Thursday, June 7, 2007

Gudummawar Finafinan Hausa Game Da Addini Da Al’ada


Na Gabatar da Wannan Takarda a Bikin Makon Hausa na 23 Wanda Kungiyar Hausa ta Jami’ar Bayero ta Shirya a Tsakanin
5 Zuwa 8 ga Watan 1/2001.


Gabatarwa
Da sunan Allah mai girma mai daukaka wanda ya yi halitta ba tare da ya kwaikwayi wani ba, nake bude wannan takarda. Tsira da aminci su tabbata ga shugaban Manzanni mabudin alheri, Manzon Rahama, wanda Allah ya yi umarni da a kwaikwaye shi a kan abin da ya zo da shi, Sallallahu alaihi wasallama.

A ko da yaushe, ina rokon Allah ya ci gaba da karfafa zukatanmu bisa halartar tarukan da ake shiryawa don kokarin inganta ilimi da kara rayar da shi. Akwai fa’idantuwa mai tarin yawa da akan samu idan aka halarci majalisai da akan gayyaci jama’a don kara wa juna sani, musamman ta hanyar jawaban da za a gabatar masu shiryarwa izuwa ga rayuwa managarciya.

Na rubuta wannan takarda ne a cikin shekara ta 2000, a wani taro da aka so a yi a dakin taro na Arewa da ke Kaduna, wanda Vision Trust Foundation suka shirya, a ranakun 5 da 6 ga watan Fabrairu, mai taken Babban Taron kasa A Kan Finafinan Hausa A Najeriya. Amma taron bai yiwu ba saboda wasu dalilai. Da farko an bukaci in gabatar da takarda mai taken Akidar Kamfanonin Finafinan Hausa Da Mahangarsu Ga Addini Da Al’ada. Amma saboda batun yana da matukar nauyi kuma yana neman isasshen lokaci ta yadda za a kalailaice shi ciki da bai, kuma a sami tattaunawa mai sauki sai na juya wannan batu izuwa Gudummawar Finafinan Hausa Game Da Addini Da Al’ada. Bisa dukkan alamu na yi wannan canji ne don gudun kada takardar ta kasa cim ma manufa ingantacciya.

Saboda sha’awata da son ci gaban Hausa ya sa da aka nemi in gabatar da takarda a kan finafinai a wannan biki na makon Hausa na dauko wannan takardar na kade mata kura na yi mata gyaran fuska da ‘yar kwaskwarima domin gabatarwa a wannan waje. A sane nake da cewa an shirya jawabai ne akan finafinai a wannan taro don kara wa juna sani da kuma yin gyara bisa wasu kura-kurai da ake yi a harkar finafinan Hausa.

Domin haka, manufar wannan takarda ita ce bayyana gudummawoyin da finafinan Hausa suke bayarwa ta fuskar addini da al’ada tare da duba wasu hanyoyi da matakai da suka kamata a bi don dada kyautata su har su zama masu amfani ga al’ummar Hausawa.

Mece ce Gudummawa?
Muwa wata mata ce mai tabin hankali wadda take tafiya gudu-gudu sauri-sauri, idan ta zo ta tarar da mutane sai ta ba su kyautar abin da ta zo da shi amma fa tare da ita za a cenye abin, wato za ta zauna a ci abin tare da ita, idan ta ga ya kare sai ta tashi ta tafi, wannan ita ce al’adarta kuma kowane lokaci haka take yi wa mutane, daga nan shi ne idan mutum yana so ka ba shi taimako wanda yake sa ran nan gaba shi ma ya saka maka ko kuma nan gaba kai ma ka amfana daga abin, ko kuma Allah ya saka maka, sai ya ce wane me zai sa ba za ka yi min irin gudun da Muwa take ba, daga nan ne mutane suka juya kalmar ta koma gudummawa kai tsaye. A dunkule kalmar gudummawa tana nufin taimakawa da wani abu wanda kake sa ran samun sakamako a nan duniya ko kuma lahira, wata kuma gudummawar ba a samun sakamako sai dai a lahira.

Mene Ne Fim?
Fim tantagaryar kimiyya da fasaha ce, kuma rayuwar dan’adam ce ake nunawa. Fim yana dauke da tarihi da dabi’un jama’a da muhallinsu da abincinsu da kuma suturarsu. Fim yare ne da kowane mutum yake iya fahimtarsa a duniya, musamman bisa harshensa da tsarinsa na rayuwa da hanyoyin tunaninsa da suka hada da gani da ji da motsi.

Har ila yau, fim hanya ce ta sanarwa da ilmantarwa da jan hankali da nishadantarwa da fadakarwa da yada manufa da tallatawa. A dunkule kafa ce daga cikin kafafen yada labarai, sannan kuma hanya ce ta kasuwanci.

Don Me Ake Yin Fim ?
Sanarwa
Ilmantarwa
Nishadantarwa
Karkatarwa
Tallatawa/Sayarwa
Yada Manufa
Tsoratarwa

Tubalan Da Ake Gina Fim
’Yan wasa
Dandali
Kayayyakin bukata
Dabi’a

Mene ne Addinin Musulunci
Addini dai wata hanya ce ta bauta wadda ake bi don kai wa ga wani sakamako na musamman, kuma hanya ce wadda ta dade a duniya ana amfani da ita.

-Addinin Musulunci shi ne gasgatawa da mika wuya zuwa ga abin da Manzo Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya zo da shi daga wurin Allah madaukaki, sannan da aiki da shi. Shi ko abin nan da Manzon Allah, Sallahu Alaihi Wasallama ya zo da shi ya kunshi dukkan shari’o’in da aka saukar wa Annabawa da Manzanni da suka gabace shi tun daga Annabi Adamu, Alaihi Salam, har zuwa ga Annabi Isa, Alaihi Salam, aka hada su gaba day aka ba shi su. Musulunci ya tara dukkan bukatun dan’adam, na fili da na boye, koyarwarsa ta hada har da alakar mutum da mutum dan’uwansa da sauran halittu, kiransa kuwa ya game duniya kaf dinta.

Mece ce Al’ada
Al’ada ita ce jimlar hanyoyin rayuwar mutane, ta kunshi harsunansu da addininsu da abincinsu da sana’o’insu da yadda suke yin abubuwansu, da kuma yadda suke amfani da su. Al’ada ita ce rayuwar da muka gada daga kakanninmu aka tashi cikinta ba tare da wani gauraye ba. A takaice dai, al’ada ta hada da dokokin rayuwar mutane da dabi’o’insu ta yadda suka shafe su, su kansu da kuma wasu. Al’ada aba ce rayayya, akwai wasu abubuwa da za a iya kira tushe ko kuma mazubin al’ada. Kamar misali, mazaunin mutane da addininsu da kuma huldarsu da wasu al’adu.

Wasu ko sun dauka al’ada kawai abin da ya shafi bukukuwa, kamar raye-raye da kade-kade da wake-wake da sauran wasu abubuwa na gargajiya. Al’ada dai ta kunshi dukkan irin fasaharmu da kuma abubuwan da muka yi imani da su a al’ummarmu.

Samuwaru Finafinan Hausa A Kano
Tun daga shekara 1980 zuwa 1984 aka fara samun finafinan Hausa na bidiyo a kasuwar finafinai ta Kano inda wata ungiyar wasan kareti da ke Kano da ta wasan kwaikwayo ta Gyaranya da kuma ta Gwauron Dutse, ita ma a Kano suka gabatar da finafinai guda hudu, daya an yi shi da sigar fim din Cana wato ta fasalin fadace-fadace wanda aka fi sani da Kasko, amma sunansa na hakika shi ne Hukuma Maganin ‘Yan banza da’Yan daukar Amarya da Auren Dole da kuma wanda aka yi shi kamar na Indiya wato yadda suke rawa da waka, mutanen gari sun fi saninsa da suna Bakar Indiya, amma biyu daga cikin finafinan ba su fito kasuwa ba, wato Auren Dole da ‘Yan Daukar Amarya.

Alhaji Hamisu Mudi Gurgu da Sani Lamma su ne mutune na farko da suka fara daukar hoton fim din Hausa a bidiyo, lokacin ana yayin Bitamaks, domin duk wadannan finafinai guda hudu da aka yi su ne suka dauke su.

Ko da yake tun kafin samuwar wadannan finafinai na bidiyo, akwai finafinai da ake shiryawa a gidajen talbijin kamar N.T.A da C.T.V 67, Kano, sai dai su ba ana yin su don sayarwa a kasuwanni ba ne, ana nuna su ne a tashoshin talbijin, sai dai ‘yan kalilan da ake samu suna fitowa kasuwa ta wata hanya.

A da can gidajen talbijin ba sa fita waje daukar fim sai dai a dakin shirye-shirye suke yi (studio). A 1980, CTV 67 suka fara fita waje suna daukar finafinansu na talbijin, sakamakon haka ne har mutane suka fara fahimtar yadda ake daukar fim, daga nan ne Hamisu Mudi Gurgu da Sani Lamma suka fara, amma yanzu sun bata a taro ko labarinsu ba a ji, guguwar sauyi ta yi awon gaba da su. Ya kamata ‘yan fim su tuna da su tun dasu suka fara kokarin kafa sana’ar.

A shekarar 1990, kungiyar Tumbin Giwa ta shirya fim mai suna Turmin Danya, sannan a shekarar 1994 suka shirya Gimbiya Fatima. Daga nan sai Kamfanin Gidan Dabino suka shirya fim, In Da So Da kauna a shekarar 1995. Kamfanin Kwabon Masoyi ya shirya fim ‘Kwabon Masoyi’ a shekara 1995. Haka kuma akwai wata ungiya a garin Birnin Kudu wadda ta shirya wani fim mai suna Wata Rana… kungiyar Jigon Hausa ita kuma ta shirya fim, Munkar, duk a shekarar 1995. Dan’azumi Baba ya shirya fim dinsa mai suna Bakandamiyar Rikicin Duniya, a 1995-1996.

Samar da wadannan finafinan da wasunsu shi ne ginshikin da ya samar wa kamfanoni da kkungiyoyin kasar nan yin finafinan Hausa, domin yin wadannan finafinai ya jawo sha’awa da kaunar finafinan Hausa ga jama’a masu kallo. Da tafiya ta yi tafiya sai abin ya zama ruwan dare, wanda har ta kai ga a halin yanzu babu finafinan da ake kalla sosai fiye da na harshen Hausa.

Wasu Hanyoyin Gudummawar Finafinai
Tun da mun yi bayani game da fim da addini da kuma al’ada, sai kuma mu waiwayi hanyoyin da finafinan Hausa suke bayar da gudummawa ga addinin Musulunci. Kamar yadda aka bayyana a baya, idan aka dubi tsantsar kayan cikin fim, za a fahimci suna kunshe da wasu hanyoyin rayuwa da suke tafe a kan ruhin musulunci da koyarwarsa. Sannan abin tambaya a nan, fim ba hanya ce ta yin ishara ba? Akwai finafinan da suke dauke da wuraren da ake koyar da karatun Alkur’ani da littattafan addini da yin addu’o’i a duk lokacin da wata matsala ta sami mutum, sannan da yarda da kaddara, ga yin salloli da koyar da yin hakuri da yin umarni da kyawawan dabi’u da hana yin zalunci da almubazzaranci da cin hanci da son kai da dai sauran abubuwa makamantan wadannan.

Kai hatta wakoki da ake yi a cikin finafinai wadanda wasu suke ganin babu komai a cikin su in ban da sakarci da sharholiya da kuma son a kwaikwayi Indiyawa, to su ma akwai tasu gudummawar. Muna sane da cewa kafin finafinan Hausa su samu babu finafinan da suka fi na Indiyawa karbuwa a kasar Hausa, kuma idan an duba za a ga akwai wakokinsu wadanda babu komai a ciki face yabon gumakansu da kuma sauran abubuwan bautarsu, ire-iren wadannan wakoki ne mutanenmu suke yi da bakinsu, ba su san mene ne ma’anar abubuwan da suke fada ba, amma wakokin da ake yi a finafinan Hausa kowa ya san abin da ake fada, sannan ana ambaton Ubangiji da Annabinsa da kuma yabo gare su, kafin a shiga gundarin wakar ko a tsakiyarta ko kuma a karshenta. Kuma mu sani cewa a wasan kwaikwayo na Bahaushe na farko yakan tsarma ‘yan wake-wake a cikinsa. Fim a zamanance ya kunshi wakoki ne shi ma don kara jan hankalin masu kallo, duk da yake a soyayyar da ta Bahaushe wakoki a boye suke a zuciya.

Ta fuskar al’ada kuwa, finafinai sun bayar da gudummawa ta bangaren kayan sawa da abinci da gidaje da bikin aure da suna da wakokin tatsuniyoyi da na ‘yan mata da makamantansu. Sannan an cusa wa masu kallo al’adar kallon finafinai masu dauke da yarensu, akalla an kawar musu da son kallon bakin finafinai wadanda ganin su ba abin da yake haifarwa sai lalacewar tarbiyyar ‘ya’yanmu da jikokinmu.

Misali cikin ‘Saudatu’ an koyar da masu kallo mahimmancin yin hakuri da tarbiyantar da yara tun suna kanana don su dogara da kansu, ga koyar da ilmi da taimako da zaman karkara da kiwo da kuma rokon Allah a duk lokacin da mutum yake da wata bukata. Shi kuwa fim ‘Daskin Daridi’ daman an gina shi ne a kan wata tsohuwar tatsuniya ta kasar Hausa da kuma irin yanayin zaman karkara, saboda haka fim din ya kunshi yanayin rayuwar Bahaushe ne. “Gaskiya Dokin karfe” kuwa fim ne da yake tabbatar mana da gaskiya, gaskiya ce har abada, haka kuma karya karya ce ko yaushe. A cikin fim din an koyar da mu riko da gaskiya da gujewa karya. ‘Kilu Ta Jau Bau’ kuwa, mun ga yadda idan mutum yana da wata damuwa yake gaya wa Allah domin ya sauwake masa ita, sannan mun ga yadda ake zuwa gaishe da iyaye da kuma su kansu iyaye yadda suke tarbiyyantar da ‘ya’yansu ta hanyar yi musu fada.

‘Gimbiya Fatima’ ma gaba day al’adun Hausawa ne, musamman da suka shafi sarauta. A ‘Bakandimiyar Rikicin Duniya’ an nuna muhimmancin rikon amana da rikon dukiyar marayu da karshen maciya amana da dukiyar marayu da kuma masu gallaza wa marayu. ‘Zakaran Gwajin Dafi’ ya nuna mana duk wanda ya dogara ga Allah ba zai tabe ba, dubi yadda jarumin fim din ‘yan fashi suka zo masa ya nemi ya yi salla ko da za su kasha shi, karshe kuma suka kyale shi. ‘Kara Da Kiyashi’ an nuna mana yadda ake yin karatu da yin tambayoyi na addini. ‘Cinnaka’ ya kawo bin iyaye da shari’ar rabon gado, da yin kalmar shahada yayin mutuwa da kuma yin taimako. ‘Kogin Bagaja’ shi ma al’ada ce kusan gaba daynsa, kuma an samo asalin labarin ne daga tatsuniyar Hausa. ‘Hadarin soyayya’ ya bayyana yadda za a yi tarbiyya da kuma yin addu’a bisa al’amura idan sun taso.

“In Da So Da Kauna” ya nuna mahimmancin neman ilmin boko da addini da kuma yin addu’a a duk lokatan da wani abu ya sami mutum. ‘Karshen Makirci’ kuwa yana yin gargadi ne kada a shuka makirci. ‘Hassada Ga Mai Rabo’ ya zo da bayanai da fatawoyi a kan addini da kuma rikon zumunci. Kai hatta fim ‘Saliha’ da aka yi masa rubdugu a da, akwai wasu wurare da ya bayar da gudummawa ta fuskar addini da al’ada. Akwai wani wurin da ya nuna ana yin fatawoyi game da addini, ya kuma tabbatar da al’adar nan ta yarinya budurwa ta kai bente.

Karin Bayanai
Wadannan wasu ne daga cikin wakokin da aka tsattsamo daga finafinan Hausa wadanda suke yin ishara a kan riko da wasu sassa na addinin musulunci:

Kwai A Baka

1. Masu kudi na lokaci nan,
Da sarakai na zamanin nan,
Attijarai na lokacin nan,
Kus sani Allah ne da mulki.

2. Yi tunani da kanka,
Allah ne ya ba ka,
Zai iya bai wa waninka,
Tamkar ka motsa baki.

Na gode wa Allah gwani da ya ba ni Rukayya

- Bismillah ya Rabba,
Makagina Rabba,
Shi ba shi uwa ba uba,
Makagin duk duniya.

Hadarin Soyayya
- Allahu gwani mai ni,
Rokonka nake ba ni,
Bilkisu ta aure ni,
Don in cika burina

- Allahu gwanin Sarki,
Mai isa da cikar mulki,
Nai roko ban Bilki,
Ya Jallah ka amsa du’a’ina

Kowa Da Ranarsa
- Farko da Allah tabara Sarkina,
Ba ni basira na tsara wakena,
Wajen Amira da ke cikin raina.

- Tsira aminci Ilahu Sarkina,
Kara gurin Sidi Daha Manzona,
Mata da ‘ya’ya Sahabu na zayyana.

- Allahu don Muhammadu,
Al Mustapha mujahidu,
Kai rahama ya Samadu,
Gurin Amira Sahiba.

- Allah Ubangiji daya,
Alhayyu bai da kishiya,
Mumitu shi gwani daya,
Shi ne ya dauke Sahiba.

- Ka yi salati ga Annabi,
Mata da ‘ya’yansa bi-da-bi,
Hada Sahabu na Annabi,
Mijin Khadijatu Mujittaba.

Allura Da Zare
- Na yi rokon Allah zan yi waka a haka,
Nai Salati gun Mustapha Ma’aikinmu duka,
In ya ba ka a yau babu wanda zai ja da haka.

Hassada Ga Mai Rabo
- In Rabbi yai maka daukaka,
Ba mai isa ya hana maka,
Ko da maza ne ko mace.

Kyan Alkawari
- Jama’a Salamu Alaikum,
Nai Sallama a gare ku.
Ku Saurara na gaya muku,
Soyayya ba kudi ce ba.

- Soyayya babu ruwanta,
Da arziki ku fahimta,
Allah ne yake hada ta,
Raba ta ko aiki ne babba.

- Don Allah jama’a ku fahimci,
Arziki da talauci,
Allah ne makadaici,
Yake wa mutum ba wani ba.
Cinnaka
- Ya Ubangiji mai isa,
Taimaka min don ka isa,
Na wake ‘ya Nafisa,
Ni nata ne.

- Karo tsiranka Allah,
Gun Mustafa Rasulah,
Har ahalinsa jumla,
Bayinka ne.

Bahaushe yana cewa, mutum dan tara ne bai cika goma, a duk lokacin da ake yin wani sha’ani, ba za a rasa wasu hanyoyi da za a yi tsokaci a kansu don a gyara ba. Hikimar Hausawa tana cewa kowa ya gyara ya sani kowa ya bata ya sani.

Akwai wasu finafinai wadanda ya kamata a ce an sake salo ko kuma kada a sake kamanta abubuwan da suka faru a cikinsu domin yin hakan yana da babbar illa ga al’adunmu da addininmu. Dole ne a yi taka-tsantsan a wajan shirya finafinai. Alal-misali wadanda ba su san al’adunmu ba, cewa za su yi abin da suke gani a fim ya shafi al’ada da addininmu alhali kuwa an gurbata su ba a yi su daidai ba. Don haka wajibi ne ga masu shirya finafinai su san matakan da za su dauka don yin gyara a kan wannan lamari. An dai ce, gyara kayanka, ba zai zama sauke mu raba ba.

Tsokace-tsokacen da wannan takarda ta lura da su su ne kamar haka
- Taba jikin mace da rungumarta da yin rawa da ita.
- Yin bokanci da samun nasara ba tare da nuna illar yin haka ba.
- Fadawa rijiya
- Barin gida
- kona kai saboda an hana yarinya wanda take so.
- Maganganun batsa da ashare-ashare da maganganun da za su kai mutum ga yin ridda.
- Sanya kaya masu nuna tsiraici.
- Fito da munanan al’adun Hausa wadanda suka saba wa addini.
- Cusa bakin al’adu.
- Yin fim marar ma’ana, maras nuna darasi.
Da sauransu.

Har ila yau, ya kamata masu shirya finafinai su gane cewa, ba sai mun bar al’adunmu ba sannan za mu ci gaba. Idan kuwa muka ce za mu bari, to lallai akwai jan aiki da gwagwarmaya babba a gabanmu a cikin wannan gomiyar karni da muka shigo.

Nadewa
Kafin in kamala wannan takarda, za a bayar da shawarwari da kuma kira ga kungiyoyin addinin Musulunci da kamfanoni da masu hannu da shuni da cewa:

i. Bai kamata ba a bar masu shirya finafinai haka a kara zube ba, ba tare da tallafa musu ba. Tuni wasu kungiyoyin addinai da ba na Musulunci ba a kasar nan sun ware dubban miliyoyin Nairori saboda masu shirya finafinansu su tallata addininsu, to, shin me ya sa namu kungiyoyin ba sa taimaka wa masu shirya finafinai sai dai in an yi fim su fito a kafafen yada labarai su yi ta sukar su, shin ta haka za a yi gyara?

ii. Me ya sa masu hannu da shuni ba sa kulawa da lamarin masu shirya finafinai, musamman idan an je neman wani abu da ya shafi harkar fim, amma su ne a kan gaba wajen saya wa matansu da ‘ya’yansu domin su sami abin gani a gidajensu, amma a hadu da su a habaka abin ya gagara.

iii. Haka kuma me ya sa kamfanoni ba sa son bai wa masu shirya finafinai tallace-tallace, kuma su karbi hayar fim din don su nuna a gidajen talbijin, su ba su kamasho, inda yin haka daidai yake da yadda suke ware mukudan kudi su yi talla ta wata hanya. Shin a haka za mu ci gaba har mu shirya wasu manyan finafinai na manyan mutane da malamai da shugabanninmu masu adalci da suka gabata. Kuma ta haka ake son a habaka harshen Hausa?

Malamai
Lokuta da dama mutanenmu suna yin abu kamar wadanda ba su je makaranta sun karanci addini ba, wato akwai masu yin mummunan fata ko addu’a ga masu shirya finafinai da marubuta. An yi haka a Kano ba sau day ba, ba sau biyu ba, a tarukan mauludai da karatun tafsiri na watan azumi. Muna ganin wannna ba ita ce hanyar gyara mai kyau ba. Idan an ga kura-kurai, to sai a nemi wanda ya yi abin a ba shi shawara da baki ko a rubuce da lallausan harshe ba mai zafi ba. Mun ga yadda addinin Musulunci yake da ‘yan’adawa, amma a hankali, a hankali, ya bunkasa ya cika duniya, ba tare da cin zarafin kowa, ko tursasawa, ko zare idanuwa ko tada jijiyar wuya ba. Addinin Musulunci, addini ne na nasiha da wa’azi, Allah madaukaki ya yi umarni da cewa “Ka yi kira zuwa ga hanyar Ubangijinka da hikima da wa’azi mai kyau”. Allah ya yi gaskiya. Muna sane da irin cin zarafi da mutanen Da’ifa suka yi wa Annabi Sallahu alaihi wasallama, lokacin da ya je don yin kira zuwa ga addinin Musulunci wanda Sahabbansa suka ba shi shawara ya yi musu mummunar addu’a, amma sai ya ce Allah ya aiko shi ya zama rahama ga kowa. Maimakon ya yi musu mummunar addu’a sai ya yi musu kyakkyawa. Da haka muke hakuri da junanmu idan kuskure ya faru, a yi nasiha, da an sami gyara da ci gaban addini da kyawawan al’adunmu, fiye da yadda kowa yake zato.

Tun tuni gwamnati take kokarin ta hana shigo da finafinan kasashen waje, amma ba ta cim ma nasara ba, sai a ruwan sanyi, masu finafinan Hausa suka yi maganin wannan matsala, babu kuma wanda ya sa su. Sannan sun samar wa da matasa maza da mata aikin yi. Kasuwar masu harkar dab’i kuma ta bude wajen buga kwalaye da fastoci, masu kwamfutuci sun dada samun aiki, masu sayar da kaset sun dada bunkasa Masu mujallu sun samu sana’ar yi. Ita kanta gwamnati ta dada samun hanyar kudin shiga, domin duk fim din da zai fita kasuwa sai an biya kudi an duba shi a Abuja, sannan a zo Kano a biya a duba.

Ina mika godiyata zuwa ga wadanda suka shirya wannan taro saboda saka ni cikin masu gabatar da takarda har kuma na gabatar da wannan takarda mai taken ‘Gudummawar Finafinan Hausa Game Da Addini Da Al’ada’. Allah ya sa abubuwan da muka tattauna su zama masu amfani gare mu. Kuma wadanda suka dauki nauyin wannan taro, Allah ya saka masu da alheri, ya sa nan gaba su sake yin wani taron makamancin wannan don warware matsaloli da suke addabar mu. Kamar yadda muka hadu a nan, Allah ya hada mu a gidan Aljanna, idan Alkiyama ta yi, amin.

Manazarta
Gusau, S.M, 1989, Musulunci Da Bazuwarsa, Kano; Crystal Computer Services.

Gidan Dabino, A.A, 1993, Gudummawar Adabin Hausa Ga Addinin Musulunci, Takardar da aka gabatar a taron kara wa juna sani na Dalibai Musulmi na Babbar Makarantar Sakandaren Dawakin Tofa.
Aminu Inuwa, Umma, 1999, Share Fage Game Da Filin Binciken Tarbiyya Cikin Wasan Kwaikwayo, An gabatar A Taron Kara wa Juna Ilmi, A Tsakanin Malamai da Dalibai A Sashen Koyar Da Harsunan Najeriya, Jami’ar Bayero, Kano.
Muhammad Dawaki Alhassan, 1983, Tsarin Addinin Gargajiya Kan Hausawa, An gabatar Tsakanin Dalibai da Malamai na Jami’ar Bayero, Kano.
Oxford University Press, Oxford Advanced Learner’s Dictionary of Current English.

No comments: