Thursday, June 7, 2007

Rawar da Matan Hausawa ke Takawa Wajen Bunkasa Adabin Hausa

Furofesa Abdalla Uba Adamu (auadamu@yahoo.com) Jam’iar Bayaro, Kano

Babban Jawabin Da Aka Gabatar a Bikin Kaddamar da Littattafan Muradin Mata da Madafa – Kicin Sirrin Mata, wanda Fatima A. Maikarfi ta wallafa, ranar Lahadi 12 ga Yuni, 2005 a Dakin Karatu Na Murtala Muhammad da ke Garin Kano

Gabatarwa
Rubutu hanya ce ta fitar da kaimin da ke zuciyar mutum da kuma sadar da sako ga dimbin jama’a. Wannan hanyar tana da akalla fa’ida guda biyu. Ta farko isar da sako. Ta biyu koyawa mai karatun yadda ake karatu da rubutu. Tun lokacin da a ka fara rubutun boko a kasar Hausa, maza ne suke jagorancin rubutun. Ba wai don babu mata wadanda suma zasu iya rubutun ba, a’a, sai dai kawai saboda damar bata samu ba ta inda su ma zasu yi rubutun har a buga duniya ta san abin da suka rubuta. Amma wannan ya fi karkata ga rubutun boko. A rubuce-rubucen addini an sami mata sun yi rubutu da yawa da haruffan ajami. Babbar misali da zan kawo a nan ita ce Nana Asma’u, diyar mujaddahi Shehu Usmanu Dan Fodiyo, wacce ta yi gagaruman rubuce-rubuce a kan fannoni dabam-dabam na addini bayan Jihadin 1804. Nana Asma’u wacce ta rayu daga 1793 zuwa 1864, ta zama jagora ga duk sauran mata marubuta, ta inda ita ce ta zama mace ta farko a duk fadin kasar da gaba za a kira Najeria da tayi rubutu masu yawan da ta yi; wanda yanzu ya zarce na kowanne furofesa a yawa, kima, daraja, amfanar da jama’a da kuma dorewa, domin tun rubuce-rubucen da ta yi fiye da shekaru dari da suka wure, har yanzu ana amfana da su.

Da zuwan bokon zamani sai wannan damar da mata suke da ita ta shude. Abin sai ya juya ya zama cewa in dai ba da boko mutum ya yi rubuta ba, to bashi da tasiri wajen Turawa. Hasali ma dai an fito da dokoki daga 1903 wadanda suka tauye rubutun ajami. Sannan kuma dama bokon a lokacin sai maza kawai – mazan ma wadanda ake ganin basu da gata, domin gani ake boko hanya ce ta dulmiyar da mutane zuwa addinin Nasara, wanda kuma a idon mutanen zamanin, wannan hanya ce ta zuwa wuta.

Ilmi da Samuwar Rubutun Mata
Ko da aka fara saka yara a makarantun boko, to da maza aka fara. Ta haka maza suka samu damar iya rubutu da karatu fiye da mata. Kuma duk da cewa an bawa mata karfin gwiwar samun ilmin addini, amma an fi tsayawa ne daga su iya karatun Al-Kur’ani mai tsarki, Hadisan Manzon Allah (SAW), da kuma sauran littattafan addini. Ba a ba da damar a juwa ilmin da aka samu ta rubuta shi ta yadda mutum zai iya sarrafa abin da ya sani ta wata sigar domin ilmintar da mutane. Sai daga bayane a hankali aka ga muhimmancin yin hakan, sannan aka fara samun marubuta; amma duk da haka, marubutan mazane. Sannan tsadar a buga rubutun ya sa sai mai hannu da shuni ne kadai zai iya rubutun, domin manya-manyan gidajen dab’i na kasa babu ruwansu da buga littattafan mutane in ba na ‘yan makaranta wanda sun san za a saya da yawa; sai da kuma na masu kudin da za su iya biyansu.

A lokacin da siyasar farar hula ta yi zagaye na biyu a 1979, watau lokacin mulkin Shagari, sai madab’a na buga takardun siyasa suka samu da yawa. Bayan an gama siyasar, na ci ya ci, wanda zai fadi ya fadi, sai wadannan madab’an suka zama basu da wani aikin yi. Domin a bawa mutane damar su yi amfani da su, sai kamfanin Northern Nigerian Publishing Corporation da ke Zariya, kuma wanda ya shahara a buga littafan Hausa fiye da shekaru kusan 50 da suka wuce, ya fito da wata gasar kagaggun labarai, kamanceciniyar wacce a ka yi a 1933 wacce kuma ta fito da marubuta kamar su Abubakar Imam, Bello Kagara, Abubakar Tafawa Balewa, John Tafida da kuma Muhammad Gwarzo.

A wannan karon na gasar 1979 an sami wadanda suka yi nasara. Babban abin mamaki shine daya daga cikin wadanda suka yi nasara din mace ce, wacce ta yi nasara da kagaggen labarinta mai suna So Aljannar Duniya. Sunanta Hafsat AbdulWaheed. Wannan littafin ba karamin tubali bane wajen gina harsashin samar wa mata Hausawa ‘yancin kansu. Shine littafi na farko da mace Bahaushiya (ko in ce Bafulatana, domin Hajiya Hafsat Bafulatana ce, kuma labarin a kan Fulani yake, duk da cewa da Hausa a ka rubuta shi) ta rubuta. Bugu da kari, shine littafin farko na adabin soyayya. Wannan littafin ya fito ne a 1980.

So Aljannar Duniya shine littafin farko da ya fitar da akidar Yakin ‘yancin mata, watau Feminism. Dalili kuwa shine ya kalubalanci yadda ake sarrafa rayuwar mata a rugga, da kuma gidajen Hausawa. Ga misali daga cikin wani zance daga littafin domin nuni ga abin da nake nufi:

(Bodado) Aure! Inna[1][1] ni fa na gaya muku ba zan auri kowa ba sai wanda nake so. Kun san zamani ya sake.

(Inna) Mhm! Wannan zamani, Allah Ya saukaka. Yarinya ki zauna kina zancen aurenki, sai kace hirar nono da mai. Don haka fa ba ma son sa diyarmu makarantar boko. In kun yi karatu sai ku ce kun fi kowa. Me kuka dauke mu ne?

Wannan dan zancen ya faru ne lokacin da ita Bodado, jarumar labarin, ke hira da wata innarta a kan saurayin da take son ta aura, wanda kum ba Bafulatani bane. A bisa akidar pulaaku ta Fulani, bai kamata mace ta yi maganar aurenta a gaban magabantanta ba. Daga wannan hirar da Bodado ta yi, ta nuna ya wurgar da munyal (kame kai), semteende (kaskantar da kai) da kuma hakkillo (dabarun rayuwa) – wadanda duk nau’o’i ne na pulaaku.

Ba a jima ba sai wata mace ta ce ita ma bari a yi da ita domin tana da nata labarin. Wanna kuwa ita ce Talatu Wada Ahmed wacce to buga Rabin Raina daga 1985 zuwa 1988. Wadannan kagaggun labaran guda uku sune suka bude kofar abin da ake kira, a wulakance, adabin kasuwar Kano. Daga nan ne fa kofar ta bude, har a ka samu marubuta suka dinga kwararowa daga 1985 har zuwa yanzu, inda a ka buga kagaggun labarai na Hausa fiye da 850. Rabin Raina ya yi tsokaci ne a kan ilmin mata da kuma muhimmancin kyale ‘ya mace ta zabi masoyinta, maimakon a tilasta mata.

Ba a jima da fitowar Rabin Raina na I a 1985 was Balaraba Ramat Yakubu ita ma ta fito da nata littafin, mai suna Budurwar Zuciya, wanda ya fadada sakonnin da ke cikin So Aljannar Duniya da kuma Rabin Raina, ta nuna illar auren dole. Amma littafin da ya fito da sakon Balaraba Ramat Yakubu karara shine Wai Zai Auri Jahila? a inda ta nuna illar auren dole da kuma muhimmancin ilmin ‘ya mace.

Sabo da haka mata ne suka bude kofar kagaggun labaran Hausa na zamani. Kuma da suka bude sai suka zo da sako mai muhimmanci wanda ya nuna cewa ciwon ‘ya mace, sai ‘ya mace, domin duk sakonnin littattafan farko da suka fito sun nuna muhimmancin bawa mata ‘yancin ra’ayinsu a kan abin da ya shafi rayuwarsu, da kuma muhimmancin ilmi ga mata, sannan kuma ga yadda mata masu ilmin suka fi mata marassa ilmi. Ko da maza suka shigo fagen rubutun kagaggun labarai, sun tallafawa mata ne ta wajen nuna muhimmancin kyautatawa mata da kuma basu hakkinsu. Wadannan sun hada da Ibrahim Saleh Gumel (Wasiyar Baba Kere, 1983), Idris S. Imam (Inda Rai Da Rabo, 1984), Ibrahim H Abdullahi Bichi (Soyayya Gamon Jini, 1986) Ahmed Mahmood Zaharadden Yakasai (Kogin Soyayya, 1988).

Mata a Fagen Rubuce-Rubucen Addini
Kada a dauka wai samun nasarar mata ya tsaye ne a kan rubuce-rubucen zamani. Ko kadan. Tun ma kafin wannan lokacin Allah Ya albarkaci jihohin arewacin Najeria da mata marubuta, kuma malamai, mukaddamai, sufaye wadanda suka yi amfani da ilmin da Allah Ya basu domin ilmintar da jama’a ta wa’azi da kuma rubuce-rubuce. Wannan ya dada jadda nasarar kabilar Hausawa fiye da kowacce kabila a Najeriya wajen ilmi da rubutu.

Misali, mace mukaddama ta farko a Kano ita ce Hajiya Iya, wacce ta samu mukaddamancin dalilin ziyarar wata Shaihiya daga kasar Marokko.

Daga 1937 zuwa 1963 sai a ka samu budewar hanyar kasuwanci sa safaranci tsakanin kasashen Hausa da kasar Sudan. Wannan ya kawo malamai da yawa domin su zo su yada addinin Musulunci, duk da dai Turawa basa so. Wadannan malaman sun zo ne da matayensu, wadanda suka bazama wajen ilmintar da matan Hausawa fannoni dabam-dabam na addini. A cikin shekar 1934-1935 ne Allah Ya kawo wata mace mai suna Shayka Khadija bin Muhammad, wacce a ka fi sani da Al-Kari’a. Ta zo ne da ‘yarta Aisha. Shayka Khadija ita ce ta fara bawa mace Bahaushiya mukaddamanci, a yayin da ta bawa wata malama mai suna Hajiya Iya. An haifi Hajiya Iya ne a shekarar 1894, kuma ‘yar limamin Kano Isma’il ce na wannan lokacin. Babban wanta shine Wali Suleiman. Saboda kwazonta wajen addini da kuma iya larabci, aka dauke ta a matsayin jakadiyar hulda da baki larabawa. Ta haka ne ta hadu da Shayka Khadija har ta bata mukaddamanci. Tun ma kafin ta zo ga wannan matsayin, ta hadu da mata larabawa malamai wadanda suka zo Kano, kamar su Sayyida Salima da kuma Sayyida Maryam, wadanda don ganin fasahar da Allah Ya yi mata, suka yi kokarin ganin cewa ta je aikin Hajji a shekarar 1937.

Ta samu goyon bayan Sarakuna, takamaimai Sarki Sununi wanda ya bada gida da kuma damar ta yi tafsiri – wanda ya saka ta zama mace ta farko da yin haka. Allah Ya yi mata rasuwa a 1986. Tun kafin Hajiya Iya, akwai mata malamai, masana kamar su Hajiya Zainab (Tsohuwa) wacce ta rayu daga 1855 zuwa 1882. Sannan bayan Hajiya Iya akwai mata kamar su Umma Makaranta (watau Hajiya Saudatu), Hussaina Sufi, Malama Raliya, Hajiya Sadiya, Hajiya Maryam, Hajiya Fulani Sa’adatu, da Malama Maymuna – wadanda duk sun shahara wajen fagen ilmin addini, kuma mukaddamai ne.

Saboda haka ashe mata a fagen ilmi da rubuce-rubuce a kasar Hausa ba wani abu ne sabo ba, duk da cewa a kasar Kano kawai muka tsaya. Duhun kan wadansu iyayen ne yake hana mata da yawa daga nuna bajintarsu wajen ilmi da kuma rubuce-rubuce, ba rashin basira ba.

Marubuta Mata a wannan Zamanin
Mata kam sun taka rawar gani a wannan zamanin namu, domin wani bincike da a ka yi ya nuna mata akalla 194 sun yi rubuce-rubucen kagaggun labara daga 1980 zuwa 2004. Babu wata kabila da zata bugu kirji ta ce tana da mata masu yawan haka marubuta. Kuma duk dimbin rubutun da a ka yi, da Hausa a ka yi domin isar da sakonni iri-iri ga mutane na wajen dabam-dabam.

A yau mun taru domin mu kaddamar da littattafai guda biyu wadanda suka ci gaba da nuna bajintar matan Hausawa a fagen adabin Hausa. Domin a lokacin da wadanan mata 194 suke rubutun kagaggun labarai, akwai mata wadanda suka fi karkata ga littattafan addini da kuma nasihohi. Watau sun ci gaba da yakin ilminar da jama’a, ba wai mata kawai ba, wanda kakanin kakaninsu kamar su Hajiya Tsohuwa suka fara. Mukaddamai kamar su Hajiya Tsohuwa, Umma Makaranta da Hajiya Iya sun yi nasu rubuce-rubucen da larabci da kuma ajami domin isar da sakonninsu ga dalibansu da kuma jama’ar gari. Da yake salon karatun ya canja, yanzu jikonsu da rubutun Romananci suke wannan jihadin neman ‘yancin mata.

Na farko, Muradin Mata, wanda Anti Fatima M. Maikarfi ta wallafa ya yi kyakyawan bayani da nasiha ga mata a kan yadda ya kamata su zauna da mazajensu. Saboda haka an yi shine da damon samowa mata ma’aurata mafita don samun nutsuwa da jin dadin zaman su na aure su da mazajen su. Ta gina wannan makasudi ne a kan la’akari da yadda yawancin matsalolin mata suka karkata ga rashin jin dadin zaman aure. Ta haka ta ga ya kamata ta bayyan abin da Allah Ya nufeta da sani domin ilmintar da sauran ‘yan uwanta da fatan kawo gyaran zama don jin dadin kan su.

Littafin ya yi bayani dalla-dalla a kan manya-manyan ma’anonin zaman tare na aure. Sannan domin a yi kyakyawar shimfida, sai ta samu damar ta yi nazari a kan ire-iren mazaje, inda ta fito da salon halin mazaje guda 29, wanda kuma suka kusan cinyen littafin. A wannan jerin halayen mazajen, marubuciyar ta nuna kyakyawan da kuma cikakken ilmin sanin halin dan Adam, ta yadda ta fito da akidojin maza dabam-dabam; ta yadda duk namijin da ya karanta, tabbas zai iya tsintar inda shi kansa yake a cikin wannan bayani na ta. Ta yi shimfida ne da wadannan halayen domin ta nuna cewa sanin mutum, sanin halinsa.

Sannan sai ta waiga wajen ire-iren mata, inda ta fitar da rukunayen mata har 21. Jera wadannan rukunayen halayen maza da na matan zai iya zama wani jagora ga duk wani mai neman aure; sanin kansa, sannan kokarin sanin abokiyar zama. Kuma an gina wadannan rukunayen ta hanyar nazarin rayuwar Bahaushe da kuma gami da nazarin da bincike ya nuna a kan halayyar dan Adam. Ta rufe littafin da nasihohin tarbiyar yara, da kuma addu’o’i na kara imani da mata zau dinga yi a kowanne lokacin.

Littafi na biyu shi ne Madafa – Kicin Sirrin Mata, wanda shi ma Anti Fatima M. Maikarfi ce ta yi. Wannan ya nuna wani nau’i na basiar da Allah Ya bawa Anti Fatima wajen iya girke-girke, ta yadda ba ma wai mata kawai ba, ko mazajen ma wadanda basu da aure, zasu amfana daga wannan littafin domin zai nuna musu dabarun iya yin abinci iri-iri. A wannan littafin an yi bayani girke-girke kusan 52, wanda ya nuna irin falalar da Allah Ya yi wa kasar Hausa ta samu ire-iren wadannan abin cin, da kuma hanyoyin sarrafa su.

Mazaje da yawa basu ma san yadda ake dafa musu abincinsu ba, sai dai kawai su zauna su ci. Wannan littafin zai nuna sirrin, sannan kuma ya nuna falalar da kuma basirar da Allah Ya yi wa matan Hausawa wajen sarrafa abinci. Wannan littafin yana da amfani ga jama’a da yawa – matan aure, wadanda suke son su inganta iya girke-girkensu, ‘yan makaranta wadanda ke koyon kimiyyar girke-girke da kuma lura da iyali, da kuma gwauraye wadanda iyayensu suka yaye su.

Kammalawa
Rubuta wadannan littattafan ci gaba ne a kan yadda mata marubuta Hausawa suka dage a kan neman ‘yancin kansu. Daga abin da muka gani na tarihin shigowar mata fagen adabi, wannan ya nuna cewa ba rashin fasaha ko tunani ne ya ke hana mata rubutu ba – kusan duk inda namiji ya kai ga rubutu, to mata ma sun kai. Amma duhun jahilcin wadansu mazajen da kuma wadansu iyayen yana sa a rage ko kuma a hana damar da mata zasu samu na rubutu, domin ana ganin matsayin mace ya dogara ne a kan bautawa miji.

Anti Fatima, wacce ta dinke nasarorin da yayyenta, iyayenta da kuma kakaninta mata suka samu wajen adabi da ilmintar da mata, ta cancanci yabo saboda wannan babban yunkurin da ta yi na dada nunawa duniya cewa matan Hausawa na da ilminsu fiye da sauran takwarorinsu na kowannen fanni a wannan kasar.

No comments: