda ake yi kidan shi ne a sami masakai manya-manya a cika su da ruwa sai a kifa wata kwaryar a cikin ruwa, a sa abin kida ana kida, su kuma kwarakwarai kowace ta sha kitso Doka (za mu yi bayani sa a sakin layi na gaba) su yi da'ira suna rawa suna juyi, sai daya ta fito da sauri zuwa gaban makidiyar ta yi rawa, sai ta koma wata ta goya (ta shiga bayanta) daki-daki har sai an kewayo kan kowa. Shi wannan kidan ruwa da rawar guje ana yin su lokacin bikin sallah ko bikin 'ya'yan sarki.

Rawar Sakaina
Kowacce kwarkwara bayan an koya mata yadda ke rawar kidan ruwa sai ta taho wajen kidan sakaina ta ci gaba da koyo, sabanin kidan ruwa da 'yan soro rawa kawai za su yi, a kidan sakaina su za su yi kidan su, kuma su yi rawarsu.

Yadda ake yin rawar sakaina shi ne a samu sakaina ana kadada zabiya tana ba da waka ana amasawa ana rawa mutum daya-daya ko mutum biyu-biyu kamar rawar kureda ko rawa oba ko rawar a yi yamma, a wannan rawar mutum hudu ne suke yi ko shida a cikin fili suna maye juna wasu na shigowa wasu na ficewa.

A kidan sakaina ba wai kidan ko wakar ce mai ban sha'awa kamar rawar ba saboda irin hikima da kimiyyar da take cikin rawar, kuma ita ce ginshikin nishadin da ke ciki, shi yasa idan kwarkwara ba ta iya taka rawar ba, manyan kwara-kwaran in suna takawa sai su bude wacce bata iya ba da kasa komai fari ko tsadar zanin da ta daura.

I. Ayyaraye yurare

Ayaranye yuraye da wuya
‘Yan amshi: Ayaraye yuraye shawara da wuya
Ayyaraye iye shawara tsoro
‘Yan amshi: Ayaraye yuraye shawara da wuya
Ayyaraye duk mai shawara ba zai yaki ba
‘Yan amshi:Ayyaraye duk mai shawara ba zai yaki ba
Ba ya gudu ba ya ja da baya sai ya kama
‘Yan amshi: Baya gudu ba ya ja da baya sai ya kama
Ayyaraye mu sarkin mu Auwalin Allah ne
‘Yan amshi: Ayyaraye mu sarkin mu Auwalin Allah ne
Ayyaraye mu sarki mu Alhajin Allah ne
‘Yan amshi: Ayyaraye mu sarki mu Alhaji Allah ne
Ba ya gudu ba ya ja da baya sai ya kama
‘Yan amshi: Ba ya gudu ba ya ja da baya sai ya kama

II. Iya ranaye dede
Iya ranaye dede iyararaye
‘Yan amshi: Iya ranaye dede iyararaye
Ta ina ta haura
‘Yan amshi: ta shamakin dawakai
Ta sararin garke
‘Yan amshi: ta shamakin dawakai
Kaya kaya na keji a shamakin dawakai
‘Yan amshi: iyararaye dede iyaranaye
Ba ku amshi 'yan yara baku tafi
‘Yan amshi: Iya ranaye dede iya ranaye
Ba ku tafi 'yan yara ba ku amshi
‘Yan amshi: Iya ranaye dede iya ranaye

III. Ngalle Ngalle Ngalle
Ngalle Ngalle Ngalle
’Yan amshi: doki da rawa
Ku tafa
‘Yan amshi: doki da rawa
Ku juya
‘Yan amshi: doki da rawa
Ku amsa
‘Yan amshi: doki da rawa
Ba ga shi ba
‘Yan amshi: doki da rawa
Har na iya
‘Yan amshi: doki da rawa
'Yar mama
‘Yan amshi: doki da rawa
Ingalle le ingalle ingalle
‘Yan amshi: doki da rawa
Ku taka
‘Yan amshi: doki da rawa
Ku juya
‘Yan amshi: doki da rawa
Ba ga shi, ba
‘Yan amshi: doki da rawa
Har kun iya
‘Yan amshi: doki da rawa

IV. Ku Reda
Ayyaraye garin bara na yi dare
‘Yan amshi: ayyaraye garin bara na yi dare
Ayyaraye garin bara na yi tuwo
‘Yan amshi: ayyaraye garin bara na yi tuwo
Ayyaraye garin bara na yi fura
‘Yan amshi: ayyaraye garin bara na yi fura
Ku reda, kwarin duma ku rede mu reda
‘Yan amshi: Ku reda, Kwarin duma ku reda mu reda
kwarin duma mu reda, ku reda, mu reda.

V. Badagaraje
Badagaraje badagaraje
‘Yan amshi: Badagaraje badagaraje
Aye bada garaje yaro bada garaje kanyi raha ba.
‘Yan amshi: Badagaraje badagaraje
Da rarrashi da ban Magana
‘Yan amshi: Badagaraje badagaraje
Da kwaryar goro kanyi raha
‘Yan amshi: badagaraje badagaraje
badagaraje badagaraje
‘Yan amshi: badagaraje badagaraje
badagaraje yaro badagaraje
‘Yan amshi: badagaraje badagaraje
Kan yi raha ba.
‘Yan amshi: badagaraje badagaraje

VI. Alo lale lale
Ayyuriri a haiye alo manya
‘Yan amshi: alo lale lale
Mu sarkin mu ya tafi rangadi
‘Yan amshi: Alo lale lale
Allah kai shi Allah ya dawo shi
‘Yan amshi: alo lale lale
Ko da tuntube ko da sartse alo lale lale
‘Yan amshi: alo lale lale
Ko da 'yar kaya bai tako ba
‘Yan amshi: alo lale lale
Ayye iyara iye
‘Yan amshi: ayye iyara iye
Ayye indiro ba diro
‘Yan amshi: ayye indiro ba diro
Auririn ahaiye nanaye
‘Yan amshi: alo lale lale
Dan Allah ku sa mana 'yar guda
‘Yan amshi: alo lale lale

VII. Aya Aya Aya mai nono
Aya Aya Aya mai nono
‘Yan amshi: Haba ayalle
Aya biyar ta cika taiki
‘Yan amshi: Haba ayalle
ta goma rakumi ka dauka
‘Yan amshi: Haba ayalle
In kin ]iga ba kya tashi ba ne?
‘Yan amshi: Haba ayyalle
Ki hankali da baba a zaure
‘Yan amshi: Haba ayalle
Ki hankali da babbar tusa
‘Yan amshi: Haba ayalle
[ugus ta ]iga ta tashi
‘Yan amshi: Haba ayalle
Kanto mai dan boto
‘Yan amshi: Haba ayalle

VIII. Lallewa
Aye lalle waye, lallewa, aye lalle waye, lallewa
‘Yan amshi: Aye lalle waye, lallewa, aye lalle waya, lallewa
Kimba magani banga masoro ba
‘Yan amshi: shan yaji
na gano galadiman ki niba
‘Yan amshi: shan yaji
Ana daka ana zubga masoro
‘Yan amshi: shan yaji
Allah ya tsinewa buzu Albarka bani Kashi da bulala
‘Yan amshi: Aye lalle waye, lallewa, aye lalle waye, lallewa
Allah ya tsinewa buzu Albarka buzu mai taguwa mai mashi
‘Yan amshi: Aye lalle waye, lallewa, aye lalle waye, lallewa
Aye lalle waye, lallewa, aye lalle waye, lallewa
‘Yan amshi: Aye lalle waye, lallewa, aye lalle waye, lallewa

IX. Ga Danda
Aye ga danda ga danda
‘Yan amshi: Aye ga danda ga danda
Aye ga danda dokin kara
‘Yan amshi: Aye ga danda dokin kara
Doki na kora na zai gudu ba
‘Yan amshi: ga danda ga danda
Ko ya yi ma iska ya samu
‘Yan amshi: ga danda ga danda
Aye ga danda dokin kara
‘Yan amshi: Aye ga danda dokin
Ku bamu wuri mu sukwani danda
‘Yan amshi: Aye ga danda ga danda
Ga danda ga danda
‘Yan amshi: ga danda ga danda
Doki nakara ba zai gudu ba
‘Yan amshi: Aye ga danda a sukwane
Ga danga ga danda
‘Yan amshi: Aye ga danda dokin kara
Ga danda ga danada
‘Yan amshi: Aye ga danda dokin kara

X. Kigo mai yawan rabo
Amale amale kigo mai yawan rabo
‘Yan amshi: amale amale kigo mai yawan rabo
Kigo ka fi waiwaye amashi
‘Yan amshi: amale amale kigo mai yawan rabo
Kigo ka fi ma gamu
‘Yan amshi: amale amale kigo mai yawan rabo
Amale kafi mu gamu
‘Yan amshi: amale amale kigo mia yawan rabo
Tsara ta san tsara
‘Yan amshi: amale amale kigo mai yawan rabo
Kigo ka fi waiwaye
‘Yan amshi: Amale amale kigo mai yawan rabo
Mu sarkinmu ya ishe mu Ba za mu ko ina ba
‘Yan amshi: Amale amale kigo mai yawan rabo
Mu sarkin mu mai dubun doki mai amawali
‘Yan amshi: Amale amale kigo mai yawan rabo
Daga Daura nazo Kano lokacin ka na da dadi
‘Yan amshi: Amale amale kigo mai yawan rabo
Labarin ka na jiyo haka nan na tadda kai
‘Yan amshi: Amale amale kigo mai yawan rabo
Gara da nazo gara dana zo
‘Yan amshi: Gara da nazo gara da na zo
Gara da na zo na rarrabe
‘Yan amshi: Gara da na zo na rarrabe
dan duma duma da kabewa
‘Yan amshi: Haka na rarrabe
ga randa rana daka tulu ne ya kai ya kawo
‘Yan amshi: Amale amale kigo mai yawan rabo
Kigo mai yawan rabo
‘Yan amshi: Amale amale kigo mai yawan rabo
Amale kafi ma gamu
‘Yan amshi: Amale amale kigo mai yawan rabo
Baba Uban shamki, kowa sai ya durkusa
‘Yan amshi: Amale amale kigo mai yawan rabo
Baba uban maza da mata kowa sai ya durkusa
‘Yan amshi: Amale amale kigo mai yawan rabo
Amale Amale kigo mai yawan rabo
‘Yan amshi: Amale amale kigo mai yawan rabo
Masaki yafi ragaya, Goma ta wuce biyar
‘Yan amshi: Amale amale kigo mai yawan rabo
Idan riga ta wuya sai ba a zo wajenka ba
‘Yan amshi: Amale amale kigo mai yawan rabo
Idan wando yana wuya sai ba a zo wajenka ba
‘Yan amshi: Amale amale kigo mai yawan rabo
Idan hula tana wuya sai ba a zo wajenka ba
‘Yan amshi: Amale amale kigo mai yawan rabo
Mai Daura mai Kano, mai Jama'are mai Kazaure
‘Yan amshi: Amale amale kigo mai yawan rabo

Tashe
Tashe kamar yadda kowa ya sani al'adace da ake yin ta a lokacin watan azumin du gari, kuma kamar yadda aka sani a kasar Hausa cewa yara ne da maza manya suke yi, to amma a gidan Sarki mata ne manya suke haduwa su yi wa Sarki, kwara-warai da jadadu da sauransu.

Duk wadannan wasanni da kwarkwarai suke yi baya ga nishadantar da kansu da suke yi suna nishadantar da ubangijinsu, sannan kuma hanya ce ta samun ku]in shiga a wurinsu, don komai suka yi sai ubangijinsu ya biya su.

Nishadin Matan Kulle A Yau
Kamar yadda rayuwa da al'adar Bahaushe take samun canji haka zalika wadannan al'adu da matan kulle (Sadaku) suek canzewa, yanzu shekaru hamsin da daya (51) ke nan da daina wasan gauta kamar yadda muka fada a baya.

Samun hanyoyin nishadi na yau da kullum da ake yin su kamar su Gada duk sai bacewa suke yi, ana maye gurbinsu da abubuwan da zamani ya zo da su kamar su Ludo da "yar carafke da sauransu, bayan su talabijin ta fito, ita ma ta zama wata hanyar nishadantarwa, musamman zuwan satilayit, akwai tashoshin Indiya "Sony Channel" wasaninsu irin su: - Kusum da Kone Dilmile da Ayusha da Humbocane da Bedi da Jesi Jesi, da sauransu, sun zama hanyoyin nishadantar da 'yan soro ta yau da kullum haka zalika Kagaggun labarai na "adabin kasuwar Kano", finafinan Ibro da kuma wasannin Hausa na talabijin da na Bidiyo.

Bambancin Nishadin Da Da Na Yanzu

Da Yanzu
Ana nishadantar da kai a kuma Ya fi yawa ga nishadantar da kai
nishadantar da ubangiji

Akwai neman kudi Nishadin ne kawai ba wani neman kudi a ciki

Ana kulla alaka Babu kulla alaka da zumunci
Da al'adar Bahaushe zalla ake Har bakin al'adu na nishadantarwa
Nishadantuwa ana amfani da su kamar turanci da Indiya da sauransu.

Kammalawa
Kamar kowacce irin al'umma mutanen cikin gidan Sarki suma suna da al'ada tasu ta kansu wacce take karbar bakin abubuwa daga waje kuma take sauyawa yau da kullum, sannan tana tafiya da zamani, wannan shi ya nuna cewa cikakkiyar wayuwa ake yi kamar ta sauran jama'a ba zama ake yi kamar na gidan yari ba.

Manazarta
Littattafan da aka duba:
Sufi H. A. (1993) Mu san Kanmu, Kano Nigeria

Kofoworole, 2 da Lateef, Y. (1987) Hausa Performing Arts & Music nigeria Magazine, Lagos

Nast H.J. (1992) Space, History And Power: Stories Of Spatial And Social Change in The Place of Kano, Northern Nigeria, Circa 1500-1990 Ph.D. Thesis. Mcgrill Univesity, Montreal, Quebec.

Nast H.J. (2003) DISTRUPTING DECEPTIONS: A photographic, History of Kano Place, Nigeria Printed my Vic-O Graphic, Inc Willow Book, Illinois

Bayero, S.A (unpublish) Mata a Gidan Dabo

Hira da Mutane
Yaya Buruji ranar 13 ga watan Nuwamba, 2004 da 4:30 na yamma

Yakadiya Asabe Matar Daga, a soronta ranar 13 ga wanta Nuwanba, 2004 da karfe 3:00 na dare.

Yaya Tafada Figi, ranar 14 ga watan Nuwanba, 2004 da karfe 8:00 na dare a filin Sirada.

Yaya Maijidda ranar 15 ga watan Nuwamba, 2004 da karfe 6:00 na yamma a filin Sirada.

Yaya Rahmu ranar 17 ga watan Nuwanba, 2004 da karfe 5:00 na yamma a filin Sirada.

Yaya mai soron baki (Y aHajiya) ranar 17 ga Nuwanba, 2004 da karfe
3:00 na dare a filin Sirada

Jadadiya Uwani, ranar 18 ga watan Nuwanba, 2004 a soron Jakadiya Sabe Matar Daga

Ibrahim Mai Kano, (Galadiman Zagin Sarkin Kano), a soron gidan sa, ranar 21 Nuwamba, 2004.

No comments: